Advertisements
Chapter 72 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   72 / 108

213K to 216K   out of 321.7K words

kashe, tun
ma da suke tare da Jiddah bata ta6a xuwa gidansa ba balle yanxu, banda haka da sai ita taje can gidan
nasa, Jiddah ce ta shigo dakin da sallama rike da Tray me dauke da cooler din abinci da spoon, Ummi tana
ta kallonta har ta ajiye tray din ta daga kai ta kalli Ummi tana d'an murmushi tace "In debar maki Ummi?"
Ummi ta girgixa kai tace "Aa sai anjima, nagode" Jiddah tace "Toh" Sannan ta mike ta nufi kofa Ummi ta bi
ta da kallo. Aneesah ce xaune daki tare da Safara'u, Safara'u ta kyabe baki tace "Ni ban ma ta6a jin haka
ba wllh, ae kamata yayi idan wani abun ne ke samunsa sai ya sanar maki a matsayin ki na matarsa, amma
ba wai yayi ta abu kamar ke 6are ce, ni na ma rasa gane alkiblan mijin nan naki kamar me tambotsai, ni da
sai ince ki fita harkansa kawai ki kama kanki tunda shi d'an iska ne, idan kuma don gidansa da na xo ne
yake ta wannan halayyan na basarwa yana ciccin magani sai in tattara inyi tafiyata ni bai isa ya walakanta ni
ba, ance masa mu fakirai ne? Ko bai je gidanmu ya gani bane?" Aneesah da ta d'an hade rai jin ta xagi Aliyu
tace "Kai Aunty Safuu, wllh ke dai da fassara kike, to ina ruwansa da xamanki? Ae shi ba haka yake ba, snn
fa shi haka halinsa yake na Basarwa suna fa da jimi da jinin sarauta Aunty, yayan Babansa fa shine sarkin
Bauchi kin sani, kuma ina jin ma kamar bashi da lafiya don yanayinsa ma ya nuna karfin hali kawai yake,
kawayena ma ba ruwansa da xuwansu gidana balle ke kanwar uwata, yanxu Ahmad xan kira, kilan stress ne
daga dawowan da yayi tafiya" Safara'u ta kara kyabe baki tace "Atoh ai da sai ince ki ba banxa ajiyarsa
kawai, kowa ma na da jinin sarautar ae, mutumi ba shi da aiki sae ji da kai da nuna shi wani ne, to ta ina?
kawai ki fita harkansa kema ki koyi d'an jan ajin nan na mata mana" Aneesah ta rike ha6a tace "Ina xan iya
haka Aunty? Uhum lallai baki san yanda nake son mijina bane, in ja masa aji fa kika ce? Aa baxan iya ba
wllh, baki ga ba duk na ma kasa cin abinci saboda wannan yanayin da yake ciki, Aa wllh duk wani abu da
xai dami mijina bana so gaskiya" Safara'u ta dau ayaba daya ta 6are tana ci tace "Tsoron da nake jiye maki
shine kada ya kyallara ido ya hango wata a tafiye tafiyansa tunda suna yawon kasashe ma, duk da dai mu
bama sakankancewa balle har a mana kishiyar, a tsaye muke ta ko ina, ba gashi ba har mijina ya mutu ni
daya ce tal sai uban tarin dukiya da 'ya ya biyu da ya bar ni da shi" Aneesah tace "Ni baxai mutun ba in
Allah ya yrda, amma dukiyarsa kam nawa ne da 'ya yan da xan haifa in sha Allah, Babu wata shegiyar mace
da ta isa ta ra6ar min miji in dai ina numfashi, don ni na gwammace ma in kasheta wllh, kuma yarana uku
sun isheni xaman duniya" Safara'u ta jefar da 6awon hannunta tace "Toh dai kiyi kokari ki gama amfani da
maganin nan, idan ma baki sani ba duk danginsa sun xura maki ido ne a ga ciki amma shiru ake ji, barin
wnn kanwar uwar nan tasa da na ga alamar bata da mutunci, dama ni duk na tsaneta tun encounter dinmu
a lkcn bikinku" Aneesah ta yi tsaki tace "Umma suke ce mata ko wa, ae ina ga baki tsaneta irin ynda ni na
tsaneta ba, ko hanyar gidanta ma ban sani ba har yau, na lura ta fiye shisshigi kan lamarin Aliyu, ko da yake
ita wnn ae karamar alhaki ce" Safara'u tace "Atoh dae, duk ta karkashin kasa xa a bi masu bakinmu
alekum" Aneesah ta marairaice tace "In sha Allahu nan ba da dadewa ba Allah xae bani ciki, kinga Mummy
ma duk ta damu inyi ciki, ko daxu ta kirani ko na gama amfani da wanda aka kawo last week nace eh, wllh
