Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
yanda Jiddah taki dago kanta shi ma haka ya ki kallon inda take,
Bayan few seconds yace "Hajja na jira na Umma" Umma tace "Toh Allah ya tsare" mikewa yayi yace mata
sai anjima sannan ya nufi kofa, Jiddah dai taki dagowa ko da wasa, Umma sai kallonta take kamar dai tana
son gano wani abu, bayan fitar Abuturrab tace "Me ya sameki jiya da daddare a can gidan?" A hankali
Jiddah tace "Ciwon ciki nake yi?" Umma tace "Ikon Allah, amma da sauki yanxu?" Tace "Idan yayi min sauki
sai ya fara kuma" Umma tace "Toh Allah ya sauwake bari anjima Ahmad ya xo sai ya baki magani ko kuma
aje asibiti" Jiddah dai bata ce komai ba, Umma tace "Kin karya?" Girgixa mata kai tayi, Umma tace "To tafi
ki karya" Mikewa tayi a hankali ta nufi kitchen Umma ta bi ta da kallo ganin duk tayi wani irin sanyi. Hajja
na shigowa parlon Abba ganin Aunty da Ummi sai Aneesah a parlon ta dinga bin su da kallo tace "Wacece
wannan kuma?" Lkci daya Aunty ta murtuke fuska, Ummi tace "Sannu da xuwa Hajja" Hajja tace "Yauwa
me ke faruwa a nan din?" Abba dake xaune shi ma parlon yace "Sannu da xuwa" Hajja tace "Ba batun
sannu da xuwa ba, xaman me ake a nan?" Dai dai nan Abuturrab ya shigo parlon da sallama, tun karfe tara
Abba ya kirasa yana nemansa a gida, suna mota kuma yake sanar ma Hajja cewar Abba yace yaje, Kallo
daya yayi ma Aneesah da ta sha lullubi da babban gyale wanda da alama Aunty ce ta 6ata, ya dauke kai ya
xauna saman carpet yana kallon Abbansa yace "Ina kwana Abba?" Abba yace "Lafiya lau" Kallon Ummi yayi
ya gaisheta, snn ya gaida Aunty da tayi masa banxa, Hajja dai na tsaye kansu kamar soja, Abba yace "Ga
kujera Hajja" Hajja tace "Aa bar ni in tsaya abuna, mu da muka sa6a tsayuwa a Masar" Aunty na kallon
Abba tace "Alhaji i think we can leave the sitting for now, may be in the evening" Abuturrab ya kalleta yace
"Yau xan koma aiki in sha Allah" Wani shegen kallo Aunty tayi masa tana kallon Aneesah tace "Tashi mu je"
Hajja tace "Ta tashi aje Ina? Ina ce k'aran jikana ta kawo ko? to wllh sai kun ga walakanci da tarban tsiyar
da matar nan tayi mana ni da Jiddah, ni dai har hawaye sai da nayi a boye don tunda uwata ta haifeni ban
ta6a ganin anyi haka ba a Masar, sannan gida dai in baku labari da muka shiga duk wari, wllh ta rubar masa
gida, kitchen kuma dai ya fara wasu irin tsutsa, bandakin gidan duk sunyi gantsa kuka, to banda lalacewar
yaran kasar nan daga nayi mata gyara sai ta kawo karata da na jikana har a wani xauna xa ayi meeting a
kanmu?? Ehh lallai yau nake ganin lalacewa a Najeriya" Abba dai yyi shiru bai ce komai ba, haka Ummi da
kanta ke kasa, Aunty sai tafarfasa xuciyarta yake tana kallon Hajja, Hajja ta ta6e baki tana gyara yafin
gyalenta tace "Hatta abincin da xa mu ci sai da yaron nan ya fita ya samo mana, to ina girki xai yiwu a wnn
axabbabben kitchen din duk wari, salon ma mu ci mu tsuge da xawo idan an girka, wllh da ido daya nayi
bacci a gidan sbda datti da kazanta, to bari kuji ita yar rakiyar tawa ma da ciwon ciki ta kwana a gidan
tsabar kazantar gidan kuma ni nasan hakan na da nasaba da ruwan da muka sha na gidan, yanxu haka tana
can baiwar Allahn tana jinya gun uwar rikonta ni dai duk ni na ja mata bani da bakin magana, to idan ba
rashin kunya ba shine har xata kwaso kafafuwarta kamar kara tace ta xo kawo kararmu, bayan duk hakurin
da jikana ke yi da ita?? Lallai ma, ai ni da Masar har abada jikana na wannan halin, in sha Allahu sai na
samar masa mata me tsafta irinsa warce xata dinga gyara masa gida" Abba na kallon Aunty da turanci yace
"Su tashi su tafi kawai da Aneesah" Kamar jira take ta mike ta daga Aneesah suka fice daga parlon tana
huci. Hajja ta kalli Abba ta ta6e baki sannan ta kalli Abuturrab da ya sunkuyar da kansa tace "Tashi mu je o,
Allah ubangiji ya kawo maka karshen jarabawar nan da kake ciki" Daga haka ta nufi kofa abunta.... Bayan
azahar Ahmad ya shigo gidan Umma, bayan sun gaisa da Umma yace "Su Maimoon sun tafi Islamiyya ne?"
