Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
tafi ta xauna gefen gado tana duba farcenta
tace "Ban gama ba" Ta gefen ido Maimoon ta kalleta ta d'an ta6e baki ta nufi kofa tana cewa "Ko da yake
ke ai sai da izini, mu din dai" Daga haka ta fice, Jiddah ta bi ta da kallo. Bayan sati daya Jiddah suka gama
exams suka yi hutu ta dawo gidan Umma yin hutu... Ranan friday ita da Maimoon da Safiyya suka shirya xa
su gaida Ummi, Da yake driver baya nan, Umma ta basu kudin adaidaita tana sake jaddada masu kar su
kwana saboda Islamiyya gobe, Maimoon tace "Haba Umma karfe biyar na yi xa mu juyo, har sun nufi kofa
Maimoon ta kalli Jiddah tace "Anya baxa ki sa Hijab ba Jiddah?" Safiyya tace "Saboda me?" Maimoon tace
"A'a ba saboda komai ba, gani nayi ya fi mutunci" Daga sama har kasa Safiyya ta kalleta tace "Shi yasa naga
kin sa Hijab din ke ai" Jiddah tayi ficewarta bata sake sauraron Maimoon ba, Safiyya tace "Duk wani harka
na iyayi kin fi kowa iyawa" Maimoon tace "Aa daga magana sai cibi ya xama Kari, ni dai ba kawai
suggestion na kawo ba" Safiyya tace "Why didn't u suggest that for ur self??" Maimoon tayi ficewarta tayi
banxa da ita. Suna isa gidan direct bangaren Ummi suka wuce, Aneesah na xaune parlon da kanwar
mamarta Safara'u da ta tare a gidanta tun bayan da Aliyu ya bar kasar, Ummi ma na parlon alamar dai su
ma xuwansu kenan, Maimoon na ganin Aneesah ta hade rai tana kallon Ummi tace "Ummi ina yini?" Ummi
tace "Lafiya lau Maimuna, daga gida ku ke haka?" Maimoon tace "Ehh wllh Ummi, Hajja na nan?" Ummi
tace "Hajja ai tana Bauchi" Maimoon tace "Ohk" daga haka ta wuce dakin Ummi, Aneesah ta bi ta da kallo,
Jiddah ma ta durkusa ta gaida Ummi, Ummi ta amsa da fara'a, wani kallo Aneesah ta dinga yi ma Jiddah
kamar ta ga kashi, Jiddah ta kasa kin gaida Safara'u ganin babba ce, Aneesah na jin ta gaida Safara'u tayi
ma Safara'un alamar kar ta amsa ta hanyar ta6a ta da sauri, ai ko Safara'u taki amsawa, Safiyya ta gaida
Ummi sannan ta gaida Aneesah da Safara'u ta mike ta wuce dakin Ummi, Ummi na kallon jiddah tace
"Tashi ki bi su ko" Mikewa jiddah tayi ta bi bayansu, Aneesah dai sai kallonta ta gefen ido take, ta rasa
dalilin da yasa da taga Jiddah sai hankalinta ya d'an tashi, Safiya ce tsaye tana kallon Maimoon tace "Me
yasa baki gaida Aunty Aneesah ba?" Maimoon da ke kwance kan gadon Ummi ta mike tace "Wacece kuma
Anty Aneesah? Me na hada da ita da xan gaisheta?" Safiyya tace "Matar Yaya Aliyun??" Maimoon tayi wani
dariya tace "Ta jira dai taga matar tasa ta ainahi... Wannan matar me yi ma mutane kallon rainin hankali da
walakanci ne xan gaishe da, ji fa ranan da muka je gidanta abinda ta mana har xaki ce in gaisheta, a da nayi
