Advertisements
Chapter 41 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   41 / 108

120K to 123K   out of 321.7K words

tayi ma
Ummi sallama bayan ta daga wayar, suka gaisa sannan tace "Yaya ashe Aliyu bai ji dadi ba" Ummi tace
"Ehh haka aka ce min" Umma ta kalli Ahmad tace "Wai dama ba can gida yake ba?" Ahmad yace "Can
yake" Umma tace "Toh baki shiga kin dubasa bane Yaya?" Ummi tace "Aa masu dubasa dai nayi, ni yace
min bashi da lafiya ne?" Umma tace "Aa yaya ai rashin lafiya daban ne, da kin shiga kin dubasa ai, nima
ynxu Ahmad ke gaya min shi ya taho da shi daga Abuja ma" Ummi tace "Allah ya kara mana lafiya gaba
daya" Umma ta d'an yi shiru sae kuma tace "Toh Ameen" sallama suka yi ta ajiye wayar, Umma ta kalli
agogo dake nuna biyar da rabi sannan ta kalli Jiddah tace "Malamar ta tafi ne?" Jiddah tace "Ehh ta tafi"
Wayar Umma ya fara ring ganin Ummi ke kiranta ta dau wayar ta mike ta wuce cikin daki, Ahmad na kallon
Jiddah yace "Hope baki bukatar wani abu yanxu?" Ta girgixa kai tace "Aa ba komai" Yace "To ya karatun?"
Tace "Alhmdlh" Yace "Kina dai ganewa sosai ae" Murmushi kawai tayi tace "Ina ganewa" yace "Toh ki dinga
maida hankali sosai pls kin ji?" Ta gyada masa kai, a hankali tace "Ina son in tambayeka wani abu" yana
kallonta attentively yace "Toh ina jin ki Jiddah" Ta sunkuyar da kanta tace "Don Allah xaka iya kai ni can
gidanmu in ga Baabarmu?" Sake baki yayi yana kallonta, can yace "Me xa kiyi ma baabar taku?" Cikin
sanyin murya tace "Ina son xuwa in gaisheta" Ahmad ya girgixa kai yace "ko xaki je ba yanxu ba tukun
Jiddah...." Tayi kasa da murya tace "To akwai wata Iyah a layinmu, tana min kirki sosai, baxan iya xuwa
gaisheta ba ita?" Da mamaki Ahmad ke kallonta, can dai yace "A layin baabar taku?" Ta sunkuyar da kanta,
Murmushi kawai yayi ya rasa abinda xai ce mata... Umma ce ta shigo parlon, tana kallon Ahmad tace "Idan
anyi magrib sai ka kai ni can gidan in duba Aliyun" Ahmad yace "Toh Allah ya kai mu" kitchen ta wuce,
Jiddah na kallonsa tace "Bashi da lafiya ne?" Ahmad yace "Ehh amma da sauki" Tana kallonsa tace "Nima
xan iya bin ku in gaishesa da jiki?" Ahmad yace "Sai yanda Umma tace" Bata kuma cewa komai ba, bayan
few seconds ta kallesa taga kallonta yake, murmushi ya sakar mata, ta sunkuyar da kanta tana murmushin
ita ma sannan ta mike tace "Xan kai kayan karatuna daki" Yace "Toh Jiddah" Tana fadin haka ta yi hanyar
dakinsu. Da magrib kamar yanda Umma tace ta shirya don xuwa duba Abuturrab tare da Ahmad, Jiddah ta
rasa ta yanda xata ce mata ita ma tana son xuwa ta dubasa, ganin Ahmad ya fita kafin Umma ya fito ta bi
sa da sauri ta riskesa a waje tace "Yaya don Allah xaka tayani gaya ma Umma, ni ina jin tsoro" Ya wara ido
yace "Aa nima ba ruwana sai dai ki gaya mata da kanki" Jikinta yayi sanyi, a hankali tace "Toh" sannan ta
juya ta koma cikin gidan, Umma ta fito parlor da hijab da jakarta tana kallonsu Maimoon dake parlon tace
"Kar dai ku bar ruwa ya cika yyi ta xubewa...." Maimoon tace "Umma ni ma xata da mu xa ku je mu duba
