Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
Aliyu ya nufi bangarensa ya shiga parlor ya tadda Aneesah xaune tana shan lemon fata, idan ta
sha sai ta jefar da fatan akan farantin da aka dauro lemukan a kai, yana mata wani irin kallo yace "Aneesah
na sha gaya maki idan xaki ci abu plss ki daina ci min a parlor i detest that..." Ta kallesa daga sama har kasa
tace "Naga dai ba ni na shigo da lemun ba kai ka kawo abunka ko" Yace "For heaven sake ya xa ki maida
min parlor wajen cin abinci, what's d essence of d dinning area downstairs" Bata kuma basa amsa ba ta
dau wani lemun tana sha a hankali tana jefar da kwallon kan faranti, gajeran wando ne jikinta da yar vess,
yace "Tuwo grandma dita ke son ki girka mata ynxu" Ta sauke kafarta daga saman kujeran tace "Tuwo?"
Yace "Ehh" wani dariya tayi tace "Yanxu kai ka ta6a ganin ko indomie na girka a gidan nan balle tuwo, wllh
Aliyu ban san haka kake da takura ba sai da muka yi aure, kullum sai ka samu matsalar da xaka billo da shi
idan ka dawo weekend, kace can datti, nan datti, can wari nan wari?? sannan ma tsaya tukun, ni ka gaya
min xaka yi baki a gidan nan? To kaga baka sanar da ni ba, don da ka sanar dani akwai wata kawata chef sai
in gayyato ta ta min girki in biyata, amma waye xai maka wannan wahala da tsakar ranar nan, beside ba
naga tare da Me siyar da doya da dankali ta xo ba, ai ita ta sa6a wahala sai ta tashi ta shiga kitchen din ta
girka masu in yunwa suke ji, don wllh wllh baxan iya ba, in ma ji da gajiyar wankin bayin da kasa nayi daxu
mana" Kallonta ya dinga yi kafin ya juya ya fita daga parlon ta bi sa da wani shegen harara tana dauko
wayarta dake ring, d'an xaro ido tayi ta katse wayar sannan ta saka shi a flight mode. Eatry Abuturrab ya
tafi ya siyo take away din tuwo da gasasshiyar kaza, Hajja ta dinga washe baki bayan ya shigo masu da
ledan tace "Allah maka albarka Aliyu, sannu kaji, matar taka bata yi girki bane?" Yace "Bata yi ba" Hajja
tace "Toh Allah ya kyauta, haka fa Hafsah ta dinga yi ma Usman bata son girki" Abuturrab ya kalli Jiddah
dake kwance ta juya masu baya nan ko takaici ne duk ya bi ya isheta tayi fashin makaranta, xaunawa yayi a
dakin Hajja tayi ta jan sa da hira yana responding har aka kira la'asar, Jiddah ta sauka kan gadon ta shige
bandaki ya bi ta da ido, Hajja ta kyabe baki murya can kasa tace "Uwar rikon ce fa ta kitsa mata karya da
gaskiya, kaga ko yar cin cin din da alkaki ta ki ci wllh... Tun daxu sai nukurci take, taki sakewa" Abuturrab
yace "Kyaleta, a nan xaku kwana" Hajja ta gyara xama tace "Atoh dai" mikewa yayi ya fita don xuwa yayi
alwala ya wuce masallaci. Har kusan isha Jiddah bata ga alamar Hajja xata ce su tashi su tafi ba, ga wani
abincin Abuturrab ya kawo, bayan ta idar da sallah tana xaune kan darduma a hankali tace "Hajja wai baxa
mu wuce ba?" Hajja tace "Ke ba fa gidan 6are na xo ba, bari kiji in gaya maki, ni wllh bansan bakin hali
gareki ba sai yau, gidan jikana ne nan fa, babu ruwanki da sanda xa mu wuce, ke dai iyakarki ba rakiya ba,
xan kawoki inda xa a cuceki ne? Ni fa na rainesa yana karami, idan ban xo gidansa ba ina xanje, kuma a nan
xan kwana wllh don xuwa gobe da safe nake son ganin iyakar xabiyar matarsa da ta xo ta gaishe mu a
tsattsaye har yanxu bata sake shigowa ba, dadin abun kuma jikana ya saurareni gashi muna ta hiran yaushe
gamo da shi don haka sai Allah ya kai mu gobe xan nuna mata ni er banxa ce" Jiddah ta ji kamar ta fashe da
kuka, lkci daya hawaye ya kawo idonta ta mike ta koma can karshen gado ta xauna, Hajja ta kwashi take
away din da suka ci abinci ta fita xuwa kitchen, Sai a sannan Jiddah ta fashe da kuka ta hade kanta da
gwiwa, bayan kusan minti goma Hajja ta shigo dakin tana hura hanci tace "Tirrrrrr, ashe kazama Aliyu ya
auro? Ke kinga kitchen dinta duk wari kuwa? Wllh da nasan haka kitchen din yake ni baxan ma fara shan
ruwan gidan nan ba sai dai a fita a siyo min a waje, a garin yaya mace xata bar kitchen dinta haka ni Dije?
