Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
zaune dukanmu wajen karfe biyar na yamma Mimi na cinyata Ina mata kitso
Zainab Kuma tana kallo tana chatting,mummy ma kallon takeyi,sallamar da ake ta kwadawa a tsakar gida
muka jiyo zainab ta mike ta fita waje ba dadewa ta dawo tana "Aunty lubna Abdul abokin Mahfuz ne ke
sallama dake"
Hade rai nayi Ina "Kice Masa bana nan banasan munafirci"
"Jeki ce ya shigo"
Mummy tace tana jifana da harara ta rufeni da fada.
Mayafin abayar jikina na gyara na Kara rufe jikina,a lokacin da Abdul ya kwada sallama mummy ta amsa na
hade raina dan shi kansa Haushinsa nakeji gani nake bakinsu daya ma da mahfuz.
Da mummy suka gaisa ganin ya juyo mun hada Ido yasa na gaishe shi ya amsa cikin faraa ya mikowa Mimi
hannu ta sauka daga cinyata da Sauri ta nufi wajensa.
A daidai lokacin da Lubna ta ajiye masa ruwa a gabansa da lemo.
Sai da ya gama yiwa Mimi Wasa ya sauketa ya tsiyayi lemo ya sha ganin mummy zata mik'e yasa ya tsayar
da ita akan wajenmu yazo gabad'aya.
Mummy ta koma ta zauna yayi gyaran murya ya fara da bawa mummy hakuri akan abinda ya faru,ya juyo
ya kalleni Yana "Wlh banyi niyyar zuwa ba dan kunyarki nakeji,nasan laifin mahfuz zai shafeni Zaki iya
tunanin bakinmu daya ko halinmu daya amma wlh tallahi ba halinmu daya ba abinda Kuma Mahfuz ya miki
wlh yayi nadama ba Wai kareshi nake ba Hadeeza yarinya ce shuumar gaske wlh ita ta rinjaye shi
shaidaniya ce nasan Mahfuz nada laifi amma wlh yayi nadama lubna dan Allah kiyi hakuri ko dan zuriar
dake tsakanin ku"
Yanda ya daddage Yana Kare mahfuz yake neman jingina laifin ga iya Hadeeza yasa na hasalo na hau
masifa Ina bazan komawa Mahfuz ba Mahfuz dama can halinsa ne dan da ba halinsa bane bazai koma
mata ba a Karo na biyu abinda yafi cimin tuwo a kwarya na auren danaji zaiyi Kuma Hadeezan zai aura.
Anan ya saki murmushi ya hau bamu labarin sharrin da Hadeeza tace zata Masa idan bai aureta ba duk
yanda sukayi da mahfuz ya kwashe ya Gaya Mana,ni kuwa Sam ban yarda cikin ba na Mahfuz bane Amma
Naga mummy ta yarda da sharri Hadeeza ke san Masa bakin ciki bai bari na Kara magana ba na barshi da
mummy fuska da bai samu ba yasa yacemin zai dawo a yanzu yaga a sama nake.
Daya tashi tafiya ya kirgo Dubu goma ya ajiye a cinyar Mimi
Yana fita zainab ta hau yabonsa tana Bata jin bakinsa daya da mahfuz Abdul nada mutunci ko kulata banyi
ba dan ko zasu mutu bazan koma ba
Mahfuz
Kamar ya taka rawa a lokacin da Abdul ya bashi labarin yanda suka yi dasu lubna dan dama ba san auren
Hadeeza yake ba abinda yake gudun duk abdul ya fada musu Koda Hadeeza ta fada musu sun riga da sun
San sharri ne.
Kamar yanda Abdul ya tsara masa haka yayi ya shirya ya tafi gidansu Hadeeza a lokacin daya kirata yace
Mata Yana waje har ihunta yajiyo cikin murna.
Yana sauke wayar ta fito da saurinta bakinta a washe tana gyara mayafinta yanda kirjinta zai bayyana
"Angona na kaina Kamar kasan nayi kewarka"
"Allah ko"
"Wlh Allah mahfuz yau Aurenmu saura sati daya sai shiri nake ba kai ka ki zuwa haba masoyina"
"Hadeeza duk ba wanan ba kinsan Mai ya kawoni"?
"Aa"
Inaso ki shirya mu tafi asibiti inasan Naga lafiyar abinda ke cikinki"?