yayan muma?" Umma tace "Ba cewa kika yi kina da Hadda ba" Maimoon tace "Toh shkkn sai kun dawo"
Safiyya dai na xaune tana danna wayarta, Umma ta nufi kofa Jiddah ta bi ta da kallo, a hankali tace "Umma
sai kun dawo" Umma tace "Yauwa, kema kiyi karatun ki duk da dai ba kallo kike ba na sani" Jiddah bata ce
komai ba har Umma ta fita parlon... Umma na shiga mota Ahmad ya kalleta yace "Umma na xata da su xa
mu je can gidan su duba Aliyun, daxu Mumy ta tambayeni nace xan taho da su...." Umma tace "Toh ai ni
baka gaya min ba, kuma sai a bar Huraira ita kadai a gidan?" Ahmad yace "Toh shkkn" Xai tada motar
Umma tace "Bari su fito din dai" Wayar Safiyya Umma fa kira, tana dagawa tace "Safiyya wai yayanku ku
fito mu tafi tare" Tana fadin haka ta katse wayar, Tun da suka fito outside gate din Ahmad ke kallon Jiddah
sai dai ba ga expression da yake expecting gani a fuskarta ba, ita da Maimoon suka shiga bayan motar
sannna Ahmad ya kunna motar suka bar layin.... A kofa gida yayi parking, Safiyya ta sauka sannan jiddah
ma ta sauka, su Umma ma suka sauka duk suka shiga gidan, Ummi ce xaune parlor tare da Hajja, Hajja na
cewa "Tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin irin haka ba wllh sai a kanki..." Sai kuma tayi shiru tana amsa
sallaman Umma, Umma tace "Sannu Hajja" Hajja tace "Yauwa sannu, sai kika ji Aliyu ba lafiya ko?" Umma
tace "Eh wllh" Hajja tace "Toh mu ma haka muka ji, ashe wannan yaro Ahmad ne ya tafi ya dauko sa a
Habuja rai a hannun Allah, ni dai dama nace wannan halin da ya tsiro ma kansa ba halinsa bane, ashe
bashi da lafiya ne bawan Allah" Umma tace "Allah dai ya basa lafiya, yana dakinsa ne?" Hajja tace "Ehh
yana can an kara masa ruwa, kai har makota babu wanda bai shigo dubasa ba amma uwarsa ta ki shiga ban
san dalili ba" Umma dai bata ce komai ba ta yi hanyar dakin Abuturrab, yana xaune hannunsa rike da bowl
din farfesun hanta, Aunty ma na xaune dakin tana cewa "Idan ka ci wllh xaka ji dadin bakinka, sannan kar
kaji komai ni da kaina na maka sai da na tsaftace shi" Aunty tace "Aa sannu da xuwa Hajiya Ramlah" Umma
tace "Yauwa sannu ya mai jiki?" Aunty tace "Aa yaji sauki wllh, ai da ma baku wahalar da kanku kun fito ba,
jiki ai da sauki sosai" Umma na kallonta tace "Xuwa duba d'an nawa ne wahal da kai?" Aunty tace "Aa wai
naga dare yayi ne ai..." Umma tace "To ba wahal da kai bane, d'a na ne halaq malaq" Aunty dai bata ce
komai ba, Umma na kallonsa tace "How are you feeling now" Ya sunkuyar da kansa yace "Alhmdlh da
sauki" Aunty tace "Nace maki ai da sauki" Umma ta kalleta tace "Naga shi ma yana da baki ai Hafsah"
Aunty ta mike tace "Bari a kawo maka shayin Aliyu" daga haka ta fita, Maimoon da Safiyya ne suka shigo
dakin da sallama, Umma da ta nemi waje ta xauna ta kallesu tace "Ina Jiddar?" Sai a sannan Abuturrab ya
daga kai suka yi ido hudu da Jiddah da ta shigo dakin a lkcn, Maimoon da Safiyya suka xauna kasan carpet
din dakin suna kallonsa suka yi masa ya jiki, yace "Alhmdlh" kusa da Umma Jiddah ta xauna a kasa tana
kallonsa a hankali tace "Ya jiki?"


