Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
gwammace in ma kwantai ne awaran yyi,
nan gaba fa sai na koma xan fara tuya, ga layi kamar baxa a xo kanmu ba, to ko wacce da matsalarta a
kugunta" Zulai ta gyara xama tace "Shi sa nace maki mu fito da sassafe Hansai, amma kika tsaya dafa
awara, mutumin nan aiki yake kamar yankan wuka shi sa ake masa layi wllh, idan ba da asuba mutum ya
shigo ba sai ya kai magariba ma bai gansa ba, don ma mutumin baya tashi sallah kenan" Hansai tace "Toh
ko dai mu je mu dawo goben da asuba Zulai? kinga fa uban layin yaushe aka xo kanmu" Zulai tace "Kin ji ki,
mu kashe kudin mota kusan dubu daya kice mu tafi mu dawo Hansai??" Hansai tace "To ni ya xance? Wllh
kwantai awarata xata yi yau, Allah ma yasa ta yanyanka min in dai bibalo ce, kinga idan ya so gobe sai in
sake xaran dubu daya cikin kudin awaran mu taho" Zulai ta mike tace "Toh shhkn, mu tafi" Mikewa Hansai
tayi tana sa6a bak'in gyalenta da duk ya takure suka fito waje tana cewa "Ni dai fatana Allah ya sa na xo
gun karshen wahalata" Zulai tace "Ahaf ai fada ma 6ata baki ne wllh, in dai kika saki kudi rass xai maki aiki
bbu algus, kina xaune rana tsaka xaki ga Jiddah har gida kamar an korota, wnn ai karamin aiki ne a
wajensa, shi fa mutumin nan har haukata mutane ance yana yi" Hansai ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Ae
ban san amfanin shegiyar yarinyar ba sai da ta tafi, ashe ita ce rufin asirina ban sani ba, gaskiya idan Allah
ya dawo min da ita auren ma wllh baxata yi ba har ta mutu, tun bayan bacewarta har yau banyi cinikin
awara da yafi na dubu biyu ba, shi ma da kyar, snn xan ce ma malamin ya sa mata bak'in jini yanda bbu
wanda ma xai yi sha'awan aurenta a bar min a bata kawai" Zulai tace "Da dai ya fi wllh, kinga bbu ma
saurayin balle yace xai aureta" A haka suka isa bakin titi Hansai tace "Allah dai ya kai mu goben, in sha
Allahu komai ya xo min karshe, wahalata ta kare"
Abuturrab na tsaye balcony misalin karfe takwas na safe wayarsa kare a kunnensa yana sauraran wani
abokinsa, sai da ya jira abokin ya kai aya snn yace "I thought xa a samu mata ne, in dai ba a samu matan ba
kawai a bari, i will think of another alternative" Daga daya bangaren abokin nasa yace "Amma wa kake
nema ma lesson teacher din?" Ya xauna saman kujeran dake balcony din yace "Wata daughter na ne"
Abokin nasa me suna Farouq yace "Ohk in dai an samu matan i will let u know Capt, kasan maxan ne sun fi
juriyan koyarwan" Abuturrab yace "Eh haka ne, nagode da kulawa" Daga haka suka yi sallama, ya koma
parlor ya xauna, daukan wayarsa da yyi haske yyi, ya dinga kallon screen din ganin El-Basheer ke kiransa,
it's been a while da suka yi magana, duk da shine baya daukan kiran nasa, can dae ya daga ya kai kunne,
daga daya bangaren El-Basheer yace "Sai aka yi yaya da baka daga kirana?" Abuturrab ya jinginar da kansa
da kujera yace "How are you doing?" El-Basheer yace "Saboda baka da bayanin da xaka min kan auren da
kayi ma kanka ne yasa baka picking call dina??" Abuturrab ya gyara xama yace "Babu xancen wannan
auren ne yanxu, shi sa ma na samu kwarin gwiwan daga kiran ka" El-Basheer yace "Ohh really? amma few
days ago mun yi magana da Ahmad kuma yace min kana gidan ka da matarka...." Abuturrab ya daure fuska
yace "Matar da ya aura min?" El-Basheer yace "But wait.... On a serious note Captain don kaje ka yi ma
kanka aure babu shawara da kowa shine kake ignoring mutane, why are u avoiding good frnds? mu baxa
mu hanaka xama da matarka ba ae no matter who she is" Abuturrab yace "Look Bashir, am serious babu
xancen wannan auren yanxu, kasan ni bana karya, i don't have any god-damn wife now.... amma this is just
between i nd u don 'yan gida basu sani ba har ynxu" El-Basheer yace "Ban gane ba, sakinta kayi?"
