Advertisements
Chapter 7 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 108

18K to 21K   out of 321.7K words

ya shigo kd yanxu mu hadu by pass in amshi sakon" Ahmad
yace "Ohk, drop me home" Abuturrab ya nufi gidansu yyi parking bakin gate, Ahmad ya sauka yace
"Sunday din xaka tafi kano?" Abuturrab yace "In sha Allah" Ahmad yace "Alright... Sai da safe" Daga haka
ya shiga ciki, Abuturrab yayi reverse ya bar layin. Abuturrab ya fi minti goma tsaye a kan hanya bayan ya
iso bakin ruwa, jinginar da kansa yyi jikin kujeran da yake xaune yana tunanin wanda ya sani wanda bai yi
aure ba that he can do anything possible to see him married to this girl that is ready and wanting to kill her
self, driver din Abbansa ko wata uku ba ayi da yyi aure ba, who again? Wani senior cleaner ne a Airport din
kano ya fado masa, Guy din na da hankali... a Diploma holder, ga shi da mutunta mutane, Abuturrab ya
sauke ajiyar xuciya ganin ya kusa samun solution, and he will try all possible means sai Mu'axxam ya auri
yarinyar nan, wani ajiyar xuciyar ya sake saukewa na relieve, driving ya ci gaba da yi, yana isa u-turn ya dau
hanyar Hayi, kamar ko da yaushe parking yyi a bakin layin yana kallon cikin layin, nose mask dinsa ya saka
da glasses din ido sannan ya sauka motar ya fara tafiya, calmly yake tafiyar har ya isa kofar gidan, wani yaro
ya tura ya kira masa jiddah cikin gidan, Hansai na xaune tsakar gida tana cin shinkafa da wake da mai da
yaji da salak wanda rabon da su ci shinkafar tun rasuwan Mai gidan nata, tana kallon yaron tace "Lawali
daga ina haka?" Yace "Wani ke kiran jiddah a waje" Hansai tace "Jiddah kuma?" Jiddah dake kwance
xaxxabi ya ci karfinta ta bude jajayen idanuwanta da sauri gabanta yyi wani mugun faduwa ta mike xaune,
Hansai ta kakkabe guntun shinkafar hannunta a samiran cinyarta tace "Waye shi? Kuma daga ina?" Yaron
yace "Wani dogo ne ya sa gilashi da takunkumi a hanci, ya sa fararen kaya" Hansai ta mike da sauri tana
leka dakinsu Jiddah tace "Ke tashi, kaddai me kawo min kudin nan ne?" Jiddah ta mike tsaye da kyar jikinta
na rawa tace "Ban sani ba" Hansai tace "To ai kuwa daurewa xa kiyi ki tashi ki saka hijabi ki fita ki ga waye,
kika sani ko shi din ne wani kudin ya kawo yau ma" Kasa ci gaba da tsayuwa tayi duk ynda ta so yin hakan,
Hansai tace "Yau naga tsiya, baxa ki daure ki tashi ba kamar ba mace ba Jiddah??" Jiddah ta dafa gadon ta
kara daurewa ta tashi, Hansai ta warware Hijab dinta dake ajiye a linke kan jaka ta mika mata tace "Sa ki
fita maxa maxa ki ga waye" da kanta ta sa mata hijab din, jiddah ta fita dakin, Hansai ta xauna gefen gado
tana addu'an Allah ya sa shi din ne, kuma wani kudin xai bada yau ma, jiddah na fita kofar gidan ya juyo
yana kallonta, durkusawa tayi nan kasa ta kasa ci gaba da tsayuwa, ya dinga mata wani kallo yace "Jikin bai
maki sauki ba?" hawaye ya shiga sauka idonta, kana ganinta kasan tana jin jiki, yace "Kin sha magungunan
nan kuwa?" Kin cewa komai tayi, Ya hade rai da d'an tsawa yace "Tambayar ki nake" Ta fashe da kuka a
