Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
ma
Jiddah wasu mugayen xagi jikinta na rawa, Hajja ta karasa kusa da su bakinta alekum ta dau plate din
awaran Aneesan dake gefen Abuturrab ta kifa mata shi a kai cikin daga murya tace "Xo ki fita Shegiya uwar
kazamai, ita Jiddar kike tambaya hadinta da Aliyu? to yanxu kuwa xa kiji hadinta da shi, Don kaza kazanki
yanda kike matarsa ta sunna ita ma matarsa ce halaq malaq babu d'an kwal uban da ya isa ya canxa hakan,
ko ke baki da labarin ya koma ya sake aure abarsa bai yi shawara da ko wani shege ba?" Sai da Aneesah ta
dafa bango jin abinda Hajja ke cewa tana kallon Hajjar, ga jikinta duk awara tun daga saman kanta har
kafarta, Ita kanta Jiddah jingina tayi da bango ta daya side din tana kallon Hajja babu ko kiftawa jin abinda
take fadi, sae kuma ta juya ta kalli Umma... Aneesah ta nufi Abuturrab da sauri hankali tashe bakinta na
rawa tace "What is she talking about Aliyu? What is she talking about i don't understand" Jin ya ki bata
amsa kuma ya ki kallonta ta nufi Aunty ta riko hijab dinta kamar mahaukaciya tace "Aunty da gaske ne
abinda matar can take fadi?? Is she for real" Hajja tace "Uwarki ce matar can ba ni ba, tsoron ki nake da
xan ki fada maki gaskiya idan kowa ya ki?? ashe kwalo kwalo ake ta maki ba a sanar maki ba dama, to
Jiddah dai matar Aliyu ce yau ni dai na fada maki kai na tsaye, kuma duk mun yi farin ciki da wannan abun
arxikin, ae kowa na son nasa ya auri me tsafta...." Kaman daga sama suka ga Aneesah tayi kan Jiddah da
tayi stiff a jikin bangon da take ita ma tana jin xancen Hajja kamar a mafarki, kafin Jiddah ta kauce tuni
Aneesah ta cafkota ta hadeta da bango ta shakota iya karfinta, Abuturrab ya sauka saman gadon da yake
yayi kansu da sauri, amma Umma ta rigasa yin kan nasu tana salati tana kokarin fixge Aneesah da ta
kanainaiye Jiddah kamar macijiya tana kai mata duka ta ko ina, Hajja ta fasa wani ihu da karfi ta fice ward
din a rude, cikin daga murya ta dinga cewa "Likitoci kuna ina ku kawo dauki, nas nas kuna ina ku kawo
dauki, marasu lafiya kuna ina ku kawo dauki, an bar mahaukaciya ta shigo mana daki bamu san daga gidan
uban wa ba, wayyoo xata kashe mana ita ku kawo dauki" Da yake da xuciya Aneesah ta rike Jiddah, duk
karfin Abuturrab ya kasa kwace Jiddah daga rikon da ta mata, hakan ya sa shi ma ya shaketa da karfi amma
inaaa taki cika Jiddah, Umma sai salati take tana kai ma Aneesah duka ita ma amma ko dar bata yi ba, sai
cewa take wllh sai na kasheta nima a kasheni, wllh sai na kasheta, Allah sai na kasheta, Aunty taki ko
motsawa daga inda take tana ta kallonsu, dai dai nan Maimoon ta shigo ward din tare da likitoci da Nurses,
wani ihu Maimoon tayi tana bin dakin da kallo ta tafi da gudu ta dau cokalin diban miya ta nufi Aneesah
wata nurse na kokarin riketa har sai da ta samu ta kwala mata da karfinta sau uku, hakan ne yasa Aneesah
ta sassauta rikon da ta ma Jiddan sbda jiri da ya fara dibanta, Abuturrab ya turata baya da karfi without
mind inda xata fadi, yayi saurin riko Jiddah da ta sulale kasa ya dauketa ya kwantar saman gado, Gaba daya
likitocin where speechless a ward din... Is this movie they where acting or something of such here??? wani
likita ne yayi kan Jiddah da sauri checking if she is fine sauran colleagues dinsa suka rufa masa baya, nurses
