Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
ne ya cikasa ya sake juya bayan
takardan that is plain, Bude baki yayi with so much surprise, bai san lkcn da yayi murmushi ba ya rungume
hannunsa, so tana da irin wannan wayon ashe, bai bi ta ba sabida yasan xa ma ta dawo ne, ya tafi gefen
gado ya xauna, Jiddah ta jingina da kofar parlonsa ta xame kasa tana yarfe hannu, gaba daya a tsorace
take, sai jiran fitowarsa take anytime amma har sannan bai fito ba, bin babban parlon ta dinga yi da kallo
kamar xata hango makullin kofar, har bayan minti talatin bata gansa ya fito ba, gajiya tayi da xama a bakin
kofar, ta mike a hankali tana leka kofar dakin nasa, can dai ta karasa bakin kofar ta leka ciki don kofar ba a
kulle yake gaba daya ba, kwance ta gansa waya kare kunnensa, ta juya da sauri ta koma inda take xaune
kamar xata yi kuka, har sha biyu saura Jiddah na xaune gefen kofar, bacci ne ya fara damunta, mikewa tayi
ta tafi kan kujera ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa, can cikin dare taji ana lalubata, ta mike a tsorace
ganin duhu a parlon tace "Wayyo Allah na" Muryarsa taji yace "Ina takardan yake" Jikinta ma rawa tace
"Yana cikin hulana" Xata cire hulan ya rigata cirewa ya ga takardan a kanta ya dauka sannan ya saketa ya
koma dakinsa ya kulle kofar, har lkcn gabanta faduwa yake ta mike xaune tana bin parlon da kallo don ko
alamar haske babu, a hankali ta mike tana neman hanya har ta isa kofa ta murda taji a kulle har sannan,
jingina tayi da kofar kamar xata yi kuka, can ta juya ta koma saman kujeran ta kwanta, nan da nan bacci ya
sake dauketa, kiran sallan asuba ne ya farkar da Jiddah, ta tattaba lallausan abinda taji a jikinta, kofar daki
aka bude da sauri ta rufe idonta don hasken dakin ya hasko parlon, tana ji ya bude kofar parlon ya fita, lkci
daya kamshin turarensa ya gauraye parlon, sai bayan kusan minti biyar ta cire duvet din jikinta ta mike a
hankali jin xa a tada sallah, ajiye duvet din tayi kan kujeran ta nufi kofa ta bude ta fita xuwa dakinta. Karfe
takwas saura Jiddah ta farka daga baccin da ta koma bayan tayi sallan asuba, mikewa tayi ta shiga bandaki
sai da tayi wanka ta wanke baki sannan ta wanke bandakin ta fito, tana gama shiryawa ta hau gyaran
dakin, bude kofa aka yi ta juya da sauri, calmly yace "Ki sameni kasa" daga haka ya rufe kofar, ta gama
abinda take sannan ta sauka kasa, yana xaune parlor yana kallo, agogon wrist dinsa ya kalla yace "Na baki
minti talatin ki je ki dafa abinda xa ki ci...." tsayawa tayi tana kallonsa, ganin bata motsa ba ya daga kai ya
kalleta, da sauri ta juya ta wuce kitchen din ya bi ta da kallo, indomie ta dafa ta ci a kitchen din ta wanke
plate sannan ta fito, ya kalleta ya nuna mata karamin travelling bag dinsa da ya sauko da shi parlor yace "Ki
je ki hada kayanki kala biyu da duk abinda xa ki bukata, kar ki bata min lkci, ki saka Jilbab idan xa ki sakko"
A hankali tace "Ina za mu je kuma, amma ba jirgi xa mu hau ba ko??" ganin irin kallon da yake mata ta dau
travelling bag din ta juya ta wuce sama, kayan nata ta hada sannan ta sauko kasa a sanyaye, Hijab ne har
kasa jikinta, ya mike ya nufi kofa ta bi bayansa rike da jakar. Parking Abuturrab yayi kofar gidansu Ahmad,
Jiddah ta juya ta kallesa ganin inda suka xo, wani farin ciki taji a ranta, bude motar yayi ya sauka, ita ma ta
sauka ta bude back seat ta dau jakar kayanta, ai da ta san nan xa su xo da ta debi kaya da yawa, ganin ya
nufi gate din gidan ta bi bayansa da sauri, gaba daya farin cikinta ya kasa boyuwa, sai kallon kofar Maman
Abdallah take har suka shiga main parlor din gidan, Umma ta fito daga dakinta ganinsu tace "Aa daga ina
haka kuma" Yayi kasa da kai yace "Daga gida Umma" nan ya gaisheta, ta amsa tana kallon Jiddah tace
"Sannu da xuwa Jiddah..." Gaisheta Jiddah ma tayi tana mayar mata da murmushin, Umma ta amsa tana
tambayarta ya gida, Jiddah tace "Lafiya lau" Umma tace "To kun ma karya kuwa wannan sammako haka?"
