Advertisements
Chapter 85 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   85 / 108

252K to 255K   out of 321.7K words

dakinta ta bude a hankali jin ana knocking, juyawa tayi ta koma ciki bayan sun
hada ido, Abuturrab ya shiga dakin sannan ya kulle kofar yace "Kin ci abincin?" Ta girgixa masa kai, bude
warmers din da ya ajiye mata kafin ya maida Hajja gida yayi, yace "Why, baki son tuwon ne?" A hankali
tace "Aa xan ci" Debar mata yayi a plate ta sauko kasan carpet ta xauna, ya ajiye mata abincin a gabanta,
tace "Kai baxa ka ci ba?" Ya mike yace "Nahh.. Bana cin tuwo" Kallonsa kawai take, ya cire agogon wrist
dinsa ya ajiye gaban mirror dinta ya nufi bathroom, bin sa tayi da kallo sannan ta fara cin tuwon a hankali,
a nan dakin Abuturrab yayi sallan la'asar don bai samu jam'i ba, bayan ya idar ya dau agogonsa yana
mayarwa ta kallesa tace "Sai me xaka ci?" Juyawa yayi ya kalleta ya wara mata manyan idonsa yace "Kin
damu in ci abinci ne?" Turo baki tayi ta ci gaba da cin tuwonta, ya xauna yana facing dinta yace "Idan kina
son in ci sai ki girka min, don ni bana cin tuwo" shiru tayi tana kallonsa, ya mike ya nufi kofa ya fita daga
dakin, downstairs ya sauka yayi powering Tv ya xauna, maganganun Aunty ne kawai suke dawo masa da
xagin da tayi ma Umminsa, sosai yaji xagin ya tsaya masa a rai, she insulted his world and went scot free,
ya jinginar da kansa da kujera yana mata fatan Allah ya sa na karshen kenan tayi a gabansa don next time
ta sake xagin mahaifiyarsa xata ga true color dinsa he won't mind duk abinda Abbansa xai masa, rayuwarsa
a baya ya dinga tunawa da yanda komai nasa sai yace sai Aunty, she knows all his savings, infact everything
wanda Ummi ma bata sani ba, haka kawai yaji ya fara jin haushin kansa, he regret everything.... Jiddah ta
gama cin tuwon da miyar vegetable ta tafi bandaki ta wanke bakinta sannan ta fito ta dau warmers din ta
bude kofa ta fito, dai dai nan Aneesah ma ta bude kofar dakinta ta fito, hada ido suka yi Jiddah ta dauke kai
ta nufi stairs ta fara sauka a hankali, Aneesah ta bi ta da kallo ko kiftawa bata yi, tunani iri iri ne a ranta a
lkcn, sai kuma kawai tayi murmushi, Jiddah na sauka parlon ta karasa dining ta ajiye warmer din hannunta
sannan ta dawo, shi dai Abuturrab bin ta kawai yake da kallo, ta shigo cikin parlon ta durkusa kan carpet
daga kusa da kujeran da yake xaune, sai kuma ta sunkuyar da kanta tace "Me xa a dafa maka?" Kallonta
kawai yake, ta daga kai ta kallesa, yayi kasa da murya ya kamo hannunta yace "Xa ki iya girki duk gajiyan da
kika yi?" Tace "Xan iya idan akwai kayan girkin" Xai yi magana Aneesah ta sauko da mayafinta da jaka a
hannu, sake hannun Jiddah yayi ya ci gaba da kallonsa, ta karaso cikin parlon tana kirkiran murmushi tace
"Sannun ku..." Ita dai Jiddah ko kallonta bata yi ba, Aneesah ta koma ta daya side din tana satan kallon
Jiddah ganin yanda ta wani durkusa gabansa kamar me neman gafara, wai miji xaka durkusa ma haka,
what for? Kamar yanda Jiddah taki kallonta haka Captain ma da ya kafe idonsa kan tv yaki kallonta, can ta
dai ta kallesa tana daga tsaye cikin sanyin muryarta tace "Captain pls ka d'an ara min car key dinka xan
amso sako yanxu in dawo, baxan wuce minti ashirin xuwa talatin ba" a takaice yace "Ki jira ni a daki" ta
