Advertisements
Chapter 93 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   93 / 108

276K to 279K   out of 321.7K words

ba a ta6a gaisawa ba, bari in kira Hajiyar tana sama" Wata yarinya ce da
baxata wuce 19 ba ta fito daga kitchen, Matar tace "Yauwa Khaleesat ce ma Mama tayi baki" Khaleesat
tace "Toh" Sai da ta fara gaida su sannan ta wuce sama, Jiddah ta bi yarinyar da kallo, haka ma Aneesah...
Matar na kallonsu tace "Yaya da kanwa ce amma" Aneesah ta kirkiri murmushi, Ita dai Jiddah ta sunkuyar
da kanta, Aneesah tace "Haka ne" Khaleesat ta sauko mahaifiyarsu na biye da ita a baya, da fara'a ta shiga
welcoming dinsu, duk suka gaisheta ta amsa tace "Maa sha Allah naji dadin shigowarku wllh, ina me gidan
naku?" Aneesah tace "Yana waje" Tace "Au haba, ce masa ya shigo mana" Aneesah ta mike ta nufi kofa ta
fita... Hajiya Fatima tace "Khaleesat xo ga me shige da ke" Matar dake xaune parlon tace "Auu, ashe kema
kin lura Mama, wllh tun daxu nake ta kallonta dubi har dimple din" Khaleesat tayi dariya tana kallon Jiddah
tace "Ya sunanki?" Jiddah tayi murmushi a hankali tace "Jiddah" Hajiya Fatima tace "Maa sha Allah, amma
in ji dai babu wata matsala yanxu jiddah?" Jiddah ta sunkuyar da kanta, Hajiya fatima tace "Duk sanda kika
samu lkci ki shigo xan yi magana da ke kin ji?" A hankali Jiddah tace "Toh" Matar dake xaune warce ita ce
first daughter din Hajiya Fatima tace "Ashe kin sansu Mama, ni ban ma ta6a lura da su a anguwar ba"
Hajiya Fatima ta sauke ajiyar xuciya tace "Nima shekaranjiya na shiga gidansu, warce ta fita yanxu ai
kishiyarta ce"




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



_Lagos laces, jewelries, Cotonou wrappers, shoes and bag all at affordable prices, siyan daya ko sari_


Location lagos state, ana kuma aikawa duk inda mutum yake.....
*tested and trusted*

If interested contact
👇🏻
08052466875 via WhatsApp
Duk wannan xancen da Hajiya Fatima da er ta suke, Jiddah dai kanta na kasa sai dai tayi murmushi, Hajiya
fatima na kallonta tace "Ko dai baki da lafiya ne Jiddah?" Jiddah ta daga kai da sauri ta girgixa mata kai tace
"Lafiyana kalau" Hajiya fatima tace "A nan garin iyayenki suke?" Jiddah ta gyada mata kai tace "Ehh" Hajiya
Fatima tace "Allah sarki, yaushe mijin naki ke komawa aiki, naji kakarsa tace pilot ne shi ko?" Jiddah ta
sunkuyar da kanta tace "Wani lkcn yana komawa ranan litinin da safe, ko kuma yau da yamma" Hajiya
Fatima tace "To idan ya koma sai ki tambayesa ki kara leko mana kin ji" a hankali Jiddah tace "Toh" haka
kawai Hajiya Fatima taji Jiddah ta kwanta mata, gashi kana ganin alamarta kasan bata da hayaniya da ma
yanda take magana cikin sanyi, a ranta kuwa ta riga ta saka cewar uwargidan ce mai matsalar don a
tunaninta Jiddah ce amarya, ita kanta daughter din Hajiya Fatima kallon Jiddah kawai take, Jiddah kuwa ta
kagu su koma gida ta kwanta don ta ji bata jin dadin jikinta, taji kamar gabobinta ciwo xa su mata, Hajiya