din kuma suka dinga jan Aneesah da ta mike tsaye bayan ta fadi tana neman komawa kan Jiddah, don
banda kundume kundumen xagi babu abinda take har dai suka fitar da ita ward din tana cewa su kyaleta ta
kasheta, Abuturrab gaba daya ya gama rikicewa ya kuma ki barin kan Jiddah duk da instruction din doctors
din, banda kuka babu abinda Jiddah take tana jin ko ina na jikinta na mata ciwo, Hajja bata tsaya iya kiran
likitoci da nurses ba har masu gadi duk taje ta kira da passers by, Ta dinga ihu bayan ta ga an fito da
Aneesah haraban asibitin tana cewa "Ku fita da ita can bakin titi kar a bar ta a nan, a fita da ita
mahaukaciya ce, babu dawanau ne a kaduna? A taimake mu a mika ta can..." sbda yanda Hajja ta dage sai
da aka fitar da Aneesah outside gate din asibitin, Hajja ta nemi gossip chair ta xauna ta rushe da kuka tana
cewa "Yanxu xa ayi saki da wajewa ai ba sakin shirme da Usman ke son ayi da farko ba" Tuni Umma ta kira
Ahmad ya taho ya fitar da su daga Asibitin, bayan ta katse wayar tana huci tace "Wllh sai ta san ta ta6a
Jiddah, she must surely regret this..." Hajja ta gaji da kuka a waje ta dawo ward din bayan ta ta66atar an
fitar da Aneesah, ta kuma rushewa da kuka tana kallon Umma tace "Ashe dama yar daba Aliyu ya aura duk
bamu sani ba muke xaune da ita? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wllh bata doki banxa ba sai na shiga duk
inda xan shiga an bi ma Jiddah hakkinta daga kaduna har Masar, xan nuna mata ni na fi ta dabanci, ni da
nayi nawa dabancin a Masar" Abuturrab dai na tsaye kan Jiddah dake xaune saman gado likitoci sun bata
pain reliever ta sha duk sun fita, ya ma kasa kallon su Umma ya kuma rasa abinda xai ce a ward din, ita dai
Jiddah lokaci lokaci take share hawayen dake xubo mata ga kanta dake mata ciwo sosai har lkcn kuma
gabanta bai daina faduwa ba, Abuturrab ya rasa ta yanda xai lallasheta saboda Umma dake ward din,
Aunty dama tun da aka fitar da Aneesah ita ma ta fice sum sum sum, Maimoon da ke ta xaga ward din tana
takaicin me yasa sai da aka aiketa hakan ya faru, wani kwafa tayi tace "Ai wllh bashi ta ci, kuma idan ban
rama ma Jiddah wannan abinda ta mata ba ace ba ni bace" Umma dake ta boiling from inside sai jiran
Ahmad dai take, yana xuwa kuma bata ko tsaya ta saurari kowa ba ta kama Jiddah suka nufi kofa Abuturrab
ya bi su da kallo har suka fita... Ahmad da ke tsaye ward din bayan fitar Umma was so speechless sai kallon
Abuturrab yake, sai kuma ya juya ya bi bayan su Umma, magunguna Umma ta sa ya siya ma Jiddah a
pharmacy har da drip da xai kara mata wai, suna komawa gidan bayan ta sa ya saka ma Jiddah drip din, ta
kuma sha magani ta kwanta ta mike a dakin tana saka hijab dinta kamar boss lady tace "Kai ni station
Ahmad" Ahmad ya dinga kallonta ganin har ta nufi kofa ya bi bayanta yayi kasa da murya yace "Umma u
need to calm down plss, wannan ai family issue ne, albarkacin Abuturrab da su Ummi kada ki kai ta police
station, it won't make sense Umma" Umma ta juya a fusace ta kunduma masa wani xagi tace "A gidan
uban wa wannan ya xama family issue?? Uban me Jiddah ta hada da ita da xai xama family issue? Wato ta
doki banxa kenan kake nufi ko me?? Toh bari kaji ko Alhaji Usman bai isa ya hanani kai karar matsiyaciyar