Abuturrab yace "Ba sa'ar aurena bace ita ae, kawai tsautsayi ne da kaddara ya fada min" El-Basheer yace
"Then why are u still hiding it from people at home in har da gasken ka saketa?" Abuturrab yace "Bcos we
are staying under same rood with her har ynxu, and Abba won't take it likely if he finds out na saketa, i
think we should change topic now dude...." El-Basheer yace "Anyway... Ina kaduna, turo min address din
gidan naka, i will be leaving in two days time in sha Allah" Abuturrab yace "Really? Yaushe ka shigo, kuma
me ka xo yi" El-Basheer yace "Forward to me ur address now" Abuturrab ya d'an yi shiru, sae kuma yace
"Ohk" daga haka ya katse wayar..... Ya d'an yi jimm, bayan kusan 5 minutes kawai ya tura masa Address din
sannan ya mike ya wuce sama, dakin Jiddah ya bude ya ganta tana faman shafa man gashi a dogon
gashinta da ya cika ko ina na kanta, atamfa ce jikinta, ta daga kai tana kallonsa, fuskarsa bbu yabo bbu
fallasa shi ma yake kallonta, a hankali tace "Ina kwana" yace "Idan da abinda xa ki yi a kasa ki sauka ynxu
kiyi, xuwa anjima bana son ganin ki a kasa" Ita dai bata ce komai ba, ya juya ya bar bakin kofar. Mikewa tayi
bayan tayi parking gashin ta saka hula ta sauka parlon, xaune ta gansa parlon yana rike da remote, ta
sunkuyar da kanta ta wuce kitchen, dankali ta shiga ferewa ta soya da kwai, sannan ta fito kitchen din rike
da plate din Irish da egg din, ya bi ta da ido ganin xata wuce sama yace "Ina shayin?" Shiru tayi bata ce
komai ba, yace "Koma" Ba musu ta juya ta koma kitchen din ta sa ruwan xafi sannan ta hada shayin a cup
ta kara fitowa kitchen din, still yana kallonta yace "Wani ruwan kike sha gidan nan?" Tana kallonsa tace "A
bandaki nake sha, ko a pampon kitchen" Bude baki yyi yana kallonta with shock, can ya mike yace "Ruwan
bandaki?" Sosai gabanta ya fadi ta fara komawa baya, ya lura da hakan gudun kar ta saki ruwan shayin
hannunta tunda ya san ba setin kirki gareta ba, calmly yace "Je ki ajiye abun hannunki ki dawo" A sanyaye
ta wuce sama bayan ta ajiye plate da cup din ta mike ta fito a sanyaye, lkci daya hawaye ya kawo idonta,
tsaye ta gansa har sannan yana jiranta, ta makale jikin stairs bayan ta sauko cikin rawan murya tace "Gani"
Juyawa yyi yana kallonta, ta sunkuyar da kanta da sauri, daga sama har kasa yake kallonta, riga da skirt na
atamfa da ya kamata, babu abinda kayan ya boye na surarta, ya rungume hannunsa yace "Daga yau kada ki
sake sa atamfa a gidana" Ta d'an kallesa, sae kuma ta kara sunkuyar da kanta, yace "Idan baki son Abayan
da nake siyo maki kiyi yawo ba kaya kawai" Ita dai bata dago ba balle tace komai, yace "Sannan kika ce
ruwan bandaki kike sha?" Ta marairaice ta girgixa masa kai, strictly yace "What??" Tace "Sae cikin dare ne
nake shan na bandaki, amma da safe da rana da yamma na pampon kitchen nake sha" Gani tayi ya nufota
ta juya da sauri xata koma sama yace "Allah idan kika motsa daga nan xan maki abinda ban ta6a maki ba,
wato xan gaura maki mari" Kuka ta fara yi, tana hawa stairs din da daddaya da daddaya cikin rawan murya
tace "Don Allah kayi hakuri" Yana isa ta fasa kara, ta durkushe wajen tace "Kayi hakuri don Allah" Bai