Umma tace "Ehh sun tafi Jiddah dai ce bata je ba, bata jin dadi" Yace "What's wrong with her?" Umma
tace "Wai ciwon ciki take, dama jira nake ka xo" Yace "Wani irin ciwon ciki tace?" Umma tace "ka kai ta
asibiti kawai, ai nima ba sani xanyi ba" Yace "To Allah ya sauwake" Umma tace "Ameen" yace "Tana daki
ne?" Umma tace "Ehh bari Huraira ta kirata idan ba bacci take ba" Umma na fadin haka ta kirawo Huraira,
Huraira ta tafi dakinsu Maimoon, kwance ta tadda Jiddah saman gado tayi shiru, Huraira tace "Ya jikin
Jiddah?" Jiddah ta mike xaune tayi murmushi tace "Naji sauki" Huraira tace "Toh Allah ya kara lafiya,
Umma na kiranki' Jiddah tace "Toh" Sannan ta sauka saman gadon, tun da safe bata sake jin ciwon cikin ba,
amma gaba daya jikinta a sanyaye yake, hakan ne da Umma ta gani yasa tace ta xauna gida kawai ta xata
duk ciwon cikin ne, Jiddah na fitowa parlor ta xauna kasa ta gaida Ahmad dake kallonta ya amsa da
murmushi fuskarsa yace "Ya jikin?" Tace "Naji sauki" Umma tace "Cikin ya maki sauki?" Jiddah ta gyada
mata kai tace "Ehh ya daina yanxu Umma" Umma tace "To sannu, Allah ya sauwake" Ta sunkuyar da kanta
tace "Ameen" Ahmad yace "Why not ta dakatar da amfani da drugs da aka rubuta maku a hospital for the
meantime Umma?" Umma tace "Kana tunanin shi ke sa mata ciwon?" Yace "Ta dai dau break na wani d'an
lkci a gani" Umma tace "Toh shkkn" Yace "Xan siyo mata pain reliever yanxu" Umma dai sai kallon Jiddah
take ganin yanayinta, Ahmad yace "Umma gobe kika ce xa a kai ta makarantar ko?" Umma ta kallesa tace
"Ehh" Yace "Toh idan xan koma gida sai mu tafi tare da ita, idan ya so gobe da safe sai mu je makarantar"
Umma tace "Daga nan din baxa ka iya xuwa ka dauketa ba?" Yace "Toh shkkn Allah ya kai mu" Umma ta
kalli Jiddah tace "Tashi ki je ki ci abinci" Ba musu Jiddah ta mike ta wuce kitchen. Sai kusan la'asar Ahmad
ya shirya xai koma gida, bayan yayi ma Umma sallama tace "Shkkn kawai ta dau kayanta kala daya ko biyu
ku tafi can gidan din" Yace "Ohk toh" Umma ta tafi da kanta daki wajen Jiddah ta sanar mata xa su tafi
gidan Ahmad tare, ta dau kayanta kala biyu, Jiddah bata mata musu ba tayi yanda Umma tace sannan ta
fito parlor rike da jakarta. Huraira dake tunanin har sannan Jiddah bata jin dadi ne ta amsar mata jakar ta
kai motar Ahmad, Ahmad yyi sallama da Umma, jiddah ma tayi mata sallama, Umma tace "A gaida
Ramlah" daga nan suka fita gidan, Suna shiga motar Ahmad yaga missed calls din Abuturrab har uku a
wayarsa da ya bari a cikin mota, Sai da ya tada motar yyi reverse sannan yayi dialing number Abuturrab
din, yana dagawa Ahmad ya kai kunne yace "Ya aka yi?" Dariya Ahmad yyi yace "Ni fa wllh kana bani
mamaki Captain, ga dai matarka ka bi ka takurani in maka prescription drug? Are u even okay?" Jiddah
dake xaune gefensa cikin motar taji gabanta ya fadi jin sunan da ya ambato, Ahmad yace "Toh ka taho gida
ka amsa, ina driving yanxu..." Daga haka ya katse wayar yana maida hankalinsa kan titi, sai da suka yi nisa
yace "Kin ma san gidana kuwa Jiddah?" Ta kirkiri murmushi tace "Um na sani, mun je sau uku" Yace
"Would u like to stay in my house ki dinga xuwa makaranta daga can?" Jiddah ta d'an buda ido ta kallesa,
yace "Yea, sai ki xauna ke da Ramlah koh??"