yarinyar nan police station ba yau, wllh sai na kulleta...." Jiddah dai sai kallon Umma take daga kwancen da
take, Ahmad yace "Noo Umma plss listen to me..." Ficewa Umma tayi daga dakin kamar xata tashi sama,
Ahmad ya bi bayanta da sauri, amma Umma bata sauraresa ko na second daya ba ta kama hanyar Police
station ita kadai, ta kuma yi warning dinsa kar ma ya bi ta. Dole Abuturrab ya tilasta likita yayi discharging
dinsa daga asibitin, ya kira Ahmad yayi driving dinsu gaba daya xuwa gida, Hajja har suka isa gida bakinta
bai yi shiru ba, ba irin la'antar Aneesah da bata yi ba, tana shiga parlor ta fara kwala ma Abba kira kamar
xata tsaga gidan, Ummi dake kitchen ta fito da sauri tace "Ai bai dawo ba Hajja..." Hajja tace "Toh ai duk
gidan uban da yaje xai dawo ya sameni yanxu yanxun nan kuwa, ba shi dai babban burinsa ayi saki ba, to
ya dawo ya sa ayi wannan da wajewa, don wllh ni dai idan Aliyu bai saki yarinyar nan ba xan iya mutuwa..."
Ummi da gabanta ya dinga faduwa don a tunaninta Jiddah Hajja ke fadi tayi shiru tana kallon Hajja, Hajja
tace "Wllh Hauwa da kyar likitoci da Nas suka kwace ta a hannunta, tana can duk ta mata jina jina an kai ta
wani asibitin..." Sai kuma ta rushe da kuka, Ummi tace "Me ke faruwa Hajja?" Hajja tace "Meye kuwa baxai
faru ba Hauwa, tsinanniyar Nanisa matar Aliyu ce ta saka Jiddah a hammata ta dinga duka kamar an aikota,
daga wai Ramlah ta sa tayi ma Aliyu awara tun da ta iya ta kawo masa asibiti, ni dai can kofar gida na fita
na samo mana agajin gaggawa aka xo aka fitar da ita daga Asibitin anyi dawanan Kaduna da ita" Abuturrab
ya wuce dakinsa kawai, Ummi ta dinga salati tace "Ina Jiddar yanxu Hajja?" Hajja tace "Ramlah ta dauketa
ta kai ta wani asibitin nace maki, baki ganta ba abun ba a cewa komai duk ta ji mata rauni ta ko ina" Sosai
hankalin Ummi ya tashi ta koma parlonta da sauri ta dau waya ta shiga kiran Umma har ya katse bata
dauka ba, Ahmad dai ya ma rasa bakin cewa komai a parlon, Hajja tace "Ina jin saki kala biyu ma xa ayi a
gidan nan yau, wato Hafsah Allah ya tsine mata albarka, tana tsaye duk aka gama wnn tashin hankalin bata
yi yunkurin yin komai ba, wannan ne kuma ya tabbatar min cewar da hadin bakinta Aneesah ta xo tayi
abinda tayi, ai ita ta fara shigowa dakin asibitin da minti biyar sai ga Aneesah, to duk xan nuna masu ni er
banxa ce, xan kuma nuna masu ni na haifi uban Aliyu sannan ya haifi Aliyun" Ummi ta fito rike da makullin
mota tace "Bari xanje can gidan Hajja" Hajja tace "Wani gida bayan nace maki a asibiti aka kwantar da su,
mu kanmu bamu san asibitin ba, yanxu mijinki xaki kira min duk gidan uban da yake ya dawo yanxu yanxun
nan" Ummi tayi shiru tana kallon Hajja, Sai kuma ta koma parlonta kawai, bin bayanta Ahmad yayi ya kulle
kofar yace "Ummi plss ki kira Umma ta tafi police station i tried stopping her but she isn't listening,
wannan family issue ne bai kamata a kai station ba" Ummi tace "Police station kuma? I called but she isn't
responding" Ahmad ya nemi waje ya xauna yace "Ki kara kira Ummi, bana son hakan ya faru wllh, su Abba
baxa su ji dadi ba" Ummi ta shiga kiran Umma har ya katse still bata dauka ba, Ummi ta xauna ita ma cike
da damuwa tace "Toh wai ya aka yi wnn abun? Babu kowa wajen ne har aka bari Aneesar ta doki Jiddah?"