Abuturrab yace "Eh mun karya, i brought her ahead of the wedding...." Umma da taji dadi har ranta don
wnn shine right time da xata fahimci gaskiyan abinda Aunty ke fada tace "To maa sha Allah, that's very
good" Yace "Kudin ankon kuma wa xa a tura ma?" Umma tace "Anko kuma?" Yace "Ummi ce tayi maganan
ankon ran Friday" Umma tace "Kyale Ummi, ae ta riga ta mata, har dinki an bada" Yace "Toh Allah ya saka"
mikewa yayi yace "Sai anjima Umma, xan wuce kano da yamma in sha Allah, ranan alhamis xan dawo"
Umma tace "Toh Allah ya tsare, shi ma Ahmad din ranan laraba xai shigo..." Abuturrab yace "Ehh mun yi
waya da safe, haka yace min" Ya d'an kalli Jiddah sannan ya nufi kofa yana ma Umma sallama, Umma tace
"Toh baxa kiyi masa rakiya ba Jiddah?" D'an murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Tashi
ki je" a hankali ta mike ta nufi kofa ta fita, cike da kasaita yake tafiyar, ta bi sa da kallo, bin bayansa tayi har
suka fita gidan, ya bude driver seat xai shiga sai kuma ya tsaya yana kallonta don makalewa tayi jikin gate,
suna hada ido ta sauke nata idon, yace "Kina son wani abun ne" Ta d'an turo baki tace "Umma ce tace in
raka ka" ya shafa kansa yace "Idan Umma tace ki shirya ku je can gidan kice mata baki jin dadi baxa ki iya
xuwa ba" Tana kallonsa tace "Toh ka tayani gaya mata mana" ya daga kafada yace "Toh ki tafi ni ba
ruwana" Daga haka ya bude motarsa ya shiga ya tada yayi reverse, a hankali ta juya ta koma cikin gidan,
daren ranan Maman Abdallah na parlon Umma tare da mai aikin gidan suna ta hira, duk sbda Jiddah ta
shigo kuma, sai kusan karfe goma maman Abdallah ta bar parlon, duk yan matan gidan na can gidansu
Abuturrab, mikewa Jiddah tayi a hankali tayi ma mai aikin sai da safe ta wuce dakin da Umma ta sa ta ajiye
jakarta, tuni Umma ta tafi ta kwanta tana tunanin where to start from coz ko kadan bata yarda da Jiddah
da Abuturrab ba, Jiddah tayi wanka ta sauya kayan jikinta xuwa na bacci sannan ta kwanta. Washegari
monday Jiddah ta taya Huraira mai aiki girkin breakfast, sosai ta sake a gidan ba kamar gidan su Abuturrab
ba duk da Seeyama bata nan, Karfe sha daya na safe ta raka Umma kasuwa da driver, basu dawo gida ba
sai kusan azahar, Jiddah na sallah ta kwanta don sun ci abinci a restaurant, da yammacin ranan Seeyama
da Aisha da Safiyya suka xo gidan amsar ma Aunty sako wajen Umma, Seeyama tayi murnan ganin Jiddah a
gidan, Umma tace "Sai ki shirya ki bi su Jiddah, idan na je anjima da daddare sai mu dawo tare" Shiru
Jiddah tayi ta kasa ce mata komai, Seeyama tace "Ki tashi sister Jiddah Aunty na jiranmu" Mikewa Jiddah
tayi a ssnyaye ta saka Hijab dinta, Driver Umma ta sa ya mayar da su can gidan saboda Jiddah, tun da suka
sauka motar gaban jiddah ke faduwa ta dai bi bayan Seeyama rike da handbag dinta har suka shiga parlor,
dai daikun baki ne da suka xo biki a parlon, Jiddah ta sunkuyar da kanta ta nufi bangaren Ummi, tana shiga
parlon taga mata biyu a xaune, Xaunawa kasa tayi ta gaishesu, duk suka amsa, ba a dau lkci ba Ummi ta
fito daga daki, ganinta tace "Daga ina haka, ina Aliyun?" Jiddah ta gaisheta sannan tace "Tare muka xo da
