Advertisements
Chapter 6 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 108

15K to 18K   out of 321.7K words

bayan an yi mata iyaka da wajen daga daxu da yamma, da kyar tace "Wa kake nema?" Sai a snn
ya juyo ya sauke mask din fuskarsa yana kallonta, ta xaro ido tsoronta ya tsananta, haka xaxxabinta ma taji
yana neman fin na da, don sanyi sosai ya dinga shigarta, kallonta ya shiga yi daga sama har kasa, rasa abin
cewa tayi daga karshe ta jingina da bangon gidan, still looking at her yace "Baki da lafiya ne?" Ta gyada
masa kai, lkci daya hawaye ya kawo idonta, bin layin ya sake yi da kallo, can yace "Baki sha magani ba?"
Hawayen dake makale idonta ya silalo kasa ta girgixa masa kai tace "Babu maganin" yace "Ke da waye a
cikin gidan?" Tace "Ni kadai ce, Baabarmu ta fita yanxu" Shiru yyi kamar me naxari sai kuma ya kalli inda
motarsa yake yace "Akwai asibiti a nan anguwar?" Ta gyada masa kai tana nuna masa tace "A layin can
gaba" Yace "Mu je" Da mamaki take kallonsa tace "Ina?" Ya wani hade rai yace "Mu tafi can din nace" ta
marairaice cikin rawar murya tace "Baabarmu tace idan na sake fitowa ko nan bakin kofa sai ta kasheni
wllh" Shiru yyi na few seconds kafin yace "Saboda me?" Tana share hawayen da ya ki tsaya mata tace "An
sa min rana" Daga sama har kasa ya sake kallonta snn yace "Da wa?" Ta fashe da kuka tace "Da iliya" tana
fadin haka kamar an tunxurata ta dinga rera kuka, yace "Ohk, amma bai san baki da lafiya bane bai kawo
maki magani ba" Bata basa amsa ba sai kukan da take yi sosai, yace "Mu je" ganin ta ki motsawa ya daure
fuska sosai yace "Ke kinsan daga inda nake?" Ta shiga goge idonta bata ce komai ba, yace "Mu tafi nace" A
hankali ta fara goge idonta, ganin ya fara tafiya ta bi bayansa gabanta na faduwa tana waige waige har suka
kusa bakin titi ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta don duk maxaunin bakin titin nan babu wanda bai santa
ba, ya bude mata back seat, xuciyarta ya dinga bugawa da karfi ta tsaya tana kallonsa, ya sauke nose mask
dinsa yace "Kina 6ata min lkci" A hankali tace "Baabarmu xata....." Wani kallo yyi mata yace "Nace ki shiga
malama" shiga motar tayi a tsorace, ya rufe sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar, sai da
ya hau saman titi yace "Ina asibitin yake?" Layi uku dake gaba da nasu ta nuna masa ya shiga layin suna isa
yaga irin asibitin yyi parking yana kare ma wajen kallo, kafin yace "Nan din ne asibitin?" Kai kawai ta gyada
masa, ya ja tsaki ya tada motarsa yayi reverse ya bar wajen, ta dinga kallonsa gabanta na faduwa, wani
asibiti a cikin gari ya kai ta, yana parking haraban asibitin ba tare da ya juya gareta ba yace "Sauka" kalle
kallen motar ta dinga yi alamar bata ma san ta ina xata bude ba, ya sauka ya xagayo ya bude motar, sauka
tayi ya rufe motarsa, ganin yanda ta tsaya ya dake yace "Mu je" he sounds so pissed off, Ba musu ta bi
bayansa har cikin asibitin, nan take ya yankar mata kati, ba a dau lkci ba nurse din ta sanar masa xa su iya
shiga gun likita, yana daga xaune ya nuna mata office din likitan yace ta shiga ta gaya masa duk abinda ke
damunta, Jiddah ta mike gabanta na faduwa tana kallonsa a hankali tace "Ai tsoro nake ji" ya hade rai a
d'an tsawace yace "Tsoron likitan sbda xai cinye ki?" Sunkuyar da kanta tayi, yace "Juya ki shiga" a hankali
ta juya ta nufi office din likitan da ya nuna mata, kamar me tsoron kofar ta murda ta shiga, sai a sannan ya
mike ya bi bayanta xuwa cikin office din, tana xaune ta takure waje daya likitan na cewa ta kwantar da
hankalinta ta nutsu, ganin ya shigo sai taji hankalinta ya kwanta, ya ja kujera ya xauna suka gaisa da likitan,
likitan na kallonta yace "Me ke damun ki?" Cikin sanyin murya tace "Kai na ke min ciwo, ina jin xaxxabi,
kuma ina ganin jiri...." Mikewa yayi ya dawo kusa da ita yana duba idonta da wani d'an abu kamar fitila a
hannunsa, Abuturrab dai na xaune yana dubansu har likitan ya gama gwaje gwajensa snn ya koma ya
xauna yana kallon Abuturrab yace "Xa ayi mata test, though symptoms din na malaria ne, but it's good ayi
test din sannan kuma .... Is she ur sister?" Abuturrab ya d'an kalleta sannan a hankali yace "Yea" Likitan
yace "Me ke damunta haka, yar yarinya da ita na ga Bp dinta ya hau" sake kallonta Abuturrab yyi, likitan na
kallonta yace "Kina da damuwa ne 'yan mata, idan ma baxa ki gaya ma d'an uwanki ba ni ki gaya min"
Sunkuyar da kanta tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta, Abuturrab yace "Dont worry Dr i will talk to her
