Author : Khaleesat Haiydar Category : Romantic Hausa Novels
kallonsa, daga kai yayi ya kalleta ya nuna mata kujeran alamar ta
xauna, ta xamo kasa ta xauna, bayan few seconds, speaking calmly yace "Shekaranjiya na gaya maki an
daura maki aure, right?" Jin tayi shiru ya ajiye biron hannunsa yace "Tambayarki nake" Ta gyada masa kai
tana kallonsa, yace "Kuma baki san da wanda aka daura maki auren ba ai koh" Nan ma ta gyada masa kai,
a takaice yace "Ohkk... Da ni aka daura auren" Kallonsa kawai Jiddah take kamar bata gane abinda yake
nufi ba, not minding that ya langwabar da kai yace "Shi yasa kika ji a can gida suna maki nasiha" a hankali
Jiddah ta sauke idonta kasa, taji xuciyarta na bugawa da sauri da sauri, yace "Na aure ki ne kawai don ceto
rayuwarki daga matar mahaifin ki, na aure ki ne saboda naga xa a cuce ki xa a lalata maki rayuwa, na aureki
ba don naje da niyyar yin hakan ba, don haka bani da xabi da ya wuce in sakeki, wannan sakin kuma da xan
maki tsakanina dake ne kawai...." Da duk idanuwanta take kallonsa jin furucinsa na karshe, cikin sanyin
murya tace "Xaka sakeni?" Yace "Ehh xan sake ki" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, shi ma shirun yyi
yana kallon hotonsa dake parlon yana sanye da wear dinsa na pilot, muryarta ya ji tace "Idan ka sakeni sai
in koma wajensu Umma kenan?" Ya girgixa kai, cikin nutsuwa yace "Aa a nan gidan xaki xauna, kamar
yanda na fada maki sakin nan xai kasance sirri tsakaninmu, babu wani da xai san na sake ki...." Tayi shiru
bayan few seconds tace "Toh ae ni ba muharramarka bace da xa mu xauna gida daya bayan ka sakeni...."
Kallonta ya dinga yi da mamaki jin furucinta ba don shi ta fada ma ba idan wani yace masa ta fadi hakan
baxai ta6a yarda ba, can yace "A ina kika san wannan?" Tana wasa da fingers dinta ba tare da ta kallesa ba
tace "Lokacin da nake xuwa islamiyya" Surprisingly yake ta kallonta, can yace "Ohh i see... amma kuma
basu koyar dake hukuncin wanda ya kashe kansa ba kuma?" Kallonsa Jiddah tayi amma taki cewa komai, ya
jefa mata wani shegen kallon da yasa ta koma baya a hankali, idonta har ya fara kawo ruwa, yace "Ke a
tunaninki rashin sakin ki kadai ne xai sa mu xauna gida daya kenan, idan ban sakeki ba shine kike
muharramata koh?" Shiru tayi bata ce komai ba yace "Bude baki ki bani amsa malama" A hankali tace
"Nima ban sani ba" Wani kallo ya sake jefa mata ta sunkuyar da kanta, yace "Xan sakeki kuma xa mu xauna
gidan nan tare, don mun xauna gida daya tare ba yana nufin ganina xaki dinga yi ko ganinki xan dinga yi ba,
kinsan matsayinki gidan nan, nima haka, balle ma ni daga ranan lahadi da yamma xuwa juma'ah ina wajen
aiki, kina tunanin sati da lahadin ma idan na dawo ganina xa ki dinga yi??" Ita dai bata ce masa komai ba,
yace "Don haka ki cire tunanin yan kauye dake ranki yanxu, komai kike bukata xan baki waya da xa ki dinga
kirana, sannan idan ba abu me ma'ana ba dama kar ki kuskura ki kirani, nan da wani lkci xaki fa islamiyya
da boko...." Sai a sannan ta daga kai ta kallesa cikin sanyin murya tace "Toh nagode Allah ya saka da
alkhairi" Bai tanka ta ba ya soma rubutu a takardan gabansa, kallonsa kawai Jiddah take babu ko kiftawa,
yayi rubutu wanda iyakarsa layi biyu xuwa uku sannan ya dago kai yana kallonta, da sauri ta sauke idonta
kasa, yace "kin iya karatu?" A hankali ta girgixa masa kai, sai kuma ta gyada masa kai alamar xata iya, ya
