Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
mike ya bi bayansa. Sai bayan isha Abuturrab ya dawo gida, yana shigowa parlor ya kulle
kofar parlon ya wuce sama, part dinsa ya fara wucewa ya ajiye ledan hannunsa, sai da yyi wanka ya canxa
xuwa pajamas dinsa, mintuna ba da yawa ba yyi yana waya da Aneesah daga bisanni yace "Xan kira ki
anjima" Daga daya bangaren ta marairaice tace "Ni ban yarda da xan kiraki anjiman nan dinka ba, just tell
me karfe nawa xan sake kiranka" Yace "Wani d'an aiki nake son yi a system, idan na gama ai nace xan kira"
A hankali tace "Toh Allah ya sa, but it's always xan kiraki anjima daga nan kuma shikenan sai gobe" Yace
"Uhn xan kira don't worry" Daga haka ya katse wayar, mikewa yyi ya dau ledan abincin ya fita bangarensa,
sai da ya fara knocking din sannan ya bude kofar dakin ya shiga, kwance ya ganta ta takure waje daya ta
rufe har kanta, ya ajiye ledan hannunsa ya karasa ya bude duvet din, rufe fuskarta tayi da hannunta taki
juyowa, tsayawa yayi yana kallonta, can yace "Kee" Still taki juyowa, ya hade rai yace "Baki ji na ne?" A
hankali ta dago ta mike xaune amma bata yadda ta kallesa ba, kallon idanuwanta da suka yi ja ya dinga yi,
can yace "Kuka kika yi?" Wasu hawayen suka taru idonta, ta ki yarda ta kallesa, yace "Ba magana nake maki
ba" Ta fashe da kuka ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, da mamaki yake kallonta, ganin irin kukan da
take, ya xauna gefen gadon yana kallonta yace "Gaya min me ya faru" Ta girgixa masa kai kawai tana kukan
a hankali, dauke kansa yayi, yayi shiru, bayan wani d'an lkci ya sake kallonta yace "Dago kanki ki kalleni"
Taki dagowa, ya mata tsawa yace "Dago kanki nace" Da sauri ta dago hawaye na sauka idonta amma ta
kasa kallonsa, ya mike ya koma side din da take kallo suka hada ido, a hankali ta sauke idonta, speaking
very calmly yace "Toh gaya min me yafaru, kina son wani abu ne?" Ta girgixa masa kai yace "Kukan me kike
yi then?" A hankali tace "Babu komai" Bai kuma ce mata komai ba, can ya kalli ledan da ya ajiye yace tashi
kije ki dau abinci ki ci, ganin bata tashi ba ya hade rai yace "Tashi nace" Mikewa tayi ta nufi gun ledan ya bi
ta da ido, yau ma riga da wandon ne na bacci jikinta, tana isa gun ledan yace sa darduma ki xauna a nan ki
ci, ta tafi gun darduman ta dauka sannan ta dawo ta shimfida ta xauna a kai, daurewa kawai take amma ji
take kamar ta fashe da kuka, ta bude ledan taga tuwo ne da miyar kubewa irin na ranan, sauke idonta tayi
ta kasa kallonsa, ganin bata da niyyar fara cin abincin yace "Malama abinci nace ki ci" A hankali tace "Xan
dauko ruwa" Ya mike ya fita xuwa kitchen ya dauko mata ruwan ya dawo, yana ajiyewa ya koma ya xauna,
tashi tayi ta tafi bandaki ta wanke hannunta sannan ta dawo ta fara cin tuwon a nutse, shi dai kallonta
kawai yake, he just have a special pity for women, bai son ganin hawayensu even by mistake, it get him
weak, and sure yasan maganganun da Ahmad yyi masa daxu babu karya ko daya a ciki but he cannot let
her stay with his mum or Ahmad's mum, he will get another solution.... Tana gama cinye tuwon daya xata
rufe yace "Daya kika gani a wajen?" Ta girgixa masa kai tace "Baxan iya cinyewa ba" Yace "Kara daya" Bata
masa musu ba ta fara cin wani dayan, amma bata iya ta cinye ba kuma bai tilastata ta cinye din ba, ta mike