na kagu ace yau ga d'a na haifa ma Aliyu" Safara'u tace "In sha Allahu kuwa kamar anyi an gama, nan da
wata tara xaki sullubo masa d'a ko 'ya" Aneesah ta washe baki tace "Allah ya tabbatar Small mum" Da
daddare Aneesah na parlor suna kallon wani movie da small mum dinta wayarta ya fara ring, dauka tayi
ganin Abuturrab ke kiranta, ta d'an buda ido tace "Ina xuwa Aunty yana kirana, ya tashi kenan" daga haka
ta wuce sama da sauri.... Tana shiga bedroom din nasa ta samesa kwance har sannan da duvet a jikinsa, ta
karasa kusa da shi ta xauna gefensa da damuwa tace "Ka tashi Captain? I still can't reach Ahmad ni kuma
bani da number Ramlah" Tana magana ta kai hannu goshinsa, xaro ido tayi ta dauke hannun da sauri tace
"Subhanallah, Ur temperature is very high Captain, plss ka samu ka tashi mu tafi hospital, this is getting
out of hand" Sai kuma ta washe masa baki tace "U need not worry about the driving, ur wife can now
drive expertly, na koya sanda baka nan, babu inda bana shiga da mota yanxu" Ya mike xaune da kyar yace
"With whose car kika koya?" Ta fara kas kas da cingam tace "Whose car kuwa banda naka? D'an
kurkurjewa ne kawai yayi kafin hannuna ya fada, har by pass naje da mota na xagayo har Mando, baka ga
yanda na kware ba yanxu nake gudu" Shi dai kallonta kawai yake can yace "Sai kuma wa ya koya maki?"
Tace "Ehh to da farko da Aunty Safara'u muka fara naga dai ba abun arxiki shine nayi ma wani frnd dina
Auwal da muka yi makaranta tare magana, shi dai yake ta koya min muna yawo a gari har hannuna ya
fada" Kallonta yake bbu ko kiftawa, ta mike tana cewa "Bari in fito maka da kaya mu tafi asibiti gaskiya, tun
jiya kana kwance baka da lafiya ka ki yarda baka da lafiya, ai ba wai ance wani abu na damunka bane, kowa
ya san stress ne from ur long journey, journey din nan kuma har da kai aka dinga piloting jirgin, body no be
firewood ae..." komawa yayi ya kwanta don idan ya fiye magana yana jin xuciyarsa babu dadi, ganin tana
kokarin dauko masa kaya ya ajiye mata wayarsa yace "Akwai layin Ahmad ki kirasa" Ta jefa masa wani kallo
tace "Sau nawa xan ce maka na kirasa bai shiga ba" Abuturrab yyi kasa da murya yace "His other line, Dr
Ahmad" Daukar wayar tayi ta shiga contact ta duba number sannan tayi dialing, yana fara ring ta kallesa
tace "Ashe yana da wata number dama nake ta trying na cikin wayata" Shi dai bai ce mata komai ba,
Ahmad na daga wayar ta marairaice tace "Hello Dr, it's Aneesah wllh i am telling u for the pass 2 days now
Captain ba shi da lafiya sosai kuma ya ki xuwa asibiti, ko masallaci baya fita wllh balle a xo ga cin abinci...."
Shiru tayi sai kuma tayi saurin cewa "Toh shkkn, sai ka xo, na gode" Daga haka ta katse wayar tana kallon
Abuturrab tace "Kaji wai yana can gidanku ma, he is on his way coming right away" Shi dai bai ce mata
komai ba tace "Let me make a cup of tea for u sai ka daure ka sha ko kadan ne kafin ya iso" Daga haka ta
fice daga dakin....



*In kinsan kin samu full document na Jiddatul Khair, kar ki fitar min da shi i am begging in the name of
God* 🥹
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada
wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;

Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan
kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun
fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan
wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan
link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697



Tun da Ahmad ya shigo yake kallon Abuturrab dake xaune with a cup of tea a hannunsa, can ya karasa jikin
window ya tsaya ya rungume hannunsa still looking at him yace "So what's wrong with you now?"
