Advertisements
Chapter 55 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   55 / 108

162K to 165K   out of 321.7K words

kinyi wauta barin gidan da
kika yi, bar masu gidan fa kika yi kenan" Aneesah ta fashe da kuka tace "Captain din fa ce min yayi in tafi
sai da safe" Salma tace "Toh ai dadi kakar da ita tsinanniyar yarinyar xa su ji, ke dai wani lkcn idan kinyi
wani abun kamar er fari, ke da gidanki kawai ki hado kaya ki bar masu, wato sun ma ci nasara a kanki,
sannan karyar da ita yarinyar tayi ma kakar Captain din ya xama gaskiya kenan tunda har kika bar gidan"
Aneesah tayi wani murmushi tana girgixa kafa, Salma ta ta6e baki tace "Wllh sakwa sakwan da kike ma
wnn pilot din yayi yawa, sai kace shine autan maza? Shi yasa har ya iya budan baki ya maki maganar banxa,
banda kilan suna da wani kudurin a ransu meye na xuwa da yarinyar da ya saka gidan tun tale tale? Me ya
kawota bayan ga kanninsa da cousins dinsa da xasu iya rako tsohuwar, to wllh ki farka daga wnn slumber
din naki kina da aiki ja a gaba, da kyar idan ba sake cusa masa me dankali da doyan xa su yi ba" Aneesah ta
sakko da kafarta daga saman kujera da sauri alamar xancen ya gigitata tana kallon Salma, er dariya tayi
tace "Ka ji ki da wani xance, to babu wani aure tsakaninsu sai in ta sake wani auren, ya mata saki sau uku
kenan, daya a lkcn auren na farko farko, sannan suna tare ma ya saketa, sai na karshen da Abbansa ya
umarcesa da ya saketa kuma ya saketa din" Salma tace "Ke wa ya gaya maki haka?" Ta gyara xama tace
"Aunty, kuma Aunty Safara'u ma taje wani waje haka aka ce mata babu aure tsakaninsu har abada, don
haka mu kwantar da hankalinmu, balle ma captain ba class dinta bane shi ma ya sha fada, me xai ci da
ita?? yar hayin rigasa ce fa bama birnin hayi ba kauyen hayi, ko numfashinta baxai so ya shakka ba balle
wani abu ya hadasu" Salma tace "To har naji hankalina ya kwanta maki, da kika ce babu auren, amma duk
da haka sai kin taka burki a daina taho maki da ita gida gaskiya, ba fa dangin iya ba na baba" Aneesah tace
"Ita kanta tsohuwar xuwanta na farko da na karshe kenan tayi idan anyi duniya don manzon Allah, wllh ko
da kudi aka hadota ta taho gidan Aliyu baxata sake xuwa ba" Salma tace "Yauwa, haka nake son ji dama, ki
tashi xaune daga kwancen da kike wllh... Yanxu kowa ta kansa yake duk inda kika ji ance aiki na kyau ki cire
kyashin kudi kije" Aneesah ta jawo wayarta ta daga ganin Aunty ke kiranta ta kai kunne da sauri, kuka ta
sakar mata, nan kuma ta bata labarin duk abinda ya faru, Aunty da ta kakance idonta tace "Kina nufin tare
da shegiyar taje maki gida?" Aneesah tace "Wllh kuwa" Aunty tace "Toh ke banda shashanci meye na barin
gidan, wato Hajjar taji dadi kenan ma kin bar masu gidan" Aneesah tace "Aa wllh Aunty ni baxan iya xama
ba suna ci mun mutunci kuma babu abinda Aliyun yace, sannan da kansa yace in tafi" Aunty tace "Toh
abinda xai faru yanxu ki dauko jakar taki ki taho nan gida, Abbansa na gari ai, maza ki taho yanzu, kuma
wajen maida magana duk ki san abubuwan da xaki kara a xancen, ai in sun san wata basu san wata ba"