Wllh sai da tsoro ya kamani, yaushe Aliyu shi ma ya lalace da son kazanta? A yanda na san sa a da fa har
tunani muke ko aljanun tsafta ne suka auresa, to naga duk ya lalace ya xuba ido kitchen dinsa ya ru6e duk
wari" Jiddah dai bata ko kalleta ba, Hajja ta xauna tayi shiru alamar dai tunanin kitchen din take kuma abun
ya dameta, can tace "Tirrrr" Sai kuma tace "Huhuhu kazama ce wllh, kwanukan duk wari naji suke, ni
kamar har da kiyashi naga suna yawo a kitchen din, ga dai kitchen har kitchen" Sai kuma ta kalli Jiddah
murya can kasa tace "Wllh ban san ta ina xanyi wanke wanken bane kar inje in jika kitchen din abu ya kara
lalacewa ai da nayi, amma ke tunda naga duk kun saba ki daure domin bama tsafta hakkinsa kije kiyi
wanke wanken nan, wllh babu kyan gani kinji na rantse, to ko dai ba mace ya auro ba" Jiddah tace "Hajja
bata sa ni in mata wanke wanke ba fa" Hajja ta kara yin kasa da murya ta marairaice tace "Na sani er nan,
duk don a fita hakkin tsafta ne, wllh da Masar ne kitchen din nan ya tashi aiki, sai ma a iya rushesa kawai,
domin Allah ki tashi ki je ki gyara, ai ba don yar iskar xa muyi ba, kawai don Allah, don tsafta xa mu yi"
Jiddah ta dinga kallon Hajja, Hajja ta mike tace "To ai Shikenan bari in kwashi kwanukan in fita da su tsakar
gida in wanke don a gaskiya idan xa su kwana a haka ni baxan kwana gidan nan ba ba ruwana, baxan ci
amanar tsafta ba a gaskiya" Ganin da gaske fita xata yi Jiddah ta mike tace "Toh naji xanyi" Hajja ta koma ta
xauna tana huci, Jiddah ta fita dakin, babu kowa parlon ta shiga kitchen din, tafi minti uku a tsaye tana
tunanin ta inda xata fara, sai yamutse fuska take, can dai ta fara hada kayan wanke wanken waje daya.. Har
karfe tara Jiddah na kitchen din, lkci daya kitchen din ya dawo fess duk ta gyara ko ina ta goge, tana wanke
wajen sink din aka dauke wuta, lkci daya kuma taga kamar an kunna hasken waya a parlor, ko gama
dauraye wajen bata yi ba ta kashe tap din xata fito kitchen din da sauri, ta kusa cin karo da shi, ta ki
tsayawa xata bi ta gefensa ya rikota, kwace hannunta take son yi, ya ja ta xuwa kitchen din ya kulle kofar ya
jinginar da ita jiki, ta buda ido sosai tace "Meye haka" ya kife wayarsa saman cabinet din kitchen ta daina
ganin hasken komai, a tsorace tace "Wai meye haka" yace "Me ya hanaki cin abincin da na kawo maku??"
