Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
kai kunne fuska daure, Kafin tace komai yace "Kuna ina?" Ta turo baki tace "Aa muna nan
gidan amarya yaya..." Yace "Ke da wa da wa?" Tace "Ni, Aunty Safiyya, Aunty Ramlah, Nafisah, Aisha da
Yusra, sai Jiddah amma ita xata wuce gida ynxu, mu kuma muna son mu kwana ne" murya can kasa tace
suna son su kwanan don bata san me xai ce ba, instead sai taji yace "Wacece xata tafi?" Ta kalli Jiddah da
har ta nufi kofa ta fita, tace "Jiddah" Yace "Xata tafi ina?" Maimoon tace "Wai gida, tace ita baxata kwana
ba" yace "Gidan da babu kowa?" Maimoon tace "Nima dai haka na gani... Amma Ummi na nan ai" Yace
"Bata wayar" ta mike da sauri tace "Toh bari in kai mata ta fita yanxu" Yace "Do that quickly" cikin hanxari
Maimoon ta fita dai dai second stairs taga Jiddah a tsaye tana kallon parlor, Jiddah da bata ma san
Maimoon ta fito daki ba, ta sauke idonta daga kallon da take ma 3 seater din parlon, ta ci gaba da sauka
downstairs a hankali, Maimoon ta kwalo mata kira tace "Yaya xai maki magana" Daga haka ta karasa kusa
da ita ta mika mata wayar, amsa Jiddah tayi tana kallon screen din sannan ta kai kunne, daga daya
bangaren taji yace "Ina xa ki?" Tace "Gida" yace "Toh kar ki kuskura ki fita daga gidan nan ba tare da su
Maimoon ba" shiru tayi ta ma rasa abinda xata ce, a takaice yace "Bata wayar" Ta mika ma Maimoon
wayar, daga daya bangaren yace "Nafisah dama xan yi ma magana kai mata wayar yanxu" Maimoon tace
"Toh" daga haka ta juya ta tafi kai ma Nafisah waya a daki ranta fari tass bai ce su wuce gida ba duk da ta
sanar da shi xa su kwana, Gaba daya mood din Jiddah ya canxa, ta ci gaba da sauka a hankali ta nufi kofar
parlon ta fita, har sannan Ali na jiranta bakin gate, ta karasa kusa da motar don glass a sauke yake, cikin
sanyin murya tace "Kayi hakuri don Allah brother dinmu yace mu kwana a nan kawai" Yace "Ohh really, to
shkkn Jiddah, can i get ur digit plss?" Tace "Bana rike waya ae" ya xaro ido yana kallonta, yace "Saboda
me?" Sincerely tace "Karatu nake yanxu" kallonta yake yi da kyau, but come to think of her age kamar ynda
ya kiyasta a ransa sae ya yrda da abinda tace, ya shafa lallausan gashin kansa yace "Then how will i be
contacting u?" Tayi shiru, yace "Amma yar uwarki na da waya ita ai" Tace "Ehh ai ta girmeni" Yace "Ohh ok,
gobe da karfe nawa xa ku bar nan?" Tace "Nima dai ban sani ba" Yace "Toh xanyi sallama da safe hope it's
okay?" Ta xaro ido tace "Aa idan yayanmu na nan fa" yace "Ohk sai yayi maki fada?" Ta gyada masa kai,
shiru yayi, can yace "Okay then xan turo kanwata Khaleesat, she is just ur mate i guess, and kuna yanayi da
ita sosai, ranan farko da na ganki a balcony daga nesa sai na ga kamar ita but i know i was mistaken coz
tana boarding schl... She is available now sun yi hutu, and i want u two to be frnds..." Tayi murmushin
karfin hali tace "Toh" Yace "Let me not keep u standing in sha Allah xata shigo da safe sai ta baki waya mu
yi magana okay?" a hankali tace "Allah ya kai mu" murmushinsa me kyau yyi mata ta juya ta shiga
compound din gidan, a parlor ta ci karo da Aunty da kawayen Aneesah rike da warmer din abinci iri iri sun
fito daga kitchen, Da mamaki Aunty ta tsaya tana kallon Jiddah, can ta ajiye babban warmer din hannunta