Fatima tace "A kawo maki abinci Jiddah?" Jiddah ta girgixa kai da sauri tace "Aa mama na ci abinci"
Aneesah ce ta shigo parlon Abuturrab na biye da ita a baya, Hajiya Fatima ta dinga kallonta sai ta ga ita din
ma ba mummuna bace, kawai dai kana gani kasan ta girmi Jiddah sosai, kuma da gani kasan wayewarsu da
Jiddah ba daya ba, Abuturrab ya xauna saman kujera ya gaida Hajiya Fatima da first daughter dinta
Rahmah, Hajiya Fatima na murmushi tace "Ya gidan fatan komai lafiya" Yace "Alhmdlh" Tace "Toh maa sha
Allah, sai ayi ta hakuri Ali, Allah ya ba ku xaman lafiya, ya kauda fitina" Yace "Ameen" Tace "Takwaran naka
baya nan yana wajen aiki..." Abuturrab ya kalleta yace "Ohk toh, ina gaishesa idan ya dawo" Tace "Xa a
gaya masa in sha Allah" Mikewa yayi yace "Mun gode Mama, just to say hi ne dama" Tace "Haba dai har xa
ku tafi, ko ruwa baku sha ba fa" Ya d'an yi murmushi yace "Alhmdlh...." tace "Toh xauna ban gama magana
ba" komawa yayi ya xauna, Nasihan few minutes Hajiya Fatima tayi ma Aneesah da Jiddah, sai dai kuma ta
fi stressing nasihar tata a kan Aneesah, Aneesah dai ba ma direction dinta take kallo ba amma tana
sauraron duk abinda take cewa, daga karshe Hajiya Fatima ta kalli Abuturrab tace "Kai kuma reminder daya
xan maka Ali... kayi kokarin xamo me adalci tsakanin matanka in har kana son wanyewa da duniya lafiya"
Abuturrab ya sunkuyar da kansa yace "In sha Allah" Tace "That's all i have to say, Allah ya hade kanku, ya
kauda duk wata fitina a tsakaninku, idan ma kaga da wata matsalar i am always around kafin dae ayi
involving close ones" Da haka suka yi sallama da Hajiya fatima yana kara yi mata godiya, Aneesah ta mike
ta bi bayan Abuturrab, sannan Jiddah ma ta tashi tayi masu sai anjima ta nufi kofa, Hajiya Fatima ta bi ta da
kallo... Abuturrab na tsaye compound Aneesah ta fito, ya dauke idonsa daga kanta ya mayar kan kofar yana
jiran fitowar Jiddah sae ga ta ta fito, kallonta ya dinga yi ganin kamar she is finding it a bit difficult to walk,
Aneesah dai ta nufi gate abunta ta fita, yayi lowering voice dinsa bayan Jiddah ta iso inda yake yace "Are
you okay?" Bata ce masa komai ba, ya kama hannunta suka fita daga gidan. Jiddah ta xame hannunta daga
nasa bayan sun shiga parlon su ganin Aneesah a xaune, ta wuce sama tana tafiya a hankali, Aneesah ta bi
ta da kallon gefen ido, kwanciya Jiddah tayi ta rufa da bargo jin kamar xata yi xaxxabi, Abuturrab ya dau
makullin motarsa dake parlon yana kallon Aneesah da ta kunna tv yace "Xan fita siyo abinci yanxu, hospital
da kika ce kuma I think it will be better a bar shi anjima da daddare tunda gobe xan koma aiki" Ta kallesa
tace "Baxan iya jira har dare ba saboda ni kadai nasan me nake ji a jikina" Ya dinga kallonta yana juya key
din hannunsa, sai kuma yace "Nan da awa nawa ne daren xai yi idan Allah ya yarda?" Tace "Kaga Captain....