about that, ynxu dai idan ba damuwa kawai a hada mata drugs if there is need for injection ayi mata ba sai
an yi mata test din ba cos i guess it will take up to 40mins kafin result din ya fito mu kuma a kan hanya
muke" Likitan yace "Toh shkkn babu damuwa" daga haka ya fara rubuce rubuce yana gamawa ya mika ma
Abuturrab ya amsa snn ya mike yyi masa godiya, ganin har sannan bata mike ba yace "Mu je" Mikewa tayi
yana gaba tana biye da shi har suka fita office din, wajen bada allura Abuturrab ya ga abinda bai ta6a gani
ba, don kememe taki yarda ta dinga rusa masu kuka a asibitin tana rokansu, hakan yasa ya koma office din
likitan yasa ya rubuta magunguna kawai gaba daya ya biya bill din sannan suka fita asibitin, har sannan
shesshekan kuka take, ya bude front seat ya hade rai yana kallonta a hankali ta shiga ya kulle sannan ya
xaga ya shiga maxaunin driver, sai da suka fita asibitin yace "Kin ci abinci?" Girgixa masa kai tayi tace
"Baabarmu ta ba almajiri nawa" Ya dinga nanata sunan da ta kira a ransa, wai Baabarta, girgixa kai yyi cikin
ransa still yace ba dai baabarki ba, gidan wani cin abinci ya tsaya ya siya mata abinci sai malt guda biyu da
bottle water, yana shigowa motar ya ajiye mata, kallon ledan ta dinga yi, can ta bude ta ciro malts din ta
ajiye gefe tace "Ban iya sha ba" Yace "Sai me?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Tambayarki nake" a
hankali tace "Ban iya shan lemo ba ni" Bai kuma ce mata komai ba, sai da suka shigo titin hayi yace "Taron
me naga aka yi a layinku daxu da yamma?" Shiru tayi sai kuma ta kallesa a hankali tace "Baabarmu ce take
dukana" Da mamaki yace "Saboda me?" Ta share hawayen da ya kawo idonta tace "Dama Iyah ce tace xata
sa ni a motar tirela in gudu legas don kar a min aure da Iliya, shine sai na gaya ma wata kawata da muke
xuwa makarantar dare tare da ita da, don gobe Iyah tace xata kai ni tasha, sai kawata taje ta gaya ma
baabarta shine baabarta ta xo ta gaya ma Baabarmu, shine Baabarmu ta dinga dukana wai xata kasheni,
duk aka taru a layin...." Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Shi dai sauraronta kawai yake yi, bayan few
seconds yace "Wacece Ita warce tace xata sa ki mota ki tafi lagos?" Cikin rawar murya tace "Wata tsohuwa
ce a layinmu ana ce mata Iyah...." Ya kalleta yace "Har yanxu xa ki tafi lagos din kenan don kar a maki
auren?" Ta girgixa masa kai hawaye na sauka idonta tace "Aa baxan je ba amma xan kashe kai na" Bai ta6a
expecting jin hakan daga bakinta ba, yyi parking yana kallonta da mamaki yace "Xa ki kashe kanki?" Ta
gyada masa kai, yace "Da me xaki kashe kan naki?" Cikin rawar murya tace "Piya piya xan siya in sha" Bai
san lkcn da ya bude baki ba yana kallonta ganin she is so damn serious, da wani expression yake kallonta
ganin she is truly depressed and frustrated, tana goge hawayen dake xuba idonta tace "Dama ae Abbana
ma ya tafi ya bar ni, ba sai in bi sa ba" ya kwantar da murya yace "Amma kina xuwa islamiyya kuwa?" Ta
girgixa masa kai a hankali tace "Na daina tun da dadewa, tun sanda muka fara sana'a" Yace "Toh saboda xa
a maki aure kike son kashe kanki?" Ta gyada masa kai, sai kuma ta hade kanta da gwiwa ta fashe da
matsanancin kuka tace "Shaye shaye fa iliya ke yi, kuma har kwaya yana sha shine Babarmu take son in
auresa...." Kallonta kawai yake, can yace "To wa kika ta6a ganin ya kashe kansa sbda xa ayi masa aure da
wanda baya so?" Tana shessheka tace "Akwai wata ma ai ta kashe kanta a nan hayi" yace "Shine ke ma xaki
kashe kanki?" Ta gyada masa kai, yace "Toh duk sanda kika shirya ki min magana ni da kaina xan kawo maki
piya piyan, kin ji ni?" Ta dago tana kallonsa tace "Toh ai ni na shirya" yace "Yaushe?" Da kyar tace "Yau da
daddare nake son in sha" yace "Aa kinga ni sai yau na sani, ki bari ko xuwa jibi xan kawo maki" tana
shessheka sae kuma ta sakar masa kuka tace "Yayi min nisa" Yace "Ya sunanki?" Tana kallonsa da hawaye
idanuwanta tace "Jiddah" Ya d'an yi shiru, bayan few seconds yace "Jiddah.... shekaranki nawa??" Cikin
sanyin murya tace "Babaarmu tace sha bakwai" yace "Toh ki jira sai na kawo maki da kaina, kar ki kuskura
ki siya da kanki, kin ji me nace maki?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ki yi min alkawari xa ki jirani" Tace
"Nayi" yace "Kina komawa gida ynxu ki ci abinci ki sha maganin ki ai nurse din ta nuna maki ynda xa ki sha"
Ta gyada masa kai, tada motar yyi ya ci gaba da driving dinsa gaba daya yana kara naxarin xancenta.


