Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
bayan an idar da sallah sun fito masallaci Ahmad na
kallon Abuturrab yace "She isn't comfortable staying with the gate man and his wife, may be because daki
daya ne, kaga baxai yiwu suna ciki tana ciki ba shi yasa take yawan xaman waje, na lura da hakan"
Abuturrab bai ce masa komai ba har suka shiga compound din, sae a sannan yace "Idan na gaida Umma
xaka saukeni gida yanxu" Suna bude kofar parlon Abuturrab yyi ido hudu da jiddah tana tsaye daga kusa da
kofan parlon, sunkuyar da kanta tayi ta koma gefe cikin sanyin murya tace "Ina yini" Bai ce komai ba ya
karasa cikin parlon, Ahmad ya sakar mata murmushi yace "Ki karasa ciki mana, kin tsaya a bakin kofa" Tana
jan yatsunta tace "Abinci xan amsa inji Maman Abdallah" Ahmad yace "Toh ki karasa ciki" Ta d'an karasa
amma ba can cikin parlon ba tace "Na gaya ma Aunty Huraira tace toh" Umma ce ta fito kitchen ganin
jiddah tace "Yau ma jikin kofar kika makale Jiddah?" Jiddah ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Ma su
sunan ki kuwa suna da sakin jiki ke ban san ya haka ba" Ahmad yace "Bakuwa ku ka yi gidan Umma"
Umma tace "Ehh bakuwar Amina ce, gashi har yau taki sakewa" Ahmad ya kalleta yana murmushi yace "Ya
sunanki?" A hankali tace "Jiddah" tausayinta Ahmad ya ji har cikin ransa, without allowing that to show...
ya buda ido yace "Lahh Ummin Captain ce ashe" Umma tayi murmushi tace "Kai ba Umminka bace
kenan?" Ahmad ya shafa kansa yana murmushi ya kalli Abuturrab da ya hade rai kamar bai ta6a dariya ba
yana kallon TV, yace "Captain ga mai sunan Ummin mu fa" Umma na kallon Jiddah tace "Karasa kitchen din
ki ga ko ta gama xuba maki, kinji" Kitchen din Jiddah ta nufa ta shiga ciki, Abuturrab ya gaida Umma a
hankali, amsawa tayi da murmushi tace "Alhmdlh jiki yayi sauki kenan, ai daxu da muka je kana bacci" D'an
murmushin karfin hali yayi yace "Naji sauki Umma" Tace "Toh Allah ya kara lafiya Son, bari a kawo maku
abinci yanxu" A nan parlon ta barsa shi da Ahmad, Jiddah ta fito rike da abinci, bata yadda ta kallesu ba ta
nufi kofa kamar mara gaskiya ta fita... Washegari Thursday karfe tara da yan mintuna Abuturrab ya fito
daga bedroom dinsa, Bangaren Abbansa ya nufa, sai da ya bude kofar parlon Abbansa yace "Alhmdlh....
Much better now" sisters dinsa ne xaune parlon suna masa ya jiki kamar baxai amsa ba kuma bayan ya isa
bakin kofar parlon Abbansu ya amsa sannan ya shiga parlon da sallama, Aunty ce tare da Abba a parlon,
tun da ya shigo Abbansa ke kallonsa, ya xauna kasan carpet yace "Sannu da dawowa Abba" Abba yace
"How are you feeling now?" A hankali yace "Alhmdlh na ji sauki" Abba yace "Allah ya kara lafiya" Aunty
tace "Jiki kam Alhmdlh, kamar ba shi ba shekaranjiya" Abba na kallonsa yace "Kana stressing kanka da
yawa ko, you look stressed out" Abuturrab ya girgixa kai yace "Aa Abba" Aunty tace "Kamata yayi ka dau
hutun ko da sati biyu ne ka huta har ka murmure gaba daya, you look so lean" Shi dai Abuturrab murmushi
kawai yayi bai ce komai ba, Aunty ta mike ta nufi kofa bayan ta dau tray din da ta kawo ma Abba shayi ta
fita, Abba na kallon Abuturrab yace "Hope babu damuwa Aliyu?" A hankali Abuturrab yace "Akwai Abba"
Da mamaki Abba ke kallonsa, kafin yace "Talk to me, meye damuwar" Abuturrab ya kallesa lkci daya jikinsa