Kamar Yaya fa
"Kamar yanda kikaji dan banma yarda kina da ciki ba idan ma kina dashi sai kin zubar zan aureki idan har
baki zubar ba wlh bazan aureki ba"
"Wlh bazan zubar ba mahfuz ka dauka Wasa nake ko wlh tallahi a yanzu zan tafi gidansu lubna naje na fada
mata Ina dauke da cikinka"
"Ga kudin mota nan ko ki hau mota muje na kai ki da kaina"..........
Bayan few minutes Ramlah ta sake komawa ta leka compound sai bata ga Hajja ba, wani ajiyar xuciya ta
sauke ta wuce dakin da Jiddah take, tana cire Uniform ta sameta, Ramlah ta jingina da kofa tace "Toh
Aneesah ta maki wani abu ne da baxa ki je gidan nata ba Jiddah?" Jiddah taki kallonta tace "Bata min
komai ba, kawai dai baxan je bane..." Ramlah tace "Amma ai nace idan ma kin rakatan xa ki iya kin shiga
kiyi tsayuwarki a waje har ta fito" Jiddah tace "Kofar gidan ma baxan iya tsayawa ba" Murmushi kawai
Ramlah tayi ta juya ta fita daga dakin. Ranan Friday da daddare Aneesah na xaune parlor downstairs bayan
Magrib tana kallon wani indian Series tana shan fruit salad, ta ji footstep ana saukowa downstairs din,
daga kai tayi ta gansa yana sakkowa, lkci daya kamshinsa ya baxa ko wani lungu da sako na parlon, kafin
tace komai yace "You still haven't pray Aneesah" Tace "I know, ina xaka je da daddaren nan haka Captain?"
Ya shafa beard dinsa yace "Wajen Budurwa ta" tayi wani dariyar da bata shirya ba tace "Hmm, kar Allah ya
nuna min wannan bakar ranan, ni fa kasan wani abu captain?" Yana sakkowa yace "Sai kin fada" tace "Wllh
duk ranan da yau aka ce da gaske kayi wata budurwa Allah xan iya kashe koma wacece har lahira, sai dai
nima a daureni...." Yana kallonta bayan ya sakko parlon yace "Toh duk ranan da aka ce nayi wani auren fa?"
Ta kallesa kamar baxata ce komai ba don gaba daya mood dinta ya canxa, sai kuma tace "Wai ka auri wata
matar a duniya bayan ni?" Yace "Ehh" Wani murmushin ta kuma yi tace "Gwara a bar xancen kawai
Captain..." Sai kuma ta hade rai tace "Kasan Allah? Wllh wllh xan iya kasheta in kashe kaina sannan kai ma
in kashe ka duk mu hadu a lahira" Da mamaki ya dinga kallonta ganin how serious she is, cikin bacin rai
tace "Wllh duk ka bata min mood wnn xancen da kayi captain, mu fa kaf xuri'armu fa ba a mana kishiya
wllh, Aunty Salaha ma da aka yi ma satin amaryar uku ta bar gidan babu wanda ya koreta" Shi dai
Abuturrab kallonta kawai yake ganin da gaske ran nata ya baci sosai, D'an murmushi yyi yace "Sai na
dawo..." Ta mike babu yabo babu fallasa tace "Wai ina xaka da daddaren nan ne?" Yace "Ban ma Umma
sallama ba, daxu gida kawai naje" kauda kai tayi ta ta6e baki, sai kuma ta kallesa tace "Toh bari in saka
hijab mu je tunda ban ta6a xuwa gidan nata ba dama" Yace "No, ni kadai xanje, duk ranan da kika shirya
sai kije ki gaisheta" Da mamaki take kallonsa tace "Ban gane No ba, yanxun idan naje laifi ne?" Yace "Eh
saboda sai da xanje mata sallama sannan kika san xaki gaisheta" Bai jira cewarta ba ya nufi kofa ta bi sa da
wani irin kallo xancensa na sake yawo a kanta wai duk ranan da aka ce yayi wata matar fa?? Tabb shi me
ma ya kai sa fadin wannan mugun xance, ai daga ita ya rufe aure har karshen rayuwarsa, ita ce first and last
dinsa, shi din nata ne ita kadai, tsaki tayi ta koma ta xauna ta ci gaba da kallonta amma ba cikin dadin rai
ba... Abuturrab na parking ya dau wayarsa yayi dialing number ya kai kunne, wayar na fara ring aka daga,