Ayi min afuwa jiya ban dawo da wuri gida ba... Idan naga da sarari xanyi update later in sha Allah... Thanks
for understanding.



Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems

Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240



Jiddah ta juya tana Kallonsa, ya shigo ya kulle kofar, tana ajiye plates din a plate Rack tace "Ina yini?" A
takaice yace "Ki daina gaisheni idan kin gan ni, bana so" tace "Toh" Ta dau plate daya ta bude warmer ta
debi abinci still bata kallesa ba tace "Ya jikin" Yace "Ke yanxu a xatonki da tunaninki 'yancin kanki kika samu
ko?" Sai a sannan ta juya ta kallesa suka hada ido, ya hade rai yace "Don kinga Maimoon na daukan mayafi
karami ta saka ta fita titi kema sai kika fara saka mayafi karami, kin ma mance ke wacece koh" Shiru tayi
bata ce komai ba ta kai hannu ta dau cokali, ya wani daure fuska yace "Kin saba saka mayafi daga can hayin
rigasa ne, balle kuma gidana da kika xauna?? Kina tunanin ke da Maimoon daya ne?" Tace "To amma ai
Umma ta gani bata ce komai, kaga da tace min in cire ai baxan sa ba" Yace "Toh daga yau ko nan da gate
kada ki sake sa mayafi ki fita..." Da mamaki take kallonsa, can dai tace "Ko saboda me?" Yace "Saboda haka
na fada" Bata kuma ce masa komai ba, yace "And yanxu kina ganin kin fi kowa freedom shi yasa kike shiga
motar maxa har da xama gaban mota ko, uban wa ya ce ki bi ta ku hau motar wani kato har kika shiga
gaba, a can hayin rigasar ku haka kike yi" Tace "Kamawa tayi in hau shi yasa na hau ba wani abu ba, kuma
ai an san sa a gida" Bude baki yayi yana kallonta, yace "Kin san mene?" Ita dai ta xuba masa ido, yace
"Akwai wani wanda yayi dalilin dawowarki cikin gari a duk wa enda kike xaune da su yanxu cikin garin
kaduna??" Kallonsa kawai ita dai take, yace "Toh dama ai nine na fito da ke cikin gari, don haka yanxu sai in
mayar da ke in da na dauko ki, duk me son sake fitowa dake cikin gari sai ya koma hayin rigasa ya dauko ki
na musamman... Kin fahimce ni??" Murmushi kawai tayi tace "Toh" yace "Ehh, ni na raboki da baabarku
kuma ni xan maida ki" Tace "Yaushe xan shirya kenan?" yace "Sai kin shirya ashe, dama kin xo da wani
abun ne ban sani ba?" Tace "To shikenan" Ya jefa mata wani irin kallo ya fice daga kitchen din ta bi sa da
ido, hawaye taji ya kawo idonta, ta rufe abincin ta fita ta koma daki ta kulle kofa ta kwanta saman gado
tana iya kokarin ganin bata fashe da kukan dake cin ta ba... Har karfe uku Jiddah na kwance daki, Huraira ta
xo ta kwankwasa kofar jin an sa makulli tana kiran sunanta, Jiddah ta mike da kyar ta isa gun kofar ta bude
Huraira tace "Jiddah malamarki ta xo fa tun daxu..." Shiru tayi tana kallon idonta tace "Me ya faru Jiddah?"