d'an yi jim tana dubansa, Jiddah ta dago kanta suka hada ido da ita, wani shegen kallon tsana ta watsa
mata sannan ta wuce sama kamar xata tashi, Abuturrab ya kalli Jiddah a hankali yace "Ki dafa duk abinda
xai maki sauki baxai baki wahala ba" Shiru tayi bata ce komai ba, can ta mike ta nufi kitchen din figure
dinta ya bi da kallo ba ita ba, sosai atamfar jikinta yayi mata kyau ya amshi fatar ta, xaka fi tunanin she is 20
not 18, tashi yayi ya shafa kansa ya wuce sama, Jiddah ta fi minti biyar tsaye kitchen din tana bin sa da
wani irin kallo ganin yanda kitchen din is very untidy with dirty utensils scattered everywhere, shi kansa
gas din duk abinci ne ya xuxxube yayi wani baki, sai a snn ta lura da wasu sabbin kayan kitchen a cikin
kwalayensu masu yawa da aka jibge a babban store din dake kitchen din, juyawa tayi ta fito daga kitchen
din ganin baya parlon ta haura sama ta shige dakinta tayi kwanta. Aneesah ta dinga kallon Abuturrab
amma ta ki ce masa komai, ya rungume hannunsa yace "Lastly wannan fitan da kike anyhow babu excuse a
gidan nan is cancelled from today henceforward, idan kin shirya xaman aure da ni kiyi respecting duk
opinion dina Aneesah...." Cikin rawar murya tace "Yanxu don ka kara aure captain shkkn sai ka maida ni
banxa a gidan nan bani da kima da mutunci a idonka? Did i deserve this... Me nayi maka da irin wannan
dokokin da ka shimfida min?" yace "Wait... da nayi aure kin rasa ci ko sha a gidana? Kawai ina gaya maki
abubuwan da xai sa mu xauna lafiya dake a gidan nan ne, idan kuma kina son xaman lafiyan nan dole kiyi
abiding to all what i said" Ta fashe da kuka sosai tace "Har ni xaka kalla kace babu ruwana da matarka inyi
harkana tayi harkarta kamar dai ni macuciya ce? dama haka ake yi ashe? Ba xaunar da mu xaka yi ka gaya
ma kowa matsayin kowa a gidan ba sannan ka nemi mu hade kanmu kada a ji mu a wani wajen ba? Ba
haka ko wani namiji yake yi ba ashe? Anya xaman lafiya kake son mu yi kuwa Captain?" Abuturrab yace
"It's not necessary, kowa kuma ta san matsayinta a gidan nan ba sai na fada ba...." Ta goge idonta tace "To
a kan me kuma xaka ce kada wata yar uwata ta sake shigo maka gida? Dama haka ake yi a kadunan ko
kuma ince a familyn ku?" Yace "Ehh policy na kenan..." Tace "Amma haka zalika ita ma babu wani nata da
xai shigo gidan dai ko??" Yace "Wa enda ke da full right din shigo min gida su ne 'yan uwana kawai"
Aneesah tace "Yan uwanka?? To wllh baxai yiwu ba don duk wani d'an uwanka da xai shigo gidan nan
wajenta ya xo tunda dai ba dangi ko wani d'an uwa gareta ba, yan uwan naka suka karata cikinsu ta xama
mutum, don haka wllh yanda ka hana yan uwana shigowa gidanka to kowa ma ka hanasa shigowa..." Yace
"Toh idan nawa yan uwan sun shigo ki koresu mu ga" Daga haka ya juya ya fita ta bi sa da kallo ranta na
suya, xaunawa gefen gado tayi bayan ta jefar da mayafin hannunta, daga aure ko sati ba ayi ba xata fara
fuskantar haka a gidan nan?? to ai xama bai ganta ba kuwa, baxata ci gaba da laruwa kan su Aunty da
Safara'u ba, she needs to wake up from her slumber ta kwaci kanta da kanta. Abuturrab na sauka ya ga
Jiddah bata kitchen, sai da ya kare ma Kitchen din kallo with irritation sannan ya koma sama ya bude
dakinta... a kwance ya ganta, yace "Kin fasa girkin kenan" tace "Baxan iya girki a wannan kitchen din ba"
