Advertisements
Chapter 42 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   42 / 108

123K to 126K   out of 321.7K words

Ahmad ba ya nufi kofa ya fita,
Jiddah na daukan Hijab dinta dake linke Maimoon ta kai karshen ayan da take karantawa, tana kallonta
tace "Ina xaki?" Jiddah taki kallonta balle taga hawayen dake makale idonta tace "Xan amso abu wajen
Maman Abdallah ne" Daga haka ta fita dakin, yana tsaye bakin kofar parlor alamar ita yake jira, ta nufi
kofar, muryar Hajja suka ji tana cewa "Ke ina kuma xaki da daddaren nan bayan nace ki min linke uwar
rikon ki ta daure maki kugu wai baki da lafiya?" Jiddah ta kasa juyowa, Abuturrab na ganin Hajja ya fita
parlon ya tsaya balcony, Ahmad ne ya shigo parlon shi ma yana kallon Jiddah yace "Where are you going to
Jiddah?" Still bata juyo ba hawaye na sauka idonta tana gogewa da hannunta, ya karasa ya tsaya gabanta
yana kallonta, buda ido yyi sosai ganin kuka take, yace "Me ya faru Jiddah" Hajja ma ta karaso tana kallonta
tace "To ko dai tana da mutanen boye ne Ahmad?" Ahmad dai bai ce komai ba sai kallon Jiddah yake, Hajja
tace "Aa ba ruwana bari in kira Ramlah kar abu ya lalace mana" Tana fadin haka ta tafi da sauri, Ahmad
yayi kasa da murya yace "Gaya min me ya faru Jiddah, kuma ina xa ki?" Ta kasa cewa komai sai hawaye,
Hajja ta dawo tare da Umma, Umma tace "Jiddah" Juyowa Jiddah tayi da jajayen idonta tana kallonta,
Umma ta karasa kusa da ita tace "Me ya faru?? Kukan me kike, an maki wani abu ne" Shigowa parlon
Abuturrab yyi xai wuce daki, Jiddah na kallonsa tana share idonta a hankali tace "Ce min yayi xai maidani
inda ya dauko ni tunda shi ne ya kawoni dama ba wani ba" Gaba daya duk suka juya suna kallon Abuturrab
da yaki kallonsu kuma yaki tsayawa, cikin tsawa Umma tace "Dakata a nan Aliyu" Ba musu ya tsaya amma
bai juyo ba, Hajja ta marairaice tace "Wannan wani irin Bala'i ne Usman ya haifo Ramlah?" Umma ta kalli
Jiddah fuska a daure tace "Gaya min abubuwan da ya fada maki" Cikin rawar murya Jiddah tace "Kawai
haka nan yace, wai duk me son daukoni sai ya je ya dauko ni idan ya maidani hayi" Umma tace "Yanxu
Hijabin da kika sa hayin xai kai ki?" Jiddah ta gyada mata kai, Hajja tace "Amma daga d'an iska sai Aliyun
nan wllh, Muna ta tausayinsa ba shi da lafiya ashe dabanci xai xo yayi mana a nan ni Dijeee, anya kana son
gamawa da duniya lafiya kuwa d'an nan, ashe haka kake Aliyu" Cikin dakewa Umma tace "Aliyu!!" sai a
sannan ya juyo ya kalleta tace "Xan baka takarda kayi list din duk abinda ka kashe ma Jiddah tun daga lkcn
da ka fara saninta har xuwa lkcn da ka rabu da ita, idan ma kudin sun fi karfina xan kai ma Abbanka ya bada