hankali ta kara jingina da bango tace "Ni amai xanyi idan na sha" Da mamaki ya dinga kallonta, Hansai dai
na ta tsaye tsakar gida tana jiran ganin shigowar jiddah, jin shiru shiru ta nufo xauren cikin sanda tana leko
waje, hada ido suka yi da Abuturrab, ta sunkuyar da kanta da sauri tana d'an kame kame tace "Sannu da
xuwa Alhaji.... Ae da ta fito maka da tabarma ko" kallonta kawai Abuturrab ke yi daga sama har kasa, can
yace "ina wuni" Hansai ta rutsuna tace "Lafiya lau Alhaji, sannu da xuwa, ko xaka shigo daga ciki...." Yana
kallon jiddah yace "Ya mai jikin?" Hansai ta marairaice tace "Wllh da sauki kenan xa a ce, kuma fa ta sha
magunguna amma shiru har yanxu" yace "Toh bari mu je asibiti" Hansai tace "Kai Alhaji da dai a je chemist
kar hidiman yyi yawa, ga chemist can bayan mu" yace "Aa xa a je asibitin kawai" Hansai tace "Toh shkkn
Alhaji, daure ki tashi Jiddan Mama, sannu... Ga dai ana shan maganin kamar ba a sha" tana fadin haka ta
dagota, Abuturrab na kallon Hansai yace "Motata na bakin titi" Hansai ta kwance dankwalin kanta ta rufe
jikinta da shi tace "Toh bari mu je can din" tana rike da jiddah suka isa bakin titin ya bude back seat ta saka
jiddah ciki, mutanen layin sae kallonsu suke, Abuturrab na kallonta yace "Ina 'yar uwarta mu tafi tare"
Hansai tace "Au wai Bibalo, ai kuwa bata anguwar nan yanxu haka, ko in shiga mu je ni?" Ya kalleta daga
sama har kasa sannan yace "Yanxu xa mu dawo in sha Allah, ba sai kin je ba" tace "Atoh dama ae bai ma
kamata in bi ku ba, toh Allah ya kiyaye Alhaji, a dawo lafiya" xagawa yyi ya shiga driver seat ya tada motar
ya bar wajen Hansai sai washe baki take tana daga masa hannu, sai kuma ta hade rai tana kallon 'yan layin
da suka xuba mata ido da kallo tace "To wai lafiya wannan shegen kallo haka??" Tsaki ta ja ta juya ta fara
wucewa tana cewa "Jama'ah baxa su ji da talaucin da yyi masu katutu ba sai shegen sa ido da neman abun
fade, to d'an uwanmu ne daga Habuja sai kowa yyi ta kansa haka kuma" Abuturrab na hawan saman titi ya
kalli Jiddah ta madubi yace "Wato baki sha maganin jiya ba??" Shiru tayi bata ce komai ba, ya hade rai yace
"Ki bude baki kiyi min magana ina tambayarki" kai kawai ta gyada masa, yace "Me yasa baki sha ba?"
Kamar xata yi kuka tace "Nace maka amai xan yi idan na sha" Yace "To xa mu je su maki alluran yanxu ai"
Ta mike xaune da kyar tace "Aa ni bana son allura" Wani kallo ya wurga mata, tayi shiru bata sake cewa
komai ba.... Sai kusan karfe taran dare Abuturrab ya dawo da ita bakin layin nasu, yau ma da ledan take
away din abincin da ya siya mata, ya sauko motar ya xaga ya bude mata side din da take xaune, da kyar ta
sauko motar da wasu ledan magungunan daban da aka kara bata a asibitin da ledan abinci, ya rufe
motarsa, har ya xaga xai shiga maxaunin driver ya sa hannu aljihu ya ciro dubu goma ya dawo ya bata yace
"Sai ki ba Baabar taku" daga haka ya shiga motar yayi wucewarsa, da kyar ta dinga jan kafa har ta isa gida,
Hansai na xaune da Bibalo dake cin abinci, ganin ta shigo Hansai ta mike a xabure tace "Me ya baki?"