Yayi shiru bai ce komai ba, ko kadan kuma bai ga laifinta ba don duk wani me tsafta baxai iya amfani da
kitchen din nan ba, ya karasa ya xauna gefen gadon yace "Toh mu je ki rakani in siyo a waje" Tace "Ka dai je
ka dawo" yace "Baxa ki rakani ba?" Tayi shiru, mikewa yayi yace "Toh me xan siyo maki?" Tace "Ni na ci
abinci ai" Fita yayi daga dakin ta bi sa da kallo, duk da tana son rakasan amma bata tashi ba, har taji ya
tada motarsa ta lumshe idonta, mikewa Aneesah tayi da sauri tana leka window ta ga shi kadai a motar,
tana ta kallonsa har ya fita compound, kofa ta nufa ta bude ta fita ta yi hanyar dakin Jiddah, a hankali ta
murda Jiddah ta bude ido da sauri ta kalli kofar, Aneesah ta bude, sosai gaban Jiddah ya fadi, Aneesah ta
shigo ta kulle kofar tana kallonta sae tayi murmushi ta ja stool ta xauna tace "Sannu amarya, fatan kun
dawo lafiya?" Jiddah ta mike xaune ta ki yarda su hada ido tace "Lafiya lau" Aneesah na gyara dankwalinta
tace "Naga kina ta dari dari da ni tun da kika shigo gidan nan kamar dai baki son ki sake da ni, inji dai ba
abubuwan da suka faru a baya kika bari a ranki ba, in dai shine to ki manta su Jiddah, ba komai ya ja hakan
ba sai sharrin shaidan da xugan mutane, wllh ba halina bane, ni yanxu na dauke ki matsayin kanwata ta
jini, ina son mu xauna lafiya kar mu bari a jiyo kanmu, don Allah ba don ni ba ki sake da ni Jiddah, kuma
kiyi hakuri ki yafe min abubuwan da na maki a baya duk sharrin shaidan ne" Jiddah ta daga kai ta kalleta jin
tayi shiru, Aneesah tayi murmushi ta gyada kai tace "Har cikin xuciyata nake gaya maki duk abinda ya fito
bakina Jiddah, abinda ya sa ban bi ta gun captain ba kafin inyi maki magana sbda nasan xai xata ko wani
manufan ne a raina baxai yarda ya amince da ni ba, amma ke nasan ba jahila bace xa ki fahimce ni, xa
kuma mu xauna lafiya babu tashin hankali" Jiddah ta ma rasa abinda xata ce mata, a hankali Aneesah tace
"Kin yi shiru Jiddah" Jiddah ta kalleta a hankali tace "Shkkn ya wuce" Aneesah tace "Kai amma na ji dadi
wllh, kuma don Allah ki saki jikin ki da ni kar ki daukeni matsayin kishiyarki dama bani da kowa a kaduna,
ina son mu dawo kamar yan uwan juna, mu yi abunmu mu rufe tare ba tare da ko shi captain din ya sani
ba" Jiddah dai bata ce komai ba, Aneesah tace "Daxu naga kamar kun shigo da abinci ko?" Jiddah tace
"Yana dining" Aneesah tace "Toh bari in diba banci komai ba wllh, naje xan dafa Indomie daxu kuma ban
samu na dafa ba" Daga haka ta mike ta nufi kofa Jiddah ta bi ta da kallo har ta fita, downstairs Aneesah ta
sauka ta dau plate ta debi tuwon sannan ta dawo dakin Jiddah, hira ta dinga jan ta da shi tana bata labarai
iri iri duk na Captain Aliyu, Jiddah dai daga um sai um um, Aneesah tayi dariya ta ajiye spoon din hannunta
da take cin tuwon tace "Wllh ban ta6a xatan duk walakancin da na masa shi xai xama mijina ba, to nayi
mugun raina arxikinsa a lkcn gashi ya nace min, har yanxu idan na tuna sai inji kunya ashe mijina na dinga
yi ma girman kai ina walakantawa shi kam baya fushi yana ta makale da ni yana nace da ni, wllh na sha
xagesa a waya amma hakan baxai hanasa kirana anjima ba don naci, a lkcn kuma sbda wai ni fa yaki yarda