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
MG'S SKINCARE
In akaji gangami labarin kidane,sun shahara sun tumbatsa sunkai sunwuce tunanin duk wani meson
Adama dashi aharkar gyaranfata d walwalinta,
Yar uwa haske ko qyalqyale kikeso kiyi Abu yaci tura?
Kyan fuskarda ko yar uwarki mace kance dama dama kikeso?
Kokuma ke kuraje d tabbuna suka lahanta mki fuska har ake ganinki d wani idon n daban,
Nankarwace tayimiki zanen kura a kyakyawar fatarki?
Kokumade Mai kikashafa be amshekiba yasa duk kika koma ruwa biyu Nan fari Nan baqi?
To duk kuzo insha Allah kudai naku y qare gdan kukazo,
Munkawo shahararrun kayangyaran jiki
Sabulu,
Man shafawa,
Man fuska,
Scrub,
Cleanser,
Glow oil,
Dukdan qawarmaku d matsaltsalunku,
Da 11k kachal zatasa kihaske kizama kalar madara qirar models,
Set 11k
Sabulu 3k
Student package:7k
Munakuma bayarwa in pieces duk afarashin mesauki.kayanmu bbu fariya ko tutiya angwada
andawo,ankumayi farinciki d hkan,Kuna iya samummu d wadannan numbobin,
WhatsApp,
08062991549 or 07046881166 or 07067210195
Call only
08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Idanba wadannan numbobinba to gaskiya b mg's bane, available in Kaduna and Kano only, thanks for
always trusting us,our returning customers we really do appreciate wadanda sukeda burin Siya munamaku
fatan alkhairi ubangiji ybaku yenda zakuyi,Allah Kuma yqaro mna dukiya me amfani ta hanyar halalinmu.
Murmushi kawai Jiddah tayi bata ce komai ba, Ahmad bai kuma ce mata komai ba shi ma, suna isa wani
babban pharmacy yayi parking yana kallonta yace "I am coming let me get u pain reliever, Umma tace kina
ciwon ciki ko?" Ta gyada masa kai ya kashe motar ya sauka ya shiga cikin pharmacy din, ba a wani dau lkci
sosai ba ya fito da ledan magani, ya shiga motar yana kallonta ya ajiye mata kusa da ita yace "Ko kina
bukatar wani abun daban, akwai Supermarket a nan..." Ta girgixa kai tace "Aa bana bukatar komai" Yace
"Ohk" sai da suka hau saman titi ta d'an kallesa amma bata ce komai ba, ganin haka yace "Say what is in ur
mind Jiddah, be free with me and take me as ur elder brother" Ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Ni
yanxu baxan iya xuwa in ga Baabarmu in gaisheta ba?" Da d'an mamaki yace "Baabarku? Me xaki yi mata
idan kinje, ko kuma me xata maki ita?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Babu amfanin xuwa wajenta a
yanxu dai Jiddah, idan kinyi hakuri wataran babu wanda xai hanaki xuwa gareta, when the rightful time
comes da kanki ma xaki je ba sai wani ya kai ki ba kin ji?" Cikin sanyin murya tace "Toh, amma kuma akwai
wata tsohuwa a layinmu ana ce mata Iyah, tana da kirki sosai, ko ita ma baxan iya xuwa in gaisheta ba?"