Jiddah ta mika mata duk ledojin hannunta da kudin sannan ta xauna nan bakin kofa ta jingina da bango
kanta na juya mata, Hansai ta kirga kudin ganin dubu goma ne tace "Toh ya baxai bani dubu goma ba
bayan kudi ya kare a shegun magungunanki, munafuka kawai, ciwo kalilan duk ta bi ta langwabe ma
mutane kamar kyanwa, kuma da ganin asibitin me tsada xai kai ki, to Allah ya isa wllh...." Kallonta kawai
Jiddah ke yi, Hansai ta ja tsaki ta shiga fiddo magungunan a fusace tana kyabe baki, can ta watsa mata su
tace "Abun takaicin ma asaran kudinsa kawai yyi, ke din ce xaki sha ma mutane magani" watsa mata ledan
magungunan tayi gaba daya sannan ta bude dayan ledan ganin shinkafa da dunkulelen kaza ta murmusa
tace "Allah sarki bawan Allah" Tuni Bibalo ta tura kwanon gabanta ta dawo kusa da uwarta, Hansai tace
"Toh bai saka da lemo ba sai ruwan gora?" Jiddah dai bata ce komai ba, Hansai da Bibalo suka shiga cin
abincin kamar mayunwata, sai da suka kusa cinyewa ta kallo jiddah tace "Au, to ai ba mu sam mata ba"
kwanon abincin da Bibalo ke ci ta jawo, tana kallon guntun shinkafar da Bibala ta rage ta debi na take away
din loma biyu ta yarfa a kai, sannan ta dau tsoka me K'ashi, sai da ta ta66atar ta kwaye tsokan sannan ta
saka k'ashin a kwanon ta tura ma Jiddah tace "Gashi kema" Jiddah dai bata ce komai ba, suka cinye nama
da abincin tass sannan Hansai ta maka uban gyatsa ta mike ta shige daki tana cewa "Bibalo ke da yar yabi
sai ku bibbi gobe ku kai cingam da sweet din sa ranan da aka yi, har yau ba a ba jama'a ba" Bibalo ta mike
ta bi bayan uwarta tana cewa "Yo ai cingam din kwali daya ya rage..." Jiddah ta jingina da bango hawaye ya
kawo idonta a hankali tace "Kuma bai kawo min piya piyan ba" Washegari lahadi Abuturrab ya fito gida
misalin karfe sha daya na safe, Waya ne kare kunnensa yana driving a hankali don bai fita layinsu ba,
girgixa kai yyi yace "No kai dai ka samu adaidaita ni na riga da na fito da mota, sai ka fadi inda xan sameka"
Murmushi yayi bayan few seconds yace "Okay then, tunda kasan hospital din ba sai ka tafi ba" Yana fadin
haka ya katse wayar hannunsa. Dai dai inda suka yi xai dau Ahmad yyi parking yana jiransa, bayan kusan
minti goma Ahmad ya iso wajen da adaidaita ya shiga motar yana kallon Abuturrab yace "Amma ba yau
xaka bar kaduna ba Captain" Abuturrab yace "probably.... Akwai abinda xan yi yau din" Ahmad yace "Ni
train xan bi in sha Allah yau xan koma Abuja..." Abuturrab bai ce komai ba har suka isa wani hospital
domin duba wani frnd dinsu da aka yi admitting, fruits iri iri suka siya masa a hanyarsu ta xuwa wajen,
suna shiga ward din da yake suka tarar da abokansu hudu su ma sun xo dubiya, bayan an gaisa, wani frnd
dinsu Umar na kallon Abuturrab cike da tsokana yace "Captain ko dai a hayin rigasa kake gini ne? Or
probably neman aure...." Da mamaki Abuturrab ke kallonsa har ma da sauran abokansu, Ahmad yayi
dariya yace "Haka yace maka Umar?" Umar ya gyara xamansa yace "To for the past 4 days kullum sai na ga
motarsa a hayi" Abuturrab ya xaro ido yace "Ni kuwa?" Umar yace "Kai mana, yawanci kana ta daya side
din nake ganinka, kai akwai ranan da ma na kiraka ina jin ka bar wayar a mota and u didn't even follow my
miss call" Abuturrab yace "Subhanallah on a serious note ban lura ba...." Umar yace "To airport xa a bude
mana a hayi ne kullum muke ganin Captain a can" Murmushin yake kawai Abuturrab yyi yana kallon Nasir
dake kwance da drip a hannunsa yace "Barrister guda a gadon hospital, so how are u feeling now?" Nasir
ya jefa masa wani kallo yace "Kai ma baka wuce a kwantar da kai gadon asibitin ba ai" Dariya kawai
Abuturrab yyi, sun fi minti ashirin a dakin suna labarin duniya, daga karshe Ahmad ya sanar masu xa su
koma bayan sun ma Nasir addu'an samun lfya, a tare suka fito da Umar daga ward din don shi ma wucewa
xai yi, Abuturrab ya d'an kalli Ahmad dake bayansa suna magana da wani abokinsu da ya fito rakasu, ya
kalli Umar da har ya kusa fita reception din hospital, ya kara pace dinsa har ya isa gunsa yace "Kai me kake
xuwa yi hayi har kake ganina?" Umar yyi murmushi yace "A can fa Mahaifiyata take, so kusan kullum nakan
je can din" Abuturrab yace "Ohhh Allah sarki..." Umar yace "To kai wajen wa kake xuwa?" Abuturrab ya
d'an shafa kansa ya saci kallon Ahmad dake tahowa yace "Aboki nayi nima a can din" daga haka ya fiddo
wayarsa ya d'an yi gaba kamar xai yi answering call don bai son Umar ya ci gaba da maganan gaban
Ahmad. Abuturrab yana kallon Ahmad bayan sun hau saman titi yace "Gida xan sauke ka?" Ahmad yace
"Yeah..." Driving kawai Abuturrab ke yi, Ahmad dake kallonsa yace "Wajen wa kake xuwa a hayi Captain?"