Aneesah tace "Toh" Aunty tace "Wai ya ma baki wannan kudin kuwa?" Aneesah ta tabe baki tace "Ina fa,
ce min yayi sai sabon wata da xa a shiga..." Aunty tace "Anya Aneesah kinyi amfani da maganin karshen da
na baki a daren ku na farko kuwa?" Aneesah tace "Aunty sai dai na xo gidan, yanxu xan fito dama gidan
Salmah na taho" Aunty tace "To na gane, taho gidan maxa yanxu" Driver Salmah ta saka ya kai Aneesah
can gidansu Abuturrab. Har wajen karfe sha daya Abuturrab na xaune downstairs tare da Hajja da babu irin
labarin Masar da bata masa ba, with much interest yake sauraronta yake biyeta duk da labarin ba dadi
yake masa ba, ya gyara xama yana kallon agogo yace "To ai nan ma akwai turarruka masu kamshi ba can
kadai ba" Hajja tace "Inaaa har yau banji turare me kamshi irin ta Masar ba, akwai wani turare da Usman
ya bani wai dubu hamsin ya siya ni dai yana can na jefa cikin kwambodi.... to ba kamshi" Yace "Toh bari in
dauko maki wani turarena yanxu ki ji kamshinsa ko ya kai na Masar din" Mikewa yayi yace "Ki jirani yanxu
in dauko maki" Hajja tace "Toh yi maza, kaga idan kamshin ya min sai ka bar min kawai" Yace "Ba damuwa"
Daga haka ya haura sama, gently ya murda kofar dakin ya bude, kwance take saman gadon ta rufe duk
jikinta da hijab dinta idonta a lumshe, ya karasa cikin dakin ya kulle kofar, kallon switch din dakin yayi kafin
ya nufeta walking slowly ya tsaya kusa da gadon yana kallonta, ya kalli kayanta da ta linke ta ajiye sannan
ya kara kallonta, daga hijab din da ta lullube jikinta yyi yaga babu abinda ke jikinta sai undies, lkci daya ya
sake hijab din ya juya ya fita dakin ya tafi bangarensa yana shiga bedroom dinsa ya kashe wutan dakin ya
fada saman gado yayi rub da ciki. Hajja ta gaji da xama, ta sha gyangyadinta har ta gode Allah sannan ta
mike wajen karfe daya ta wuce sama tana cewa "Gantalallen ba sai yace min bacci yake ji ba sai da safe,
me hali dai baya fasa halinsa kawai..." Tana bude kofar daki taga Jiddah durkushe kusa da gado ta hade
kanta da gadon, Hajja tace "Meye haka?" Ta dago da kyar tana kallonta ta girgixa mata kai, a fusace Hajja
tace "To meye kika wani rungume gado kamar me nakuda?" Jiddah dai ta kasa ce mata komai, Hajja tace
"A gaskiya da na sani baki biyoni ba, daga abun arxiki? Me ya sameki?" Jiddah ta kara girgixa mata kai
kawai, Tabe baki Hajja tayi ta Kashe wutan dakin tace "Baxan iya da wahalanki ba bacci xanyi wllh, babu
wanda xai shiga hakkin bacci na" Tana fadin haka ta kwanta daga kwanciya kuma sai minshari, Jiddah tayi
ta juye juye... tun tana daurewa har ta kasa ta dinga hawaye tana yarfe hannu, rabonta da irin ciwon nan
da take ji yanxu tun tana gun Babaarta, har karfe biyu Jiddah na durkushe yanda take, da ya lafa mata sai
ya fara kuma... Shesshekarta ya farkar da Hajja, Hajja ta mike xaune sai kuma ta tashi ta kunna wutan
dakin, xaro ido tayi ta kalli agogo ta kalli Jiddah sannan ta bude kofa ta fice, bangaren Aliyu ta nufa ta buga
kofa, Abuturrab dake xaune saman kujera a parlon ya rike kansa ya juya da sauri yana kallon kofar, Hajja ta