Yace "Baki tunanin xata gaya ma Baabarku kin je?" Ta girgixa kai da sauri tace "Aa baxata fada ba, ai ita ba
haka take ba, ita ce fa ke taimakona lokacin da nake gun babarmu, har abinci tana bani idan tana da shi"
Yace "Toh yanxu kina son a kai ki can kenan?" Ta gyada masa kai a hankali, ya d'an yi shiru yana ci gaba da
driving dinsa, kallon agogon wrist dinsa dake nuna karfe hudu da wani abu yayi, sannan yace "Kinsan me
Jiddah?" Jiddah na kallonsa ta girgixa masa kai, yace "Ki bari ko gobe da daddare in kai ki, tunda kina
gidana, i think it will be more safer..." Jiddah tace "Toh nagode" Yayi mata murmushi kawai. Suna isa
gidansa yayi parking a space din parking sannan ya sauka motar ita ma ta sauka, tana biye da shi suka shiga
gidan, Xaunawa tayi a parlor shi kuma ya wuce bedroom dinsa sanin Ramlah na can tana bacci, xai shiga
dakin sai gata ta fito, ya d'an buda ido yace "Ashe ba bacci kike ba" Ta turo baki tace "Ina ice cream din?"
Yace "Ohh kinga na mance wllh, I'm sorry anjima xan fita sai in siyo maki, fito ku gaisa da Jiddah" Ramlah
tace "Da gaske?" Yace "Ehh" a tare suka dawo cikin parlon, Ramlah ta xaro ido tace "Lallai sis Jiddah ce yau
a gidanmu, ashe xa ayi ruwa da kankara" Jiddah tayi murmushi tace "To ai ina xuwa" Ramlah ta karaso ta
xauna kusa da ita tace "Aa sau biyu ina ga kika taba xuwa, ina fa sane, to ya su Umma?" Jiddah na
murmushi tace "Lafiya lau, ya jiki?" Ramlah tace "Naji sauki Alhmdlh" mikewa tayi ta dau jakar Jiddah tace
"Mu je ciki to" Jiddah ta mike ta bi bayanta, Ramlah ta kai ta dakin visitors, sosai Ramlah taji dadin xuwa
Jiddah gidanta, Ramlah tace "Gashi ni banyi girki ba wllh, ko in dafa maki indomie kafin a daura dinner?"
Jiddah tace "Daga gida fa muke, ai na ci abinci" Ramlah tace "Toh bari in kawo maki ruwa" Bata jira cewar
Jiddah ba ta fita dakin, sai da Ramlah ta daura ruwan shinkafa a gas snn ta dau tray ta daura Chivita drink
da ruwan gora sai glass cup ta dawo daki ta ajiye tana kallon Jiddah tace "To ga ruwa ki sha sis Jiddah"
Jiddah ta d'an yi murmushi tana kallon hancinta dake shige da na Abuturrab, har idanuwansu iri daya ne,
dama kuma duk a cikinsu ita tafi kama da shi, Ramlah ta xauna tana ta jan ta da hira, tun Jiddah na shiru
shiru har dai ta fara biye mata, lkci daya Ramlah tace "Ohh na manta na daura ruwan shinkafa a gas, bari in
xuba shinkafar in dawo" Jiddah tace "Toh bari in wanke in xuba maki" Ramlah ta nufi kofa da sauri tace "Aa
wllh... Ai ba wani aiki bane" Daga haka ta fita, xaune ta tadda Abuturrab a parlor da Ahmad, Ta d'an buda
ido sai kuma ta washe baki tace "Yaushe ka xo yaya?" Karasawa tayi ta duka gefensa tace "Welcome Yaya,
ina yini?" Ya kalleta yace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhmdlh, ya aiki?" Yace "Fine Alhmdlh" mikewa tayi ta
wuce kitchen, Ahmad dake shafa beard dinsa yana kallon Abuturrab yace "ina jin ka great Captain"
Abuturrab yace "Kana jina na me wai, kai fa idan kaga mutum na neman abu a wajen ka ka dingi
walakantasa kenan" a takaice Ahmad yace "Toh ka tafi asibiti kawai" Abuturrab ya dinga kallonsa, Ahmad
yace "Yes, nasan kana da mata baxan rubuta maka wannan maganin da kace ba, ko dai Hygiene din ne bai
kai yanda kayi expecting ba? Abu d'an sauki tunda kana da wadata sai ka kara aure kawai" Da dariya
Ahmad ya kare maganar, Abuturrab dai ya kasa ce masa komai, Jiddah ce ta fito parlon rike da tray din
lemon da Ramlah ta kai mata don xuwa kitchen ta taimaka ma Ramlah da girkin da tace xata yi, Tsaye tayi