Abuturrab ya kallesa da sauri cos the question came unexpected, ya dake yace "Ka yarda da Umar kenan,
he was just pulling my leg idan ba dai a train station ba ya gan ni wa gareni a hayi da xanje? Wa na sani a
hayi? Kawai dai idan mun hadu dole sai ya tsokane ni ne..." Ahmad na gyara xama yace "To na sani ko
budurwa kayi a can baka sanar min ba kake boye min, ai idan tayi tsami ma ji" Wani kallo Abuturrab ya jefa
masa yace "In rasa inda xanyi budurwa sai anguwar nan???" Ahmad na kallonsa da mamaki yace "Meye da
su 'yan anguwan, ba mutane bane su din? Or sai da aka halicceka specially sannan aka halicce su aka ce
maka? What's wrong with u Abuturrab? Why do u sometimes behave like...." Abuturrab yace "Illiterate
right?" Ahmad yace "Of course" Abuturrab yace "Fine, but do not forget everyone is entitled to his or her
opinion, ra'ayinka daban ra'ayina daban, kai xaka iya budurwa a can infact har ma ka aureta ku xauna a can
din, it's ur opinion, ni kuma last thing da baxanyi ba kenan a rayuwata, and this is my opinion, so stay
entitled to urs, and i stay entitle to mine also" Ahmad yace "Baxa ka iya aure a can ba sbda kafi su a wajen
Allah ko??" Abuturrab yyi masa wani shegen kallo yace "Wai Ahmad ance maka ni kai ne?? Ni fa ina da
class ina da taste, as in i am far beyond that ka daina yi min irin wannan maganan bana so wllh" Ahmad yyi
d'an murmushi bai kuma ce masa komai ba, Abuturrab yyi tsaki yace "Haka kawai sai kace kowa sai ya bi
ra'ayinka, kai mace ko min kazantarta da locality dinta xaka iya aurenta ku xauna lafiya, ni kuwa it's a big
No for me, bana walakanta 'yan adam kai shaida ne, sannan kasan ko kai baka kaini tausayin d'an Adam
ba, idan naga mutum na cikin damuwa ko wani yanayi more especially mace ina bakin kokarin ganin nayi
duk abinda xan iya yi ko a ina ne kuwa, even with my last card i can help, amma sai ka dinga hadani da su
kana wasu maganganu marasu ma'ana" Ahmad bai kuma ce masa komai ba har suka iso gidansu,
Abuturrab yyi parking, Ahmad ya juya yana kallonsa still bai ce komai ba ya bude motar ya sauka ya rufe
masa motarsa, tsaki Abuturrab yyi, yyi reverse ya bar layin kallon agogonsa dake nuna masa sha biyu da
rabi yyi ya nufi gida kawai....


07087865788.... Almost done with free pages
✍🏻


💖💖 *Jiddatul Khair*💖💖




_By khaleesat Haiydar_✍🏻




7.....