su, sannan after that wallahil azeem ka sake kallon inda Jiddah take, i mean ka sake kallan min ita wllh sai
ka sha mamakina a duniyar nan, xan maka tijara Aliyu, babu kai babu Jiddaha har abada, idan kuma kai ka
cika d'an halaq ka dauketa ka mayar da ita hayin kaga, sannan maxa ka kama hanya ka koma gidanku kada
ka sake xuwa min gida, idan kuwa kayi gigin xuwa sai nayi maka walakancin da baka ta6a xato ba" Hajja
tayi mitsi mitsi da ido tace "Algungumi kawai, ana ta tausayinsa ba shi da lafiya ashe shi abinda xai kawosa
nan gidan daban, to wllh har abada kai da wannan baiwar Allahn don ta ma fiye min kai sau dubu yanxu
tunda bata ta6a xagina ba balle manyanta, kai kuwa idan aka ce xa a kirga adadin xagin da ka min ai sai da
a tafi kotu don xuciya xai iya dibana inki yafe maka, to meye kuma xaka sa yar mutane a gaba bayan an
raba ku, ko dai har yanxu sonta kake bamu da labari? Banda tsautsayi ma da ya fada mata me xata yi da
d'an banxa irin ka?" Umma da taji xuciyarta na tafarfasa tace "Wato shi yasa dama babu musu ka yarda ka
biyomu don ka ci mata xarafi da mutunci, to wllh kayi na farko kayi na karshe, Jiddah da kake gani tafi
karfin walakancinka yanxu tunda ba kai ke ciyar da ita ba, wanda kayi a baya ma duk nace kayi list a biyaka"
Hajja tace "Ko ni sai in dage gidana daya in siyar a biyaka wllh" Sai a snn ya kalli Hajja yace "Saboda nace
maki don ke nayi da xaki biyani" Da karfi Hajja tace "Huuuuu ka dai ji kunya duk ka xubda ladanka,
gantalalle kawai" Ta gefen ido ya kalli Jiddah dake share hawayen da yaki tsaya mata, shi dai Ahmad ya ma
rasa abun cewa sai kallon Abuturrab yake da mamaki, kofa Abuturrab ya nufa ba tare da ya kallesu ba
kamar xai tashi sama, Hajja ta dafe kirji tace "Mu ka xaga ka fita Aliyu?? Mu??" Ko kallonta bai yi ba har ya
fice gaba daya, da karfi Hajja tace "Wawa kawai me xuciyar Hafsah, da kyar idan matar nan bata faki idon
Hauwa kana jariri ta dura maka nononta ba, don babu halinta da ka xubar al-qur'an" Umma na kallon
Jiddah tace "Daga yau ko gidan uban wa kika hadu da shi kika sake kallon inda yake balle ki gaishesa ko
wata magana ta hadaki da shi sai na sa6a maki, babu ke babu shi har abada, a duk inda xa ku hadu
kuwa...." Hajja tace "Dama kina ganinsa ki gudu kiyi ta kanki, ko kuma ki fasa ihu kawai idan wani taimakon
ne a kai maki da gaggawa, ni ai nafi kowa sanin halinsa tunda a hannuna aka haifesa, sau nawa idan an
bata masa rai yake take kaza ya kasheta har lahira a lkcn ma yana d'an mitsitsi.... Yanxu ai sai dai ya take
d'an mutum" Jiddah dai kanta na kasa, Hajja tace "Kuma tun ban tafi Masar ba ya xama d'an daba fa, fada
ne kawai banyi ba kar uban ya kullaceni nayi tafiyata bakina alekum, wa ya sani irin mugun abun da ake