yayi sanyi, cikin sanyin murya yace "Abba i did something...." Sai kuma yayi shiru, Abba ya ajiye cup din
hannunsa yana kallonsa da kyau yace "Feel free son, tell me what happened" Abuturrab ya sunkuyar da
kansa nan ya sanar ma Abbansa komai tun daga farko, bai boye masa komai ba, Abba couldn't stop looking
at him da wani expression da shi kansa ya kasa fahimta, Abuturrab ya xauna kan kneels dinsa a hankali
feeling so remorseful yace "Kayi hakuri Abba, i neva thought things will turn out that way da ban yi komai
gaban kaina ba, ban san haka lamarin xai kasance ba, i am sorry father, I don't know if this means failing
you, kayi hakuri Abba..." Abba ya dafa shoulder dinsa ya sauke ajiyar xuciya amma kuma ya rasa ma abinda
xai ce masa, da alama ya girgixa sosai da batun shi ma, Abuturrab yace "Xan iya kai ka gun mai anguwan
ma so u can believe me 100%, ban ta6a xaton haka abubuwan xa su tafi ba da ban yi ba" Abba ya kara
sauke wani ajiyar xuciya yace "Ikon Allah, to Allah ubangiji ya sa hakan shine mafi alkhairi gare ka Aliyu, but
this is astounding..." Abuturrab yayi shiru bai ce komai ba, Abba ya dinga pondering kan lamarin, sai yake
ganin abun kamar a mafarki, his son getting married babu shi, babu yan uwansa, infact unprepared
marriage, hakan bai ta6a faruwa a xuri'arsu ba kaf" Abuturrab ya katse ma Abba tunaninsa ta hanyar cewa
"Amma xan saketa Abba" Da sauri Abba ya kallesa yace "Why? Ba saboda ka taimaketa ka aikata hakan ba,
xaka saketa saboda me kuma?" Da mamaki Abuturrab ke kallon Abbansa, can yace "Abba amma ai ni
baxan iya xama da ita as a wife ba, i just can't Abba, she is not my class" Abba ya dinga kallonsa, Can ya
girgixa kai yace "Dole hakan xaka xauna da ita kuwa, before making the decision of marrying her ai ya
kamata ka fara naxarin ko xaka iya xama da ita din as wife or not, ka saki yarinya for what reason, i thought
it's ur decision? Ko ka dau aure abun wasa ne, ka xata film ku ka yi acting a wajen ranan, ko kuma wasan
yara ku ka yi?" Abuturrab ya marairaice hankalinsa a mugun tashe yace "Abba wllh kawai don in taimaketa
a wannan moment din ne yasa na amince da auren ba wani abu ba, naga xa ayi ruining rayuwarta ne yasa
na amince Abba, amma kuma nayi niyyar sakinta ai bayan daura auren" Abba na masa wani kallo on a
serious note yace "Erase that harebrained idea right away, babu wani sakinta da xaka yi, tunda har aka
daura auren shaidu duk sun shaida ka bada sadaki, babu wani abinda ya rage illa kayi accepting fact din ka
tare da matarka, kada in sake jin ka yi xancen saki, ba drama ko film din Hausa kuka yi acting ba a wajen"
Da mugun mamaki Abuturrab ke kallon Abban nasa baki bude, sanin arguing further won't favor him yasa
yayi shiru, but deep down him yasan in har yana son ci gaba da rayuwarsa yanda yake yi a da to sai ya
datse igiyar yarinyar nan a kansa, idan bai saketa ba he will never have peace of mind, he might even turn
a Sadist, sakinta kuma da xai yi babu wanda xai bari ya sani, they will stay in the same roof but not as
husband and wife, muryar Abbansa ya ji yana cewa "Sai ka karasa gyara gidanka na nan garin ku tare, i will
call all my brothers and inform them what happened, since u chose this for ur self" Abuturrab ya ji kamar
yayi kuka sanin in har cousins da frnds dinsa suka ga cewar wannan yarinyar ce matarsa ai tasa ta kare
