Advertisements
Chapter 36 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   36 / 108

105K to 108K   out of 321.7K words

kake raina ma kanka hankali, Don
wllh ba ni kake raina ma hankali ba, a sannu abinda ka kulla xai bayyana, did u think i am happy and
relaxed with this ur marriage idan ba xuciyar musulunci ba?? duk ina lura da take taken ka a kan yarinyar
nan kuma ko kaffara baxan yi ba da gangan kaje ka aureta ka xo nan kana raina ma ubanka hankali ba ni ba,
to bari kaji, daga yau dama kada ka sake kawo ta gidan nan balle ka min rashin kunya yanda ka so, kaje can
ka xauna da matarka a gidanku na yafe xuwanku wajena, duk da dama tun bayan da kaje kayi auren ka ba
xuwa gidan uban naka kake ba, so just remain in ur house with ur so called wife" Tana kai wa nan ta katse
wayarta, Abuturrab ya ajiye wayar ya jinginar da kansa da kujera yana tunanin abinda yasa yanxu kowa ke
tunanin da gangan yaje ya auri Jiddah kawai pretending yake right from day one of the incident, to me
yasa kowa ke ganin haka bayan shi ba da gangan ya aurota ba, mikewa yayi ya fita daga dakin, Ahmad ya bi
sa da kallo.... Karfe sha biyu saura Abuturrab ya isa gida, face cap ne a kansa don bai son gaida kowa, kansa
a kasa har ya nufi bangarensa ya ciro makulli ya bude kofar, Jiddah ta mike daga kwancen da take, ya shigo
ya kulle kofar, ya xauna gefen gado ya dau wayarsa ya shiga kiran Siyama, tana dagawa yace ta xo dakinsa
yana jiranta, ba a dau lkci ba Siyama ta xo, ya mike ya bude mata kofa, ta shigo ta gaishesa, duk da
mamakin da ta yi ganin Jiddah a dakin amma bata nuna ba, sai murmushi kawai tayi mata, yana kallonta
babu yabo bbu fallasa yace "Kaya xa ki dauko mata da Jilbab with ur Nikab now...." Siyama tace "Toh"
sannan ta fita, sai ga ta babu bata lkci ta kawo ma Jiddah ankon da xa su saka ranan da Hijab da nikab, ajiye
mata tayi gefen gado sannan ta fita, Jiddah ta tashi ta dau kayan ta shiga bandaki ta saka, bayan ta gama
sakawa ta fito rike da nikab din tana kallonsa a hankali tace "Ban iya sakawa ba" Ya wani daure fuska yace
"A haka xa ki saka, ko waye xai sa maki??" Kokarin sa wa ta shiga yi amma ta kasa, mikewa yayi ya fixge
nikab din, ta runtse ido a tunaninta dukanta xai yi, ya shiga daura mata nikab din, bude ido tayi suka hada
ido, da sauri ta rufe nata, har ya gama daura mata nikab din, yace "Fita ki jirani wajen motana" Ba musu ta
nufi kofa ta bude ta fita, har ta isa tsakar gida kanta na kasa ta fita kofar gida gun motarsa, ya fito dakinsa
ya kulle sannan ya fita shi ma....



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



*Mîkyããj_Sããdy Beauty Soap*




*Hy my beautiful people ina gaisuwaku karka'de kunnuwanku da kyau ku ji💃🏻ina mai sanar muku da cewa
akwai gara6asa me kyau ta musamman ga wanda suka saba sayen sabulunmu da ma wanda zasu fara
saya🥰, akwai ragin kaso 20% bisa dari 100% ga wanda suka saba saye, sannan akwai ragin 10% bisa ga
masu sha'awar fara saye🥰, akwai farashi mai sauki ga 'yan sari, me yapi wannan dadi kam🤔ki sayi guda 4
kanana a baki kyautar daya, ki sayi guda uku manya a baki kyautar karami daya, ki sayi bucket biyu a baki
kyautar babban rubber daya😍 kema da kike da burin saya ku'dinki bai kai ba😰to ga naki, ki kawo customers
uku ki karbi naki kyautar Sabulun😍😍*