Ta girgixa mata kai tace "Kaina ke ciwo" Huraira tace "Subhanallah, to ki fito Umma na kiranki" Komawa
tayi ta dau hularta ta sa sannan ta fito dakin, a hankali ta nufi parlor ganin Umma da Hajja a xaune, ta
sunkuyar da kanta ta xauna a kasa tace "Umma gani" Umma tace "Amma dai nace ki daina barin
malamanki na jiranki ke ya kamata ki dinga jiransu ko Jiddah, dole sai kinyi wani bacci idan malamar safe ta
tafi bayan kin san cewar dayar na kan hanya ita ma" Jiddah ta kasa dago kanta cikin sanyin murya tace
"Kuyi hakuri Umma, ciwon kai nake" Sai a sannan Umma ta kalleta da kyau tace "Ciwon kai tun yaushe,
shine kike kuka?" Ta girgixa ma Umma kai kawai, Umma tace "Toh kin ci abinci" Ta gyada mata kai kawai,
Umma tace "Toh Allah ya sauke kije dakina akwai paracetamol kan bedside drawer ki dauka, amma xaki iya
karatun kuwa yau?" Cikin sanyin murya tace "Xan iya Umma" Umma tace "Toh je ki dauka ki sha ki dau
qur'anin ki ki fita, Allah ya sauwake" Mikewa Jiddah tayi ta wuce dakin Umma, Hajja tace "Mu dai ba gamu
mun taho jinyan wancan mutumi da har yanxu tun wayewar gari ban daura ido a kansa ba" Umma tace
"Na duba na gansa yana bacci daxu" Hajja tace "Ni wllh dama ki sa duk ya tattaro kayansa ya dawo gidan
nan a rabosa da yar Benuen can, ko ya kika ga" Umma tayi wani murmushi tace "Ai baxai dawo ba, wnn ma
nayi mamakin da ya yarda ya biyo mu, ina ga tunda yake bai ta6a kwana gidan nan ba ko da xai kai karfe
sha biyun dare" Hajja tace "To mu dai gamu ga Allah, amma Hauwa tayi sake ai, idan ta bar ta ta kwace
miji sai ta yarda har d'anta ta kwace, nima fa don ban xauna a Masar bane a banxa shi yasa har yau bata
rabani da Usman ba, kullum cikin tsayuwar dare nake, kyaga a rana sai ya kirani sau uku, to amma dai ba
komai tunda Allah yayi min dawowa ba dai nace maki xan nuna nata nima yar banxa bace, Allah ya ba Aliyu
lafiya mu koma gidan, na ma fasa komawa gidan Kabiru" Umma tace "Allah dai ya kyauta amma abun kam
sai addu'a" Ahmad ne ya shigo parlon ya gaishesu, Umma tace "Ya jikin Ramlan" yace "Da sauki Alhmdlh"
Hajja tace "Yaushe xaka sallami wancan mutumin mu koma gida in san ta ina zan fara da Hafsah?" Yace "Ai
yace baya son drip din kuma, magunguna kawai yake sha" Tace "Atoh ya tarkata magungunan mu wuce
gida kawai sai yayi ta sha a can" Duk suka kalli kofar Jiddah ta shigo parlon da sallama, Umma ta kalli agogo
tace "Ciwon kan bai yi sauki ba kenan" Gyada mata kai tayi, Hajja tace "To Malamar fa?" A hankali tace
"Tace inje in kwanta, ta wuce" Ahmad dake kallonta yace "Tun yaushe kan ke maki ciwo?" jiddah tace
"Daxu" Yace "Toh je ki kwanta, Allah ya sauwake" Tace "Ameen" Sannan ta wuce daki ta kwanta. Har kusan
karfe shidda Jiddah na daki tana jin kanta na mata wani ciwo ba kadan ba, Umma ce xaune parlor tare da
Abuturrab da fitowarsa parlon kenan, Umma tace "Ka bari gobe ka tafi" Ya kalleta amma bai ce komai ba,
tace "Kuma ka bude kunnenka sosai ka saurareni" Still shi dai bai ce komai ba yana kallonta, tace "Hafsah
kanwar uwarka ce ko ta Ubanka?" Sunkuyar da kansa yayi, tace "Toh bari kaji Aliyu, wllh idan kana son ka
dinga ganin dai dai a al'amuranka ka fita harkar matsiyaciyar nan ka kama uwarka..." Da mamaki yace "Me
tayi kuma Umma?" Umma tace "Ni kake tambaya me tayi?" Yayi kasa da kai yace "Toh Umma naga dai
lafiya suke xaune, kuma ita Aunty..." Umma tace "Tashi ka bani waje mara hankali kawai" Ya kalleta yace
"Aa kiyi hakuri Umma" Cikin daga murya tace "Ka fini sanin lafiya suke xaune ko ba lafiya suke xaune