kuma, he don't even want to imagine how they will make jest of him and even laugh at him, yayi narai
narai da ido ya marairaice yace "Abba don girman Allah ba sai ka gaya ma kowa wannan abun ba pls I'm
begging you Dad" Dariya ya kusa ba ma Abban nasa ganin yanda ya marairaice, wanda he couldn't help it
but laugh, duk da kasancewarsa musulmin kwarai sannan dattijon kwarai ne kadai ya sa ya saduda yayi
give up da wannan auren na d'an sa, amma banda haka shi da kansa xai iya sa Abuturrab ya saketa don har
cikin ransa bai ji dadin wannan lamarin ba, Lkci daya idanuwan Abuturrab suka kada sosai ya kife kansa da
kujera, Abbansa yaji tausayinsa ba kadan ba yana murmushi yyi patting shoulder dinsa cikin kwantar da
murya yace "Abu me kyau kayi my son, and i am proud of you, Allah kadai ya san ladanka, kar ka damu it
shall be well, Allah yayi maka albarka, and kada ka sake tunanin sakinta a ranka shine xai yi helping
matters, ka xauna da ita tunda ka aureta, you won't regret it in sha Allah coz you've got a good heart,
nasan wataran xaka yi alfahari da ita...." Da sauri Abuturrab ya dago ya kalli Abbansa da jajayen idonsa, ji
yayi xaxxabi na neman kara rufesa, amma tunawa da yayi xai saketa ba tare da sanin kowa ba sai ya ji
hankalinsa ya d'an kwanta, Abba yace "Xuwa yaushe xata tare din yanxu?" Abuturrab ya kalli Abbansa a
sanyaye, Abba yace "Let me talk to ur mothers about it first, i hope they won't be disturb much..."
Wayarsa ya dauka ya shiga kiran matan nasa, Abuturrab gabansa ya dinga faduwa don bai san yanda
Umminsa da Aunty su kuma xa su dau lamarin nan ba, ba a dau lkci ba duk suka shigo, Abuturrab ya kalli
Abbansa a hankali yace "Can i excuse my self sir..." Abba yace "Sure dear" Mikewa yayi ya nufi kofa walking
slowly, Ummi ta bi sa da kallo, tun a shekaranjiya ta san abu na damunsa yana cin sa har cikin ransa,
though tasan da kyar ya gaya mata koma meye da ya shafesa sai dai kishiyarta amma wannan karan ta lura
ita din ma bai gaya ma ba, hakan yasa abun ya dameta sosai tun daga jiya bata da nutsuwa, don duk da
baya gaya mata sabgarsa in dai xai gaya ma Auntyn da sauki, ko ba komai ita ma tana basa shawaran.....
Aunty da ta bi sa da kallo tace "Alhaji ko ya gaya maka damuwarsa, tun safe nake fama da shi yace min ba
komai, kuma nasan ba gaskiya bane, and this is so unlike him" Abba ya d'an sauke ajiyar xuciya yace "Kiran
da nayi maku kenan yanxu" Duk suka maida hankali kan Abba don jin damuwar Abuturrab din.
*Tohm Khaleesat Haiydar dai bata Allah ya isa kuma baxata fara ba a kan littafin Jiddatul Khair, sannan
nasan ni baxan iya hana fitar book din nan ba, kawai dai idan xaka yi ma kanka adalci if u should come
across this book, keep it in mind that ba free book bane, littafin kudi ne, if u are willing to read just make
ur payment ka sha karatunka ba wani shakku a ranka, and bana tunanin u will regret paying and reading
this book in sha Allah....*
✍🏻
_And i really appreciate my lovely fans patronage..... na samu sabbin fans da yawa da suka yi patronizing
Jeedahh kuma naji dadin haka... Ina godiya da maku fatan alkhairi_ 🥰
The book is 500 via 3276052019
Fcmb
Hauwa Bello Jiddah... And u show ur evidence of payment via
07087865788....
Thank you.😇
Mikewa Aunty tayi bayan Abba ya kai aya cikin tashin hankali tace "Ban gane ba Alhaji?? Are you for real?