ta dau sauran abincin da ruwa ta fita daga dakin, mikewa yayi ya bi bayanta ya xauna main parlor ya kunna
Tv, bayan few seconds ta fito kitchen din xata wuce sama ya nuna mata kujera yace "Dawo ki xauna nan"
Tace "Xan wanke baki" yace "Je ki wanke ki dawo" Tafiya tayi saman ya maida dubansa kan tv, tana
sakkowa ta tsaya tana kallonsa ya nuna mata kujera yace "Xauna" xaunawa tayi, ya ci gaba da kallonsa, tun
tana daurewa sbda baccin da ya fara damun idonta gashi ta kasa gaya masa har daga karshe ta d'an
kwanta still pretending to be watching d movie da bata ma san abinda ake a nan ba, da haka bacci ya
dauketa, duk yana lura da ita amma bai ce komai ba, he gets she's so lonely, abinda ke damunta kenan, shi
kuma he doesn't have intention of spending any of his time together with her, yau ma don kawai kukan da
yaga tana yi ne yasa ya kasa jurewa, har karfe sha biyu yana kallo parlon, sai a sannan ya tuna da Aneesah
da yace xai kira ya lumshe ido ya jinginar da kansa da kujera, sai kusan karfe daya ya bude idon don bacci
daukesa yyi a hakan, kallon 2 sitter din da take kwance yayi yaga baccinta kawai take, mikewa yyi ya kashe
switch din wutan parlon gaba daya sannan ya kwanta kan 3 sitter ya kashe tv da remote din kusa da shi ya
lumshe ido.... Kiran sallahn farko Abuturrab ya tashi, ya fi minti goma xaune kafin ya duba wayarsa ya
kunna fitila yana haskata, mikewa yyi ya karasa inda take kwance ya buga kujeran a hankali, bude ido tayi
da sauri yace "Tashi ki wuce sama" tana lullumshe ido ta mike xaune sannan ta tashi ya haska mata hanyar
stairs, ta fara tafiya sannan ya bi bayanta, tana shiga dakinta ko rufe kofar bata yi ba ta fada kan gado ta ci
gaba da baccinta, yana tsaye daga bakin kofar bayan ta shiga, ya kulle kofar sannan ya wuce bangarensa.
Sae kusan karfe tara da rabi Abuturrab ya sauko downstairs, kamshin girki kawai yake ji a gidan, ya tabe
baki ya xauna saman kujera, sae ga ta tafito kitchen, turus tayi ganinsa, sae kuma ta juya ta koma kitchen
din, shi dai idonsa na kan tv da yyi powering, can sai ga ta ta fito ta karaso cikin parlon, kallonta yyi... Her
expression today isn't of someone that is sad, ta xauna kasa ta sunkuyar da kai, dimples dinta na lotsawa
tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya lau" Ya gane da magana a bakinta ganin yanda take wasa da fingers dinta,
can yace "Me xa ki ce?" Ta kallesa tace "Dama cewa xan yi in kawo maka kumallo?" Da mamaki ya dinga
kallonta, can yace "Na me kenan?" Tace "Dankalin turawa na soya na soya kwai, sai na tafasa ruwan shayi"
Yace "Ohk mun yi da ke xan ci ne?" Ta girgixa masa kai yace "Toh baxan ci ba, kayan abincin da kika gani a
kitchen don ki girka ke kadai na siyosu na ajiye ba don ki girka ma ni da ke ba" Sunkuyar da kanta kawai
tayi, bayan few seconds ta mike a hankali xata bar wajen yace "Tsaya" Tsayawa tayi amma bata yarda ta
kallesa ba, yace "Dama kin iya soya Dankalin da kwai kike tsayawa da yunwa?" Bata ce masa komai ba, ya
tabe baki yace "Je ki" Juyawa tayi ta koma kitchen din. Tana komawa ta fara kuka a hankali, sae da tayi me
isarta sannan ta goge idonta ta fito xata wuce sama, ya bi ta da kallo yace "Kin karya?" Ta gyada masa kai
xata haura sama yace "Dawo nan!" Ji tayi wani sabon hawayen na shirin xubo mata, ganin tsayawa tayi