Abuturrab ya d'an hade rai jin tambayar da yake masa, ya ajiye cup din hannunsa yace "Kawai ka rubuta
min magani xa a amso min a pharmacy" Ahmad ya d'an yi murmushi yace "Ana rubuta magani without
knowing d cause of a sickness?" Abuturrab yyi kasa da murya yace "Headache, dizziness, loss of appetite,
Nausea, and... yawan faduwan gaba" Ahmad ya kuma yin wani murmushin kamar baxai ce komai ba, sai
kuma yana kallonsa yace "And all this while Jiddah matarka ce kake fooling each and everyone of us
Aliyu...." Abuturrab ya dauke idonsa daga kallonsa as if the question came unexpected, Ahmad bai kuma
cewa komai ba, ya ciro biro a aljihunsa ya nufi gaban mirror ya dau takardan da ya gani a ajiye, ya d'an yi
rubuce rubucensa snn ya dawo ya mika ma Abuturrab yana kallonsa yace "I think this drugs will do, Allah
ya kara lafiya" Daga haka ya juya ya nufi kofa Abuturrab ya bi sa da kallo kafin ya fita cike da karfin hali yace
"Ahmad" Ahmad ya tsaya sannan ya juyo, Abuturrab ya sauke idonsa kasa yace "U are not saying anything
about the topic u brought up just now?" Ahmad ya girgixa kai yace "Nahh!! I have nothing to say, and i am
wishing u nothing but d best" Yana fadin haka ya fice daga dakin, Abuturrab ya dinga kallon kofar sae kuma
ya dafe kansa ya lumshe ido... Washegari da safe Abuturrab ya gama shiryawa with so many restless
thought in mind, he wish this is all but a dream, ji yake xuciyarsa is getting weaker day by day and he really
need to go to the hospital, Amma kuma idan ba yanayinsa ka duba da kyau ba baxa kace ba shi da lafiya
ba, sbda taurin halin da yake yi, ya kalli agogo dake nuna karfe tara snn ya kalli Aneesah dake baje saman
gado tana ta baccinta, buga gadon yyi gently amma ko motsawa bata yi ba, ya tafi daya side din ya janye
pillow din da take kwance kai a hankali, bude ido tayi sai kuma ta mike xaune da sauri tace "Haba Captain
kai komai naka baka yin sa romantically or in a romantic manner? yanxu haka ake tashin mutum
fisabilillahi?" Speaking calmly yace "Ina makullin motata?" Ta dauke kai hade da jan tsaki kasa kasa, sai
kuma tace "Saboda makullin mota xaka min irin wnn tashin walakanci?" Yace "Kinyi sallah ne da xa a maki
tashin da ya kamata? Kullum sai karfe goma bbu tsoron Allah xaki shiga bathroom kiyi alwala ki fito ki
shimfida darduma kice xa ki yi sallah, who does that Aneesah?? Not even a 10 year old child" a fusace tace
"Toh a je a banyi sallahn ba sae me? Ae ba kai ake ma sallan ba naga, balle ma ni nasan nayi sallata, kuma
wllh ba laifinka bane nice na fita tsakar dare naje pharmacy na samo maka magani ka sha har ka samu karfi
da bakin yi min walakancin da baka min ba tunda ka dawo kasar, for the pass 2 days da baka da lafiya waye
ya ji kanmu, sae yau don ka samu kanka?" A hankali yace "Bani makullin motata malama" Tace "Ai kana
ganinsa gaban madubi" Tafiya yyi gun mirror din ya dauka ya fice daga dakin feeling so irritated at her.
Ramlah ce ta bude kofar parlon ganinsa ta koma gefe da murmushi fuskarta tace "Sannu da xuwa Yaya"
Yace "Yauwa" tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya... Ahmad?" Tace "Ehh yana ciki ka shigo yaya" shiga parlon
yayi ya xauna, ta wuce daki, Abuturrab na xaune ya jinginar da kansa da kujera bayan minti biyar Ahmad ya
shigo parlon, ya xauna kujeran dake facing din nasa yace "Good morning" Abuturrab ya d'an yi shiru, sae
kuma yace "Ina ce idan kowa xai yi misperceiving dina kai baxa kayi ba, no not you Ahmad... and i was
hoping u will understand me better then anyone, but do u mean i am mistaken?" Ahmad yace "U never
wanted me to understand u, kana tunanin ni xan ki abinda kake so ne Captain?" Sai kuma yyi murmushi ya
girgixa kai yace "Ka bani mamaki sosai, har gida na bi ka na sameka kan maganan Jiddah not long ago, kilan
a lkcn ma ka koma kaje ka aureta ban sani ba, amma u almost blasted me telling me u have nothing to do
with her, and u are leaving happily with ur wife, kana ganin ni xan maka bakin ciki idan ka kasance tare da
Jiddah a matsayin mai dakin ka? Kana ganin i will also be against that bayan nasan komai tun daga farko
har karshe? Da kuwa baka min adalci ba, coz i tried my very best tun farkon aurenka da Jiddah ka xauna da
ita as ur wife, though i know u never bargained for that... amma nace ka dauka kaddarar ka ce a haka, kayi