su Seeyama" Ummi tace "Ohk toh ki shiga can ciki" mikewa Jiddah tayi ta wuce bedroom din Ummi, Hajiya
Murja kawar Ummi tace "Kaddai ita ce matar Aliyun?" Ba tare da Ummi ta kalleta ba tace "Ehh ita ce"
Hajiya Salaha tace "Allah sarki, ashe yarinya ce ma, toh Allah ya basu xaman lafiya, ga ta dai kamar ba sa
wa ba hanawa" Ummi ta d'an yi murmushi kawai, Seeyama ce ta shigo parlon tace "Ummi Aunty Jiddah ta
shigo nan" Ummi tace "Tana ciki" Seeyama ta shiga sai ga ta sun fito tare da Jiddah suka fita parlon, sosai
gabanta ke faduwa tana tsoron kar ta hadu da Aunty har suka shiga dakinsu Ramlah, Ramlah na ganin
Jiddah ta washe baki tace "Aunty Jiddah sannu da xuwa" Jiddah ta xauna tana murmushi tace "Ya gida"
Ramlah tace "Lafiya lau, yaya fa?" Jiddah tace "Ya tafi kano" Seeyama tace "Shi sa ya kai ki gidan Umma?"
Kai kawai Jiddah ta gyada mata. Suna nan xaune har aka kira magrib, bude kofar dakin aka yi Aunty ta leko
tana cewa "Wai baxa ku fito kuje ku yi wanke wanken can ba dake bakin pampo gashi har anyi magariba,
ko waye xai maku? Ai sai ku hakura xuwa gobe ku sakankance tunda nasan yan kauye masu wanke wanken
xa su iso" Jiddah dake kan darduma ta sunkuyar da kai gabanta na faduwa, tsit Aunty tayi ganin Jiddah kan
darduma, can tace "Ko da yake tun safe ai ku ke ta aiki, ke ya kike da suna??" Jiddah ta kalleta, Aunty tace
"Ehh da ke nake kike kallona haka, tashi ki fita ga wanke wanke can bakin pampo kije ki wanke" Mikewa
tayi da sauri, Seeyama ta mike tace "Ta barshi kawai xa mu yi aunty" Aunty ta jefa mata wani kallo tace
"Toh ita xa ta yi, ku kuma xan aikeku yanxu tare da driver xa ku je min siyayya a supermarket" Jiddah ta nufi
kofa ta bi gefen Aunty da ta bi ta da wani kallon tsana ta fita, kitchen Jiddah ta nufa ganin kofar kitchen din
a bude ta fita taga uban kayan wanke wanke a bakin pampo ga omo da soso, ruwa ta tara ta fara wanke
wanken, ba a dau lkci ba sai ga Aunty ta shigo kitchen din ta dinga fitar da plates wankanku tana ajiye su
kan marasu wanki, ita dai Jiddah bata ce komai ba, har tukwanen sai da ta fitar da su sannan ta dau soson
waya ta jefa mata tace ki tabbatar kin bi bayan tukwanen nan kin wanke su fess, xuwa gobe kuma xan san
yanda xanyi da ke, daga haka ta juya ta koma ciki, Jiddah dai ta ci gaba da wanke wanken da take a
sanyaye. Ba ita ta bar bakin pampon nan ba sai kusan karfe tara da rabi, duk ta gaji ga uban yunwan da
take ji, bbu kowa parlon sai yara dake ta wasa, iyayensu kuma na can sama, Jiddah ta rakube jikin kujera
tana jin kanta na mata ciwo, har ta mance rabon da tayi irin wannan aikin, tun bayan rabuwanta da Hansai,
Aunty ce ta shigo parlon da sauri tana sanye da Hijab, har ta nufi kitchen sai kuma taga Jiddar a rakube a
parlor, tana kallonta tace "Yauwa mu je ki rakani xan amso sako yanxu"
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
*Mîkyããj_Sããdy Beauty Soap*
*Hy my beautiful people ina gaisuwaku karka'de kunnuwanku da kyau ku ji💃🏻ina mai sanar muku da cewa
akwai gara6asa me kyau ta musamman ga wanda suka saba sayen sabulunmu da ma wanda zasu fara
saya🥰, akwai ragin kaso 20% bisa dari 100% ga wanda suka saba saye, sannan akwai ragin 10% bisa ga