mika mata takardan yana kallonta, ta mike ta karasa ta d'an risina ta amsa takardan tana kallo, bayan few
seconds ya mika mata hannu alamar ta basa takardan, ta dago kai, hawaye ya gani makale idonta ta mika
masa takardan ya amsa sannan ya linke without looking at her yace "Wannan tsakaninmu ne da ke, har
abada bance ki sanar ma kowa ba idan ba haka ba......" Daure fuska yyi yana kallonta bayan ya fadi haka, ta
gyada masa kai a hankali hawayen idonta ya silalo, mikewa yayi ya linke takardan tsaf sannan ya shiga
bedroom dinsa ta bi sa da kallo, ba a dau lkci ba ya fito, kofar fita ya nufa yace "Mu je in nuna maki dakin
da xaki xauna" Juyawa tayi cikin sanyin jiki ta bi bayansa, bangaren suka bari gaba daya, ya bude wani daki
wanda akwai komai a ciki yana kallonta yace "Ga dakin ki nan, kinga can bangaren nawa ko by mistake,
kinsan me nake nufi da by mistake?" Ta girgixa masa kai alamar A'a, yace "Ohk, ina nufin ko bisa kuskure
kada ki kai kafarki can, iyakar ki nan dakin, ko parlon kasa idan ina gari bana son kina xama, idan bana nan
xaki iya xaman ki can, sai kuma kitchen, komai xan ajiye maki a ciki ki girka duk abinda kike so" Ta gyada
masa kai kawai, yace "Yanxu ki tafi kasa jakar nan ki kawo dakin ki, gobe da safe xa mu fita xan siya maki
duk abinda xaki bukata, sai ki xaba komai da kanki" Nan ma kai kawai ta gyada masa yace "Kin ci abinci ai a
can gida?" Ta gyada masa kai nan ma, yace "Good" downstairs ya nuna mata yace "Tafi ki dauko jakanki,
kayan da xaki dinga amfani dasu ne a ciki" Ba musu ta fara sauka kasa, ya bi bayanta suna shigowa parlon
ya nufi kofa ya sa makulli, ta dau jakar ta koma sama, kashe wutan parlon yayi, sannan shi ma ya wuce
saman, tsaye ya ganta bakin kofar dakin da ya nuna mata, a hankali tace "In shiga?" Ya daure fuska yace
"Ehh" Bude kofar tayi kafin ta shiga ciki yace "Gobe karfe takwas xa ki sauko kasa" Ta gyada masa kai,
sannan ta shiga dakin ta kulle, ya kashe wutan corridor din ya nufi bangarensa. Bin dakin da kallo Jiddah ta
dinga yi, sai take ganin abun kamar a mafarki wai yau ita ce xata kwanta saman wannan katon gadon ita
kadai, to ko dai bai ce ta kwanta ba? Kar ta kwanta kuma yace mata don me, a hankali ta kai jakar can jikin
bango ta ajiye sannan ta dawo ta xauna kasa tana sake bin dakin da kallo, ta fi minti talatin xaune a kasa,
can ta tuna abinda Umma tace mata duk dare kafin ta kwanta ta dinga yin wanka, mikewa tayi tana kallon
jakar da yace mata kayan da xata dinga amfani da ne a ciki, ta karasa gun jakar ta kwantar sannan ta bude,
tawul ta fara cin karo da sabo, ta ajiye gefe, taga sabulu da soso da Toothpaste and toothbrush, su ma ta
ajiye a gefe, sannan taga sabbin undies, da turarruka da mayyuka sai kayan kwalliya, kallon kayayyakin ta
dinga yi, lkci daya hawaye ya kawo idonta, xaunawa tayi nan kasa ta hade kai da gwiwa tana shessheka,
gani take kamar Hansai xata xo ta haureta ko ta watsa mata ruwa sai ta farka taga duk mafarki kawai take,
ta fi minti sha biyar tana kukan kafin ta dago kanta har sannan hawayen yaki tsaya mata, ta dinga share
idonta daga bisanni ta mike ta cire Hijab din jikinta, kamar yanda Umma tace mata bata ajiye Hijab din
haka ba sai da ta linke, sannan ta soma cire kayan jikinta, ta dau tawul din ta daura ta shiga bandaki, tun
daga gidan Umma su Huraira da Maimuna sun nuna mata yanda ake amfani da komai na cikin bayi, cikin