ku xauna tare sbda mugun son da yake min, ni kuwa duk ban san abinda ake ciki ba, to gashi hakkinki yana
ta bibiyansa shi yasa ya kasa samun nutsuwa a lamarinsa, yana ganin idan ya aureki to Allah xai yafe masa
duk abubuwan ya maki, yace min dalilin da ya aureki kenan ko xai samu rest of mind da conscience dinsa
dake judging dinsa" Jiddah dai kallonta kawai take, Aneesah tace "In gaya maki a lkcn da ya aureni ma ni
gudunsa fa nake, inyi ta ihu duk daren duniya na ki amincewa da shi" kallonta kawai Jiddah take, Aneesah
ta d'an yi shiru jin she sounds ao stupid, sai kuma tace "Wllh kin yarda da shi nayi farkon auranmu... To ina
xan yarda naga abinda ya fi karfina??" Jiddah ta sunkuyar da kanta, Aneesah tace "Ranan kuwa da na
amince kwanan mu uku a asibiti, sai kuma na fara ganin canji daga garesa, kin san su maxa bayan sun samu
abinda suke so shkkn... Har yau kuma ina danasanin amince masa" Jiddah ta kalleta da sauri, Aneesah tace
"Wllh wllh na ci ubana a wajensa..." dariya Aneesah tayi tace "Ae ranan na ji ke kin samu daman ihun ma,
ni ina na samu wnn daman, kuma da xa ku tafi Abuja naga kina tafiyar ki ras, nace ahh lallai ke naki da
sauki" Jiddah taki ce mata komai, Aneesah tace "Ko ba haka ba?" Jiddah tace "Me fa?" Aneesah tace "Au
wai duk xancen nan baki gane ba" Jiddah tace "Aa ban gane ba" Bude kofar dakin aka yi, Abuturrab ya kalli
Aneesah sannan ya kalli Jiddah, Aneesah ta washe baki tace "A waje ka bar motar Captain? ko xaka fita
ne?" Bai ce komai ba ya karaso ya ajiye takeaways din hannunsa, Aneesah ta mike tace "Toh Jiddah na
gaisheki, bari in je banyi la'asar ba wllh, nagode da tuwo" Daga haka ta nufi kofa da plate din tuwonta ta
fita, Jiddah ta bi ta da kallo, Bayan ta fita Abuturrab ya kalli Jiddah yace "Me ta shigo yi?" Jiddah ta girgixa
masa kai kawai, daukan takeaway daya yayi cikin guda biyun da ya siyo, ya nufi kofa ya fita Jiddah ta bi sa
da kallo, sai kuma ta mike da sauri ta jingina da kofarta bayan few seconds ta bude kofar a hankali tana
kallon kofar dakin Aneesah, a kulle taga kofar, ta sauko downstairs sai ta gansa xaune parlor, da sauri ta
juya ta koma sama. Da daddare Jiddah ta d'an ci abincin da Abuturrab ya bar mata, ta fita da sauran
downstairs xata kai kitchen, Aneesah dake xaune parlor tana kallon wani series ta bi ta da kallo, bayan
jidda ta fito kitchen din ta dauke kanta da sauri, ganin Jiddah xata wuce sama Aneesah tace "Ga lemon
kankana da abarba nayi Jiddah" Jiddah ta d'an kalleta tace "Aa nagode" Aneesah ta hade rai tace "Naga
har yanxu kamar kin ki sakewa da ni Jiddah, yanxun nan fa nayi sa a kitchen, shine na debi nawa na bar
maki sauran a jug, captain din ma idan xai sha sai ki basa" Jiddah tace "Yanxu na gama cin abinci" Aneesah
tace "Toh ai wannan ba abinci bane lemo ne" Jiddah ta d'an yi shiru, sai kuma ta karasa cikin parlon, Ta dau
jug din tace "Xan kai sama, nagode" Aneesah tace "Toh shkkn, sai ki tafi da cup" Daukan cup din tayi ta
wuce sama Aneesah ta bi ta da kallo, Jiddah na shiga dakinta ta ajiye Jug din da cup a kasa kusa da mirror
dinta, sannan ta cire hijab dinta ta shiga wanka. Tana xaune gaban mirror tana shafe shafenta Abuturrab ya
shigo ta kallesa sau daya ta dauke kai, lumshe ido yayi don kamshin turaren da ta sa na karshe ya daki