tana kallon hanyar stairs ta nufota, Jiddah ta fara komawa baya gabanta na faduwa, Aunty na nunata da
yatsa tace "Wai ke wacce irin natattciya ce mayya? Ban koreki daga gidan nan ba kika kara dawowa don
ubanki, kin ga wani bare a nan banda ke? Duk fa babu bare a gidan nan wllh, Me kika sake dawowa yi
banda rashin xuciya don Allah, idan muna abu na family me yasa xaki dinga cusa kanki, wllh tunda nake
ban ta6a ganin me naci mara xuciya irinki ba.. ke a wa xaki biyo jama'a xuwa gidan nan idan ba kin yada
xuciyarki kare ya lashe ba, bamu hada komai dake ba fa, babu dangin iya balle na baba, yar talakawa dake
ma idan ba kaddara ba da kuma Aliyu da ya ja mana wannan masifa da fitina me xai shigo dake irin
wannan family din, ke kin ma samu waje ko waiwayon kauyanku baki yi kin shigo birni ko..." Jiddah ta
sunkuyar da kanta bata ce komai ba, duk kawayen Aneesah na tsaye parlon suna kallonsu da alamar abun
ya masu dadi, Aunty ta bude kofa ta hankadata waje a fusace tace "Fita ki bar gidan nan don uwarki, wllh
kika sake dawowa sai na kwara maki tafasasshen ruwan xafi sai dai duk abinda xai faru ya faru" Juyawa
Jiddah tayi ta fara tafiya, taji xuciyarta yayi mata rauni sosai, tun da aka fara shirin kai amarya dama tace
ita baxata ba amma Hajja tayi ta fada wai ita ma xata fara koyon mugun hali irin nasu Aisha da Maimoon,
xata fara yi ma mutane musu da taurin kai, haka ne yasa bata sake cewa komai ba aka shirya da ita aka tafi
kai Aneesah, banda wannan bata tashi da intention din bin yan kai amarya ba don karatu ma tayi niyyar yi
idan an tafi, da gefen hannunta ta share hawayen da ya gangaro fuskarta me xafi, tana fitowa kofar gida ta
nufi titi da kafa, ta fi minti goma a tsaye tana jiran adaidaita sahu kafin ta samu daga karshe, har suka isa
gida hankalinta baya jikinta, ta sauka ta basa kudi, snn ta juya xata shiga gate dai dai fitowar Aliyu daga
gate din rike da makullin motarsa, kana ganin fuskarta kasan tayi kuka duk da ba me yawa ba, daga sama
har kasa yake kallonta, yace "Tafi wajen motata ki jirani" cikin sanyin murya tace "Me xanyi a can? Don
Allah ka barni in shiga gida" Yace "Are u questioning me?" Juyawa tayi ta nufi motar walking slowly, har ta
isa gun motar ta tsaya, sai a sannan ya nufi motar ya bude back seat yana kallonta, hawaye ya kawo idonta
tana kokarin ganin bai xubo ba cikin rawan murya tace "Don Allah ni baxan shiga ba, ka barni in je inyi
sallah" Ya dinga kallonta, sai kuma ta juya masa baya ta fara kukan dake cin ta, sai a lkcn maganganun
Aunty ke mata xafi sosai a xuciyarta, taji she really wants to go back to Hansai, don ita kadai ce idan tayi
mata bata kuka kuma bata Jin xafi a ranta tunda a ko da yaushe kallon mahaifiyarta take mata, ita ta taso
ta gani a matsayin baabarta, kuma ita take ma kallon baabarta, Kallonta Abuturrab ya dinga yi cause kana
jin yanda take kukan kasan she is hurt, bin wajen yayi da kallo sannan ya kama hannunta ya shigar da ita
motar, ta hade kanta da gwiwa tana rera kuka, ya xauna gefenta ya kulle motar yana kallonta yace "Jiddah"
kin dagowa tayi, ya dago kanta yace "Me aka maki?" Girgixa masa kai kawai tayi, yace "Aunty ko?" Nan ma
ta girgixa masa kai kawai, Tsawa yayi mata yace "Baxa ki bude baki ki min magana ba" ta kuma rushe masa
