Advertisements
Chapter 32 Reading Jeedderhh by Khaleesat Haiydar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jeedderhh by Khaleesat Haiydar

Author :  Khaleesat Haiydar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   32 / 108

93K to 96K   out of 321.7K words

wannan mutumin
da na ganku tare?" Tace "Wai da gaske kai ne kake tukin jirgin in ji sa? Ni dai nace masa ba kai bane ae
baxa ka iya ba" fixgota yyi, tayi wani kara xata durkusa ya dagota yace "Tambayar ki nake waye shi??"
Kamar xata yi kuka tace "Toh ba q jirgin muke haduwa ba" ganin taki tsayawa cikin tsawa yace "Baxa ki
tsaya ba" Kin tashi tayi tace "Toh don Allah ka sakeni" kallonta kawai yake yi, can ya saketa, xamewa tayi ta
xauna kasa, yace "Waje daya ku ka xauna da mutumin?" Tace "Aa, kawai da na sauka jirgin shine ya bi ni
yana min magana" Shiru yayi yana kallonta ita dai bata yarda ta kallesa ba, can ya juya ya bude kofar dakin
ya fita. Bayan la'asar suka bar kano xuwa kaduna a motarsa, Jiddah na kallonsa after the 20 mins silence
tace "Meyasa muke ta shiga jirgi bayan ga mota, kyauta ake tafiya a jirgin ne?" Ya mata wani kallo yace
"Kyauta? Tsoronki ake xaki shiga jirgi kyauta?" Tace "Toh Iyah ta ta6a ce min kudin jirgi yana da tsada kusan
miliyan ne" Ya d'an kalleta yace "Haba??" Ta wara ido tace "Wllh, kasan ta ta6a xuwa makka sau daya,
yaranta ne suka biya mata, toh ni na xata masu kudi ne kawai ke hawan jirgi" D'an murmushin da bai shirya
ba yyi yace "Ni ba me kudi bane kenan?" Ta d'an xaro ido tana kallonsa tace "Aa bance haka ba, amma
wannan motar taka ce?" Bai ce komai ba, a hankali tace "Kayi shiru..." Yace "Aa na Abbana ne" Tace "Toh
gidan fa?" Yace "Wani gida?" Tace "Wanda muke ciki?" Yace "Shi ma na Abbana ne" Tace "Kenan shi ne ya
biya kudin jirgin da muka shiga?" Yace "Ehh" Tayi shiru tana kallonsa, ta gefen ido ya kalleta, ta sauke
idonta, bayan few seconds tace "Abbana ya ta6a ce min watarana xan shiga jirgi, amma Makka yace xanje"
Ya kalleta yace "Haba" Ta gyada masa kai, tace "Kuma gashi na shiga amma ban je makkan ba" Yace "Toh
idan kina da kudi ki kawo in biya maki Umrah ki je" Ta buda ido tace "Kudi?? A ina xan ga kudi ni ba sana'a
nake ba" Yace "Ohk kina son kiyi sana'a ne? Ko awaran xaki siyar a bakin layin gidanmu?" Dariya ta fara yi,
ya dinga kallonta don bai ta6a ganin dariyarta ba, tayi me isarta sannan tace "Idan kace inyi sai inyi in dai
xa a siya" Da mamaki ya d'an kalleta kafin ya maida dubansa kan titi yace "Xa kiyi kenan idan nace kiyi"
Tace "Ehh, sai in yi har da wainar flawa da dankali" Yace "Toh bari mu je a samar maki waje a bakin titin
ko?" murmushi ya ga tayi tace "Toh" Ji yayi kamar ya fixgota ya rankwasheta, tace "Toh amma kudin xa su
taru har in je makkan kuwa?" Yace "Wannan ke xan tambaya ai, babarku ta tara kudin ya isheta har taje
makka?" Shiru tayi tana kallonsa, can tace "Toh ai abinci muke ci da kudin sana'ar, wannan kuma baxan
siya abinci da kudin ba tunda akwai abinci a gida koh" Shafa millionaires belt dinsa yyi still wondering if
yarinyar nan xata ta6a wayewa, though ya ma yi mamakin yanda har ta fara iya dressing ko don kayan da
ya siya mata sunyi correlating da mahadinsu ne, sannan bai ga tana irin kwalliyan nan na masu talla ba, a ja
gira a shafa barbada kumatu, a shafa gazal, babu wanda xai kalleta yace she is local or even an illiterate sai
ya ji xancen dake fita daga bakinta, mamaki ma yayi yanda ta bude baki take creating conversation da
kanta yau, muryarta yaji tana cewa "Idan kudin ya taru da yawa kai ma sai in biya maka tunda ka taimakeni
koh?" Ya d'an kalleta da sauri sannan yace "Haba?" Tace "Ehh, ko kuma in biya ma Umma" Murmushin