ni bance lallai sai ka kai ni asibiti ba, idan ka dawo daga siyo abincinku ka bani makullin mota kawai in kai
kaina asibiti ba wani big deal bane, ko kaji na tilasta maka ka kai ni hospital?" ya mata wani kallo ya juya ya
fice daga parlon, ta hararesa sannan ta ci gaba da kallonta, tana ji motarsa ya fita gidan, ta kalli hanyar
stairs, ta fi minti biyu tana kallon saman deep in thought taji an kara bude gate din gidan, ta juya da sauri
sai kuma ta mike ta isa window tana leka waje, kallon babbab motar da ya shigo na sababbin furnitures ta
dinga yi babu ko kiftawa, ta koma da sauri ta xauna a parlor, knocking aka yi bakin kofa ta ki tashi balle ta
bude, sun kusa minti biyar a tsaye suna kwankwasa kofar, ita dai ko motsawa bata yi ba daga inda take, ta
kalli wayarta dake ringing bayan wani minti biyar din, ganin me kiranta tayi silencing wayar ta ajiye a gefe,
ya sake kira ta ki dagawa daga karshe ta mike ta haura sama, kallon kofar dakin da Jiddah take tayi kafin ta
shige nata dakin ta kulle, har sai da Abuturrab ya dawo daga wajen da yaje siyan abinci sannan ya bude ma
masu kawo furnitures din gidan suka shiga, yana xaune parlor suka dinga fitar da fasassun kayan dakin
Jiddah suna sakawa a motar bayan sun sauke sababbin, ya mike jin mota ta shigo compound din ya fita
waje, motar Ahmad ya gani, and he couldn't help it but smile, yana tsaye har Ahmad ya sauko, Ramlah ma
ta fito daga cikin motar, Ahmad yayi er dariya bayan sun hada ido ya nufosa yace "This is serious.... kaga
wani fresh da kayi kuwa Captain?? Meye haka Jiddah ke baka?" Abuturrab ya shafa beard dinsa a hankali
yace "Abinda ya kamata ta bani" Dariya kawai Ahmad yayi, giving him a hug yace "I guess yanxu kasan kayi
aure right?" Abuturrab ya dage girarsa murya kasa kasa yace "I am telling u" dariya kawai Ahmad yake
yana gathering tsokanar da xai yi ma Abuturrab a xuciyarsa amma ba yanxu ba, Ramlah ta karaso wajen ta
gaishe da yayan nata da ladabi ya amsa mata, ta shiga parlon, Ahmad yace "Ina matan naka?" Murmushi
Abuturrab yayi ya juya ya shiga ciki Ahmad na biye da shi, stairs Abuturrab ya haura ya fara bude dakin
Jiddah ya ganta kwance tana bacci, ya karasa ya duka kusa da ita yana shafa hancinta ta bude ido a hankali,
turo baki tayi ganinsa xata juya masa baya ya dagota yace "Baccin ya isa haka, yamma yayi..." Kamar xata
masa kuka tace "My legs are aching" ya cire duvet din yana massaging kafar ta hade rai ta rike hannunsa
gabanta na faduwa tace "Bana so" ya kalleta da lumsassun idonsa yayi kasa da murya yace "Baki son me?"
Bata san lkcn da ta fashe da kuka ba cause it started just exactly like this daxu, ya saketa da sauri, a rikice
yace "Toh yi hakuri plss..." Ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, bai ta6a ta ba ya marairaice yace "Na
fa ce kiyi hakuri wife, don Allah kiyi hakuri" ta dago kanta taba goge idonta a hankali, ya langwabar da kai
yace "To taso ki gaisa da su Ahmad, they are around" ta bude ido sosai tace "Da gaske?" a hankali yace
"Yea wife..." Mikewa yayi ya dagota tsaye, kamar xata sakar masa kuka tace "Ni wllh bana jin dadi" Ya
xaunar da ita gefen gado da damuwa yace "Toh ko mu tafi asibiti yanxu?" Ita dai tayi shiru ya rungumeta
tayi lamo jikinsa yana patting bayanta, ya kai bakinsa kunnenta a hankali yace "Toh baxan kuma ba, till u
are healed...." Ta lumshe idonta tana jin yanda xuciyarsa ke bugawa a kirjinta, murya can kasa yace "I love
u with every breath of mine Wife" Ta kara shigewa jikinsa amma taki cewa komai kuma bata bude idonta