da kuka, ya kamo hannunta yana kallonta, sai kuma ya ciro handkerchief a aljihunsa ya mika mata yace
"Clean of those tears..." Bata masa musu ba ta amsa amma bata goge idon ba, ya karbe a hannunta ya fara
share mata idon yace "Me Auntyn ta maki?" Taki ce masa komai, bayan few seconds yyi kasa da murya
yace "Kiyi hakuri" Kamar jiran jin hakan take ta hade kai da gwiwa ta fara sabon kuka, ya dagota ya hade rai
yace "Ba nace kiyi hakuri ba?" Cikin shessheka tace "Dama nace ma Hajja baxan je ba shine ta sa sai
naje..." Bai ce mata komai ba sai kallonta yake but he is boiling from inside, mota ce tayi parking dai dai
kofar gate aka bude motar Aunty ta sakko da wasu kawayenta suna ta labari, ya dinga kallonsu har suka
shige cikin gida, Jiddah taji hankalinta ya tashi ganin Aunty ta dawo gidan, ta marairaice tana kallonsa tace
"Don Allah ko xaka kai ni gidan Umma kilan ta koma gida..." Bai ce komai ba ya bude motar ya sauka ta bi
sa da ido ya shiga driver seat ya tada motar ya bar layin, a hanya aka yi ta kiran wayarsa, ya daga daga
karshe, calmly yace "Kun ga Ahmad ni ba yaro bane da xa a wani jera dani kafin in shiga gidana, this isn't
my first marriage, my first marriage ma babu wanda yayi min haka, i went home my self, don haka duk
sanda nayi niyyar shiga gida xan shiga, yanxu ina wani sabgar ne..." Ahmad yace "Ohh really?" Abuturrab
yace "Yes Ahmad, bana anguwan ma ni" Ahmad yace "To idan kaje gidan sai ka sallami kawayenta..."
Abuturrab yace "Sun wahala in dai sallamata suke jira... xa mu yi magana good night" daga haka ya katse
wayar, dai dai kofar gidan Umma yayi parking ya kashe motar, Jiddah da taji wani relieve ta bude motar ta
sauka tana kallonsa tace "Sai da safe" Daga haka ta shiga gate din gidan ya bi ta da kallo. Gidansa ya wuce
daga nan, Aneesah da kawayenta na daki banda complain babu abinda take, Fauziyya tace "Nima ban ta6a
ganin haka ba wai kannin ango su wani xo gidan amarya suce xa su kwana ranan da aka kawota, wllh sai
kinyi da gaske wajen tattaro hankalin mijinki gaba daya gareki ya share kowa ya daina ganin kowa sai ke,
don wnn dangin nasa baxa su bari kiji dadin rayuwar aurenku ba" Aneesah tace "Baxa su bari in ji dadin
rayuwar aurena ba??" Wani dariya tayi tace "Lokacin da shigowa gidan nan xae fara gagaransu xan kira in
sanar maku, ni fa Captain da ku ke gani nawa ne ni kadai wllh, haka plan din yake dama" Naja tace "Atoh,
dama wa xai xauna ya xuba ido, barin ma miji irin naki, wllh kar kiyi sanya Aneesah... Kowa tashi tsaye
yake" Aneesah tace "Ni nasan bani da matsala da yan mata tunda nasan wanene captain, nasan root din
matsalata a aurenmu kuma magancesa ba wani big deal bane wllh" Jin an bude kofar parlon duk suka yi
tsit, Maimoon ta shigo cikin dakin tana wani cika tana batsewa tana kallonsu Fauziyya tace "Ya Aliyu yace
idan kun gama xaman ku fito xa a maida ku can gida" Aneesah ta cire gyalen kanta da sauri tace "A maida
su gida?? Budar kan fa??" Maimoon bata ko kalleta ba ta juya ta fice, Mikewa Aneesah tayi ta fice daga
dakin bayan ta daura mayafi a kanta ta sauko downstairs, tsaye ta gansa a parlor, da mamaki tace "My
Captain kace xa a maida su Fauziyya gida? As in how?" Yace "Ehh" ta daure fuska tace "Toh wai budan kan