masu sha'awar fara saye🥰, akwai farashi mai sauki ga 'yan sari, me yapi wannan dadi kam🤔ki sayi guda 4
kanana a baki kyautar daya, ki sayi guda uku manya a baki kyautar karami daya, ki sayi bucket biyu a baki
kyautar babban rubber daya😍 kema da kike da burin saya ku'dinki bai kai ba😰to ga naki, ki kawo customers
uku ki karbi naki kyautar Sabulun😍😍*
*Kawata 'yar 'kwalisa me kike jira,ita mace fa kullum cikim yin ado da 'kãwa take😍 ya kamata ki yunkuro
wajen ganin kin rabu da wannan kurajen da tabo tabon fuskan nan haka🥺, kinga kema sai a saka ki a layin
masu 'kwalisa da bajakolin ado💃🏻😍uwar gida a daure ayi gyaran jiki, sbd karbar goron a wajen me gida🥰,,
ina amaren bayan sallah ku pito ku sayi naku Sabulun kuje kuyi ta wanaka hmmm 😍kamshi kawai zaku yi
tayi kaca kaca😍😍, laushin fata Baja baja😃😂😂a yunkuro azo a karbi kayan gyaran jiki tare da sabulun gyaran
fata a wurin _Mîkyããj_Sããdy_🥰*
*Duk wanda suka gwada Sabulun mu sun san babu 'karanta a ciki🥰in dai fannin gyaran jiki ne to
sabulunmu shine amsarku,, shi ke mai da fata ta zama babu Pimples, Acne, Spot, Stretch Mark, da Duk
wata matsala da ta shafi fata,, akwai lightening, nd glowing😍*
_*In kina son jikinki yai su6ul da shi, fata tai santsi da sul6i, ki yi haske me aji, 'kamshi kaca kaca ko ta Ina,
ki ta fresh abunki hankali kwance ki zama Wankan madara yauqin zuma😍💃🏻Anty madam😃To ki mallaki 3d
(Extra Whitening Soap, Ko da kudinki sai da rabonki hajiyata)💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*_
*Akwai hadin:*
*Mai da tsohuwa yarinya*
*Uwargida ta koma amarya*
*Amarya ta koma tamkar 'yanmata*
*'Yan mata su koma 'yan dagwai²*
_Ga masu bu'kata sai su tuntu6emu ta kafar sadarwa kamar haka;_
_Call/WhatsApp:08061570778_
_IG@mik_yaaj_saady_
Mikewa Jiddah tayi tsaye tana kallonta, Aunty da har ta nufi kofa ta juyo ganin Jiddah bata biyota ba ta
hade rai tace "Ba magana nake maki ba" Jiddah tace "Ban saka hijabi ba" Aunty tace "Nan nan ne ba nisa
muje baxa ki rasa mayafi a tsakar gida ba" Jiddah bata ce komai ba ta nufeta, Umma ce ta shigo parlon da
sallama, Aunty ta koma gefe tana yake tace "Sannu da xuwa Hajiya Ramlah" suka gaisa Umma tace "fita xa
ki yi halan" Aunty tace "Ehh wllh sako xan amso nan bakin titi, da har nace mu je da Jiddan tace min
Hijabinta na sama" Umma ta kalli Jiddah tace "Toh ki tafi saman ki dauko hijabin naki" Aunty tace "Aa bari
kawai inje ae nan bakin titi ne" bata jira cewar Umma ba ta fice daga parlon tana jin wani mugun takaici,
Umma ta kalli Jiddah tace "Kin ci abinci kuwa?" Jiddah ta girgixa masa kai, Umma tace "Toh saboda me, ke
ba sai ki je ki diba ba, Ummi na sama ne?" Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace "Mu je" Jiddah ta bi
bayanta suka wuce sama, Bangaren Ummi suka shiga, bayan Umma ta gaisa da yayarta tace "Yaya wai bata
ci abinci ba" Ummi ta kalli Jiddah tace "Ae nayi tunanin tana tare da su Ramlah ne, kuma an kai masu
abinci tun daxu, taje can dakinsu ta diba" Umma ta kalli Jiddah tace "Ki je ki deba abincin a can" Juyawa
Jiddah tayi ta fita, Umma na kallon yayarta tace "Naga kamar baki saki jiki da ita har yanxu ba yaya" Ummi
tace "Aa ko daya, baki ganin ita ma ba maganar take ba" Umma tayi murmushi tace "Ae kam ni muna hira