vow har in mutu baxan sake komawa gidan yaya Aliyu ba, amma dai nayi istigifari kwanan nan don can ne
ma dabar mu idan Allah ya so nan ba da dadewa ba, sai ta raina kanta wllh, don ni tattara kayana ma xanyi
in koma gidan sai dai in Umma ce ta hanani ko shi ya korani" Daga Safiyya har Jiddah dai kallonta kawai
suke, ta murguda baki ta mike ta fice daga dakin yanda xata sake bin gaban Aneesah ba tare da ta gaisheta
ba, ai ko Aneesah ta bi ta da kallo kasa kasa xuciyarta na tafarfasa har ta fita parlon. Kamar yanda suka
sanar ma Umma karfe biyar suka fara shirin komawa gida, Ummi ta basu kudin mota sannan tace "Amma
fa ku shiga ku sallami Aunty duk da bata dade da dawowa ba" Sallama suka mata suka fita, Jiddah tayi
pretend kamar xata je ta sha ruwa, Maimoon da Safiyya suka shiga part din Aunty, Tana xaune parlonta da
Aneesah da Safara'u, suna gaisheta ta mike rai bace tace "Wato ke Maimoon don baki da kunya baki gaji
kunya ba ita Aneesar xa ki gani ki ki gaisarwa ki wuce don Ubanki??" Maimoon ta tsaya tana mata kallon
tara saura amma taki cewa komai, Aunty na tafe hannu tace "Maxa fitar min daga parlor kada in rotsa maki
kai, shegiya fitsararriya kawai" Aneesah tace "Ae kawai da kin kyaleni da ita Aunty, ita karamar alhaki ma??
Wllh so nayi watarana Allah ya kawota gidana in mata koran kare, uwar me gaisuwarta xai kare ni da shi
dama?" Maimoon tayi wani dariya tace "A gidan yayan nawa xa ki yi min koran kare??" Aneesah ta mike
tana huci tace "Kya dai je ki nemi yayanki amma ba Aliyu ba, idan kuma da akwai abinda ya fi koran kare
wllh sai na aiwatar gareki in har rashin hankalinki ya ja ki xuwa gidana, don wannan gidan a yanxu ko shi
Aliyun ba shi da wani say a kansa, yau da Ramlah ko Nafisah ko Aisha ce suka ki gaisheni shine xan ji takaici
amma banda ke karere gayyar tsiya" Maimoon tayi wani shewa tace "To mu xuba dake shege ka fasa, kuma
wannan gidan da kike takama da shi sai ya gagareki xama kwanan nan ba da wani dadewa ba wllh, abota
xa ki kulla da sleepless night very soon..." Da gudu Maimoon ta fice daga parlon tana murguda baki ganin
Aunty ta yo kanta tana kunduma mata wasu axababben xagi kamar bamagujiya, ita dai Safiyya na tsaye
kamar shashasha, Safara'u kuwa sai dannan xuciyarta take tunda Aunty da Aneesah nayi ita bai kamata ta
sa baki ba, Aunty tayi mata tsawa tace "Fita kema, gantalallu gayyar tsiya kawai...." Safiyya bata ce komai
ba ta fita daga parlon, tuni Maimoon ta ja Jiddah suka fice daga gidan ranta fess ta fesa masu rashin kunya
iya rashin kunya, sai da suka nufi titi Safiyya ke cewa "Wllh baki ji Maimoon, baki jin magana, Umma ta
hanaki wannan halin kin ki, idan ma sun xageki meye na biyesu bayan kin san ba sa'anninki bane su??"