07087865788
✍🏻


💖💖 *Jiddatul Khair*💖💖




_By Khaleesat Haiydar_
✍🏻




6.....

Suna kusa layinsu cikin sanyin murya tace "Toh me xan ce ma Baabarmu idan ta dawo, wllh har dukana
xata yi" Bai ce komai ba yyi parking d'an nesa da layin snn ya d'an kalleta yace "Amma ba Baabar da ta
haife ki ba ko..." Ta girgixa masa kai a hankali tace "Abbana yace ita ta rasu tun ina yar karama" ganin
hawaye idonta ya dauke kai bayan few seconds yace "Allah ya gafarta mata" Ta sunkuyar da kanta ta amsa
da Ameen, yace "Sai kice mata saurayin da xaki aura ne ya xo kika fito" Ta marairaice tace "Ai yana legas
bai dawo ba" Yace "Kwanaki da na baki kudi ki bata don kar ki sake fitowa bakin titi, kin sake fitowa?" Ta
girgixa kai tace "Aa bamu sake yin awaran ba sai shekaranjiya ta fara" bai ce komai ba ya tada motarsa
ganin ya fara tafiya ta kallesa da sauri tace "Ina kuma xaka kai ni?" Bai bata amsa ba ganin wani shago da
ake cire kudi ta Pos ya tsaya sannan ya sauka motar, without taking much time ya dawo ya shiga motar....
Dai dai layin nasu ya sake parking ya ciro kudi a aljihu yace "Gashi ki kai mata yanxu ma" Kallon kudin ta
dinga yi, sannan ta kallesa tace "Ince wa?" Yace "Kice wani ya bata" Amsan kudin tayi gabanta na faduwa,
yace "Me nace kiyi idan kin koma gida yanxu?" tace "Kace in bata wai in ji wani" Yace "Kafin wannan" Ta
d'an yi shiru sannan tace "Kace in ci abinci in sha magani" Ya d'an daure fuska yace "To sauka" yana fadin
haka ya bude mata motar ba tare da ya yarda ya ta6a ta ba, ta sauka, yace "Kulle min mota" Ba musu tayi
yanda yace sannan yayi wucewarsa without looking at her, sai a sannan bugun xuciyarta ya tsananta, ta
fara tafiya a hankali xuwa cikin layinsu, ta fi minti biyu bakin xaurensu ta kasa shiga, daga karshe ta kutsa
kai ciki, tuni hawaye ya fara sauka idonta tana jiran jin saukan duka, sai dai me... Har sannan Hansai bata
dawo ba balle Bibalo, gidan babu kowa, dakinsu ta shiga duk da akwai wutan nepa amma kamar ko da
yaushe wutan is very low, xaunawa tayi ta ajiye ledan hannunta sannan ta boye kudin cikin ghana must go
dinta, a hankali ta bude take away din abincin ta ga shinkafa da katon kaza, ta xaro ido, ita yaushe rabon da
ta ci shinkafa balle wata kaza, shinkafa sai suyi kusan sati uku ma basu ci ba daga tuwon masara sai taliya
'yar Hausa ko garin rogo, Kaza kuma dama ranan sllh ne kadai Hansai ke bata kai da kafafuwan ko kuma
wuya, yau kuma ga kaza kato a gabanta har da shinkafa, kasa cin abincin tayi tana ta kallonsa, tunawa da
tayi Hansai na iya dawowa yanxu ko Bibalo yasa ta xaro ido, a hankali ta fara cin abincin, sbda a tsorace
take ta kasa nutsuwa ta ci abincin, ta dai ci wanda xata iya ci, jin almajiri na bara ta mike da sauri ta fita da
abincin da ta kunshe a ledansa ta mika ma almajirin ta dawo ciki, ta fi minti daya tana kallon magungunan,
kafin ta fito da su tana kallo, ganinsu kadai taji xuciyarta ya fara tashi ta mayar da su da sauri ta cusa a
ghana must go, duk ciwon da xata yi bata shan ko d'an paracetamol da Abbanta ke siyo mata lkcn da yake