Shi Abuturrab din ne yaje ya daura ma kansa aure without our knowledge????" Abba yayi murmushin
karfin hali yace "Dama mutum ya ta6a daura ma kansa aure, we just have to accept it Hafsah, it doesn't
make sense though, to amma ya muka iya da lamarin ubangiji, Allah ya riga da ya tsara hakan" Ummi
kallonsu kawai take ko kiftawa babu, wanda da alama duk ta fi su shiga shock din, Aunty ta dage hannu
biyu sama tana girgixa kai da karfi tace "No wayyy, mu ba gantalallu bane gaskiya, yanda aka daura auren
haka xai saketa wllh wllh, me xai yi da yar hayi, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yar hayi fa kace Alhaji?? To
na rantse da Allah baxai yiwu ba" Wani kallo Abba ya dinga yi mata har tayi shiru tana huci kafin yace "Ja
xa ki yi da lamarin ubangiji??" Aunty ta dalla masa wani harara ta nufi kofa rai bace tana cewa "Allah ya
kiyaye, wllh sae ya saki wannan yarinya dai, banda fitinarsa ma ina shi ina shiga tsabgan talakawa mutan
anguwan nan balle har wannan mummunan kaddararran ya fada masa, wllh saki kamar yayi sa...." sai
kuma ta fashe da kuka ta fice ta rufe kofan, Abba ya kalli Ummi bayan kusan minti biyu da fitan Aunty jin
taki cewa komai yace "Kinyi shiru Hauwa" Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh me xance, jin abun nake
kamar a mafarki ai, an ta6a aure haka dama Yallabai?" Abba yace "Gashi nan dai d'an ki yayi, kinsan babu
abinda taimako baya sa mutum yyi, to kinga inda nasa taimakon yayi leading dinsa to" Ummi ta girgixa kai
tace "Toh yanxu meye abun yi Yallabai? Wannan ai ba abun ayi shiru bane ayi ta kiran taimako, wani irin
aure ne wannan kamar a wasan kwaikwayo" Abba yace "Meye kuwa abun yi banda ya tare da ita yarinyar,
ai an riga da an daura aure, kuma lamarin aure ba lamarin wasa bane" Da mamaki Ummi ke kallonsa tace
"Kana nufin haka xai yi rayuwa da ita? Ya tare da ita fa kace" Abba yace "Kwarai, tunda har an daura auren,
ai yanxu matarsa ce ita din, ko ke wani shawara xaki bada a nan?" Ta girgixa kai tace "Haba Alhaji, a ina aka
ta6a irin wannan auren, ni dai tunda nake ban ta6a jin irinsa ba ma, me xa muce ma 'yan uwa da abokan
arxiki, me xa ace ma Hajja, ya kake ga xata dau lamarin nan? shi Abuturrab din shaye shaye ya fara da xai
kai kansa ga irin wannan taimakon? Ba gwara ma ace yau kawota yayi gidan nan ba yace mana ga ta, ai
babu wanda xai hanata xama gidan nan idan anyi bincike an gano gaskiyar lamarin, kuma baxa mu ki riketa
ba, idan ma wani ya ki ni baxan ki ba ka sani" Abba yace "A takaice kema dai kin goyi bayan ya saki yarinyar
kenan" Ummi tace "Toh idan bai saketa ba me xai yi, ai sakin kadai ne best solution a nan, ko a garin ga6a
ga6a ba a irin wannan auren Yallabai" Abba yace "Toh duk kun yi kokari, amma ku sani auren nan bbu fashi
tunda ba wani ya dau sadakin ya kai masa ba, da kansa ya aikata duk abinda ya aikata gaban kansa ba tare
da ya duba cewa yana da iyaye da magabata ba, to don me xa ace sai yayi saki, tunda har ya amince aka
daura masa aure da ita wllh dole ya amince ya xauna da ita, ba dai taimakonta yake son yi ba, gata nan sai
ya taimaketa har karshen rayuwarta, nan gaba sai kiga ba shi ba har ke sai kiyi alfahari da ita a matsayin
matar d'an ki, sannan a rayuwar nan there is reason for everything, Allah ya riga ya tsara hakan to mu a su
wa da xa mu ce tsarin bai yi ba??" Mikewa Ummi tayi bata sake sauraronsa ba ta fice daga parlon, ya daga