gefen baki yayi yace "Ashe na taimake ki?" Tayi shiru tana kallonsa, sai kuma ta gyada masa kai a hankali,
Bai kuma cewa komai ba, kuma bai kalleta ba, jin tayi shiru bayan kusan minti goma sha biyar, breaking the
silence yace "Bayan awaran da dankali babu wani sana'ar da xa ki yi?" Ya d'an kalleta da yaji bata amsa
masa ba, bacci yaga tana yi, xuwa lkcn sun fara fita outskirt din garin kano, ya kai hannu a hankali ya
kwantar mata da kujeran motar, snn ya kara Ac din motar, har suka shigo garin kaduna bayan magrib bacci
take, amma ta farka yyi sau biyar a hanya, mai gadi na bude masa gate yayi parking a parking space, ya
sauka motar yana stretching kansa, coz he is very tired bayan tukin jirgi ga na mota, jingina yayi da motar
ya rungume hannunsa, har ya mance rabonsa da workout, tun sanda burden din Jiddah ya hau kansa,
xagawa yyi ya bude side dinta ya bubbuga motar slowly, a hankali ta bude ido ta fara kalle kallen inda suke,
yace "Sakko" sauka ta fara yi daga motar ya koma gefe tana fitowa ya kulle motarsa. Bayan sun shiga gidan
xata wuce dakinta yace "Ki tabbatar kinyi sallah" Wanka jiddah tayi sannan ta dauro alwala bayan ta idar
da sllh ta saka kayan baccinta ta kwanta. Karfe tara ya shigo dakin da abinci, tunda ya kalleta sau daya ya
dauke kai, kawai ya ajiye ledan ya fita. Washegari da ya kasance ranan juma'ah Jiddah na idar da sallan
asuba ta sauko kasa ta hada shayi ta dumama abincin da ya kawo mata jiya da daddare ta wanke tukunyar
da ta bata ta koma dakinta, duk kafin ya shigo gidan daga masallaci, don sai ya gama azkar dinsa yake
shigowa gida, bata mance warning din da yayi mata ba, ganin har karfe sha biyu Abuturrab dake xaune
parlor bai ga ta sakko ba, lkci lkci kuma ya ke kallon sama, daga karshe ya mike ya haura stairs din sannan
ya bude kofar dakinta, bacci ya sameta tana yi, yayi knocking kofar da karfi wanda hakan ya farkar da ita ta
mike xaune da sauri, ya wani daure fuska yace "Baki da hankali har yanxu bacci kike?" Tace "Aa nayi wanka
na gyara dakin" Ganin hararan da yake mata ta dauke kanta, yace "Ohk kin fi so ki kwanta daki kullum in
fita in siyo maki abinci in kawo maki anjima kice ai bani da kudi?" Buda baki tayi tana kallonsa tace "Ni
yaushe nace baka da kudi?" Ya rungume hannunsa yace "Jiya a mota" Tace "Aa ni fa kudin jirgi nace baka
da shi tunda ya kai miliyan daya, kuma kace min Abbanka ne ya biya ai ko??" Yace "Ehh abincin da kike ci
ma ai duk shi yake siyowa in kawo maki ko" Tayi shiru tana kallonsa, can tace "Toh me yasa baka son kayi
sana'a, kaga Umar yana fita kasuwa kullum, don kawunsa na da shaguna uku a kasuwan bacci..." Kallonta
yake ko kiftawa baya yi, tace "Kai ma xa ka iya ce a neman maka waje a kasuwa tunda Abba na da kudi ae"
Ya shafa fine beard dinsa yace "Haka ne kuma, amma ya aka yi kika san bana sana'an komai" Ta sakko da
kafafuwanta daga saman gadon tace "Naga to ko da yaushe kana gida, idan baka son ka xauna a gidan
kuma sai ka tafi kano, to ko sana'a kake xuwa yi a kanon?" Ya girgixa kai da sauri yace "Can ma kawai xama
nake a gida, ai ba a bani sana'an da xan yi ba" Tayi shiru, sai kuma ta kallesa tace "Amma lkcn da kake xuwa
hayin rigasa a ina kake samo wannan kudin da kake bani in ba Babarmu?" Yace "Abbana ke bani" Tace
"Toh, shkkn" Yace "Yanxu kasuwan xan fara xuwa nima kenan" Tace "Eh ka gaya ma Abbanka ya bude maka
shago" Yace "Sai ni dake mu dinga xama a ciki ko?" Kallonsa tayi ta fashe da dariya sosai dimples dinta na
lotsawa, ya dinga kallonta, second time da yake ganin dariyarta kenan, tayi me isarta tace "Dama mata na
xuwa kasuwa?" Ya rungume hannunsa yana kallon large eyeballs dinta yace "Tunda xa su iya xaman gefen
titi su siyar da awara da dankali me xai hana??"