Maimoon tana tafe hannu tace "Ba ruwana da tsufansu, ai ance respect begets respect, Respect should
only be given to he who deserves ita, wato dai he who respect his or her self, basu yi respecting din kansu
ba balle inyi respecting dinsu, haka kawai a xagi ubana dake kabari a kan wata banxa jaka can kaxama da
ita kike expecting inyi shiru kamar ban san ciwon kai na ba?? To wllh ban rama yanda nake so ba ma, sai
ranan da muka fara bata sleepless night a gidanta sannan xata gane ni ba kanwar lasa bace..." Wani shewa
Maimoon tayi cike da farin ciki, Safiyya tace "Ke da wa xaki bata sleepless night din" Maimoon ta bude
hannu tace "Ohoo a xuba ido a gani, shi sa Jiddah asirinta a rufe taki shiga nima da na sani wllh kawai ce
ma Ummi xanyi to amma inyi wucewata, uwata ce ita da dole sai na gaisheta??" Safiyya tace "Ni dai ba
ruwana ki daina wnn halin da kike...." Maimoon tayi gaba ta ki sauraran Safiyya kuma, Jiddah dai tafiyarta
kawai take bata ce masu komai ba, a ranta kuwa taji dadin dubaran da tayi na shigewa kitchen da yau har
da ita xa a hada a xage ubanta dake kabari. Bayan kwana biyu Jiddah na xaune kan darduma ta idar da isha
Maimoon ta shigo rike da wayarta dake kare kunnenta, ta nufeta ta mika mata wayar tace "Kema ku gaisa,
Safiyya ma sun gaisa, har da Umma ma sun gaisa" Jiddah na kallonta ta amshi wayar, screen din ta fara
kalla ta ga "Yaya A" ta kai wayar kunne tayi shiru, Maimoon tace "Toh kiyi magana mana ai bai katse ba fa"
daga daya bangaren taji yace "Shiru kika yi?" Lokaci daya ta dau muryarsa wanda hakan ya ja mata
faduwar gaba, ta d'an hade rai a hnkli tace "Ina yini" Yace "How are you?" Tace "Lafiya" juyawa Maimoon
tayi ta lallaba ta fita dakin....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada
wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;
Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan
kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun
fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan
wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan
link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697
Kallon screen din wayar Jiddah tayi jin shirun yyi yawa, taga har sannan bai katse ba, ta d'an turo baki tace
"Ina jin ka" Yace "Ohk... Ae ban san kina ji ba" mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, ganin Maimoon a xaune
parlor ta tafi ta dungurar mata da wayarta ta juya ta koma daki... Umma ce xaune parlor tare da Maimoon,
Jiddah kuma na xaune dinning area rike da littafi a hannunta tana dubawa, Umma na kallon Maimoon tace
"Ke a ina ku ka yi magana da shi kika san bashi da lafiya?" Maimoon tace "Ba muna chatting ba Umma,
wani lokacin ma har video call muna yi" Umma ta kyabe baki tace "Toh Allah ya basa lafiya" Maimoon tace
"Ameen, Umma har fa ya je asibiti yace min" Umma tace "Ikon Allah, kila change of weather ne, barin
yanda ya dade bai fita waje ba, Allah ya basa lafiya" Maimoon tace "Dama nima nace change of weather
gashi he still have some months kafin ya dawo" Umma tace "To kuma wannan shirin gulman da ku ka tsiri
yi da shi na meye?" Dariya Maimoon tayi har da kwanciya, tace "Toh ba ya ga ya tafi inda baxae dinga
ganin mu ba Umma, gashi bashi da kowa a can, kinga yanxu da a kasar nan ne bashi da lafiya ae da duk
mun je duba sa har da abinci... To amma yanxu babu me kula da shi" Umma dai tayi dariya kawai, can tace
"Dama yaje da matar tasa ne da sauki, to bai je ba, kuma ranan da Ummi tayi masa magana cewa yyi kawai
bai da niyyar xuwa da ita ne but he is allowed to go with his wife" Maimoon ta rike ha6a tace "Toh ba
sonta yake ba Umma, don dai kawai baxai yiwu ya tafi da warce yake son bane amma ni nasan da ya tafi da
ita" Umma tace "Wacece ita warce yake son?" Maimoon ta d'an rufe baki tace "Aa wai imagining kawai
nake" Umma ta tabe baki tace "Haka yace maki baya son matar tasa? Da baya sonta ai baxai aureta ba"