Ahmad yace "Ni bana nan na bar wajen Umma ce ta kirani after the incident" Ummi tace "Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un" Bayan kusan minti ashirin Abuturrab ya fito daga dakinsa ya nufi kofa, Hajja dake ta
xaune tana jiran Abba ta bi sa da harara tace "To banda ta dalilinka a gidan uban wa Jiddah xata san
axxalumar matarka? Wllh Allah ya isar mata... Xan ga abinda ubanka xai ce a kan wnn lamarin kuma ai" Shi
dai bai ko kalleta ba ya fita.... Aunty na can bedroom dinta ta kulle da makulli kafin kowa ya kira Abba
dama ta kirasa ta giggilla masa karya tana kuka, yace ta kwantar da hankalinta gashi nan dawowa... Kiran
Safara'u ne ya sake shigowa wayarta for the 5th time, bayan na Aneesah kusan takwas da ta ki dagawa, ta
dake dai ta dauka don ta ji abinda xa su ce mata, bayan ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren cikin
tashin hankali Safara'u tace "Hafsah to ga motar yan sanda guda sun shigo gidan Aliyu sun xo tafiya da
Aneesah don ma Allah ya rufa asiri kamar mun sani muka garkame kofa.... Banda bubbuga kofa bbu abinda
suke yi yanxu haka" Aunty tace "Yan sanda kuma??" Safara'u tace "Wllh, da muka leka ta window muka ga
wnn matar Ramlah ce tayi masu jagora" Aunty tace "Ina xuwa" daga haka ta katse wayar, ta shiga kiran
Abba, yana dagawa ta sanar masa abinda Umma tayi, yyi shiru sai kuma ya katse wayar, Ummi ya shiga
kira, tana dagawa yace "Ki kira yar uwarki ta sallami yan sandan nan da ta kwaso idan ba haka ba xan dau
mummunan mataki a kan ke da ita wllh" Rasa ma abinda xata ce masa Ummi tayi.... Bai kuma jira me xata
ce din ba ya katse wayarsa, Ummi dai ta dinga kallon Ahmad. Cikin minti ashirin Abuturrab ya isa gidan
Umma... Direct dakinsu Maimoon ya nufa, yana bude kofar Jiddah dake kwance ta juya da sauri ta mike
xaune don duk a tsorace take tana ganin kamar Aneesah xata ce xata xo gidan, Ya shigo dakin yana
kallonta, mikewa Maimoon dake dakin tayi ta fice don ta ji har shi tana jin haushinsa, Jiddah ta ki kallonsa
tana gyara duvet din jikinta gabanta na faduwa.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk
wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun
mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda
kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm
yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga
glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulu mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd
guess what😍munyi upgrading kayanmu gbdy domin jindadinku🥰bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku
domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida
💯 Natural/organic
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki komai da komai
Akwai soap 3k
Student package 7k
Beauty kit 11k
Bridal kit 18k
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏
Abuturrab ya xauna gefen gadon yana kallonta, still ta ki yarda ta kallesa, yayi kasa da murya yace "Look at
me Jidderh..." Dauke kanta tayi ya kamo hannunta kamar jira take ta fashe masa da kuka ta rufe ido, a
hankali ya daura kanta bisa shoulder dinsa cikin sanyin murya yana patting bayanta yace "Kiyi hakuri pls, i