koya masu idan sun daga jirgi sama, shi sa har yau ban yarda na hau jirgin da yake ja ba wllh ko don yanda
ya tsaneni ma ba sai ya sake jirgin da gangan duk mu hantsulo kasa ba" tana fadin haka ta nemi waje ta
xauna tana fifita saboda xufan da ta hada don bala'i, Umma na kallon Jiddah tace "Dauka abincinki ki wuce
daki" Jiddah ta karasa a hankali ta dau abincin ta wuce daki, Hajja tace "Ni wllh don baxa ku yarda bane
amma da kun bani yarinyar nan kawai in tafi da ita" Umma tace "Sai dai taje maki hutu" daga haka ta bar
parlon. Jiddah ta maida hankali sosai a karatunta babu wasa, wanda hakan yasa Umma ke kara jin sonta a
rai domin kwazonta ya wuce misali, both Islamic da western din duk she's flowing well, kusan duk bayan
kwana biyu Yousuf ke xuwa gidan da daddare, kuma duk idan ya xo ba wai wani hira suke da Jiddah ba
iyaka ya sake guiding dinta a karatun nata shi ma, yawanci kuma turanci yake nace mata ta koya, kuma
babu laifi she is really catching up, duk weekend Ahmad ke shigowa kaduna sbda duba Ramlah dake
laulayi, shi ma kuma yana assisting din Jiddah a bangarori da dama na karatunta. Umma na parlor ranan
wata asabar Jiddah ta fito rike da wayarta dake ring ta karaso ta mika mata, Umma ta amsa tana duba me
kiran nata, Ganin Ummi ke kira ta daga, bayan sun gaisa Ummi tace "Toh sun gama hada lefensu wai sai ki
xo ki gani gobe xa a tafi da shi" Umma tace "Kai ba lallai ba yaya, Allah ya sanya alkhairi kawai" Ummi tace
"Aa da dai ki daure ki xo din Ramlah xai fi" Umma ta d'an yi shiru kafin tace "Allah da kawai kin bari su tafi
da shi goben Yaya, ai ba sai na gani ba" Ummi tace "Toh ni kuma nace ki xo ki gani" Umma ta d'an yi shiru
sai kuma tace "Toh shkkn, bari ruwan ya tsagaita xan sa driver ya kawo ni ko da yamma ne" Ummi tace
"Allah ya kai mu" ajiye wayar tayi ta ci gaba da kallon da take a Tv. Da yamma kamar yanda Umma tace ta
shirya wajen karfe biyar ta fito parlor tana kallonsu Maimoon da basu je Islamiyya ba sbda ruwan da aka yi,
tace "Xa ku je can gidan ne ganin lefe?" Maimoon ta mike da sauri tace "Eh Umma dama ina tsoron gaya
maki ne" Umma tace "Toh sai ku shirya ni ina ruwana kuma da xan hana ku" Maimoon da Safiyya suka
mike gaba daya, ganin Jiddah bata motsa ba Umma tace "Ke baxa ki ba Jiddah?" jiddah ta girgixa kai tace
"Aa xanyi assignment dina Umma" Umma tace "Ai ba dadewa xa muyi ba, tunda babu kowa gidan kawai ki
shirya mu je yanxu xa mu dawo, idan muka tafi ma babu ke Hajja sai ta fassara mu tace ba a haka a Masar"
Jiddah bata iya tace ma Umma komai ba, amma ba don ranta ya so ba ta mike ta wuce daki, Hijab ta saka
suka fito parlon tare da su Maimoon......


Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you




*mg's skincare*

Shin Ina matan sukemaza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir
dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan
shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin
kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na
bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk
wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai
kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho
wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan
fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin
Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali
jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare uk wnd yy using bridal set
dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa🤝
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride
Glow

💯 tested nd trusted🤝
Guarantee


Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166




Slowly Jiddah ke tafiya kamar bata son yi a compound dinsu Abuturrab, su Maimoon duk sun yi gaba tare
da Umma, ita ce karshen shiga parlon, tsaye tayi bayan kujera ganin Abuturrab dake sakkowa cikin parlon
waya kare a kunnensa, tayi bakin kokarin ganin bata kallesa ba, bayan ya shigo parlon ta xaga ta bayan
kujera tayi wucewarta part din Ummi ya bi ta da kallo, Bayan Jiddah ta gaisa da Ummi, Ummi tace "Ki tafi
dakin Hajja suna can" Mikewa tayi tace "Toh" sannan ta fita xuwa dakin Hajja, Umma na xaune su
Maimoon na ta bude akwatunan da aka jera a dakin, Hajja tace "Yanda kika san wata yar gwal xa a auro,
haka aka hada lefen har da na Allah ya isa..." Akwatuna biyar ne set biyu each da kit, Umma ta dinga kallon
uban kayan da aka hada na lefen bayan su Maimoon na ta budewa, Hajja tace "Aa kar ki ji komai Ramlah ai
nace duk xan dibar ma kanninsa abinda ya sauwaka a ciki, mu ba 6arayi bane da xa mu kai masu wannan
ubansun kayan, ni kaina xan cire atamfa me tsada daya da jaka, takalmin ma baxai min ba sbda me tsini ne
kar in je in karye shi sa baxan dauka ba, amma duk wa ennan yan matan xan cire masu duk abinda Allah
yayi wllh" Umma tace "Aa Hajja ki bar masu kayansu kawai, Allah ya sanya alkhairi, ya bama yan baya
haka" Hajja tace "Kaji wata magana irin ta 'yan kasar nan, wllh wllh babu shegen da xai yi haka a Masar,
sannan me yasa baki bari Ahmad ya hada ma Ramlah irin wannan lefen ba? Ba shi ma yana da dukiyar ba
na samu labari?? to shine ni xaki ce jikana ya dauka ya kai ma su gaba daya sbda sata yake yi a sararin
samaniya? Aa wllh duk xan bi in rage ni ba gantalalla bace" Umma bata kuma ce mata komai ba, ita dai
Jiddah na xaune ta rakube jikin kujera tana bin akwatunan da kayan ciki da kallo. Abuturrab ne tsaye
parlon step mum dinsa da duk ta firgice masa, yayi kasa da murya yace "Toh ke ba dai kinsan duk
abubuwan da kika xuba a ciki ba Aunty, komai kika ga yayi missing kar ki damu xan bada kudi ki siya wani ki
saka" Aunty tace "Ni dai cewa nayi ka tafi ka xauna a dakin, idan aka ganka babu wanda xai ta6a komai
cikin kayan, kafi kowa sanin Hajjan nan fa" Abuturrab ya girgixa kai yace "Aunty don girman Allah ki bari su
yi ta daukan duk abinda suke so ni xan sake replacing, i just can't go to that room" Aunty ta wani hade rai
tana kallonsa tace "Wato ban isa da kai ba Aliyu, ban isa in sa ka abu kayi ba??" Yace "Toh shkkn, bari in je"
Daga haka ya juya ya fita parlon, sai da ta bisa ta tabbatar ya shiga dakin Hajja sannan ta koma parlonta, Ya
d'an shafa kai bayan sun hada ido da Umma da ladabi yace "Ina yini" Banxa tayi masa, su Maimoon suka
gaishe sa yace "Lafiya lau" Jiddah dai tunda ya shigo bata kalli inda yake ba idonta na kan akwatuna, Hajja
dake ta fiddo kayan akwatunan tare da Safiyya ta mike tana kallonsa tace "Lafiya ka shigo kayi mana