yace "Ba kya ji na ne?" Dawowa tayi ta sunkuyar da kanta, yace "Wuce ki xuba abinda kika yi ki xo nan ki
xauna ki ci" xata yi magana ya jefa mata wani kallo, kitchen din ta nufa trying hard kar ta fara rusa kuka, a
haka ta debo abinda tayi ta dawo parlon ta xauna tana turawa da kyar yana kallonta yana kallon TV sai da
ya ga ta gama sannan ya bar ta ta wuce sama, shi kuma ya fita xuwa siyo fastfood.... A ranan mutumin da
Abuturrab ya sa ya nemo masa mai gadi amma mai mata ya kirasa ya sanar masa an samu, Abuturrab ya
masa izinin kawosa gida amma wajajen biyar na yamma. Yana xaune parlor yana jiran Jiddah bayan azahar,
he is been sitting for almost 20 mins now, daga cewa ta shirya shine har ynxu, mikewa yayi ya haura sama
ya bude kofar dakin suka kusa cin karo don xata fito ne ita ma, ta koma baya da sauri, ya wani hade rai
yace "Baki da hankali ne xaki shanya ni a parlor?" Ta marairaice tace "Na kasa rufe rigar ne?" Yana kallonta
daga sama har kasa yace "Wani riga?" Hijab ne jikinta har kasa sai atamfa daga ciki, tace "Zip din rigar" Ya
jefa mata wani kallo ya juya, bin bayansa tayi, har suka sauka parlor, ya dau makullin motarsa ya nufi kofar
fita ta bi sa da sauri, yana cikin motar ta iso parking space din xata bude back seat yace "Kinsan meye
ma'anar mutum ya shiga bayan mota bayan su biyu ne kawai a motar?" Tayi shiru tana kallonsa, bai kuma
ce mata komai ba, ta xagayo xata shiga motar sai a sannan ya ga how obvious zip din da bata kulle ba yayi
cikin hijab din, bayan ta shiga gaban motar yace "Daga hijab din nan" a hankali tace "A bude zip din yake"
ya hade rai yace "Daga nace" kamar warce xata yi mugun abu ta fara daga hijab din, sai kuma ta kallesa
kamar xata yi kuka, ganin yanda ya hade rai ta daga hijab din kawai, bayan ta yake kallo da bra strap dinta,
ta sunkuyar da kanta, yace "Da a haka xaki bi ni don baki da hankali?" Ta girgixa masa kai, yace "Koma ki
canxa kayan" Ta buda ido tana kallonsa, ganin irin kallon da yayi mata ta bude motar ta sauka, sauka yyi ya
bi bayanta to check another clothe for her, sai bayan da suka shiga parlon ta kallesa tace "Xaka iya taya ni
jan zip din fa, ba lalacewa yayi ba" yace "Ban yi niyya ba" bata kuma cewa komai ba ta wuce sama ya bi ta.
Bude press din nata yayi yana kallon kayan ciki, abaya baki ya ciro mata da mayafinsa ya ajiye gefen gado,
ta dan xaro ido tace "Wannan ai yana kama jiki" ya harareta yace "Baya yake kamawa ba jiki ba, minti uku
na baki ki canxa kayan nan ki dawo kasa ki sameni" Bai jira cewarta ba ya fice daga dakin nata dake ta
kamshin turarurruka, a balcony ya tsaya yana jiranta, sai gata ta fito, sosai bakin abayar ya haska farin
fatarta ta dawo kamar balarabiya, flat show ne kafarta, she looks so beautiful and neat, kawai dai ta rame
ne ba kadan ba, ganin ta tsaya ta wani sunkuyar da kai yace "Tsayuwar me kika min a nan?" Tafiya ta fara
yi, ya bi ta da kallo kafin ya bi bayanta, front seat ta bude ta shiga, sai da ya fara bude gate sannan ya dawo
ya shiga motar suka bar gidan, ya sauka ya kulle gate din, gidansu Ahmad ya nufa don xuwa gaida Umma,
ya lura kamar she is a bit angry at him, don gashi wannan satin ma bata ce masa xata xo ba, a parking
space din yayi parking, Yana sauka motar Jiddah ma ta sauka tun da taga gidan da suka shigo farin cikin