hakuri ku xauna, Aliyu sbda haka ka maida ni makiyinka, daga karshe kuma ka munafurce ni, Yes ka
munafurceni, and you made me feel as if i am not trustworthy of, ban yi tunanin idan xaka boye ma kowa
nima xaka boye min ba..." Abuturrab ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, looking so confuse yace "U
misperceived me instead Ahmad, i never knew xan iya gathering courage lkci daya in fadi abinda ke raina
kwana kusa, ban san xan iya ba, and abinda yasa bana involving dinka I don't want to look foolish after
everything, ban san ta ina xan fara ba bayan abubuwa da yawa da suka faru, plss I don't want to go deep
into this coz i am not okay Ahmad, but i am here to just say to u that.... i am sorry about everything, nasan
a ko da yaushe kana sona da alkhairi fiye da kowa, kuma da na dau shawaranka tun farko abubuwan dake
faruwa yanxu baxa su faru ba, i will accept all this in good faith in sha Allah" Ahmad dai bai ce komai ba
yana sake mamakin Abuturrab, his pretence is just something else, ba a ta6a predicting dinsa, can yace
"Allah ya tabbatar da alkhairi, ya Kuma kawo sassauci cikin lamarin" Abuturrab yace "Ameen, But i need a
favour from u plss" Kallonsa Ahmad yake yana jiran jin favor din, a hankali Abuturrab yace "I want u to help
me convince Umma" Ahmad ya girgixa kansa yace "I am sorry i can't involve my self in this because naga
yanda suka dau issue din too personally, most especially Abba nd Hajja, sannan idan nace xan sa baki
Umma cewa xata yi da sanina kayi komai kaga nima ka ja min kenan" Abuturrab bai kuma ce masa komai
ba ya mike, har ya nufi kofa sai kuma ya tsaya ya juyo yace "Thank you" sannan ya fita Ahmad dai ya bi sa
da ido cike da tausayinsa, fuskarsa kawai xaka kalla kasan yana cikin damuwa sosai, jinginar da kai Ahmad
yyi da kujera wishing he can help. Abuturrab na xaune parlonsa a sama yana rubutu saman wani plain
sheet aka bude kofar parlon, juye takardan yyi upside down ya maida idonsa saman laptop din gabansa
dake a kunne saman center table din kamar dai yana operating dinsa, Ta gefen ido ya kalli wanda ya shigo
parlon ganin Ahmad ne ya ci gaba da rubutunsa a hankali, Ahmad ya karaso cikin parlon walking calmly
yana kallonsa har ya iso ya tsaya gabansa yace "How are you feeling now?" Abuturrab bai ce komai ba
idonsa na kan takardan da yake rubutu, Ahmad ya duka ya dauke takardan, Abuturrab xai kwace amma
tuni ya koma baya yana kallonsa, Abuturrab ya mika masa hannu yace "Pass it to me..." Ahmad bai tankasa
ba sai da ya gama karance abinda takardan ke dauke da shi tsaf, ya kalli Abuturrab da wani irin mamaki
yace "What the heck... kana da hankali kuwa Captain?? Are u okay? what is this u are trying to do, are you
even okay?" Bai jira me Abuturrab xai ce ba ya dauke har laptop din nasa, Abuturrab ya mike kafin yace
komai Ahmad ya fita daga parlon... Aneesah dake downstairs tare da wasu kawayenta biyu da suka xo ta bi
Ahmad da kallo ganin laptop din Abuturrab a hannunsa, sai bayan da ya fita kawarta Suhaila tayi kasa da
murya tace "Ni dai ina son gayen nan wllh, sau biyu kenan nake ganinsa a gidan nan, d'an uwan captain
ne??" Aneesah tace "Mijin kanwarsa ce fa" Suhaila ta hade rai tace "Toh ina ruwana, ni dai har raina naji
ina sonsa wllh" Aneesah tayi kasa da murya tace "Toh xan tura maki numbersa" Rungumeta Suhaila tayi
tace "Ko ke fa sweety" Gida Ahmad ya tafi direct, bayan yyi parking kofar gidan ya sauka ya shiga ciki,
Umma ta fito daga dakinta kenan ta shirya xata fita ya shigo, Umma na kallonsa tace "Mu je ka ajiyeni
gidan Yaya yanxu" Ahmad ya ajiye laptop din hannunsa ya mika mata takardan ta amsa tana cewa "Meye
wannan din?" Har ta kai karshen content din sannan ta kalli Ahmad da mamaki tace "Did he send this?"
Ahmad yace "Shi yasa na taho da laptop din, ni ban sani ba" Umma ta ma rasa abinda xata ce, haka ta
bude baku, can tace "Toh ko bashi da hankali ne dai??" Bata jira abinda Ahmad xai ce ba ta bude jakarta ta
nemi waje ta xauna ta shiga dialing numbersa amma ta ji a kashe, ta kalli Ahmad tace "Kana da number
Aneesah ne?" Ahmad ya ciro wayarsa yace "Eh" Umma tace "Kira min ita kace mata ta kai masa wayar
yanxu" Dialing kiran yyi Aneesah na dagawa yace "Pls ki d'an kai ma Captain waya, his phone isn't going
through"

72 / 108