Xuciyarta na bugawa tace "Ni wllh na ci kadan, ai nace mata na koshi ne, amma kuma na ci ai..." Gaba daya
ta daburce, yace "To ni dodonki ne da kika ce baxa ki kwana a gidana ba" Ta dake tace "Toh ai ba dole sai
na kwana a gidanka ba, ko ya xa ayi in kwana a gidan wanda ban sani...." xaro ido Jiddah tayi jin goshinsa a
nata tana juyo breathing dinsa, sai kuma ta rufe ido a tsorace tana turasa da duk karfinta tana son kwace
kanta amma ko gezau, bata ankara ba sai ganin abun tayi kamar a mafarki, and he gave her a perfect
french kiss da ya gigitata ya rikitata, ba don rikon da yayi mata ba da tuni ta kai kasa dama.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
*EXCLUSIVE FABRICS &MORE* provides you with exclusive, and Affordable fabrics such as laces,
Ankara,materials shoes,bags and so much more on wholesale and retail EXQUISITE, AND AFFORDABLE
THANK U
LOCATION: LAGOS
*EXCLUSIVE_FABRICS_AND_MORE* Na siyar da kaya kamar Laces, Atampopi, Materials, Jewelleries,👡👠👜👛
da dai sauran su
Tana maraba da masu siyan daya koh sari
Location : Lagos
Tana aika kaya duk inda kake da yardan Allah
WhatsApp me via.... 09080058848
Lkci daya Abuturrab ya saketa ta dalilin hasken wuta da ya dawo kitchen din, ta rufe bakinta a rikice ta juya
ta bude kofar kitchen din ta fice da gudu, Aneesah na tsaye parlor bayan ta kunna solan gidan, ta bi jiddah
da kallon mamaki barin yanda taga ta rufe bakinta da hannu har ta wuce sama, can ta kalli kofar kitchen
din, sai kuma ta tafi can da sauri ta tura kofar xata shiga suka kusa cin karo da Abuturrab xai fito, ya d'an
buda ido kafin yace komai ya juya mata baya, walking toward the gas yace "Na xata kinyi bacci ai...." Daga
sama har kasa ta dinga kallonsa, yana tsaye gaban gas din bai yarda ya juyo ba tace "Me kake yi a kitchen
Captain?" Yace "Gyaran kitchen din da kika bari kaca kaca" Sai a sannan ta bi kitchen din da kallo taga sai
walkiya yake, ko ina yayi fess, sake kallonsa tayi tace "Who just left the kitchen now?" Ya dau lighter kamar
xai kunna gas din yace "The person that helped in transforming the kitchen back to it normal sef..." Tace
"To wannan juya min bayan da kake na meye haka?" Wani boyayyen ajiyar xuciya ya sauke ya daga wayarsa
da ya fara ring duk da Ahmad ne ke kiransa ya kai kunne still backing her, Aneesah ta gaji da tsayuwarta
ganin ba gama wayar xai yi ba gashi yayi backing dinta ta juya ta fice daga kitchen din, sai a snn ya d'an
waiga, ya dau mug ya bude flask ya xuba ruwan xafi ya saka Lipton, sannan ya dau lime din da yake siyowa
a kitchen din ya yanka uku yayi squeezing a ruwan lipton din... Hajja ce tsaye kan Jiddah dake xaune kasan
dakin ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, rai bace Hajja tace "Naga abinda ya fi karfina ni Dije, yanxu
baxa ki bude baki ki gaya min me aka maki ba in san ta inda xan fara, matar gidan ce ta maki wani abun
koko?" Jiddah taki dagowa hawaye sai sauka idonta yake duk jikinta yayi sanyi, Hajja bata sake ce mata
komai ba ta juya ta fita daga dakin ta tafi can bangaren Abuturrab, da karfi ta kwankwasa kofar, Aneesah
dake xaune saman kujera a parlon tana kokarin dialing number Aunty ta kalli kofar, jin an sake kwankwasa
kofar kamar xa a cire ta mike a d'an fusace tace "Wai waye wannan" Tura kofar parlon Hajja tayi ta shigo
ciki, tana huci tace "Ni dai kafin ince komai ina son sanin waye mai gidan nan tukun??" Aneesah tace
"Haba dai.. ai ba girmanki bane shigowa wannan bangaren Hajja, duk abinda kike so da sai ki jira a fito....."