ba, shi haka kadai ma ya ishesa ko bata mayar masa i love u din ba, narkar masa da xuciya da tunani gaba
daya Jiddah take, she is the best thing that have ever happened to him, he felt complete with her, kamar
me rada yace "Mu tafi asibitin a dubaki?" Ta make masa kafada, yace "Toh kin ce baxa ki iya tashi ba, ko in
kira Ramlan ta shigo ku gaisa a nan kawai su tafi?" Da sauri ta bude ido tace "Aa xan je" Ya dago kanta ya
shiga yi mata single lip kiss... Vibration din wayarsa ne ya dawo da shi ya mike xaune da sauri sannan ya
dau wayar ya duba yaga Ahmad ne, buda ido yayi sosai sai kuma ya kalleta ganin yanda ta kulle idonta ya ja
hancinta ya mike ya fita daga dakin, Yana sauka downstairs Ahmad yace "Captain da sai kace mana mu tafi
kawai da dai shanya mu da kayi a parlor haka" Abuturrab ya kasa kallonsu yana shafa kansa yace "Ohk... I
was suppose, ohhh sorry..." Sai kuma ya juya da sauri ya koma sama, dakin Aneesah ya shiga yana kallonta
yace "Ki sauko ku gaisa da su Ramlah" ya juya ya fita ya koma downstairs yana kallonsu yace "Jiddah bacci
take, she is having headache since morning, so Aneesah will be coming down now" Yana fadin haka ya
nemi waje ya xauna, Ahmad dae kallonsa kawai yake yana murmushi ganin duk a birkice yake, masu gyara
sababbin kayan dakin Jiddah dai na ta faman gyara a sama, Aneesah taji wani abu ya tokareta a
makogwaro bayan ta fito, kallo daya tayi ma dakin Jiddah ta sauka kasa da sauri, babu yabo babu fallasa ta
gaida Ahmad sannan ta amsa gaisuwan da Ramlah tayi mata, Shi dai Abuturrab fa gaba daya hankalinsa
yayi sama, soul dinsa kawai ne a parlon amma spirit dinsa na can sama, can dai ya kalli Aneesah yace "Baki
basu ko ruwa ba" ya mike ya dau abincin da ya siyo ya ajiye masu ya dau daya xai kai ma Jiddah sama, A
stairs ya ganta tana saukowa a hankali, hakan ya sa ya ajiye ledan, har ta shigo parlon taki yarda ta hada
ido da su Ahmad ta xauna kan kujera ta gaishesu cikin sanyin muryarta tana murmushi, Ahmad dake
kallonta yace "Duk kewan Umma ne yasa kika rame haka Jiddoh" Ita dai murmushi kawai take ta d'an kalli
Ramlah tace "Yaushe ku ka xo?" Ramlah dake ta kallonta ganin yanda ta kara haske tayi kyau amma kuma
ta rame kamar yanda Ahmad ya fada, ta sakar mata murmushi tace "Yau da safe muka xo Aunty Jiddah, ya
gida?" A hankali Jiddah tace "Alhmdlh, ya jiki?" Ramlah tace "Mun gode Allah" Tun da Aneesah ta shiga
kitchen kmr xata dauko ruwa ta ki fitowa, Ahmad ya lura how uncomfortable Jiddah is a parlon kamar dai
bata jin dadi, shi kuma ogan da ya xo wajensa sai kallonta yake kamar xae cinyeta, it's just as if he is
obsessed with her... Ahmad yayi wani murmushi yana mamaki iri iri, sai kuma yace "Dama nace bari mu xo
mu duba amarya Jiddah, yanxu kuma xa mu je can gida wajen Ummi, sae kuma wani lkcn in sha Allah"
Abuturrab ya kallesa da sauri yace "So early, naga baku ci abincin ba fa...." Ahmad yace "Aa sae yanxu nayi
reason, ba a wannan lkcn ya kamata mu kawo ziyara ba, in sha Allah xa mu dawo lkcn da ya kamata, but
before then yaushe xaka barta ta koma makaranta Captain? cause satinsu biyu kenan da resumption"
Abuturrab ya shafa kansa yace "Makaranta kuma?? Wani makaranta?" Ba Ahmad ba har Jiddah kallonsa
take da mamaki, Ahmad yace "Ohh baka san ma wani makaranta ba ko, to Umma xata maka bayani da
kyau" daga haka ya mike yace "Mu xa mu koma" Abuturrab yace "Shkkn sai mun yi waya" tare suka nufi
kofa suka fita yana son gaya ma Ahmad abubuwa da yawa, bayan sun fita Ahmad bai basa daman magana
ba yayi patting shoulder dinsa yace "Kar dai kayi ma er mutane ciki da wuri, kaga she is still very young...."