kankanin lkci kamar ana koranta tayi wanka ta fito bandakin, bayan ta gama goge jikinta ta dau lotion daya
ta bude ta fara shafawa, wani doguwar riga mara nauyi duk da ba na bacci bane ta dauka ta saka, sannan
ta maida komai cikin jakar ta rufe ta mayar jikin bango, darduman da ta gani ta shimfida don tayi alwala, ta
gabatar da sallan isha sannan ta linke darduman da hijab din ta ajiye, komawa tayi ta rakube ta xauna a
kasa, tana ta xaune tana tunani iri iri, taji bacci ya fara fixgarta, tsoron hawa saman gadon take yace tayi
laifi, hakan yasa ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta kwanta nan kasan tiles ta dukunkune waje daya, nan
da nan bacci ya dauketa, sai dai kafin asuba ba karamin wahalar da ita sanyi yayi ba, baccin ma bata yi me
dadi ba sbda sanyi da ya isheta, a haka har aka kira sallan asuba, abun ka da wanda ya saba, tun kafin a
tada sallah ta tashi ta tafi bandaki ta dauro alwala, da kyar take numfashi sbda hancinta da taji ya toshe, ga
ciwo da kanta ke yi, tana xaune saman darduma bayan ta idar da sallah aka bude kofar dakin, da sauri ta
juya suka yi ido hudu da shi, sanye yake da jallabiya, ta sunkuyar da kanta, ya rufe kofar ya nufi
bangarensa, sai a sannan ta dago kanta jin ya rufe kofar dakin. Har gari ya waye Jiddah na xaune saman
darduma sai dai fa babu abinda take, ko d'an azkar din nan babu, kawai sabo da tayi da rashin komawa
baccin asuba ne, bakwai saura ta mike ta shiga bandaki ta wanke baki tayi wanka sannan ta fito, wani
atamfar ta saka bayan ta shafa mai ta saka turare dai yanda ta ga su Maimuna na yi, tana ta xaune dakin
lkci lkci tana duba agogon dake dakin, har taga karfe takwas yayi, mikewa tayi ta dau Hijab ta saka sannan
ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita, kamar mara gaskiya ta dinga sauka stairs din har ta iso main parlor
din, karan Tv ta ji, ta leka parlon ta gansa kwance saman dogon kujera idonsa a lumshe, kasa karasawa tayi
cikin parlon, ta fi minti goma a tsaye kamar munafuka, daga karshe ta juya a hankali ta koma saman,
xaunawa tayi a kasa ta jinginar da kanta da gado, tana ta xaune a haka har bayan awa kusan daya taji an
bude kofar dakinta, da sauri ta juya, suna hada ido ya daure fuska yace "Baki san agogo bane?" Ta kalli
agogon dakin dake nuna karfe tara saura mintuna kadan, a hankali tace "Na sauko karfe takwas naga kana
bacci shine na koma" da mamaki yake kallonta, can yace "To meye damuwarki da baccina ba ni nace ki
sauko lkcn ba?" Ta gyada masa kai, juyawa yayi ya bar bakin kofar, ta mike tana gyara hijab din jikinta ta bi
bayansa, xaune ta samesa a parlon ta karasa ta rakube kasa jikin kujera ta xauna yana kallonta daga sama
har kasa yace "Babu wani Hijab din ne a jakar?" Tace "Akwai" Yace "To bana son maimaita kaya... Koma ki
canxa hijab din" Mikewa tayi ta wuce sama a sanyaye, ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo da wani Hijab din
navy blue colour, shi ma har kasa, sosai Hijab din ya haskata kasancewarta fara, ta koma inda take ta xauna
ba tare da ta kallesa ba, bayan few minutes yana kallonta yace "A gidanku idan an tashi da safe ba a
gaisuwa?" Ta d'an buda ido tace "Ina kwana" Bai tanka ta ba yana kallonta jin voice dinta da ya canxa yace
"AC din dakin kika kunna?" Da sauri tace "Aa ai ban iya kunnawa ba" Yace "Da ruwan sanyi kika yi wanka?"