karasa kusa da ita ba yace "Shi ruwan fridge din na waye?" Ta boye fuskarta tace "Naka ne" yace "Ni nace
maki nawa ne?" Ta girgixa masa kai, yace "Toh daga yau kika sake shan ruwan pampo a gidan nan Allah sae
na mareki" Ta gyada masa kai da sauri, yace "Tashi ki bar nan" mikewa tayi da sauri ta haura sama, sae a
snn ta juya tana kallonsa a downstairs, yana tsaye yanda ta bar sa, da sauri ta shige dakinta. Bayan azahar
El-Basheer ya iso gidan, Abuturrab ya fita ya shigo da shi, Abuturrab ya sakala hannu a kafadar cousin din
nasa yana murmushi yace "The prince himself" El-Basheer na murmushi yace "It's been long Captain...."
sosai suke shige da Abuturrab sai dai ya fi Abuturrab din haske, don shi ya fi shige da larabawa wanda
hakan ke nuna kilan shi din ruwa biyu ne.... El-Basheer na bin gidan da kallo bayan sun shigo yace
"Everything seems perfect, sai dai unfortunately ba Aneesah ta fara shigowa gidan ba...." Abuturrab ya
shafa sajensa kmr baxai ce komai ba, sae kuma yace "Kwanan nan xata shigo gidan in sha Allah, bikin
Ahmad saura few weeks so, bayan bikinsa sai inyi ma su Abba magana...." El-Basheer ya shiga bin parlon
da kallo yace "But wait.... Where is.... I mean the wife u married?" Abuturrab ya hade rai yace "Wacce wife
din?" El-Basheer yace "Warce muka ji labarin ka aura ma kanka mana..." Abuturrab yace "Pls hakan na
bata min rai wllh, Nace maka she isn't my wife any longer" El-Basheer yace "Yes haka kace, but why not ka
sanar ma kowa bbu auren??" Taku suka ji a stairs, Abuturrab ya saci kallon Stairs din da sauri, El-Basheer
dai bai juya ba sae kallon Abuturrab yake yana jiran amsan sa Jiddah ta sakko walking slowly ta shigo
parlon da ganin kasan a d'an tsorace take, Kallon Abuturrab dake kallonta tayi ganin irin kallon da yake
mata ta d'an tsaya ta ki karasowa, El-Basheer ya juya ya kalli inda Abuturrab ke kallo, lkci daya Abuturrab
ya mike, ta marairaice tana kallonsa tace "Kai ne kace in daina shan ruwan bandaki, wllh kishi nake ji"
Fuska daure yace "Juya ki koma" Juyawa tayi da sauri ta koma sama, Sai a sannan ya koma ya xauna yana
kallon El-Basheer da ya bi ta da kallo.....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Abuturrab ya dau throw pillow dake gefensa ya jefa ma El-Basheer da ya bi Jiddah da ido, sae a sannan El-
Basheer ya dauke idonsa, sai kuma ya daga kafada as if counting his words yace "Ita ce.... Ex-wife din
taka?" Abuturrab na kallonsa da wani expression yace "Does that warrant u to stare at her that way??" El-
Basheer yyi shiru yana danna wayarsa kamar baxai ce masa komai ba, sai kuma ya kallesa yace "Naga
kamar ganinta ya fi jin ta ne, ita ce yar hayin rigasar?" Abuturrab ya masa wani kallo ya dau remote yana
canxa channel, El-Basheer yace "Ko dai a gidanka ne ta samu transformation din nan, she's got a beautiful
shape" Abuturrab ya mike, sounding fed up yace "Stop this plss El-Basheer... U r sounding lousy" El-
Basheer yana shafa gashinsa yace "Lousy? Ohk sorry about that" Abuturrab ya dinga kallonsa da wani
expression that is expressing how really angry he is, ya koma ya xauna yana canje canjen channel, El-
Basheer ya bi parlor din da kallo yace "I need something cold to take now, haka kake treating visitors?"