Wani xagi Hajja ta mulmula mata tace "Ke har kin isa ki gaya min yanda xanyi a gidan jikana? Kaji min yar
banxa, Ashe dama bayan bak'ar kazanta har da rashin kunya da fitsara kika iya ban sani ba? To wllh na fasa
komawa wannan gantalallen Masar din dai tunda ba uban da na hada dasu, ina nan kasata Najeriya sai na
nemo ma jikana auren tsaleliyar mata me bama tsafta hakkinsa, yar gayu me kamshi xan samar masa ba
irinki kazama me wari ba, mata daga aure ko wata biyu ba ayi ba kin hallakar min gidan jika da kazanta ko
ina banda tsutsa babu abinda yake fita, ko irin kamshin turaren nan na amare gidan nan bai samu gatan yi
ba, to tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin mace kazama aminiyar dauda irin ki ba, amma duk ba
wannan ya dameni ba, ya xan sa yarinya karama wanda kika kusa haifa ta tsaftace kitchen din da kika
halaka yake fitar da tsutsa kuma ki saka min ita kuka babu gaira babu dalili??" Aneesah dai na tsaye sai
kallon Hajja take baki bude with shock, Hajja tace "Ba kya kalleni kamar shashasha ba dama, wllh dole in
nemar ma Aliyu mata me tsafta da son kamshi dai dai shi, ina ta kallonsa ganin ya d'an rame ashe kaxantar
ki ne ke tsotse mana shi, to Allah ya isa wllh, mu kaf xuri'armu babu kazami...." A fusace Aneesah ta nufi
kofa ta fice fuuuu, Hajja tace "Uwar kazaman Najeriya kawai, mata haka kazama na bugawa a jarida, dubi
farin kafet din parlon nan fisabilillahi yanda ya fara fita hayyacinsa, parlon ma naji kamar karni yake wllh,
ko da yake dai ba ruwana bari inyi shiru, ba abinda Usman ya aikoni inyi a gidan nan ba kenan, amma da
yau kinji maganganu a kan kazantarki wllh" Aneesah na sauka downstairs ta tadda Abuturrab xaune ya
gama shanye cup din Lipton da ya hada, tana shigowa parlon ta rushe masa da matsanancin kuka tace
"Aliyu dama grandmum dinka xuwa tayi ta ci mun mutunci ta ci xarafina har gidana? Dama haka kuke ban
sani ba?" Kallonta ya dinga yi don bai san me ya faru ba, sai ga Hajja tana sakkowa tana cewa "Wllh kinci
albarkacin ba abinda Usman yace in xo inyi a gidan nan ba kenan, amma yau da na maki bankada iri iri,
kuma gida muna nan babu yanda kika iya da mu tunda ba wani ya haifo min Usman din ba har Allah ya
basa Aliyun" Da mamaki Abuturrab ke kallon Hajja yace "Me ya faru Hajja?" Tace "Me kuwa baxai faru ba
Aliyu, daga na tura Jiddah ta farfado da kitchen din da ta fara hallakarwa kawai sai ta saka min ita kuka na
rasa abinda tayi mata, yanxu haka yarinyar na can tana rusa kuka ta inda take shiga ba ta nan take fita ba
kuma taki gaya min menene, da kyar fa Ramlah ta amince ta biyoni, yanxu in maida mata yarinya idanuwa
a kumbure me kake tunanin xai biyo baya matar da ba mutunci gareta ba kowa ya san da haka..."