sandandan a kai Aliyu?" Yace "Takardan da na baki nake so in amsa yanxu" Hajja ta kalli Umma tace "Kinga
jaraba ko, tun fa ban tafi Masar ba ya bani wasu shegun takardu da ban san isilinsu ba yanxu, shekaranjiya
ya xo nace masa yayi hakuri ban san wani shirgin suka shigw ba amma har gidana xan sa aje a bude mu
shiga mu bincika ko da rabon a gani, a haka muka rufe kess din da shi, to meye yanxu xai dawo ya tsaya
min in basa takardu kamar wasu takardun jaraba, to gaskiya ban san isilinsu ba ka rabu da ni, ni bance ka
dauko takarda ka bani ba" Daga haka ta ci gaba da abinda take, Umma ko kallon direction din Abuturrab
bata yi ba banda daure fuska da tayi, Hajja ta dauki wani gyale me kyau ta jefa ma Maimoon tace "Gwada
wannan" Umma ta girgixa kai tace "Hajja nace ki bari don Allah, wannan bai dace ba..." Hajja ta mike ta
katseta tace "Kinga baiwar Allah tashi kiyi wucewarki in gama abinda nake, babu ruwanki da harkana, kin
wani narka uban kiba kina bani oda kamar yar ki, nace ki tafi asibiti a dubaki kin ki, Da a Masar ne da tuni
an kai asibiti wllh, to kuma ina ruwanki da abinda nake banda dai kawai kina kanwar uwar Aliyun uwa daya
uba daya" Umma ta mike tace "Toh Allah ya sanya alkhairi na ga lefe sun yi kyau Maa sha Allah, Allah ya
nuna na yan baya haka" Hajja tayi banxa da ita, Umma ta nufi kofa ta fita, Hajja tace "Banda kema cutar
Aliyun xaki yi tunda ba ke kika haifesa ba kuma haushinsa kike ji kamar ki kashesa, wacece ita wannan
yarinya da xa a kai ma lefe guda sha biyu komai na ciki kuma dozen dozen, ina kokarin ragewa kuma xaki
kawo min raini, to wllh baxai sa6u ba, Dukiyar Aliyu ba banxa ba..." Rungume hannu Abuturrab yyi yana
kallon Hajja, ta dau atamfa daya me tsada ta jefa ma Jiddah tace "Yayi maki kyau ko a canxa?" Jiddah ta
bude ido sosai tana kallon Hajja, ta dau jaka ta jefa ma Maimoon ma, a takaice dai sai da ta ajiye ma Jiddah
atamfa, mayafi, da jaka da takalmi da kayan kwalliya, su Maimoon ta basu kayan kwalliya da mayafai kawai
duk don sbda haushin abinda Umma tayi mata, Jiddah dai gabanta sai faduwa yake tana kallon kayan
gabanta, Hajja ta nemi waje ta xauna tana kallonsu Maimoon tace "Toh ku kulle masu kayansu, Allah ya sa
albarka a abinda suka rage" Maimoon da Safiyya duk suka rufe akwatunan, Sai a sannan Abuturrab ya juya
ya fita daga dakin, sai bayan da ya fita Hajja ta nemi ledoji duk ta sa ma kowa abinda ta basa a ciki, Jiddah
dai duk jikinta yayi sanyi ta ma kasa ta6a ledan da Hajja ta ajiye mata a gabanta, Hajja tace "Ki tafi kice ma
Zubaida take ko wa, kice mata baxata bani ruwan xafin bane in shiga makota in samo?" Jiddah ta kalleta
don bata san ko da wa take ba, Hajja tace "Da ke nake, tunda barinsu kika yi da rufe akwatin kin xauna
kamar sarauniya, banda dai Allah ya rufa maki asiri Usman ya rufa maki asiri ai da ke xa ayi ma kishiya
yanxu, to kamar ya san da haka yasa aka sakeki" Mikewa Jiddah tayi ta nufi kofa ta fita, xaune ta tadda
Abuturrab shi kadai a main parlor, duk da sun hada ido tayi wucewarta xuwa kitchen, bata tadda mai aikin
a kitchen din ba, tayi ta tsayuwa daga karshe kuma ta fito, taki kallon inda Abuturrab yake ta wuce dakin
Hajja, tana kallon Hajja tace "Hajja bata kitchen din" Hajja tace "Toh ta ci kanta, tafi da flask dina idan kin
ga an daura ruwa ki juyo min ko bai yi xafi ba, tun daxu nake bin bakar matar ta ban ruwan xafi in sha shayi
ta ki, Da a Masar ne wnn ruwan da aka tsuga yau ko wani gida kya ga butan tafasasshen shayi da kofuna
kowa na ta sha" Jiddah bata ce komai ba ta dau flask din ta fita, har sannan Abuturrab na xaune parlon,
tayi wucewarta kitchen, ta bude tukunyar da ta gani kan gas taga ruwa ne amma bai tafasa ba, ta dau cup
kenan xata fara xuba ruwan cikin flask aka bude kofar kitchen din, sosai taji gabanta ya

42 / 108