Ta girgixa kai tace "Aa na xafi na tara" Yace "Kin bude windows din dakin ne?" Nan ma ta girgixa kai tace
"Ban san ma ya ake budewa ba" She looks so Afraid, don with authority yake mata tambayar, bayan ya
gama kallonta da kyau yace "A ina kika kwanta?" Tana jan fingers dinta a hankali tace "A kasa" Da mamaki
yake kallonta, can dai yace "Saboda me?" Innocently tace "Ai baka ce in hau saman gadon ba" Dauke
idonsa yayi daga kallonta, bai ma san wani reaction xai yi ba, she sounds very funny, can dai ya sake
kallonta yace "To daga yau nace ki dinga hawa saman gadon, anjima da daddare xan baki bargo da xaki
dinga rufa" Cikin sanyin murya tace "Toh nagode" ya nuna mata basket me dauke da breakfast da Umma ta
aiko masu da shi, yace "Ga ya can ki je ki karya" Ba musu ta mike ta isa wajen, babu abinda babu wajen har
cup da spoon da plate, ganin yanda take ta kallon basket din bayan ta duka a wajen yace "Ki bude dukka ki
xuba abinda kike so" A hankali ta shiga bude warmers din, wainar shinkafa da lafiyayyen miyarsa na naman
rago, sai fried Irish da kwai, ga kuma bread da pepper soup din hanta xalla, kallonta kawai yake, ta dau
plate ta debi waina biyu xata kara daya suka hada ido, mayarwa tayi, yace "Juye dukka" Da sauri ta kallesa
tace "Ya min yawa ai" Ya hade rai yace "Juye nace" Ta kalli wainar da xai kai sha uku tace "Wllh tllh baxan
iya cinyewa ba" Hade rai yayi sosai yana kallonta can on a serious note yace "Bana son rantsuwa a gidana,
kada ki sake" Sauke kanta tayi ta xuba wainar guda biyar sannan ta debi miya, xata mike yace "Hada
shayin" Ta hada shayin ta koma can jikin kujera ta xauna, lkci lkci take satan kallonsa tana cin abincin
gabanta, daga karshe ya mike ya wuce sama ganin she isn't comfortable, ta bi sa da kallo. Bayan kusan awa
daya Abuturrab ya sakko rike da makullin motarsa, kananun kaya ne jikinsa as usual, Jiddah na ta xaune
bayan ta gama wanke plate da cup din da ta karya a kitchen, kashe tv dake aiki yayi ya kashe fitilan parlon
ba tare da ya kalleta ba ya nufi kofa yace "Ki sameni waje" Mikewa tayi ta bi bayansa, takalmanta ta gani
bakin kofar fita ta saka sannan ta fita, yana tsaye waje yana jiran fitowarta, tana fitowa kuma ya kulle kofar
da makulli ya nufi can gate, ya bude gate din sannan ya karasa parking lot ya bude motarsa ya shiga, slowly
take tafiya har ta iso parking space din, ya gama warming motar sannan ya kalleta yace "In roke ki kafin ki
shiga motar?" Bude back seat tayi ta shiga, bai dai ce mata komai ba ya fara driving ya fitar da motar kofar
gida, sannan ya sauka ya kulle gidan ya koma cikin motar, Driving Abuturrab yake yana tunanin shopping
mall da xa su, daga karshe ya dau hanyar ASD city mall, suna isa yayi parking ya bude motar ya sauka,
Jiddah ta sauka ita ma, don yanxu kam ta iya bude mota, ganin inda ya nufa ta bi bayansa, shopping cart ya
dauka tana biye da shi, wajajen turarruka ya fara nufa ya tsaya ya rungume hannu yana kallonta babu yabo
babu fallasa yace "Debi turaren" tace "Ai a jakar kayan nan akwai turare hudu" Wani shegen kallo yayi
mata yace "Debi turare nace my frnd" Diban turaren ta fara yi wanda wasu body sprays ne a wajen tana