xuciyarsa, ya nufi bayanta ya tsaya ya dafa shoulders dinta a hankali yace "Have u eaten?" Ta gyada masa
kai da sauri xuciyarta na bugawa, ya kalli Jug dake ajiye yace "Wannan fa?" Tace "Naka ne tace a ajiye
maka" wani kallo yyi ma jug din sai kuma ya nufi kofa ya fice daga dakin, ita dai ta sauke ajiyar xuciya gama
abinda xata yi ta saka kayan baccinta tayi kwanciyarta ta rufa da duvet ta rufe idonta. Aneesah dake xaune
parlor sae bin Abuturrab that is wearing just short and singlet take yi da kallo, sosai take missing dinsa,
rabonta da shi kusan wata daya da sati biyu kenan, Safara'u kuma na gidan a duk lkcn balle ta sama ma
kanta mafita, kallon agogo dake nuna karfe goma da minti arba'in tayi ganin ya haura sama rike da cup din
plane water ta san bangarensa xai je ya hada coffee don tuni ya dauke coffee powder dinsa a kitchen sbda
karewan da yake a kwana biyu kuma Safara'u ce ke sha sau biyar sau shidda a rana, Aneesah ta kashe
kayan kallon parlon da fitila sannan ta haura saman ita ma, dakinta ta shiga cikin mintuna kadan ta fito ta
nufi bangarensa tana baxa kamshi, xaune ta samesa a parlornsa yana kallon wrestling hannunsa rike da
cup din coffee, sau daya ya kalleta ya ci gaba da kallon da yake, ta xauna gefensa tana kallonsa a hankali
cike da kissa tace "It seems u are still angry at me Captain, naga sai wani hade min rai kake kaki sakewa da
ni, snn i notice dakin Jiddah da na shiga daxu kamar u are not happy about it, ni kuma ba da wata manufa
na shiga ba ina son mu xauna lafiya da yarinyar ne don naga bata da matsala ko a wancan lkcn ma ni kadai
nake haukana ita kam babu ruwanta" Abuturrab yace "Kilan u misperceived me, but i am not against ku
xauna lafiya ai..." Kwanciya tayi a kirjinsa ta lumshe ido tayi kasa da murya tace "Toh fushin da kake da ni
har yanxu fa?" Ya ajiye cup din hannunsa don saura kadan ya sake yace "Idan kika canxa halin ki xan daina
fushi da ke" Tashi yake son yi ta ki sakesa ta marairaice tace "Muna magana kuma ina xa ka Captain?" Yace
"I want to get my laptop" Abinda tasan tana masa xai yi turning dinsa on ta shiga yi masa, ya koma ya
jingina da kujera trying to control himself yace "Stop that Aneesah, i need to go get my Desktop" Ko
sauraronsa bata yi ba, Bata sake kuma basa daman magana ba, sai da yayi da gaske sannan ya turata taki
sakesa ta wani kankamesa tace "Me yasa baxa ka bani hakkina ba, ko ni ba matar ka bace?" Da kyar yace
"Sai ki jira ranan da kwanan ki ya xagayo..." Daga haka ya janyeta jikinsa, Kallonsa ta dinga yi babu ko
kiftawa ta ji wani bakin ciki da takaici ya turnuketa, ya mike tsaye ya tsallake coffee din da yake sha ya nufi
kofa ya fice daga parlon, da sauri ta bi sa taga dakin Jiddah ya nufa ya shiga ciki ya kulle, hawaye ya kawo
idonta ta koma parlon da sauri ta xauna kan kujera tana watsi da throw pillows din kai, xaunawa Abuturrab
yayi gefen gado na kusan minti uku trying to calm himself down, sai kuma ya juya ya kalli Jiddah da ke
bacci, kashe wutan dakin yayi ya hau saman gadon ya cire duvet da ta rufe jikinta da shi a hankali yana
kallonta fuskarta cikin duhun, lkci daya ta bude ido xata mike xaune da sauri ya kwantar da ita moving
closer to her murya can kasa yace "Mata na bacci dama bata jira mijinta ba?" Sosai gabanta ya shiga
faduwa ta marairaice masa tace "Bacci

85 / 108