da ita" Ummi tace "Did u know what is baffling me Ramlah?" Umma ta girgixa kai tana kallonta, Ummi tace
"Yanda Aliyu ya mayar da mu shashashai ya maida mu wasu 'yan yara, kinsan da gangan yaje yyi ma kansa
aure da yarinyar nan?" Ummi tace "Me yasa kika ce haka yaya" Ummi tayi wani murmushi tace "Ai ni na
haifesa ba shi ya haifeni ba, bai kuma isa yyi deceiving dina ba, he intentionally did what he did, abubuwan
da nagani game da shi da yarinyar bai yi kama da abun da mutum yyi ba da son ransa ba, kinsan satinsa
nawa rabonsa da gidan nan yanxu?" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Nima ae ya daina xuwa min
yaya..." Ummi tace "Toh yayi kyau... Xai gane bashi da wayo" Umma tace "Amma duk da haka akwai ayar
tambaya fa a kan xaman da suke, don duk inda kika ji kishin kishin din magana da akwai kamshin gaskiya,
ina jiran Ahmad ne yanxu inji matsayin auren nasu" Ummi tace "Ni ma dai nayi shiru ne kawai, amma ban
aminta da xaman nan ba" Umma tace "Toh kin ga, don dama da bakinsa yyi ta cewa xae rabu da ita, na
dinga hanasa tare da Abbansa to wa ya sani ko watsar da xancenmu yyi" Ummi tace "Ni kuma haka kawai
naji ina son rabuwan nasu Ramlah" Umma dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta sauke ajiyar xuciya tace
"Allah dai yyi mana me kyau, kuma bana tunanin ya sa ta a karatu har yanxu, and she doesn't look happy
always...." Ummi tace "Sannan ina ma son xanyi magana dake tun kwanaki, kinga lamarin rayuwar Aliyu?
dama ina son in cire idanuwana da komai na a kai, sai yaje ya kara rike warce yake ganin ta fini daraja da
hannu bibbiyu, ita yake ga xai iya komai na sirrinsa, ita yake ga xai fi ji da yarda da maganarta, to suje su
karata, ni gaisuwan da yake min duk sanda yaga dama ma ce masa xanyi na yafe masa ya daina" Umma
tace "Wannan ba magana bane yaya, tun farko ke kika xuba ido aka janye maki shi, Ahmad ya sha kawo
min wannan same complain din, idan baki manta ba akwai wani lkci da na maki magana a kan hakan kika
ce min ai ba komai duk daya ne, wnn mata ni ban ta6a ganin makira irinta ba..." Ummi ta girgixa kai tace
"Aa ba ruwanta, ai shi ba yaro bane ya kuma mallaki hankalin kansa, he knows what is right from wrong,
kawai dai hakan yake ga yafi masa alkhairi, sai yaje ya karata, amma ina dab da yi masa wankin babban
bargo a gidan nan" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Ki dai yi hakuri yaya, Allah xai ganar da shi, wankin
babban bargo kuma sai dai ki hada har Kishiyarki don munafuka ce" Bayan kusan minti talatin Umma ta
gama abinda ya kawota, sallama tayi da yayarta har ta nufi kofa tace "Toh in tafi da Jiddar ne don can ya kai
ta" Ummi tace "Aa wannan kuma ban sani ba" Umma tace "Naji xa su fita saloon gobe, kawai su tafi tare
ita ma tayi gyaran gashin idan ya so ko driver sae ya maido min ita goben" daga haka tayi ma yayarta
sallama ta fita dakin. Kwana dayan da Jiddah tayi gidansu Abuturrab ta fadi ma yan garinsu gashi gidan ya
cika da mutane yan biki, Aunty tayi mugun saka ta gaba tun da garin Allah ya waye, ko wani aiki da aike ita
ake sa wa, da ta xauna xata tasota gashi abincin kirki