sake bugawa, xai mike daga kan kujeran yayi kicking ruwan Lipton din lemun tsami dake cup a ajiye daga
kasa kusa da shi, lkci daya ya malale saman carpet din parlon, tsallakewa yyi ya nufi kofar ya bude, cikin
tashin hankali Hajja tace "Aliyu awa uku kenan wancan yarinyar bata ko rintsa ba, sai kuka take na rasa me
ke damunta, ni fa tsorona Allah tsorona tijaran da Ramlah xata min a kanta" Da mamaki yace "Me ya
sameta?" Hajja tace "Ina xan sani Aliyu ko kwanciya taki yi, tana can duke kamar me nakuda nayi nayi ta
gaya min meye taki" Abuturrab yace "Ina xuwa" Daga haka ya koma daki ya dau jallabiyarsa ya saka sannan
ya fito, yana gaba Hajja na biye da shi suka isa dakin, Yana bude kofar dakin suka ganta durkushe kofar
bandaki tana kwarara amai, Hajja tace "Na shiga uku ni Dije ta kashe bandakin, wani aman arxiki ne baxa
ta shiga can ciki ba sae a bakin kofa?? Tirrrrr" Abuturrab ya karasa da sauri ya duka kusa da ita yace
"What's wrong with u?" Ta kasa basa amsa ya dagata xuwa cikin bandakin, Hajja ta fice daga dakin hankali
tashe tace "Baxan iya ba wllh, ko ni ya na kare da nawa aman balle na wani..." Abuturrab ya wanke mata
fuskarta bayan ya xuba ruwa gun aman, xai cire mata Hijab din jikinta ta rike gam tana xaro ido amma taki
yarda ta kallesa, hade rai yayi yace "Cire hannunki" Da kyar cikin kuka tace masa "Aa bana so wllh" lkci
daya ya fixge hijab din a jikinta da karfi, ta turasa ta durkusa a kasa hankali a tashe tana cewa "Wayyo na
shiga uku don girman Allah ka bani hijabina ka fita" Yana kallon ko ina na jikinta yace "Me yake damunki?"
Duk a gigice take tace "Ai naji sauki" Yace "Saukin me" Taki yarda ta kallesa tace "Don girman Allah kayi
hakuri ka fita" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tana kara rufe jikinta, shi dai kallonta kawai yake,
can ya d'an shafa kansa ya ajiye mata hijab din saman washing machine ya juya ya fita bandakin, banda
rawa babu abinda jikinta yake, tun da take bata ta6a ganin irin wannan iskanci ba, ko a gaban mace bata
ta6a tsayawa a yanda take yanxu ba, gaba daya ta nemi ciwon cikin da take ta rasa, ta kalli jikinta ta kara
takurewa waje daya xuciyarta na bugawa, ta fi minti biyar a haka kafin ta mike da sauri ta figi hijab dinta ta
saka gabanta na faduwa, ta makale jikin kofa sannan ta leka dakin a hankali, ido hudu tayi da shi yana tsaye
har lkcn a dakin, da karfi tayi banging kofar bandakin ta sa makulli, ganin haka ya shafa kansa ya juya ya
fita, xaune yaga Hajja a corridor din ta shimfida darduma sai xuba gyangyadi take, yayi mata kallo daya ya
wuce bangarensa, throughout daren nan Abuturrab bai rintsa ba, banda juye juye babu abinda yake, idan
ya gajiya da kwanciyar saman gadon ya koma kujera a parlor, har aka kira sallah. Karfe takwas Jiddah ta
lallaba ta saka kayanta da Hijab tana kallon Hajja dake kwance kan darduma tana bacci, ta dau jakarta ta
nufi kofa a hankali ta bude ta fita, kallon direction din bangaren Abuturrab tayi kafin ta sauka downstairs
da sauri, mai gadi ne ya bude mata gate ta fice fittt daga gidan....




Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems

Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240



Har Jiddah ta isa bakin titi waigen layin take xuciyarta na bugawa, tana ta tsaye har ta samu adaidaita ta
hau ta gaya masa inda xai kai ta, dai dai kofar gidan Umma mai adaidaita sahun yayi parking ta sauka ta
ciro kudin da Umma ta bata jiya a jaka ta mika masa, ya bata canji sannan ta shiga cikin gidan... Babu kowa
parlon don su Maimoon sun tafi Islamiyya, ta karasa kitchen don gaida Huraira dake aiki a ciki, Huraira tace
"Dama Umma tace sai yau xaki dawo da aka ji shiru har dare jiya" Jiddah ta d'an yi murmushi kawai tace
"Umma bata tashi ba?" Huraira tace "Bata tashi ba ko" Juyawa Jiddah tayi ta wuce dakinsu, sai da ta fara
shiga bandaki ta wanke baki tayi wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga bayan ta gama shafe shafenta
sannan ta kwanta, da ta runtse ido abinda Abuturrab yayi mata kawai take gani, tana ganin hakan kuma sai
gabanta ya fadi, ita har yanxu ganin lamarin take kamar a mafarki, da yake bata wani samu baccin kirki
daren jiya ba nan da nan bacci me nauyi ya dauketa. Karfe sha daya saura Umma ta fito daga dakinta ta
dalilin kiranta da Huraira taje tayi wai tayi bakuwa, Tsaye taga Hajja a parlon sai hura hanci take, Umma ta
karaso tana kallonta tace "Lafiya Hajja?? sannun da xuwa" Hajja ta dakatar da ita tayi mici mici da ido tace
"Jiddah ta dawo??" Umma ta kalli Huraira dake bayan kujera a tsaye, Huraira tace "Ehh ta dawo tun daxu
amma tana daki tana bacci" Umma ta kalli Hajja, Hajja ta rushe da kuka ta nemi kujera ta xauna tace "Toh a
gaskiya Allah ya isa, wannan daga min hankali da tayi taje don kanta, idan kuma ke kika koya mata hakan
kema kije don kanki... Kuma ni ban san haka take ba da ban fara xura jiki ina kulata tun farko ba, ashe su
Maimu da Aisha kananun yan iska ne a inda wannan yarinya jiddah take ban sani ba?? Amma ba komai
nasan duk karatunki ne ta dauka ba wani abu ba" tana fadin haka ta fyace hanci, Umma da ranta ya gama
baci tace "Kawai sai in xaunar da ita don rashin aikin yi ince ta baro gidan da ku ka je da sassafe ko Hajja??"
A fusace Hajja tace "Oho... Xaki aika wllh, waye bai sanki da halinki ba? dama kuma da ya kika bari ta bini,
bai sai da na hadaki Allah... annabi ba?? ni dai ai na gode Allah da ta dawo gida lafiya abu bai sameta a
hanya ba balle hukuma su garkameni ko jikana, wai kawai ina farkawa daga bacci barawon da ya sace ni da
asuba sai naga daki wayam babu mata babu dalilinta, ban kawo komai a rai ba ina ta jan carbi har kusan
karfe tara, nace kai bari dai in sauka in duba ko kumallo take nema mana a kitchen, ina sauka naga gidan
wayam babu ita babu isilinta, na duba inda takalmanmu suke naga ai babu nata sai nawo kwallin kwal
kamar maye, da gudu na koma sama na taso wancan mutumi Aliyu shi ma dai ya fito muka yi ta bulayin
neman yarinya a cikin gidan, banda kuka da rokon Allah ya taimakeni babu abinda nake a lkcn, daga karshe
ya bada shawaran mu taho nan kilan ta dawo, shine fa na taho ko wanka banyi ba yanxu haka, abinda ban
ta6a yi ba a Masar, gudun fitinarki ma gashi can yaki shigowa yana can xaune cikin mota, to yana da
gaskiya mana tunda bai san ko yarinyar ta dawo ko bata dawo ba, daga ni har shi sai ki iya sa a garkame mu
kadan da aikin ki" Umma ta kalli Huraira tace "Kira min Jiddah" Huraira ta tafi daki, a durkushe taga Jiddah