Maimoon dai bata sake cewa komai ba sai murmushi take, Safiyya ta fito daga daki rike da wayar Maimoon
dake ring ta mika mata sannan ta koma dakin, mikewa Maimoon tayi bayan ta saci kallon Umma ta wuce
dakin da sauri, tsaye tayi bakin kofa dai dai nn wayar ya katse, tabe baki tayi sai gashi an sake kira ta daga
ta kai kunne tare da sallama, cikin faram faram tace "Lafiya lau wllh Engineer, amma kuma bata dawo ba
har yau fa...." ta d'an yi shiru sai kuma ta kyabe baki tace "Toh gaskiya nima ban sani ba dai, amma babu
rana kam, kasan nace maka ta bar nan sbda karatu, mu ma sai season season muke ganinta..." Da sauri
tace "Toh ae ita ma matar Ya Ahmad din ba wayar gareta ba ya fada cikin ruwa..." Ta d'an sosa kai tace
"Toh ina jin dai nan da sati biyu ne xan je can gidan sbda kaga baxa mu je mu tarar ma yaya Ahmad a
gidansa ba, amma dai idan naje din xan bata in sha Allah" Ta kara da cewa "Toh shkkn bye" katse wayar
tayi ta juya xata fita Safiyya tace "Wacece bata nan?" Maimoon ta juyo ta kalleta bata amsata ba ta fita
dakin Safiyya ta bi ta da kallo... Tunda Maimoon ta fito Jiddah ke kallonta, Umma da ta bi ta da kallo tace
"Waye ya kiraki don munafurci kika shiga daki Maimoon?" Maimoon ta sosa kai tana er dariya tace "Aa
Umma kawata ce ta kirani tace akwai gist daxu ina aiki ban samu mun yi waya ba sai yanxu ta sake kira"
Wani kallo Umma ta dinga yi mata ta wuce kitchen da sauri tana dariya... Da daddare Jiddah na kwance
amma ba bacci take ba, tana son yin baccin amma ta rasa abinda yasa ta kasa, sannan tana jin abu da ita
kanta bata san meye ba ya tsaya mata a rai yana damunta, Maimoon ce ta shigo dakin bayan ta gama
kallon da take a parlor, ajiye wayarta tayi gefen gado ta shiga bandaki, Jiddah ta bi ta da kallo, sae da taga
ta kulle kofar bandakin sannan ta mike xaune ta jawo wayar a hankali don bai shiga lock ba, call logs ta fara
shiga ta d'an yi scrolling sae kuma ta fita da sauri ta shiga application din WhatsApp, second to the last
chat din da ta ga an sa Yaya A... Ta shiga tana sake kallon kofar bandakin, dai dai nan taji an bude kofar
saboda rudewa kawai ta kashe wayar tana kan What'sapp din ta mayar da sauri ta ajiye ta kwanta ta rufe
ido, Maimoon ta fito ta dau wayarta ta bude lock din, mamaki ne ya cikata tana kallon wayar ganin chat
dinta da Abuturrab ne gaban screen din bayan ita ba kan WhatsApp take ba, ta kalli Jiddah da ta ki bude
ido, kofa kawai ta nufa ta tafi parlor ta xauna kan kujera sannan ta fara kyalkyale dariya har da kyakyatawa,
Safiyya tace "Meye haka??" Dariya kawai Maimoon take, Safiyya tayi tsaki ta mike ta wuce daki, Sae da
Maimoon tayi dariyar me isarta sannan ta tashi ta koma dakin, Jiddah dai ta rufe har kanta ko da Maimoon
ta koma dakin. Da safe Jiddah taki amincewa su hada ido da Maimoon, Maimoon dai sai harkan gabanta
take, karfe goma Umma da Safiyya suka fita xuwa kasuwa, Bayan fitarsu Maimoon ta shigo daki ta dinga
jan Jiddah da hira don sun gama aikinsu tun safe, tun Jiddah na kin tanka mata har dai ta sake, labarin
wata kawarta da tayi aure mijin ke gallaza mata Maimoon ke yi mata, Jiddah tace "uHum! To ko dai ita ma
akwai abinda take masa ne kawai fada maku ne baxa tayi ba" Maimoon ta takarkare tace "Aa wllh, babu
wani abu da take masa, d'an iska ne kawai ta aura, ke kinga soyayya kamar xa su cinye kansu kafin ayi
auren?? Wllh soyayya kamar indiyawa har suna intimidating dinmu, to yau dai ga shi sun koma enemies
din juna, abun da mamaki" Jiddah tace "Ke dai kawai kiyi shiru tunda ba a gidan nasu kike ba balle kiyi
siding dinta, ba dole sai ta fada maku gaskiya ba" Maimoon tace "Ji wani magana da kike, to ke duk
xamanki gidan yaya Aliyu kullum ne yake kula da kin ci abinci ko baki ci ba? Ba wahala ya dinga baki ba duk
kika rame kika kanjale har kika gwammace bai dauko ki daga gidanku ba" Kallonta kawai Jiddah ke yi, sai
kuma ta dauke kai tace "Aa ni bai ta6a bani wahala ko ya bar ni da yunwa ba, in ji waye yace maku haka..."