Abuturrab ya d'an saci kallon Aneesah, lkci daya ta sake fashewa da kuka tace "Wllh baxan kwana gidanka
ba yau Aliyu, ni ai bansan bayan duk hakurin xama da nake da kai a yanda kake akwai wani kalubalen dake
tunkaroni ba...." Tana fadin haka ta wuce sama kamar xata tashi sama, Hajja tace "Oho dai Allah ya ishi
Jiddah, kai kuma kayi ta istigifari don wnn ba karamin laifi ka aikata ma mahaliccinka ba ya jarabe ka da
mata kazama, ni wllh kawai nayi shiru ne amma tun daxu da na shigo parlon nan naji yana wari" Tana fadin
haka ta juya ta koma sama, Abuturrab ya d'an yi murmushi, shi dai ya ki tashi har sannan, Aneesah na
komawa sama ta saka kayanta ta dau kaya kala biyu a karamin akwatinta ta dau hand bag ta yafe gyalenta
ta fito, tana saukowa downstairs bata ko kalli Abuturrab ba ta nufi Kofa, ya bi ta da kallo yace "Ina xaki je
Aneesah?" A mugun fusace tace "Wllh baxan kwana gidan nan da tsohuwar nan a ciki ba, baka ce min
bayan hakurin da xanyi da kai har ita ma xanyi hakuri da ita ba, sannan ita wannan yar iskar mara asali da
ta kawo min gida...." Dakatar da ita yayi yace "Tafi kije, Allah ya tsare" Bude baki tayi tana kallonsa, tace
"Kace in tafi inje?" Fuska daure yace "Ehh, sai da safe" Kofa ta nufa fuu ta fice, ko kulle kofar bata yi ba ta
nufi gate, ya mike ya karasa kofar ya kulle ya sa makulli. Hajja na komawa daki ta tadda Jiddah kwance ta
takure waje daya, Hajja tace "Kiyi hakuri duk ni na ja maki don uwar rikon ki ma da kyar ta amince kika
biyoni, ban san gidan er iska xa mu xo ba da ban fara xuwa da ke ba, amma kema wannan simi simin da
kike baxai fissheki ba, gwara ki samu kiyi baki ki dinga kwatar kanki, naga kin cika wani sanyi kamar
kankara, ai yanxu idan kace xaka yi sanyi sanyi a duniya kullum cikin cutarka ake, da kin gaggasa mata
magana kin gaya mata irin kazantarta ai da ta kama kanta amma kin wani taho sama kina kuka kamar er
yarinya, ni sai yanxu ma kika bani haushi wllh, da ba don Allah ya takaita aurenku da Aliyun ba ai kishiyarki
fa xata xama, to a haka xa ki xauna kina mata kuka kullum??" Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, har
sannan xuciyarta bugawa yake, scene din abinda Abuturrab yayi mata ya ki daina dawo mata, ganin abun
yake kamar afresh, Cike da damuwa Hajja tace "To ko dai wani mugun abun ta maki naga duk a firgice kike
wllh, ki gaya min gaskiyar me ta maki Jiddah" Jiddah ta lumshe ido ta bude a karo na farko ta bude baki a
hankali tace "Bata min komai ba" Hajja tace "Oho dai ita da Allah ni dai na gaya mata duk abinda ya
kamata ta sani" Tana fadin haka ta sake fita daga dakin, Jiddah ta ji hawaye ya kawo idonta ta kai hannu
bakinta da take jin kamar bai cire nasa ba har sannan, ita idan ba a tv ba bata ta6a sanin ana haka a reality
ba ma, hancinta ta kai kayanta jin kamshin turarensa ya cikata, ta wani turo baki ta mike ta fara cire kayan,
sai da ta cire tas sannan ta saka hijab ta kwanta tayi lamo saman gadon, scene din da bata so na sake dawo
mata kamar a lkcn yake faruwa. Aneesah na xaune parlon kawarta Chef Salma, Salma tace "Kan bala'i!!! to
ai ni duk a xancen ki babu abinda ya tsaya min irin yarinyar da kika ce ta biyo kakar tasa... Ita yar kauyen da
ya saka ce ake miki sintirin xuwa gidan ki da ita? Sannan kuma ta bi ki da sharri haka? To me hakan ke
nufi?" Aneesah ta fyace majina da handki din hannunta tace "Ai shine nake jiran kiran stepmom din tasa,
wllh ni rabona da su gaba daya tun xuwansu da rana da nayi shigewata parlonsa, ban ganta ba balle har
wani abu ya hadani da ita, amma ban san me taje ta gaya ma makirar tsohuwar ba ta shigo har bangaren
mijina tayi min wankin babban bargo ta ci min mutunci" Salma tace "To kuma ai