ya amsa gaisuwarta yace "Ki turo ta ta amsar maku sako!" Ramlah tace "Wa xan turo yaya?" Yace "Warce
ke gidanki" Kallon agogo tayi don anyi isha, sai kuma ta mike ta fita xuwa dakin Jiddah, Jiddah ta gama sa
kayan baccinta kenan tana shafa turare kafin ta dau takardanta ta fara karatu saboda exams da take da shi
gobe Ramlah ta shigo, tsaye Ramlah tayi bakin kofar tana kallonta, Jiddah ta ajiye turaren hannunta tace
"You need something?" Ramlah tace "Wai sako xaki amso a kofar gida" Jiddah ta dinga kallonta tace "Sako
kuma? Sakon me? Kuma wajen wa?" Ramlah tace "Ya Aliyu" sosai gaban Jiddah ya fadi jin sunan da
Ramlah ta ambato, Jiddah ta girgixa kai tace "Sakon me da daddaren nan, maimakon kice ya shigo da shi ki
amsa don Allah, ji fa karfe nawa" Ramlah dai ta ma rasa abinda xata ce, Jiddah ta tafi ta dau takardanta ta
xauna gefen gado, irin ita baxata je din nan ba, wayar Ramlah dake hannunta ne ya fara ring, ta daga ta sa
handsfree tana kallon Jiddah, daga daya bangaren yace "Kuna bata min lokaci" Ramlah ta d'an fara kame
kame, sai kuma tace "Yaya ko dai in fito in amsa ni? ita naga ta kwanta ne" Calmly yace "Taso ta" Tace "Wai
dama exams..." Katse ta yyi yace "Ki taso ta nace" a hankali tace "Toh Yaya" ya katse wayar, Ramlah ta kalli
Jiddah da ta 6ata fuska kamar xata yi kuka jin duk abinda yace, cikin rawar murya tace "Bayan ya Ahmad
bai sani ba xan je kofar gida amsan sako, to gwara ki kirasa ni dai" Ramlah ta xaro ido tace "Ince masa me,
salon ya kira yayan?? ke dai kawai ki sa hijab dinki ki daure kije kiga sakon meye" Jiddah ta girgixa kai da
kyar tace "Ni baxan iya fita ba wllh, dubi fa agogo" Ramlah tace "Toh me kike so in ce masa bayan kinji
yanda muka yi da shi Jiddah" Jiddah ta kwanta kan gadon ta lullube tace "Da gaske fa ni baxan je ba kawai
ki kashe wayarki gaba daya, tun da rana me yasa bai kawo sakon ba" Ramlah dai ta rasa abun cewa tana ta
tsaye, sai ga kiransa ya sake shigowa, ta xaro ido tace "Na shiga uku Jiddah ki rufa min asiri ki tashi kije, ni
dama ba ni ya kira ba, bakin gate ne fa kawai xaki tsaya ya baki sakon da yace ki juyo ki shigo, wllh ban san
kuma me xance masa ba idan na daga kiran nan" Ganin ya kusa katsewa ta daga tana rawar baki tace "Yaya
na kuma ga tana wanka ne..." Yace "Ramlah" ta xaro ido tace "Na'am yaya" Yace "Mika mata wayar"
karasawa tayi ta ajiye wayar kusa da Jiddah tace "Ga ta" Jiddah tayi narai narai da ido tana sauraronsa,
yace "Fito ki amshi abinda nace yanxu, minti biyu na baki..." daga haka ya katse wayar, Jiddah ta mike
xaune har hawaye ya kawo idonta, Ramlah na lallabata tace "Ki daure ki je pls Jiddah ai nan da kofar gida
ne, kawai yana mika maki sai ki shigo kin ji" Mikewa Jiddah tayi daga kan gadon ta bude wajen kayanta ta
dau hijab har kasa ta saka sannan ta fita, tun da ta isa gate gabanta ke faduwa, tana fita taga motarsa ta
karasa tana tafiya slowly ta tsaya kusa da motar ta tsaya, sauke glass yayi yace "Shigo ki amsa" kamar xata
yi kuka tace "Don Allah ka bani a nan, wllh ya Ahmad...." Yana kallonta directly in the eyes yace "Shiga
nace" Sosai hankalinta ya tashi ta rasa yanda xata yi, da kansa taga ya bude motar ta matsa gefe ganin
kallon da yake mata sai kawai ta shiga xuciyarta na bugawa, amma bata kulle motar ba, yace "Kulle min
mota" Ta xaro ido tace "Don girman Allah ka bani sakon in koma wllh karatu nake gobe ina da exams, kaga