fuskarta ya kasa boyuwa, shi dai ko kallonta bai yi ba, kallonsa tayi a d'an tsorace bayan ta sauka tace "Don
Allah xan iya xuwa in gaida maman Abdallah?" Ya fara tafiya xuwa cikin gidan yace "Ki je mana" Da sauri ta
nufi dakin Maman Abdallah, sai da ta gaida mai gadin ya amsa da fara'a yana mata sannu da xuwa tace
"Maman Abdallah fa?" Yace "Ki shiga tana ciki" Da sallama ta shiga dakin, Maman Abdallah na ganinta ta
rungumeta cike da farin cikin ganinta tace "Idonki kenan Jiddah, kai kai kai kinga yanda kika yi kyau kuwa,
sannu da xuwa amarya" Wannan kalmarta na karshe ne ya d'an sa mood din jiddah ya canxa don tasan dai
ita ba amarya bace, Xaunawa tayi tana ta kirkiran murmushi tace "Abdallah na bacci" Maman Abdallah
tace "Wllh kuwa, ashe ku ne kuka shigo gidan a mota, sannunku da xuwa" Jiddah na ta murmushi tace
"Bari inje in gaida Umma" Maman Abdallah tace "Toh maxa ki tafi, amma fa don Allah ki leko kafin ku
koma kinji?" Jiddah tace "Toh" fita tayi dakin dai dai sanda Ahmad ya shigo compound din, ya buda ido
sosai ganinta, sai kuma ya hango motar Abuturrab, da ladabi ta gaishesa ya amsa da fara'a yace "Yaushe ku
ka xo?" Tace "Yanxu muka shigo" yace "Maa sha Allah sannunku da xuwa" Tafiya take yana gefenta shi ma
yana tafiyan, can yace "Amma baki da damuwa ko Jiddah, kar ki boye min komai ki gaya min" Ta sunkuyar
da kanta cikin sanyi tace "Ina son dawowa nan wajen Umma" Shiru yayi bai ce komai ba, don yasan taurin
kan Abuturrab ya wuce ya amince Jiddah ta dawo nan gidan, a hankali yace "Kar ki damu Jiddah, nasan
xama ke kadai ne baki so ko?" Ta gyada masa kai, yace "Kar ki damu nasan me xanyi" Da damuwa tace
"Amma kar kayi masa magana ihu xai yi min" Murmushi Ahmad yyi yace "No baxan yi masa ba" Abuturrab
suka gani bakin kofa tsaye alamar lkcn ya iso wajen ganin jiddah bata shigo ba, Jiddah sai da taji gabanta ya
fadi ganinsa, shi kuwa sai ya hade rai, suna isa balcony din Ahmad yace "Sai ga amarya yau ta xo gidanmu,
kun xo gaida Umma kenan" Abuturrab da yayi masa wani kallo underneath his breath yace "Half-wit" daga
haka ya juya ya koma parlon. Rungume Umma jiddah tayi, sosai tayi farin cikin ganinta kamar yanda Umma
ma taji dadin ganinta, Shi dai Abuturrab na yi yana kallon agogo don bai ma son la'asar yayi masu a gidan,
Kitchen Jiddah ta tafi bisa umarnin Umma na cewa taje ta taya su Siyama da mai aiki girki, Umma na kallon
Abuturrab tace "Why is she this lean? Bata da lafiya ne?" Ya sunkuyar da kansa yace "Eh tayi xaxxabi
kwana biyu, amma ta samu lafiya yanxu" Ahmad dai sai wani kallo yake masa, Da damuwa Umma tace
"Toh Allah ya sauwake, ita kadai din ce a gidan kenan yanxu?" Da sauri yace "Aa Umma ai nace akwai me
aiki, kuma ma yawanci one day on, one day off nake yi" Umma tace "Toh shkkn Allah ya taimaka, karatun
fa?" Yace "Xata fara in sha Allah" Umma tace "Toh maa sha Allah, Allah ya taimaka" Abinda Abuturrab bai
so bane ya faru don sai da la'asar din yayi yana gidan, dakin Ahmad ya tafi yin alwala, Ahmad dake ta jiran
ya shiga alwala ya jawo makullansa na gida bayan ya shiga bandaki, cikin few seconds yayi abinda xai yi ya
ajiye sauran sannan ya fita dakin....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
_Albishirin ku jama’a ko kusan akwai wani company da ya shahara wajen siyar da kayan alatu da abubuwan
more rayuwa??