*Kawata 'yar 'kwalisa me kike jira,ita mace fa kullum cikim yin ado da 'kãwa take😍 ya kamata ki yunkuro
wajen ganin kin rabu da wannan kurajen da tabo tabon fuskan nan haka🥺, kinga kema sai a saka ki a layin
masu 'kwalisa da bajakolin ado💃🏻😍uwar gida a daure ayi gyaran jiki, sbd karbar goron a wajen me gida🥰,,
ina amaren bayan sallah ku pito ku sayi naku Sabulun kuje kuyi ta wanaka hmmm 😍kamshi kawai zaku yi
tayi kaca kaca😍😍, laushin fata Baja baja😃😂😂a yunkuro azo a karbi kayan gyaran jiki tare da sabulun gyaran
fata a wurin _Mîkyããj_Sããdy_🥰*


*Duk wanda suka gwada Sabulun mu sun san babu 'karanta a ciki🥰in dai fannin gyaran jiki ne to
sabulunmu shine amsarku,, shi ke mai da fata ta zama babu Pimples, Acne, Spot, Stretch Mark, da Duk
wata matsala da ta shafi fata,, akwai lightening, nd glowing😍*
_*In kina son jikinki yai su6ul da shi, fata tai santsi da sul6i, ki yi haske me aji, 'kamshi kaca kaca ko ta Ina,
ki ta fresh abunki hankali kwance ki zama Wankan madara yauqin zuma😍💃🏻Anty madam😃To ki mallaki 3d
(Extra Whitening Soap, Ko da kudinki sai da rabonki hajiyata)💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*_


*Akwai hadin:*
*Mai da tsohuwa yarinya*
*Uwargida ta koma amarya*
*Amarya ta koma tamkar 'yanmata*
*'Yan mata su koma 'yan dagwai²*




_Ga masu bu'kata sai su tuntu6emu ta kafar sadarwa kamar haka;_
_Call/WhatsApp:08061570778_
_IG@mik_yaaj_saady_