fa?" Calmly yace "Duk budewar nan da kika yi ma kan bai yi ba sai wani special one kike jira" Da mamaki
take kallonsa, yace "Pls Aneesah I'm tired and i need rest now... idan xa su sakko in ajiyesu tare da su
Maimoon su sakko, or i leave the house duk sanda suka tafi in dawo" Kallonsa kawai Aneesah take, sai ga
su Maimoon da Aisha da Nafisa ko warce da jakarta a hannu tana cika tana batsewa suka sakko suka ma
Aneesah sai da safe suka fita waje, juyawa yayi ya bi bayansu, ya fi minti goma xaune a mota yana jiran
fitowar kawayen Aneesah uku amma shiru shiru, su Maimoon dai na xaune bayan mota, daga karshe ya
tada motar ya maida su gida, ko sai da safen kirki Maimoon bata yi masa ba ta shige gate tare da su Aisha,
sai a sannan tace "Da nace masa xamu kwana fa daxu bai ce komai ba don har cewa yayi in kai ma Jiddah
wayar ita ma ta dawo ta kwana I don't know what made him Change his mind all of a sudden" Aisha dai sai
ta6a bake take tace "To ba gashi dai mun dawo gidan ubanmu ba" Direct hotel Abuturrab ya wuce yyi
lodging daki, sai da ya watsa ruwa sannan ya kwanta bayan ya kashe wayarsa. Har karfe biyun dare
Aneesah bata yi bacci ba, bata ta6a xaton haka nata first night din xai kasance ba, yanxu duk abubuwan da
aka ce tayi a wannan daren baxata yi ba kenan ya tashi a banxa, gashi tayi ta kiran layukansa duk a kashe,
dama rashin mutuncin Aliyu ya kai haka bata sani ba, lallai kamar yanda aka ce mata xama ba nata bane,
xaman kuwa ba nata bane, she needs to bring down Aliyu to d level she wants him to be for her,
kawayenta uku na kwance saman gadon sun yi bacci abunsu hankali kwance, mikewa xaune tayi daga
karshe ta fita parlor ta xauna tayi tagumi, duk irin burikan da ta ci ma daren nan ya tashi a banxa kenan?? a
takaice sai wajen karfe hudu bacci barawo ya sace Aneesah, Washegari da safe aka kawo abinci daga can
gidansu Abuturrab, Fauziyya ce ta bude kofar parlon ta amshi abincin a hannun su Safiyya ta kai masu can
sama, bayan sun hada shayi me kauri ga uban kwai da dankali a gabansu Fauziyya tace "Wllh ki nuna ma
Captain din nan bacin ranki, wacce amarya ce aka ta6a yi ma wnn walakancin da yayi maki, ni ko a tarihi
wllh ban ta6a jin haka ba, kar ki kuskura ki amince masa duk dadin bakinsa sai kin gwara kansa shi ma kin
rama... Wannan ai walakanci ne wllh, duk wani ango na xumudi a ranan da aka kai masa amarya amma
banda naki angon...." Aneesah dai bata cewa komai amma gaba daya ranta a dagule yake, daga karshe ta
mike ta dau wayarta ta fita, wani dakin ta shiga ta kulle ta yi dialing number Aunty, yana fara ringing Aunty
ta daga tace "Amarya bakya laifi, har kun tashi? Fatan dai komai normal?" Aneesah ta fashe da kuka, Aunty
ta xaro ido ta mike tsaye ta fita daga dakinta don akwai wasu baki, murya can kasa tace "Lafiya Aneesah
me ya faru? Da matsala ne?" Cikin kuka Aneesah ta shiga ba Aunty labarin abinda Abuturrab yayi jiya,
Aunty ta saki baki har Aneesah ta kai aya, can tace "Abinda ya maku kenan Aliyun?" Cikin kuka Aneesah
tace "Wllh kuwa Aunty, ni da babu kawayena ma da baxan ji wnn kunyan da nake ji ba ynxu, duk fa sun san
komai kar suje su yada ni a Abuja, har cewa suke ko a tarihi basu ta6a jin amaryar da aka yi ma wnn rashin
mutuncin ba" Aunty da ranta ya dau tafarfasa tace "Shikenan, share hawayenki Aneesah, xan kiraki nan da