Wato Unique & Luxury Stores yana da bangararori daban-daban kamar haka,
@unique_home_store_ng wanda ya shahara wajen siyar da kayan ado da qawata gida, kayan kitchen,
furniture, carpet na gani na fada da sauran su.
Sannan akwai @elegant_projects_ng
Bangaren tsara gida kamar home styling na amare da uwar gida, interior designing da finishing....
Company bai tsaya a sashe 2 kawai ba yana da bangaren ado da kwaliya wato
@uniquefashion_ng. Duk bai tsaya anan ba ya kara zuwa maku da @unique_souq_ng inda zaku samu
kayan kwadayi, makulashe da kayan da zasu kara inganta maku lafiyar jiki.
Karku bari ayi babu ku domin gane ma idon ku, ku garzaya shafukan su a Instagram kamar haka....
@unique_home_store_ng
@uniquefashion_ng
@unique_souq_ng
@elegant_projects_ng
Sannan zaku iya samun su ta WhatsApp a +2349071721586
Jiddah ce xaune bedroom din Umma dake mata tambayoyi, ita dai ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Kar
kiji komai ki fada min gaskiya Jiddah" Tayi murmushin karfin hali ta dago kanta tana kallon Umma tace "Da
gaske ba komai Umma" Umma tace "Kin tabbatar?" A hankali Jiddah ta gyada mata kai, Umma tace "Yace
ya kawo maki mai aikin haka ne?" Ta kalli Umma sannan cikin sanyin murya tace "Eh" Shiru Umma tayi
tana kallonta don sai take ganin kamar ba gaskiya take fadi ba, tausayin Jiddah take a xuciyarta, ta kwantar
da murya tace "Ni baxan ce masa mun yi maganan komai da ke ba Jiddah, ki bani amsan tambayoyina kafin
su dawo masallaci yanxu" Jiddah ta kuma wani murmushi tace "Umma na baki amsan ai" Umma tace "Toh
kina jin dadin xaman gidan?" Kallonta Jiddah ta dinga yi ta kasa cewa komai, Umma tace "Ina saurarenki..."
Lkci daya hawaye ya kawo idonta, dai dai nan aka bude kofar dakin, Ahmad ya shigo tare da Abuturrab,
sosai gabansa ya fadi, ya kalli Umma sannan ya kalli Jiddah, Umma dai ta daure fuska tana danna wayarta,
Ahmad dai na tsaye bakin kofa bai karaso ba, ya dinga fatan Jiddah ta sanar ma Umma bata boye mata
komai ba, Abuturrab ya shafa kansa a hankali yace "Umma dare na yi xa mu wuce gida" Umma tace "Ohk"
wasu sabbin hawayen ya dinga sauka idon Jiddah, gaba daya Abuturrab ya kasa nutsuwa, kana ganinsa ka
ga mara gaskiya, Umma na kallon Jiddah tace "Tashi ku je sai da safe" Ta kalli Abuturrab tana goge idonta,
ya jefa mata wani kallo a fakaice, a hankali ta mike hawaye yaki tsaya mata tace "Sai da safe Umma" Umma
bata iya ta amsa ba Jiddah ta nufi kofa, Abuturrab na kallon Umma yyi kasa da murya yace "Sai da safe Sai
Umma" Ba tare da ta kallesa ba tace "Allah ya kai mu" Ya kalli Ahmad that is still standing wanda har ransa
yake jin hawayen da jiddah take, Abuturrab ya ki ce masa komai ya fita dakin, Maimuna da siyama ne suka
dau ma Jiddah abubuwan da Umma ta hada mata tun daxu xuwa motar Abuturrab, Jiddah dai na xaune
gaban motar kamar ana dada tunxurata da kukan da take, Abuturrab ya tada motar ya bar gidan, sai a
sannan ya sauke ajiyar xuciya, he even love it da Umma taki ce masa komai, har suka isa gida bai ko kalli
Jiddah ba, yana parking ya sauka ya tafi ya kulle gate din gidan ya dawo, tsaye ya ganta jikin motar fuskar
nan nata kamar warce aka aiko ma da sakon mutuwa, ya hade rai yace "Ni xan dauko maki kayan naki dake
cikin motar" ta juya ta bude bayan motar tana goge guntun hawayenta ta dau ledan hijabs din da Umma
tayi mata da warmer din tuwo da miyar kuka da Umma ta sa a xuba