dare yayi" da kansa ya kulle motar ya tada motar, hawaye ya shiga sauka idonta tace "Na shiga uku don
Allah ka bude min in fita" barin layin yayi ba tare da ya saurareta ba, ta fashe da kuka sosai tana kallonsa
cikin tashin hankali.... Bai ko kalleta ba ya ci gaba da driving dinsa, jingina tayi da kujeran motar tana kuka a
hankali, bayan tafiyar kusan minti ashirin taga sun shiga wani katon shopping mall wanda wajen kamar da
rana saboda fitilu da ya haska ko ina, ya nemi waje yyi parking ita dai bin wajen take da kallo gabanta na
faduwa, sauka yyi daga motar ya xaga ta inda take ya bude motar, kasa kallonsa tayi shi kuma bai ce mata
komai ba, bayan few seconds ta goge idonta ta sauka daga motar ya kulle, tafiya ya fara, da farko ta d'an yi
jim ta bi sa da kallo, amma tsoron kada ya bace mata ta bi bayansa da sauri, tare suka shiga ciki tana bin
wajen da kallo, inda ya ta6a kawota ya mata siyayya Washegarin ranan ta na farko a gidansa ne, cart ya tafi
ya dauka tana biye da shi, ya mika mata handle din yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi ta amshi cart din,
ya dau wani ya fara tafiya, bin bayansa tayi tana turawa a hankali, wajen turarruka ya nufa, yace "Pick" tace
"Ni ina da turare da yawa" Bai kuma sauraronta ba ya dinga debar mata turaren, ta dinga bin sa da kallo
tana mamaki, bayan ya gama ya tafi gun mayukan shafawa da sabulu da shower gel, su ma ya dibar mata,
ita dai bin sa kawai take da cart din hannunta, duk wasu kananun abu na bukatar yau da kullum sai da ya
dibar mata, har ta fara gajiya da binsa, don sun siya kaya da yawa, wajen sanitary pads taga ya nufa, ganin
uban pads din da ya debo bata san lkcn da tace "Ai basu kare ba na gida" Yana juyowa ta sunkuyar da
kanta, yace "Meye basu kare ba" Kasa cewa komai tayi, ya xuba pads din a cart ya bar wajen, ta bi bayansa
tana tafiya a hankali, sai da yaga cart din ya cika sannan suka tafi wajen kayan ciye ciye, nan ma bai jira
yace ta dau komai ba, ya dinga debar mata duk wani abu da shi yake ci yana xubawa a cart din da take
turawa, har kayan shayi duk sai da ya daukar mata, Jiddah dai sai kallon wani chocolate dake side dinta
take ta yi don Ahmad na kawo masu irinsa daga Abuja, chocolate din kuma ba dai dadi ba, ta d'an kallesa
taga yayi backing dinta yana duba wani tsadadden biscuit, kwasan chocolate din tayi kusan biyar ta juyo da
sauri xata xuba su a cart din dai dai nan shi ma ya juyo rike da biscuits din da yake kallo suka kusa cin karo,
juya masa baya tayi da sauri taji kamar ta nutse ta rufe ido, xata maida chocolates din taji ya fixgota, tayi
narai narai da ido tana kallonsa da manyan idonta, ya amsa ya xuba su a cart din yana kallonta shi ma, ita
ta fara sauke idonta, sauran siyayyan duk tana gefe har ya gama, suka tafi wajen biyan kudi, a booth duk
aka xuba ledojin kayan siyayyan, eatry din mall din ya shiga ya siyi ice cream da pizza with shawarma
sannan ya fito, ita dai tana tsaye bakin motarsa tana jiransa, bayan ya shiga ita ma shiga motar, cikin minti
ashirin da biyar suka iso kofar gidan Ramlah. Jinginar da kansa yayi da kujeran motar ita dai jira kawai take
taji ya bude lock din motar ta sauka, amma sai taga yaki budewa, bayan five minutes, taji muryarsa calmly
yace "Xan mu fita
Dubai gobe in sha Allah, from there xa mu tafi Uk..." Ita dai bata ce komai ba, ya juya ya kalleta.... ta