Abuturrab ya d'an 6ata fuska yace "Ciki kuma? Aneesah bata dau ciki ba sai ita?" Dariya Ahmad yayi sosai
ya ma kasa ce masa komai, wato Aneesah da suke yi for long bata dau ciki ba sai wata Jiddah tunda an
gaya masa it's by that, kwafa Ahmad yayi yace "Xaka sha mamaki ka ci gaba da relying a kan haka... Sae
kaga cikawar aikin ka" Jiddah na kallon Ramlah da ta mike da kyar, cike da damuwa tace "Baki ci komai ba
kuma xa ki tafi, ko in kawo lemo sai ki tafi da shi?" Ramlah tace "Wllh mun ci abinci gidan Umma kar ki
damu, Maimoon tace yaya ya siya maki waya da mota, and i saw the car da muka shigo yanxu, a very
hearty congratulations dear, Allah ya sanya alkhairi" Da murmushi ta kare maganar, Jiddah dai ta sunkuyar
da kanta a hankali tace "Nagode" Ramlah ta bi parlon da kallo to make sure Aneesah bata nan ta mika
mata ledan hannunta murya can kasa tace "Duk na rubuta maki yanda xa ki yi amfani da ko wanne, idan
ma baki gane ba ki amshi lambata wajen yaya ki kirani" Jiddah ta amsa tana kallonta cikin sanyin murya
tace "Toh nagode, yanxu haka xaku tafi ko ruwa fa baku sha ba" Ramlah tace "Sai kace wata bakuwa, kar ki
damu wllh... Sannan maganar makarantarki ki lallaba yaya don naga kamar in don ta shi ne baxai bari ki ci
gaba ba, do all u can ya barki ki xana waec dinki kin ji?" Jiddah tace "Toh nagode" Ramlah bata bi ta kan
Aneesah da ta walakanta su ba ta nufi kofa, ta juya ta kalli Jiddah dake biye da ita, ganin kamar tafiyar na
mata wahala ta dafa ta tace "Ki koma Jiddah, we will talk on phone in sha Allah..." Daga haka ta fita parlon
Jiddah ta daga mata hannu ta bi ta da kallo, dai dai nan Aneesah ta fito kitchen tayi wucewarta sama
kamar xata yi tsuntsu Jiddah ta bi ta da kallon gefen ido.... Bayan magrib Abuturrab na dawowa mosque ya
shiga dakin Aneesah, earpiece ne jone kunnenta tana daga xaune kan duvet da ta kwana jiya, dakin nata
dai babu kyan gani kamar anyi yaki a ciki, suna hada ido da shi tayi pausing wakar da take ji amma bata cire
earpiece din ba, bai ga alamar tayi sallah ba ma shi ma kuma bai damu yace tayi ba, ya rungume hannunsa
yace "Naga u didn't make any food ko baki amshi girkin bane har yanxu?" Tace "Make food for who?" Yace
"For the entire house" tace "Ohk let me make this clear captain, ko wacce ta dinga girka abinda xata ci iya
cikinta ko ranar girkinta ne ko ba ranan girkinta ba, idan ita ce da girki sae tayi har mijinta, yau da na amshi
girki kuma ban yi maka ba ma sbda bani da lafiya!!" Ya dinga kallonta thinking if at all Aneesah xata iya
canxawa daga yanda ya santa, duk da fa ba cikin fada take masa maganar ba, yace "Ke kika ajiyeni gidan
nan ko ni na ajiyeki da xaki tsara min yanda xa ayi Aneesah?" Ta cire earpiece din kunnenta tace "Baxan
kulaka muyi tashin hankali ba Captain, amma dai naga gidaje da yawa haka suke yi, ni idan na amince na ci
abinda kishiya ta girka kana tunanin ita kishiyar xata yarda ta ci nawa? So u just have to reason it captain,
shi yasa kawai na kawo wannan shawaran amma ba hukunci na yanke maka ba" Yace "Ki shirya in the next
five minutes mu tafi asibitin" Daga haka ya juya ya fice daga dakin, ta jawo wayarta da ta ajiye ta danna ma
Chef salma kira, murya can kasa tace "Ke ya ake ciki ne wai shiru shiru har yanxu?" Chef Salmah tace "i am
almost done my dear, ya xa ayi tahowan da shi kenan?" Aneesah tace "Probably yanxu xa mu fita hospital
da shi...." Salmah tace "Tooo har da amaryar xa ku dugunzuma xuwa hospital din?" A takaice Aneesah tace
"Akan wani dalili? Shi ma baxai fara wannan haukan ba tunda ai ba girkinta bane" Dariya Salmah tayi tace
"Goben dai xai koma aikin ko?" Aneesah tace "Eh" Salmah tace "Yana tafiya xan shigo in Allah ya yarda,
akwai magananganu da yawa ke dai" Aneesah na kyabe baki tace "Wai ki ji shigowa yayi yanxu wai ina
abinci, ni kuwa nace kowa yayi nasa" Salmah tace "Kika gaya masa haka??" Aneesah tace "Eh mana"
Salmah tace "Amma wani lkcn idan kin

93 / 108