ta daura kanta saman gado idonta lumshe, baccin ma gaba daya ba me dadi tayi ba banda mafarkan
Abuturrab babu abinda take, ga ciwon ciki da ya matsa mata, Huraira tace "Lafiya Jiddah" Da sauri ta bude
idonta sai kuma ta dago kanta daga saman gadon ta nuna mata cikinta alamar yana mata ciwo, Huraira
tace "Subhanallah sannu kinji, xaki iya fitowa kuwa, Umma na kiranki" Jiddah ta daure ta mike ta dau
hularta ta saka sannan ta fito parlor, wani kallo Hajja ta dinga mata daga sama har kasa, Jiddah ta kasa
kallonta ta karaso parlon ta durkusa, a hankali tace "Ina kwana Umma" Umma tace "Lafiya lau, why did u
leave without telling anyone?" Jiddah ta girgixa mata kai kawai bata ce komai ba, Umma tace "Ki bude baki
kiyi min magana" a hankali tace "Umma cikina ke min ciwo" Hajja tace "Kaji sharri?? Dama ba gari muke
jira ya waye a kai ki asibiti ba? in ni kina tunanin tsohuwar banxa ce don me baki sanar ma me gidan cewar
xaki koma gidanku ba xaki tafi ki bar xuciyoyin mu a gantale da fargaba??" Umma tace "To ayi hakuri Hajja,
Allah ya huci xuciyarki" Hajja tace "Aa bbu ruwana wllh, sai kinga tijaran da nayi ma matar gidan a kanta
jiya, shine ni xata watsa min kasa a ido?" Umma da mitan ya fara isarta tace "Toh ke yanxu ya kike son ayi
Hajja? Komawa gidan xa kiyi tare da ita yanxu?" Jiddah da taji gabanta yayi wani irin faduwa ta fashe da
kuka ba tare da ta shirya ba tace "Wllh cikina ciwo yake min Umma" Hajja ta rike ha6a tana kallon Umma
tace "In koma ina da ita? Matar da ta kashe mana baccin jiya duk a xaxxaune muka kwana a gidan kamar
almajirai, aa tunda ta dawo gida lafiya Alhmdlhi, nima xuwa xanyi ya ajiyeni a gida ashe matar gidan yaji
tayi daga jin mun xo, to ni ina na sani, sai yau da safe yake gaya min" Umma dai tace "To Allah ya kyauta,
kiyi hakuri Hajja" Hajja ta juya ta nufi kofa tace "D'an ba kara, tunda dai ta dawo xan turo Aliyun ya shigo
ya gaisheki mu san inda dare ya mana" Mikewa Jiddah tayi ta wuce daki kamar warce aka tsikara jin xancen
Hajja na karshe, Umma ta bi ta da kallo, Hajja na fita kofar gida tana kallon Abuturrab dake xaune cikin
motarsa tace "So tayi ta tona mana asiri Allah bai yi ba, gata can munafukar tana ciki, ka shiga kawai ka
gaida uwarka muyi ta kanmu, mu dai ba ta dawo gidan lfya ba Alhmdlh" Abuturrab yace "Ke kin ganta a
ciki?" Hajja tace "To da fa? Wai sai ta fashe da kukan munafurci daga Uwar tace mu koma tare, bata san
nima ta sire min ba baxan sake xuwa da ita ko ina ba, har abada kuwa, jiya kaga abinda dai ta dinga mana
cikin dare kamar me cikin wata tara" Abuturrab ya shafa kansa yace "To shigo mu tafi" Hajja tace "Aa rufa
min asiri so kake Ramlah tayi dani idan mun tafi tace na hanaka shiga ka gaisheta?? Kaje ko minti daya ne
ka gaisheta ka fito kawai" Bude motar Abuturrab yyi ya sauka, Hajja tace "Kayi maxa ina jiranka" Umma na
xaune parlon tana ma Jiddah dake xaune kasa kusa da ita magana a kan me yasa xata bar gidan da sassafe,
ita dai Jiddah bata ce komai, Abuturrab yyi sallama bakin kofa, sosai gabanta ya fadi tayi kasa da kanta
kamar me neman allura a kasan, Shi ma tun da ya kalli inda take sau daya bai sake kallo ba, ya dai karaso
parlon ya xauna saman kujera yace "Ina kwana Umma" Umma tace "Lafiya lau, an tashi lafiya" Yace
"Alhmdlh, ya gida" Tace "Lafiya lau" Kamar

55 / 108