Fitowa Hansai tayi tsakar gida jin ana sallama, ganin aminyarta Zulai ta ce "Aa ashe Zulai ce, shigo daga ciki
mana" Zulai tace "Ina ta addu'ar Allah ya sa in sameki wllh" Hansai tayi dariya tace "Ai ko kin ci sa'a, don
yanxu haka shiri nake xan fita kasuwar tasha in saro kayan sana'ata" Zulai ta rike ha6a tace "Kin fara wani
sana'ar ne banda awara?" Hansai tayi shewa tace "Ai ni na kwan biyu ma banyi awarar ba, amma kilan
idan na fita yau dai in siyo har da waken suyan, yanxu su maggi, kubewa, kuka, daddawa... Kai duk dai
mahadin miya da kika sani nake siyarwa, ko kwana hudu ban yi da farawa ba, sannan ina sa ran fara
dillalanci kwanan nan" Zulai dake ta kallonta tace "Ikon Allahhh..." Hansai ta shiga d'an dakinta tana
murmushi, Zulai na biye da ita a baya, bayan sun xauna Zulai tace "To ina yaran?" Hansai tace "Bibalo
yanxun nan ta shiga makota, Ita kuma warcan gantalalliyar na can kwance wai ba lafiya" Zulai tace "To
Hansai wani labari dai nake ji a gari, shine nace bari dai in sa6o gyale in taho..." Hansai ta gyara xama tana
kallonta tace "Me ke faruwa? Wani labarin kika ji?" Zulai tayi kasa da murya tace "Yawo ake da ke wai
bayan an kawo gaisuwan wannan yarinya jiddah har an saka rana kina turata gun wani me katuwar mota
kullum sai ya xo kofar gidan nan, meye gaskiyan lamarin nan?" Hansai ta saki salati tana tafe hannu tayi
mici mici da ido tace "Amma dai Allah ya tsine ma duk wani me sa ido a duniya, da yaushe da yaushe na
turata gun me mota? Yau naga lalacewa, Jiya ne fa bata da lafiya shine ya siyo mata magunguna, kai ni
Hansatu jama'a basu da gadonka amma suna da gadon maganarka..." Zulai tace "To waye shi me motar ma
dai tukun" Hansai na huci ta lafto wani uban ashar tace "Duk wanda ya fasa sa min ido bai haifu cikin
uwarsa ba a garin nan, tunda isuhu ya rasuwa wani shege ne ya ta6a kawo min kwayar masara balle
shinkafa ko man kulli yace gashi ki ci kanki Hansai?? kawai sai don bawan Allah ya ga muna cikin matsatsi
da yanayin rayuwa yana xuwa yana taimaka mana domin Allah sai a sa mana ido a hau mana bakin ciki da
hassada a anguwa? Ni wllh ji nake kamar in siyar da gidan nan in bar gantalallen anguwar nan ko xan samu
ci gaba" Zulai tace "Ke ni duk ba wannan ba tsoho ne mutumin nan ko yaro?" Hansai ta ja tsaki tana gyara
xama tana huci tace "D'an yaro ne fa Zulai, ina jin ma saurayi ne bai ta6a aure ba, baki gansa ba bawan
Allah wllh...." Zulai tace "Gun jiddar yake xuwa?" Hansai ta kalleta da sauri tace "Waye kuma jiddah? ita a
wa xai xo wajenta? kema dai da wani xance wllh, xuwa fa yake idan yaga tana tuyar awara bakin titi ya
mika mata kudade masu yawa ta kawo mana, ai ya san halin da muke ciki, d'an gayu ne fa sai kin gansa me
kuma xai yi da wata jiddah kamar warce uwarsa tace masa je ka ka gani?? Haba Zulai, wllh da kyar ma idan
ba daga Habuja yake xuwa ba don d'an gaye ne" Zulai ta d'an leka waje a hankali tace "Bacci jiddar take?"
Hansai tace "Oho...." Daga haka ta mike ta fita, bude labulen dakinsu jiddah tayi ganinta a kwance tace
"Wannan shegen kwanciyar baxai fissheki ba idan xa ki tashi ki kwashi bokitai ki fita gashi can an kawo
famfo bakin titi ki jido mana ruwa ko na alwala ina jin babu a gidan nan, tun safe kin wani makale daki a
kwance kamar ruwa" daga haka ta fice daga dakin ta koma nata, jiddah ta mike xaune daga kan darduman
da take a kwance bayan tayi sllhn azahar, duk da jikin nata ya mata sauki, amma idan ta tashi jiri take gani
ga yunwa dake dawainiya da ita, tun safe kunu kadai ta sha kosan da aka siyo ma bata ga

7 / 108