Maimoon tace "Aa fa xancen gaskiya muke yi a nan Jiddah kar ki wani rufa masa asiri, kuma kinsan a yanda
take bamu labarin mijin nan nata wllh kamar halinsu daya da Yaya Aliyu, ai ke kin xauna gidansa kinsan
wanene shi" Jiddah dake kallonta tace "Wani irin hali ne irin nasa?" Maimoon ta gyara xama tace "Kin ga
Zainab bata da wani freedom tun da ta shiga gidan nan, sannan kullum a hantare take wajensa, gashi babu
wani kulawa, ga masifa ga fada, ga yunwa, ga shi yayi ta depriving dinta of so many things, to mention but
a few..." Katse ta Jiddah tayi tace "Aa ni dai ban tuna sanda ya hantareni ba, sannan ni yana kula da ni...
freedom kuma dama xaka auri mace ne ka saketa tayi ta yawo a gari? Sannan ni dai ban ta6a xama da
yunwa a gidansa ba, and he never deprived me of anything all through my stay in his house, in dai Aliyun
da na sani kike magana a kai to ba halinsu daya da mijin kawarki ba" Maimoon ta rike ha6a tace "Ohh har
kin manta duk abinda kika yi facing lokacin kina gidansa kenan Jiddah?" Jiddah tace "Ban yi facing komai
ba, ni dai nasan ko baya nan nace ga abinda xan ci yana kawo min, ba fa wai sae yana within kaduna ba,
A'a ko daga kano ne yana kawo min, sannan xan iya kirga sau nawa nayi girki a gidan sa, kullum sai yayi
min take away din abinci ko xan ci ko baxan ci ba" Maimoon tace "Tabb da gaske haka yake da caring? Ni
wllh irin mijin da nake so kenan" Sau daya Jiddah ta kalleta ta dauke kai, Maimoon tayi tagumi tace "Toh ai
kuwa in haka ne koma meye bai cancanci ki watsar da shi ko me xai faru ba, Toh Allah dai ya kyauta, na
manta ma ban kirasa naji ya jikinsa ba" Daga haka ta jawo wayarta ta shiga kiransa, har ya katse bai dauka
ba ta ajiye wayar tayi tagumi tace "To ko dai jikin nasa ne" Jiddah bata ce komai ba, sai gashi ya kira, da
sauri Maimoon ta daga cike da damuwa tace "Hello Yaya A, ya jikin naka?" Kusan minti uku suna magana,
Jiddah dai na wajen bata ko kara kallonta ba, can Maimoon tace "Yaya A, ga Jiddah xata yi maka ya jiki"
daga haka ta kamo hannunta ta saka wayar, Jiddah dai kallon wayar kawai take, Maimoon ta mike ta dau
cup din da ta sha shayi ta fita, Jiddah ta kai wayar kunne, jin yyi shiru tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau" Tana
wasa da edge din xanin gado tace "Ya jikin?" Yace "Wa yace maki bani da lafiya" Shiru tayi, yace "Ina jin ki"
Ta d'an turo baki tace "Maimoon" yace "Amma baki min ya jikin tun jiya ba ai" Bata ce komai ba, yace "Da
sauki"