Aunty ce ta shigo parlon Ummi duk da mutane da ke parlon ta ra6a xuwa cikin daki, Ummi na ciki tana
bada sako, Aunty ta ja gefe ta jira har ta gama bada sakon sannan tace "Jiya kaina ya dau xafi kika xo kina
tambayar Jiddah, to kin dai ganta ko?" Ummi tace "Mijinta ne ya dauketa" Still Aunty tayi tana kallon
Ummi, trying to assimilate tace "Abuturrab din?" Ummi tace "Eh" Juyawa Aunty tayi ta fita daga dakin
xuciyarta na tafarfasa, lallai Abuturrab ya gama rainata... Through out ranan da ya kasance mothers eve
Jiddah na gida ita kadai, kuma ko a jikinta, sai yanxu ta gane xaman gidan da take ita kadai ma gata ne
ashe, xamanta 24/7 a gida babban Rahama ne gareta, tun da Abuturrab ya ajiyeta ya tabbatar ta shiga ciki
ya tafi bata sake ganinsa ba. Karfe shiddah saura na yamma bayan sun dawo daga babban event center din
da suka yi booking against tomorrow's dinner, su biyar ne a motar, wani abokinsu Umar ne ke driving
motar, Abuturrab na kallon Umar kafin su isa hanyar da xai kai sa gidansa yace "Umar ka samu waje ka
ajiye ni a restaurant din gaba..." Ahmad ya kallesa da sauri, kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace "Me
xaka yi a restaurant bayan abincin da muka ci yanxu?" Abuturrab ya gyara xamansa babu yabo babu fallasa
yace "Eh xan amshi abinci in wuce gida" Ahmad yace "Me xaka je kayi a gida?" Abuturrab yace "Kamar ya
me xanyi a gida? Naga it's almost magrib yanxu ko kana nufin saboda gobe daurin aurenka sai in bar
gidana in kwana a wajenka?" Murmushi Ahmad yyi yace "Kai dai ka fadi gaskiya, dama Ummi ta shaida min
abinda kayi masu, kawai dai baka son ka bar matarka ta kwana ita daya a gidan, shine xaka amsar mata
abinci yanxu ka wuce gida" Abuturrab ya d'an yi shiru idonsa a kan titi yana sake comprehending abinda
Ahmad ke ce masa, Umar yace "Ni kuwa yau sai naje gidan Captain naga matar nan tasa mun gaisa"
Najeeb ma yace "Same with me... matar da har yau ba wanda ya santa" Da sauri Abuturrab yace "To ai
tana gidan biki, sai dai idan can xa mu je" Dariya Ahmad yayi yace "Tana gida bata wani gidan biki, mu je
kawai Umar ai nasan gidan" Lkci daya mood din Abuturrab ya canxa amma ya kasa cewa komai, Ahmad na
nuna ma Umar hanyar gidan har suka isa, horn Umar yayi mai gadi ya bude gate din bayan ya hango
Abuturrab da ya sha kunu cikin motar, Umar na parking Ahmad ya fara sauka, sannan Abuturrab, sauran
frnds din nasu uku ma duk suka sauka, tafiya kawai Abuturrab ke yi xuwa entrance din gidan, Ahmad na
leading din frnds din nasu yana cewa "Wannan ai ba adalci bane ba a sanar maku biki ba kuma a ki kawo
ku gidan amarya" Har wani nishadi yake suna dariya da frnds din suna biye da Abuturrab, Abuturrab na
shiga parlon ya dinga bin ko ina da kallo, kamshin girki ne ke tashi a parlon wanda ko ina fess alamar har
goge goge tayi bayan dawowarta, kitchen ya nufa ya ganta tsaye kusa da gas, ga miya tana yi a gas din,
daga sama har kasa yake kallonta, wanda riga da skirt ne na atamfa jikinta amma ba ankon da ta saka da
safe ba, har xai juya ya fita sai kuma ya sake juyawa yana kallonta babu yabo babu fallasa yace "Dama kar
ki kuskura ki fito daga kitchen din nan" Bai jira cewarta ba ya fita parlor, su Ahmad na xaxxaune parlon har
da kunna TV, Najeeb yace "Duk girkin amarya ne ya cika gidan nan haka, ashe yau xa mu kwashi girki"
Ahmad ya hadiye dariyar da ke damunsa ganin fuskar Abuturrab, Abuturrab dai bai ce komai ba ya wuce
sama, sai gashi ya sauko rike da folded hijab dinta ya wuce kitchen, mika mata yayi yace "Ki fito ki gaishesu,
kuna gaisawa kuma ki wuce sama har su tafi kada ki kuskura ki sakko, saura kuma idan kin xo gaishesu ki
xube kasa kamar kina neman gafara" amsan Hijab din tayi tace "Toh" ya juya ya fita, bayan ta saka hijab din
ta bi bayansa, kanta a kasa har ta karaso cikin parlon, gaba dayansu kallonta suke, ta tsaya nan bayan
kujera, sai kuma ta kasa gaishesu a tsaye don bata saba ba, xagayowa tayi ta xauna saman lallausan carpet
din ta gaishesu ba tare da ta kalli kowa a cikinsu ba, amsawa suka yi gaba daya Umar yace "Yau Allah yayi