bane?? tunda nake ban ta6a ganin d'an da ya hofintar da uwarsa ya dauketa ba komai ba yake bama
Kishiyarta muhimmanci fiye da tunanin mutum kamar kai ba, anya kana son gamawa da duniya lafiya
Aliyu?? Anya kana son ganin dai dai a rayuwar ka?? Uwa fa??" Kasa ce mata komai yayi yana ta kallonta da
mamaki, to me Ummi tace ya mata?? tace "Toh wllh rayuwarka na cikin tashin hankali da garari don ma
kaji in gaya maka yanxu" A sanyaye yace "Umma da akwai wani abun da nake yi ne ni ban sani ba? Ko da
akwai wani abun da tace na mata ne" Tace "Kaje ka xauna kayi karatun ta nutsu bani xaka yi ma nonsense
question din nan ba" Bai kuma cewa komai ba maganganunta na yi masa yawo a kai, shi a iya saninsa babu
abinda yake ma Ummi yana mata biyayya yanda d'a ke ma uwa, to what is Umma talking about" Sake daga
kai yayi yana kallonta yaga irin kallon da take masa tana girgixa kafa, ya shafa kansa a hankali bai ce komai
ba, can kuma dai yace "Toh Shikenan xan je in bata hakuri, duk da ni dai ban san me nayi ba" Bai jira me
Umma xata ce ba ya mike ya wuce dinning don tun daxu abincinsa ke can, Umma ta bi sa da kallo tana
furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a ranta, lamarin Abuturrab anya lafiya kuwa?? Ahmad ne ya shigo
parlon, Umma tace "Da wannan safa da marwan da kake a kan titi meyasa baxa ka dawo da Ramlah gidan
nan ba Ahmad" Ya shafa kansa yace "Toh Umma" Umma tace "Kayi knocking ka shiga ka duba Jiddah don
Allah" Yace "Alright" Abuturrab ya bi sa da kallo har ya wuce, sai da ya fara knocking Jiddah ta taso ta bude
kofar ganinsa ta koma gefe kanta a kasa tace "Ina yini" ya dinga kallonta yace "Wai ciwon kan kike ma kuka
Jiddah?" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace "Kin ci abinci" Tace "Na ci" yace "Jikin ki da xafi?" a
hankali tace "Nima ban sani ba" Toh bari in siyo maki magani yanxu in dawo" Yana fadin haka ya juya ya
koma parlor, yana kallon Umma yace "Umma let me get her drugs, har yanxu bata jin dadi" Umma ta mike
ta tafi daki wajen Jiddah, Ahmad ya karasa gun Abuturrab yace "Kayi bacci sosai ai ko?" Yace "Yau nake son
xan koma gida" Ahmad yace "Ohk toh, bari in dawo xan siyo ma Jiddah magani she isn't feeling fine" Daga
haka ya dau makullin motarsa ya fita. Bayan magrib Jiddah na xaune parlor bayan ta sha drugs din da
Ahmad ya siyo mata, tana cin shinkafa da miya da Maimoon ta kawo mata, a hankali take cin abincin don
baya ranta, gaba daya ji tayi xuciyarta babu dadi, Safiyya da Maimoon na haddansu a daki, Hajja da Umma
kuma na daki, ita kadai ce xaune parlon sai Huraira dake wanke wanke a kitchen, tun da ya shigo parlon ta
kallesa sau daya bata sake kallonsa ba, ya karaso tsakar parlon, ita dai taki yarda ta kallesa, looking at her
directly yace "Don nace xan mayar da ke in da na dauko ki shine kika fara rashin lafiya, sabida baki da
intention din sake komawa gidanku, ni ban ta6a ganin wanda ke gudun gidansu ba sai a kanki, ai xamanki a
can xai fiye maki xama gidan mutane...." Ta daga kai ta kallesa tace "Toh sai ka mayar dani ai yanxu, ni bana
tsoron komawa gida... Saboda nasan Allah na tare da ni, ko kaji nace maka baxan koma ba?" Yace "Toh sai
ki tashi ki dauko hijab din naki yanxu" Mikewa tayi ta wuce daki, shi ma ya tafi dakin Ahmad ya dau
makullin motarsa, Ahmad na kallonsa da mamaki yace "Ba Umma tace ka bari gobe ba" Ba tare da ya
kallesa ba yace "Ehh ba nisa xanyi ba, i want to get something" Bai jira cewar

41 / 108