da rai, Hansai kuma ko kasheta ciwo xai yi bata ta6a cewa ta sha magani, muryar Bibalo ta ji tana kiran
Uwarta tun daga bakin Zaure hakan yasa ta boye goran ruwan da ta sha ta rage, snn ta kwanta ta rufe
idonta. Washegari da asuba jiddah ta kasa tashi kamar yanda ta saba, duk karfe biyar dama take tashi ta
fita ta debo ruwa a borehole ta cika jarkunan tsakar gidan da ma bokiti, ganin gari ya fara haske Hansai ta
leko dakin tace "Yau naga walakanci, Jiddah kece kwance har yanxu baki fito ba, uban wa xai debo ruwan
yau? Bibalo me ciwon kirji ko ni xan fita debo ruwan?" Bibalo dake kwance tana bacci ta gyara kwanciyarta
hade da rufe har fuskarta da xanin gadonsu, Jiddah ta dago da kyar muryata na rawa tace "Baabarmu kaina
ke min ciwo sosai, idan na tashi juwa nake gani" Hansai tace "To a rayuwar nan yanxu waye baya fama da
ciwon kai, ko digon ruwan alwala fa babu a gidan nan, ni kike son in fita in debo ko Bibalo da ba cikakkiyar
lafiya gareta ba" Jiddah dai bata ce komai ba, Hansai tace "Ai ko daurewa xa ki yi ki mike ki debo ko bokiti
uku ne, gida idan babu ruwa ai ba magana" Daga haka ta juya ta fita tana cewa "Idan ma xaki rufa ka kanki
asiri ga bishiyar gwanda da mangwara can ki tsinko ganyayyekin su ki hura icce ki dafa ki sha kiyi wanka
don sile na baxanyi amfani da shi wajen siyo maki magani ba" Da kyar jiddah ta mike tana dafa bango ta
fita, ta dau bokiti, d'an makotansu ne ya taimaka ya kawo mata ruwan har kai uku gidan, ta dawo da kyar
ko tafiyan bata iyawa ta shige daki ta kwanta ko ina na jikinta na mata ciwo... Har karfe goma na safe tana
kwance, Hansai ta shigo dakin cike da masifa sosai tace "Ke ni fa babu ruwana ki tashi kiyi ta kanki ki tsinko
abinda nace ki dafa uban waye xaki daura ma wahala bayan na ciyar da ke da nake yi" Jiddah ta mike ko ina
na jikinta na rawa sbda sanyi, tace "Xan yi" tana magana ta jawo ghana must go dinta ta fiddo kudin jiya ta
mika ma Hansai tace "Jiya wani ya kawo wai a baki" Hansai ta xaro ido tana kallon kudin ta karba tace
"wani kuma? A ina kika gansa?" Tace "Aikawa yayi in xo, ina xuwa yace in baki" Hansai ta xauna gefen gado
ta fashe da kuka tace "Amma gaskiya isuhu ya tare mana abubuwa da yawa a duniyar nan sanda yake raye,
to da ya baki sai yace me??" Jiddah ta koma ta kwanta tana fidda numfashi da kyar tace "Cewa yyi in baki
kawai" Shiru Hansai tayi tana kirga kudin har ta gama taga dubu talatin cif, ta kalli Jiddah da sauri tace "Ko
dai mutumin da ya ta6a baki kwanaki ki kawo min kada mu fito sana'a?" Jiddah ta gyada mata kai, Hansai
tace "Toh don girman Allah duk ranan da ya sake dawowa kice masa ya shigo in masa godiya" Jiddah bata
iya ta bata amsa ba, Hansai ta mike murna fal cikinta tana murmushi ta nufi kofa tana cewa "In dai haka ne
duk wani nawa amma banda Bibalo ya mutu a duniyar nan mana, daga mutuwa sai billowan alkhairi ta ko
ina? Ashe dama akwai sauran mutanen kirki a duniya ban sani ba" Jiddah ta bi ta da kallo hawaye me xafi
na sauka idonta.