caused u all this... And ni nasan matakin da xan dauka a kanta" ita dai kuka kawai take, ya dago kanta yana
kallonta a hankali ya kai hannu jikinta yace "Tell me where is hurting u now" Turasa tayi ta girgixa masa kai
har sannan ta kasa daina hawaye, Bude kofar dakin aka yi Abuturrab ya juya da sauri tare da saketa, ita ma
ta koma baya da sauri gabanta na faduwa, Umma ce ta shigo tana ganinsa a dakin ta wangale kofar tana
nuna masa hanyar waje tace "Mu je ka bude masu gidanka a tafi da matsiyaciyar yarinyar nan yanxu...." ya
mike amma ya rasa abinda xai ce mata, Cikin tsawa tace "Mu tafi nace ko baka ji na ne?" Yayi lowering
voice dinsa yace "But Umma plss ba sai anje police station ba, i will personally deal with..." Wani tsawan
Umma ta kuma yi masa tace "Ba sai anje police station ba?? Ohhh kana nufin ko bayan an kai ta police
station din kenan kai babu wani hukuncin ma da kake da niyyar yi mata tunda kai ne dalilin da yasa ta kusa
kashe yar mutane? Wait first who are u to question my order Aliyu?" Da sauri yace "Aa ba haka nake nufi
ba Umma" Umma tace "Wato tun ba a kai ko ina ba kenan a titi wannan mummunan al'amarin ya faru
babu kunya a kan idonmu, to in sha Allahu daga kai har matsiyaciyar nan bbu ajalin Jiddah a cikinku, babu
inda xa ku ganta balle ku kasheta daga kai har matarka, police station kuwa ko uban da ya haifeka bai isa ya
hanani kai ta ba balle kai..." Cikin tsawa tace "Fita mu je ka bude masu gida my frnd" kofa ya nufa ya fita
Umma ta bi bayansa, a motarta suka koma station ta sake biya aka bata en sanda suka nufi gidan
Abuturrab, a kofar gidan ta tsaya tare da en sandan tana kallonsa babu wasa tace "Go in and get her out"
Ya d'an kalli yan sanda ya kasa ce mata komai, kawai dai ya nufi gate din cikin gidan ya shiga yana tafiya a
hankali, mai gadi ya taso da sauri cike da damuwa yace "Yallabai ina fatan dai lafiya ko? Daxu ma sun xo
suka dinga buga kofar shiga cikin gidan..." Abuturrab bai tsaya ba yace "Lafiya lau" har ya isa entrance din
parlon yayi knocking, lkci daya kuma ya ciro wayarsa a aljihu ya kunna, dialing number din Aneesah yayi,
kamar wayar na hannunta yana fara ringing ta daga da sauri, fashe masa da kuka tayi kafin ta ce komai
yace "Zo ki bude min kofa" Tace "Honey yan sanda ne fa sun fi biyar suka shigo compound din nan daxu,
suna ta knocking, kai kana ina yanxu don Allah?" Yace "Ina bakin kofa" kallon Safara'u tayi sai kuma ta mike
da sauri ta sauka downstairs tana kallon kofar, tafiya tayi a hankali ta isa bakin kofar tayi kasa da murya
tace "My captain?" Yace "Bude kofar" Wani ajiyar xuciya ta sauke ta bude kofar ya shigo parlon, ta rushe
da wani sabon kukan tana kallonsa, Controlling temper dinsa kawai yake cause he felt like doing her
exactly what she did to Jiddah at the hospital, wani haushinta yake ji har cikin ransa, ya dai dake yace "Tafi
ki sako hijab din ki?" Ta dakatar da kukan da take tace "In je ina??" Yace "Inyi wucewata in bar ki ne?" Tace
"Aa..." Da sauri ta wuce sama, ba a dau lkci ba ta sakko tare da Safara'u da ita ma ta xumbula Hijab din don
xatonsu fitar da su xai yi daga gidan, yana ganinsu ya nufi kofa ya fita, Aneesah ta bi sa da sauri cike da
wani farin ciki ashe Aliyu na sonta dama haka, wato dawowa yyi ya fitar