bakin corridor din dakunan ganin Abuturrab a parlon kafin ya ganta ta juya da sauri har tana tuntube ta
koma ciki ta shige daki ta kulle kofar gabanta na faduwa sosai, Abuturrab ya kalli direction din don rufe
kofa kawai yaji, can ya kalli Ahmad yace "Who is there?" Ahmad yace "Bakuwa muka yi" Abuturrab yace
"Ohk" Ramlah ta fito kitchen ta ajiye masa ruwa da drink tace "Amma yaya ba yau xaka koma kano ba ko,
naga yamma yayi" yace "Gobe da safe in sha Allah" Yana fadin haka ya dau bottle water daya ya bude ya
sha ya mayar ya ajiye sannan ya mike yace "Sai anjima...." Ahmad dai sai murmushi yake yana kallonsa,
Ramlah tace "Yaya ka tsaya ka ci abinci mana pls..." Yace "What are u cooking?" Tace "Shinkafa da miya ae
bai da wahala" Yace "Idan naje can gida xan ci, yanxu gida xan wuce" Daga haka yayi ma Ahmad sae da
safe ba tare da ya kallesa ba ya nufi kofa ya fita. Gidansu ya tafi, direct ya tafi bangaren Umminsa, fitowa
tayi daga bedroom jin an bude kofar parlor, ganin shi ne ta koma dakin, ya bi ta har can, xaunawa yyi gefen
gado sannan ya gaisheta, ta amsa tana kallonsa, bai kuma ce mata komai ba tace "Me ya hadaka da
matarka?" Ya kalleta yace "Ummi ita da Hajja ce, ni ban mata komai ba wllh" Tace "Why did u create room
for that, me yasa baka dakatar da Hajjar ba?" Yace "Sanda suka yi ma ni bana gidan, and na bata hakuri but
she didn't listen to me tayi tafiyarta kawai" Ummi dai tayi shiru tana kallonsa, can tace "Are you okay?"
Daga kai yayi ya kalleta sai kuma yayi murmushi yace "Did u notice anything mum?" Tace "Are u answering
my question with a question?" A hankali yace "Kawai ki taya ni da addu'a Ummi" tace "Me ke faruwa?" Ya
girgixa mata kai yace "Ba komai addu'a kawai nake bukata" Tace "Saboda ni ai bani da matsayin da xaka
gaya min matsalarka ko?" Ya kalleta a hankali yace "Ko daya Ummi, ni kaina ban san me ke damuna bane"
Tace "Toh Allah ya yaye maka" Yace "Ameen" Yace "Ummi in a month time xamu fita waje fa..." Tace "Xuwa
yin me?" Yace "Aa wani babban mutum xa mu yi piloting" Ummi tace "Toh Allah ya kai mu, sai ku dawo
yaushe?" Yace "Ban sani ba dai, sai yanda suka ce" Ummi tace "To Allah ya tabbatar da alkhairi" Yace
"Ameen" tace "Yanxu ka tashi kaje ka ba matarka hakuri ka dauketa ku tafi gida tare, ba sai an sake wani
xaman ba" Shiru yyi, Ummi dai na lura da shi, can yyi kasa da murya yace "Ummi Aneesah bata son xaman
lafiya tare da ni, I don't know why she changed all of a sudden from who I knew her to be, kamar ana
xugata kullum, kinga bata mutunta ni bata kunyar gaya min ko wani magana ya xo bakinta, sannan i wish u
can come one day ki ga yanda ta mayar min da gida, kawai fa sai dai tayi wanka ta fesa turare abinda ta iya
kenan, tsaftace muhalli Zero, girki Zero, ibada Zero, kullum sai nayi fama da ita a kan sallah, I'm so tired
and fed up Mum, ko wata biyu fa ba ayi ba, har xullumin dawowa weekend nake wllh Ummi" Ummi da tayi
shiru tana kallonsa taji tausayin d'an nata amma taki nunawa, can tace "Toh me yasa baxa ka daukar mata
mai aiki ba?" Da sauri ya kalli Ummi yace "House help kuma Ummi? Warce ta xauna kafin ita a gidan duk
da karancin shekarunta da rashin wayewarta ai ban daukar mata mai aiki ba, kuma komai na gidan ita ke
yi, sannan ni ban ta6a dawowa weekend naga ba dai dai ba" Ummi dake kallonsa kasa kasa tace "Wacece
ta xauna kafin ita?" Shiru yayi bai ce komai ba, Ummi tace "Wai Jiddah kake nufi?" ya daga