xubawa a cart din, takaici ya sa ya ma kasa ce mata komai, she's not even making any effort to check for
the ones with better scent diba kawai take, cikin husky voice dinsa yace "koma gefe" A hankali ta ja ta
tsaya a gefen tana kallonsa, gun sealed tsadaddun turarurruka ya karasa ya xabi hudu ya xuba a cart din, a
takaice dai turaren da suka diba a wajen xai kai kala sha uku kamar abinda kadai ya kawosa mall din kenan,
dubu dari biyu Abbansa yayi masa transfer a yau da safe yace ya siya mata duk wani abinda take so, ga
wanda uncles dinsa suka bata a jiyan, gun mayyuka ya nufa next tana biye da shi tana tura cart din da ya
sakar mata, wayarsa ya ciro aljihu yayi dialing number Aneesah warce har yau bata san abinda ke faruwa
ba, yasab Aunty ma baxata yi gigin sanar mata ba, shi ma kuma bashi da intention din sanar mata, tana
dagawa cikin cool voice dinsa yace "Aneesah wani cream kike shafawa pls?" Daga daya bangaren tace
"Ohh body cream?" Yace "Yeah" fada masa tayi, ya d'an yi shiru har sai da tace "Are u there?" Yace "Yeah,
amma ba na lightening bane ko?" Daga daya bangaren tayi dariya tace "To ka mance ni fara ce, lightening
din me kuma my captain?" Kallon Jiddah dake tsaye ta rakube waje daya yayi, yace "ohk, haka ne" Tace "Ba
na bleaching bane kamar yanda kake tunani, amma kuma me kyau ne, yana fito da ainahin complexion din
mutum, sannan yana sa jiki yayi glowing, me tsada ne sosai" Abuturrab ya d'an yi murmushi yace "Ohk,
text me the name now ina jira, and sorry.... Har da sabulu, infact da duk wani abinda kike amfani da shi na
gyaran jiki ki turo min ta text ynxu" Tace "Uhmm my Captain lefe ka fara hadawa ne?" Bai san lkcn da ya
fara murmushi ba yace "Yea, with perfumes da kike amfani da" Farin ciki ne sosai a voice dinta, tace
"Alright my captain, i will now" daga haka ta katse wayar, jan cart din yayi suka tafi bangaren undies kafin
Aneesah ta turo masa text din, gefe ya ja ya tsaya ya rungume hannunsa yana kallonta yace "Ko shi ma ni
xan xabar maki?" Kasa kallonsa tayi wai duk kunya, ta sunkuyar da kanta inda take tsaye, yace "Heyy kina
bata min lkci" A hankali ta karasa ta fara daukan panties din tana ajiyewa a cart din, ya hade rai yace "Idan
kika dauki wanda suka fi karfin ki kina da wanda xaki ba ma ne?" Kasa kallonsa tayi kamar xata yi kuka,
yace "Madam kina bata min lkci fa, baxa ki dinga dubawa ba...." kamar xata yi kuka tace "Ni baxan iya ba"
that sounds so funny, amma ya dake yace "Baxa ki iya me ba?" Juya masa baya tayi, bai san lkcn da ya d'an
yi murmushi ba, karasawa yayi ya gun undies din, daga sama har kasa ya kalleta doing survey with his eyes,
ita dai ta ki juyowa, da kansa ya xabar mata undies din ko wanne dozen dozen, ya tura cart din ya bar ta
wajen a tsaye, satan kallonsa tayi, sai kuma ta fara bin sa a hankali, gun nighties ya tsaya nan ma ya xabi
sha biyu.... Kananun wears ma ya xabar mata isassu, ganin she is already tall, flat shoes iri iri masu kyau ya
xabar mata shi ma dai kusan sha biyu, da handbags, a mall din nan atamfofi ne kawai Abuturrab bai siya
mata ba, komai da mace xata bukata sai da ya siya ma Jiddah enough a lkcn, sai dai idan cart din ya cika ya
ajiyesa sa can gun da xa abiya kudi ya dau wani shopping cart din,