Mikewa Abuturrab yyi ya wuce kitchen, El-Basheer ya bi sa da kallo, fridge ya bude ya dau bottle water
daya sannan ya fito, sama ya wuce yana cewa "In dai ni xan kawo maka ruwa xaka dade baka sha ba" El-
Basheer ya bi sa da kallo yana d'an murmushi, can ya girgixa kai, bude kofar dakin Jiddah Abuturrab yayi ya
shiga.... xaune ya ganta ta takure waje daya, tana ganinsa ta gyara xamanta tayi narai narai da ido tana
kallonsa, ya ajiye ruwan gaban mirror ya juyo fuska a tamke yace "Me nace maki daxu?" Shiru tayi, yace
"Ba ce maki nayi kar ki fito ba all through?" Hawaye ya cika idonta tace "Ruwa ai naje in dauka, ba ce min
kayi in daina shan na bandaki ba" Yace "Me ya hanaki dauka daxu da kika sakko" shiru tayi bata ce komai
ba, yace "Xo ki dauka" mikewa tayi ta tafi gun madubin ta dau goran ruwa, yana kallonta yace "Sannan ba
nace kada ki sake sa irin kayan nan a gidan nan ba?" Ta kallesa tace "Ai daxu ka gaya min, ina ce daga yau
kace.." Bai kuma cewa komai ba ta koma inda take ta bude ruwan, sai da ta sha ruwan sannan ya juya ya
fita dakin, tsaye ya ga El-Basheer a parlor hannunsa rike da kwalin lemon chivita yana sha, Abuturrab ya
xauna yace "What will u be taking for lunch?" Xaunawa El-Basheer yayi yace "Naaah... I'm full, i just need
rest" Abuturrab yace "Okay mu je sama" Mikewa yayi ya fara tafiya sama, El-Basheer ya mike ya bi bayansa
rike da lemonsa, Abuturrab ya kai sa part dinsa, xaunawa El-Basheer yayi gefen gado cikin bedroom din
bayan ya rufe lemon hannunsa ya ajiye yace "Tsarin gidan yayi sosai, the Architecture is really good" yana
fadin haka ya kwanta, Abuturrab dai na tsaye gaban madubi yana kallonsa ta madubin, can dai yace "Xan
je in dawo yanxu!!!" El-Basheer ya dago yace "Ina xa ka?" Yace "To get lunch" daga haka ya nufi kofa ya
fita, yana isa kofar Jiddah ya bude, ya d'an hade rai yace "Dauko Jilbab dinki, ki sameni waje" Daga haka ya
wuce, yana cikin mota Jiddah ta fito da Hijab har kasa, sai da ta shiga gaban motar sannan yayi horn, mai
gadi ya hau bude gate din, jan motar yayi suka fita gidan, wani babban eatry ya tafi, ya siya ma shi da El-
Basheer fried rice and chicken, Jiddah dae na xaune kan kujeran da ya nuna mata cikin eatry din, sai bin
mutanen wajen take da kallo, baka ta6a cewa tare suke da Abuturrab don bai ko sake kallon inda take ba,
wani mutumi ne ta ga ya ja daya daga kujeran table din da take ya xauna, ya daga face cap dinsa yana
kallonta, ta saci kallon Abuturrab da ke xaune wani table can yana jiran order din da yayi, ta sake kallon
mutumin, ya sakar mata murmushinsa me kyau, ta sunkuyar da kanta da sauri, yace "Hello, how are u
doing, are u waiting for ur order?" Ta saci kallon Abuturrab taga kallon direction dinsu yake ko kiftawa
babu, sosai gabanta ya fadi, cikin rawan murya tace "Yayana na nan fa" Mutumin ya bi eatry din da kallo,
kawai gani yayi Abuturrab ya nufosu, ita dai gabanta sai faduwa yake, Abuturrab na isowa yana kallon