Ummi na kallon Abuturrab tace "Ina kuma xaka da yamman nan kana ganin hadari?" Yace "Aa ni ba nisa
xan yi ba, nan governor road xan je" tace "Ahmad din har ya tafi ne?" Yace "Aa tare xa mu fita da shi amma
xai dawo" Tace "Toh Allah ya tsare, ka siyo min tsire while coming back" Yace "Alright, in sha Allah" Daga
haka ya fita dakin nata ya dawo main parlor, Ahmad na xaune yana jiran sa, Ganinsa ya mike ya nufi kofa,
bin bayansa Abuturrab yyi wayarsa ya fara ring, dubawa yyi yaga Aunty ke kiransa, ya daga ya kai kunne,
wara ido yyi yace "Aunty yanxu ai xan dawo..." Murmushi yyi yana kallon wayar don har ta katse, juyawa
yyi ya koma bangare Stepmum din tasa, Ahmad ya ta6e baki, a parlonta ya sameta, yace "Ba nisa fa xanyi
Aunty" ta hade rai tace "Shine ni baxa ka min sallama ba amma ai naga ka shiga gun uwarka?" Yace "Toh
kiyi hakuri" Yana fadin haka ya jefa ma stepsis dinsa dake xaune parlon wani kallo sanin ita xata gaya mata,
Aunty tace "Toh me Ummin tace maka da ta kira ka?" Yace "Nothing kawai tace in taho mata da tsire while
coming back" Tace "Toh nima ka taho min da tsiren" yyi murmushi yace "Toh" Daga haka yace "Sai na
dawo" ya fita dakin. Yana driving ya d'an kalli Ahmad dake danna wayarsa yace "A ina xaka sauka?" Ahmad
ya kallesa yace "Kai ina xa ka???" Abuturrab yace "Bakin ruwa, nan by pass" Da mamaki Ahmad yace "Me
zaka je yi a bakin ruwa Captain?" Ya gyara xama yace "Xan amshi sako gun wani frnd dina ne, he is coming
from Abuja kuma kano xai wuce, so yace min

6 / 108