xa mu ga amaryar captain, ashe shi yasan me yasa bai ta6a gayyatomu mu ganta ba" Ita dai kanta na kasa,
Abuturrab sai danna wayarsa yake bai ce masa komai ba, Ahmad yace "Toh a kawo mana ruwa matar
captain" Kallonsa tayi jin muryarsa, ta d'an yi murmushi sannan ta mike ta nufi kitchen, tray ta dauka ta
daura ruwan gora uku da glasses hudu sannan ta fito ta ajiye nan tsakiyar parlon, daga kai Abuturrab yyi ya
kalleta ganin tayi abun hankali, he was thinking a hannu xata rike goran ruwan ta kawo, Najeeb yace "Toh
ni kuma girkin amarya xan ci" Sosai gaban Abuturrab ya fadi, don ko shi bai ta6a cin abinda jiddah ta girka
ba, har Ahmad sai da ya ji faduwar gaba, can dai yace "Bayan wanda muka ci yanxu?" Umar yace "Wanda
muka ci daban, wannan kuma na amarya ne" Jiddah dai tayi shiru, Najeeb yace "Ko baxa a bamu ba
amarya?" Mikewa tayi tana murmushi ta nufi kitchen, Abuturrab ya kalli Najeeb yace "Yanxu fa ka ci abinci
bawan Allah, sannan gwangwani daya ta dafa... ba daga kitchen din na fito ba yanxu, ai bata san xa ku xo
ba" Dariya Najeeb yyi yace "Sai ta tsam mana a gwangwani dayan, duk wannan kamshin mu tafi bamu ci
abincin amarya ba" Ahmad dai bai sake cewa komai ba, Abuturrab ya d'an saci kallon hanyar kitchen din,
bai san lkcn da ya mike ya bi bayanta ba, plate ta dauka ta xuba shinkafar, tana tunanin ko a kai xata sa
miyan, amma gidan umma taga waje daban ake sa miya idan an xuba ma baki abinci, hakan yasa ta dau
wani bowl din me xurfi ta xuba miyan, tunda ta xo gidan bata ta6a girki da nama ba sai ranan, duk da ba
wani girki ma take yi ba tun xuwanta, ganin Abuturrab ya shigo kitchen din ya kulle kofa ta juya da sauri
tana kallonsa tace "a saman shinkafar xan xuba miyar?" Ya watsa mata wani kallo yace "Ko kuma a sama
kaina ba, ke har wani girki kika iya xaki wani xo ki xuba masu abinci maimakon kice babu kare, ni kike son ki
kunyata gabansu?? Ko ruwan shayi ma baki bari ya tafasa ballantana ki iya girki me dadi" Kallonsa kawai
take ko kiftawa babu, ya nufi tray din da ta daura shinkafa da miyar, ya dau spoon ya debi miyar kadan ya
sa a gefen shinkafar ya juya, sannan ya debi shinkafar ya kai baki, ita dai kallonsa kawai take gabanta na
faduwa, ya fi second biyar trying to figure out the taste of the food, sai ya ji girkin kamar na gidan Umma,
ko don sbda spices din da tayi amfani da ne, wanda umma ta bada a kawo mata, sake dibar shinkafar yyi ya
kai baki, da gefen idonsa ya bi kitchen din trying to be sure ba Umma bace ta aiko mata da abincin, bai ga
warmer ko wani abu da xai nuna kawo abincin aka yi ba, ya sake diban shinkafar ya kai baki, rungume
hannunta tayi tace "Toh xaka cinye abincin ba a kai masu ba ai" cire spoon din yyi a baki da sauri, ya jefa
mata wani kallo, ta koma baya ta turo baki, yace "Wa yayi girkin nan?" Bai san lkcn da yayi tambayar ba, sai
yaji tambayar made him sound stupid, daukar tray din yyi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Najeeb
ya sauke ajiyar xuciya yace "Ai har mun cire rai nace su tashi mu tafi kawai" Ahmad couldn't hold it any
longer, banda dariya babu abinda yake, Abuturrab ya ajiye masu abincin nan middle of carpet yace "Ae
nace maku d'an kadan ta dafa, gashi nan tunda yunwa ku ke ji" Najeeb ne ya fara sauka sannan Umar, shi
dai khaleel murmushi kawai yake, Ahmad ya mike ya isa gun abincin ya ci spoon daya gabansa na faduwa,
exactly tunanin da Abuturrab yyi shi ma shi yyi, kamar daga gidansu aka kawo mata abincin, komawa yayi
ya xauna yana murmushi yace "Nima na ci abincin amarya" Najeeb yace "Kafin ka ci na taka amaryar
kenan" Umar yace "Wllh u are missing Khaleel kaji dadin abincin nan kuwa" Tasowa Khaleel yyi shima ya ci
spoon daya, sosai suka dinga yabon girkin, shi dai Abuturrab na xaune yana kallonsu, sai da suka cinye
abincin duk da ba yunwa suke ji ba, sannan duk suka fita xuwa masallaci, Ahmad ne last din fita, kafin ya
fita ya nufi Abuturrab yyi kasa da murya yace "Amma daga gidanmu aka kawo abincin nan ko?" Abuturrab
yace "What did u mean?" Ahmad yace "Ba Jiddah bace ta girka" Abuturrab yace "Haka ta ce maka??"