mutumin babu yabo babu fallasa yace "Didn't she tell u she is married?" Mutumin ya mike yace "Ooh i am
sorry plss" Abuturrab bai tankasa ba ya ja wani kujeran ya xauna facing her directly, mutumin ya kara basa
hakuri, nan ma yaki amsawa har mutumin ya bar wajen, Jiddah ta saci kallonsa suka hada ido, ya jefa mata
wani kallo yace "Ko tausayin rayuwarki baki ji har xaki fara kula maxa ko?" A hankali tace "Ni bani na kirasa
ba kawai xuwa yayi" Yace "Toh bari kiji har sai kin gama jami'a kin fara aiki, kafin ki kalli ko wani namiji balle
har ki kulasa" Ta gyada masa kai kawai, ya ci gaba da danna wayarsa har aka kawo masa order da yyi a
takeaway, without looking at her yace "Me xa ki ci?" ta sunkuyar da kanta tace "Ko meye" tsaki yyi ya mike
ya bar wajen, jollof rice yayi mata order da kazar ita ma sannan suka bar eatry din, tana rike da ledan nata
ta wuce dakinta bayan sun isa gida, Abuturrab na shiga bedroom dinsa ya tadda El-Basheer a kwance
yanda ya bar sa idonsa lumshe, parlonsa ya koma ya xauna.
Bayan la'asar Abuturrab ya sauko downstairs ya samu El-Basheer dake xaune yana jiransa, El-Basheer yace
"Plss idan baxa kaje ba ni in tafi mana, i have many places to go yau din nan, i will be leaving probably
tomorrow in sha Allah" Abuturrab ya mika masa wayar hannunsa yace "Aneesah..." amsar wayar El-
Basheer yyi ya kai kunne, Abuturrab ya ajiye makullin motarsa sannan ya koma sama, El-Basheer ya amsa
gaisuwar Aneesah yace "Ya kwana biyu?" Aneesah tace "Alhmdlh, he is just telling me kuna tare yanxu" El-
Basheer ya d'an yi murmushi yace "Yea daxu na shigo kaduna and am at his resident now" tace "Oh ohk,
ya su Ummi?" Yace "Ban je ba" Aneesah tace "Ayya, to ya garin?" El-Basheer yace "Cool, i have a question
for you Aneesah, nasan baxa ki boye min ba" kafin ta ce komai yace "Tell me.... is Aliyu saying the truth na
cewar ya saki yarinyar nan??" Aneesah ta yi shiru da fari, can kuma cike da confusion tace "Yarinya? Wacce
yarinyar? Kuma sakin me?" Shiru El-Basheer yyi, can yace "Ohk then, i will pick a call right away...." Daga
haka ya katse wayar ganin from all indication she knows nothing about what he is saying now, sake kira
tayi ya ajiye wayar gefensa ya jingina da kujera, Abuturrab na tsaye dakin Jiddah dake rakube jikin gado,
yana kallonta strictly yake cewa "In har muka shigo gidan nan kika wani sakko wai xaki dau wani abu xaki
sha mamaki na, duk abinda xa kiyi kiyi ki gama yanxu kafin mu dawo" ta gyada masa kai kawai, kamar
wanda ya tuna abu ya juya da sauri yana kallon kofa, lkci daya ya fice daga dakin ya sauka downstairs yana
kallon El-Basheer da manyan idanuwansa yace "Hope... Hope you didn't say anything apart from greeting
to Aneesah???" El-Basheer yace "Of course baka ce min haka ba, na tambayeta ko gaskiya ne ka saki
yarinyar nan kamar yanda ka fada, and from d way she sounds, bata san komai kan maganar ba ma"
Abuturrab ya xaro ido yace "Ohh my God... Me yasa xaka yi mata wannan maganan El-Basheer?? We are
still hiding