kafada yace "Yanda bai maku dadi ba nima lamarin bai min dadi ba ko kadan, but who am i to ask why
tunda haka Allah ya tsara???" Aunty ce tsaye kan Abuturrab inda take shiga ba nan take fita ba duk ta hada
xufa kai kace tayi wani tafkeken asara ne a rayuwarta, ko Salem ne yayi abinda Abuturrab yayi iyakan
abinda xata yi masa kenan take ma Abuturrab, Abuturrab dai na xaune gefen gado ya rike kansa da yyi
masa nauyi duk yana sauraronta ga wani bugawa da xuciyarsa yake, he just hate himself completely for
this foolish mistake he made, me yasa bai yi duk wannan tunanin ba kafin ya aikata wannan shirmen, me
yasa bai yi reasoning abinda xai biyo baya ba yayi abinda yayi?? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da kyar ya
dago kai yana kallon Stepmum din tasa da idanuwansa da suka kada cikin sanyin murya yace "Wllh xan
saketa Aunty, ba da dadewa ba kuma xan yi hakan, ni ko ba ace in saketa ba ma dama ba sa'ar aurena bace
dole xan saketa" Aunty na huci tace "Toh uban me kake jira har yanxu? Mu xaka kwaso ma abun kunya a
dinga nuna gidanmu a gari, wllh baxai yiwu ba ko almajiri baxa ayi masa irin wannan auren da kaje kayi ma
kanka ba, aikin banxa kawai, ko yar cikin gari wllh wllh kafi karfinta balle yar kauyen hayi, to sai ta shigo
gidan mu gani ai...." Tana fadin haka sai ta saki kuka ta fice daga dakin. Abuturrab ya dinga nanata
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a xuciyarsa, what has he done with his life, he wish he could wake up and
see that all this is nothing but a dream, mikewa yayi a hankali ya karasa kofar dakinsa ya sa makulli don ma
kar ta sake dawowa sannan ya dawo ya xauna ya dafe kansa hade da lumshe ido yana kiran Allah a ransa.
Bayan azahar Abuturrab ya dau makullin motarsa ya fito daki, tun safe bai fito ba sai yanxu da yaje
masallaci yayi sallah ya dawo, yana shigowa parlor ganin kallon da siblings dinsa ke masa yasan sun samu
labarin kenan su ma, bai kuma kallonsu ba har ya fice daga gidan, ya hau motarsa ya bar gidan, gidansu
Ahmad ya nufa, ko kallon matar mai gadi dake gaishesa bai yi ba ya nufi entrance din gidan, a yanxu dai
komai haushi yake basa, underneath his breathe yayi sallama ya shiga parlon, Huraira ce da Siyama parlon,
su ma bai sake kallon inda suke ba balle ya amsa gaisuwarsu, dai dai nan Ahmad ya fito daga wani daki
dake nan parlon, ganin Abuturrab yace "I was planning on calling you now, welcome... Duk kayi scarce yau"
Abuturrab bai ce komai ba ya nufi dakin Ahmad, Ahmad ya bi bayansa yana murmushi a ransa yana cewa
the latest ango in town, xaune ya tadda shi gefen gado, Ahmad ya tsaya bakin kofa yana kallonsa yace "Ya
ake ciki yanxu, hope it went well??" Abuturrab yace "Kamar yanda na fada, no much problem from Dad,
but aunty took the matter tooo personal, Aunty tayi misunderstanding komai" Ahmad ya masa wani kallo
yace "And so what? How about Ummi? Though she is here, daxu ta xo" Abuturrab ya xaro ido yace "Kana
nufin Ummi na gidan nan?" Ahmad yace "Yea tana dakin Umma" Abuturrab ya lumshe ido ya bude, gaba
daya abun duniya ya ishesa yanxu fisabilillah baxai farka yaga duk wannan abun mafarki bane, Ahmad yace
"Amma Ummi tayi maka magana ne?" Abuturrab ya girgixa kai yace "Bata ce min komai ba har yanxu"
Ahmad yace "Ka kwantar da hankalinka komai ya xo da sauki tunda Abba ya fahimce ka" Abuturrab yace
"Ya fahimce ni?? Ai ni da abinda Abba ke ce min yanxu