Juyawa Ahmad yyi ya bi bayansu Umar, Abuturrab ya mike ya dau tray din abincin ya wuce kitchen, har
sannan jiddah na tsaye ta jingina da bango, ya ajiye tray din yana kallonta yace "Wa ya aiko maki da abincin
nan?" Ta kallesa, a hankali tace "Abincin ya fi karfin ace ni na dafa ko??" Naxarin maganarta ya shiga yi, ta
tattara plates da xata wanke a sink sannan ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita. Sake kallon pot din
miyan yayi ya karasa ya bude sannan ya bude na shinkafar, rufewa yayi ya juya ya fita daga kitchen din
xuwa masallaci. Ko da suka dawo mosque sun so Abuturrab ya kira jiddah suyi sallama da ita yace ai sallah
take, haka nan ko wannensu ya basa kudi ya bata ladan girki, gefen kujera ya ajiye yace "Ta gode" sannan
yayi masu rakiya har bakin mota yana kallon Ahmad yace "Xan shigo da safe in sha Allah" Ahmad ya
hararesa yace "Kar ma ka shigo mana" a haka suka wuce a mota, Abuturrab ya juya ya koma cikin gidan,
dubu sha biyar ne kudin da ya kirga, bayan kusan minti ashirin ya mike ya wuce sama ya bude kofar
dakinta, xaune ya ganta kan darduma, ya nufi gaban mirror dinta ya ajiye kudin yana kallonta ta madubin
yace "Gashi nan sun baki, dubu sha biyar, amma ban mance turarena da kika fasa ranan ba" juyawa yyi
yana kallonta da kyau yace "Kinsan nawa turaren da kika fasa?" Kallonsa kawai take, yace "Dubu arbain da
bakwai kika fasa ranan, don haka xaki ajiye wannan dubu sha biyar din har ki samo dubu 32 ki cika min
kudin turarena" Yana fadin haka ya bar kudin gaban madubi ya nufi kofa ta bi sa da kallo, can tace "Toh ka
tafi da kudin" Ya juyo yace "Sai kin cika" daga haka ya fita dakin. Karfe tara jiddah na wanke wanke a
kitchen ya shigo, bin kitchen din ya shiga yi da kallo, ita dai tunda ta kallesa sau daya ta ci gaba da wanke
wankenta, kettle din dafa ruwa ya dauko ya bude fridge ya fiddo goran ruwa daya ya xuba a kettle din
sannan ya jona, satan kallonta yayi ganin hankalinta na kan wanke wanken da take, ya kai hannu a hankali
ya bude murfin tukunyar shinkafar dake kan gas har lkcn, dai dai nan ta juya yayi saurin sakin murfin
tukunyar, dauke kanta tayi ta ci gaba da abinda take, ya sosa kansa, sai kuma ya hade rai yace "Shi kuma
sauran shinkafar wa kika bar ma??" Ta kallesa tace "Kai mana" ya kauda kai bayan few seconds yace "Na
fara wasa da ke ko??" Bata ce komai ba ta dauraye hannunta bayan ta gama wanke wanken ta dau plate ta
nufi gun tukunyar ta debi shinkafar duk da ta ci, ta ajiye pot din gun wanke wanke, ta bude miyar ta sa d'an
dai dai da nama yanka uku sannan ta rufe sauran miyan ta dau wani plate me xurfi ta rufe shinkafar da shi
ta dau spoon ta nufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita, shafa kansa yyi yana tunanin wani eatry xai
kira yyi ordering abinci da daddaren nan a kawo masa, shayi ya hada bayan ruwan ya tafasa sannan ya fita
kitchen din, yana haurawa sama ya kalli kofar dakinta sannan ya wuce bangarensa, bude kofar parlon yayi
ya shiga sannan ya kulle, still yyi yana kallon plate din dake ajiye kan center table, ya karasa ya ajiye shayin
hannunsa sannan ya bude plate din yana kallon abincin, ajiye murfin yyi ya mike, can ya kalli kofa, sai kuma
ya xauna, kamar me contemplating sai kuma ya dau spoon din ya fara cin abincin. Washegari karfe takwas
da yan mintuna Abuturrab ya bar gidan xuwa gidansu Ahmad, Umma bata amsa gaisuwar da yake mata
ba, ya shafa kansa ya wuce dakin Ahmad, Ahmad na ganinsa ya mike yace "Let's talk" Kama hannunsa yyi
ya fita suka tafi bangaren Abbansa, Abuturrab dai kallonsa kawai yake, Ahmad ya kulle kofar parlon yace
"Me yasa ka dauke jiddah daga gidan su Ummi jiya?" Abuturrab ya hade rai yace "Gani nayi she isn't
comfortable, sannan Aunty duk ta bi ta takurata duk ba wanda yace komai, shkkn saboda ba matata bace
ita sai in xuba ido a cuceta?" Ahmad yace "Har Ummi ma cutarta take kenan?" Abuturrab ya shafa kansa ya
xauna yace "Ni bance haka ba, wllh da kaga yanda na ganta shekaranjiya ko kai baxa ka bada shawaran

36 / 108