sunkuyar da kanta tace "Allah ya kiyaye" ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Xan yi few months a can" Bata ce
komai ba, yace "Kina da bukatar wani abu ne??" Ta girgixa masa kai tace "Wani abu kamar me bayan su
Umma na yi min komai ni" Ya dinga kallonta yace "Wannan ne amsan tambayar da na maki?" Kin cewa
komai tayi, yace "Bude baki kiyi min magana" Tace "Bana bukatar komai" shiru duk suka yi, ita dai wata
magana ce ke cinta amma ta rasa ta ina xata fara masa, ji tayi yace "Do u have anything to say to me?" Ta
kallesa da sauri, sai kuma tace "Ehh.." yace "Ina jin ki" cikin sanyin murya tace "Ranan Hajja tace wai kunje
hayi an rusa gidanmu, ba kowa yanxu" Ya dinga kallonta yace "Sai aka yi yaya?" Ta fashe da kuka tace
"Baabarmu da Bibalo fa?" Yace "Kina son xuwa wajensu ne yanxu??" Hawaye na sauka ido ta ta kallesa
tace "Ehh ina so don Allah" Yace "Me xaki yi masu idan kinje" Cikin rawan murya tace "Ina son in gansu
mana, saboda nayi kewarsu... Ban taso na gan ni da kowa ba sai su, and it's been long... Nayi kewarsu
sosai" Tada motar yayi bai kuma ce mata komai ba yayi reverse suka bar layin. The journey was so silent,
bayan tafiyar kusan minti talatin suka iso titin hayin rigasa, tunda suka shigo hayi Jiddah ta dinga bin
anguwar tasu da kallo, ta rasa wani irin farin ciki xata yi a moment din, farin cikin nata bai bayyana a fili ba
sai da ta gansu kan layin gidan Babaarta, ta kallesa da farin ciki amma ta rasa abinda xata ce masa, she
looks so happy... shiga layin yyi da motarsa xuciyarta na bugawa tace "Don Allah ko xaka tsaya in fara shiga
gidan Iyah in gaisheta???" Ya kalleta sannan yayi parking kofar gidan Iyah, sauka tayi daga motar da sauri
ta shige gidan a guje, ya sauka ya jingina da motar tasa ya bi ta da kallo, Iyah na xaune tsakar gida da
rediyonta a hannu, tana ma jikokinta dake kwance saman tabarma fifita sun yi bacci, Jiddah ta wara ido
cike da murna tace "Iyah!!!" Fadawa jikinta tayi ta rungumeta, Iyah ta matsar da ita tana mata wani kallo
daga sama har kasa, sai kuma tace "Jiddah????" Rungumeta Jiddahh ta kara yi lokaci daya hawaye ya kawo
idonta tace "Nice Iyah, nayi kewarku wllh" Iyah ma ta fashe da kuka tace "Ashe rai kan ga rai Jiddah, ashe
xan sake ganin ki a rayuwar nan?" Jiddah ta share idonta tana murmushi tace "Gashi kin gan ni Iyah" Iyah
ta mike tsaye tana sake kare mata kallo don tabbatar da ita din ce kuwa, sai ta saki salati tace "Daga ina
kike haka Jiddah?? Kece kika dawo haka kamar balarabiya Jiddah??" Jiddah tayi murmushi ta kasa ce mata
komai tana kallonta, Iyah tace "Ke da waye yanxu haka? Daga ina kike?" Jiddah tace "Yana kofar gida, ince
ya shigo?" Bata jira me Iyah xata ce ba ta tafi da sauri kofar gidan, har sannan Abuturrab na tsaye ya
rungume hannunsa, tace "Wai tace ka shigo" kallonta ya dinga yi ta juya ta koma ciki da sauri, shafa kansa
yyi ya bi bayanta... Har kasa Iyah ta durkusa tana gaishesa bayan ya shigo gidan, hakan yasa ya xauna
saman darduma yana d'an murmushi calmly yace "Ina yini??" Iyah ta rushe da kuka tace "Wllh da kasan
irin taimakon da Allah ya baka ikon yi da ladan da Allah xai baka da ba haka ba bawan Allah, ka taimaki
rayuwar Jiddah a sanda take tsananin bukatar taimakon, ka cece Jiddah a dai dai lkcn da take bukatar ceto,
Allah ubangiji ya sa ka samu me maka abinda kayi ma marainiyar