anjima kadan, kiyi hakuri ko su Mumy kar ki sanar ma kinji!" Aneesah na shessheka tace "Toh" daga haka
Aunty ta katse wayar tana wani huci ta hau dialing number Abuturrab taji a katse, rike baki tayi tana
naxarin walakancin da xata masa, can tayi wani murmushi hade da kwafa ta koma daki xuciyarta na ci gaba
da 6ararraka.... Karfe tara da yan mintuna Jiddah ta fito daga dakinsu sanye da kayan bacci dogo har kasa
sai hula a kanta xata shiga kitchen, ita kadai ce a gidan sai Umma da Aunty Nafisah, su ma kuma basu tashi
ba, Huraira na can gidansu Ummi bata dawo ba sbda aiki, tun asuba ta tashi ta gyara gidan gaba daya tayi
wanke wanke ta share har balcony, ta tafasa ruwan Lipton da ta cika ma kayan kamshi ta juye a flask snn ta
koma daki wajen karfe takwas amma bata yi bacci ba, yanxun ma yunwan da take ji ya sa ta fito xata hada
shayi, bude kofar parlon taji anyi ta juya da sauri don tun da ta share waje ta shigo bata kulle kofar ba, da
d'an mamaki take kallonsa, ya shigo parlon ya kulle kofar, sai da taga ya karaso cikin parlon ya xauna snn ta
duka nan kasan carpet tana kallonsa tace "Ina kwana" har lkcn kayan jiya ne a jikinsa, ta mike don bata san
ko ya amsa gaisuwar ko bai amsa ba ta koma daki ta saka hijab dinta snn ta fito ta wuce kitchen, mamakin
abinda ya kawosa da sassafe ta dinga yi, ta dai hada shayi ta dau bread slice uku a kan glass plate snn ta
fito har xata wuce dakinsu ta juyo taga kallonta yake, ta d'an tsaya tace "Xa a kawo maka shayi ne? Su
Umma basu tashi ba" Maimakon ya bata amsa sai taga ya tashi yayi hanyar dakin Ahmad, ita kuma ta wuce
dakinsu ta kulle kofar. Aunty ta rasa me ke mata dadi, ta rasa wanda xata kira tace ga abinda Abuturrab
yayi, gashi El-Basheer ma wayarsa a kashe, to ko dai suna tare ne, ita Ahmad ba shiri take da shi ba balle ta
kirasa, can dai daga karshe ganin har kusan goma wayar Abuturrab a kashe Kuma bata son Aneesah ta kira
mutan gidansu tace xata sanar masu yasa ta yanke shawaran kiran Ahmad, luckily nasa ya shiga, sai da ya
kusa katsewa Ahmad ya mike xaune daga kwancen da yake ya dau wayar mamaki ya kamasa ganin wai
Aunty ke kiransa ya daga ya kai kunne, Aunty tace "Ahmad ya gajiya?" Yace "Ina kwana?" Tace "Lafiya lau,
Aliyu fa?" Ahmad yace "Aliyu kuma? Ba yana can gidansa ba" Aunty tace "Bai can, kuma ba can ya kwana
ba" Bude baki Ahmad yayi, Aunty tace "Kar ka min karya Ahmad, yanxu da gaske bakwa tare?" Ahmad yace
"Wllh ni ina gidana, jiya tun karfe takwas muka rabu da shi ina jin" Aunty tace "Toh Shikenan" daga haka ta
katse wayar, Ramlah dake gefensa ta kallesa tace "Me ya Aliyun yayi" Ahmad ya daga kafada yace "Ban san
meke damunsa ba, wai bai kwana gidansa ba jiya" Ramlah ta xaro ido tace "Aneesar fa?" Ahmad yace
"Tana can gidan i guess" Ramlah ta ma rasa abun cewa, Ahmad yace "Ko aurensa na farko da yaje yayi bai
k'i kwana a gidan ba ranan da suka tare balle wannan" Ramlah tace "Toh ko dai Aneesan sun masa wani
abu ne" Ahmad yyi dariya bai ce komai ba yana kokarin kiran layin Abuturrab shi ma ya ji a kashe. Karfe
goma Jiddah ta fito ta ajiye cup da ta sha shayi a kitchen sannan ta dau wani cup din ta hada wani shayin,
ta ajiye kan tray, kwai kwara uku ta soya da albasa shi ma ta daura a tray din, ta dau ledan