*Toh Chamo dai tace banyi addu'ar Allah yayi min katangan rodi with some set of readers ba, duk da dai
ra'ayinsu suke 6a6atu a kai nd they are entitled to der opinion, but oh God do not allow me to be seeing
der comments so that i can write happily till end without mind spoilage Ameeeeenn* 🫣 to those of u
reading my book for free know that u owe me dari biyar kacal ehe... 😚
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you



Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last
bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd
getting rid of any skin problems

Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta
samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar
rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata
masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda
zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada

Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240




Jiddah ta langwabar da kanta tace "Ai ban sani ba, in dai mata na xuwa sai mu dinga tafiya tare" That
wasn't were Abuturrab wanted the conversation to end, but because of how cautious he was with time
sbda sllhn juma'ah, ya kalleta kawai yace "Kafin in dawo masallaci ki tabbatar kin sake wanka kin shirya
cikin atamfa, sannan ki karya..." Sae kuma ya hade rai, Ta sauke idonta kasa tace "Ni na karya da asuba ai"
Daga sama har kasa ya kalleta sannan ya juya ya fita ta bi sa da kallo.... Ko da ya dawo juma'ah har ta
shirya kamar yanda yace mata, Hijab ya sa ta daura kan atamfar, bayan ta sauko ta tsaya tana kallonsa, sau
daya ya kalleta ya dauke kai yace "Fita ki jirani a waje" Ba musu ta nufi kofa ta fita daga parlon, sae a
sannan ya tashi ya kashe appliances din gidan ya dau makullin motarsa da hulansa ya fita, the ride was
silent har suka iso gidansu, gaba daya he was absentminded, yau da safe ma kiran Aunty ne ya tashe sa,
har sannan kuma ya ki daukan kiranta, then is he even suppose to go home now? bai yi parking a kofar
gidansu ba in case of necessity, ya juya yana kallon Jiddah yace "Ki jirani" Bai jira tace komai ba ya bude
motar ya sauka.... Da murmushi Abuturrab ya amsa gaisuwan mai gadinsu ya shiga cikin gidan, sosai ya ji
hankalinsa ya kwanta da kanninsa suka ce Aunty ta fita, Yana kallon Ramlah yace "Ina ta tafi?" Ramlah tace
"She left for Abuja this morning" Shiru yyi yana kallonta, can ya nufi parlon Umminsa, ganin bata parlon ya
fito, ganin ya nufi kofar fita Ramlah tace "Ummi na bedroom fa" Bai tanka ta ba har ya fita, tare ya dawo
cikin gidan da Jiddah, murmushi kawai tayi ma su Ramlah da suka gaisheta, ta bi bayansa xuwa parlon
Mahaifiyarsa, kafin yace mata komai ta xauna a kasa, ya karasa cikin bedroom din Ummi da sallama,
gaisheta yayi da ladabi, ya shafa kansa yace "Ummi xa ku gaisa da ita a parlor" Ummi tace "Ohkk" Mikewa
yayi ya fito parlon, ya xauna kan kujera, ba a dau lkci ba Ummi ta fito, jiddah ta sunkuyar da kanta ta
gaisheta, Ummi ta amsa da murmushi fuskarta tace "Ya ku ke?" jiddahh tace "Lafiya lau" Ummi tace "To
madallah, sannun ku da xuwa" Ummi dake kallonta kasa kasa ta ga ta canxa mata sosai, haskenta na ainahi
ya fito ga wani glowing da take yi, Shi dai Abuturrab danna wayarsa kawai yake, jin Umminsa bata kuma
cewa komai ba ya daga kai ya kalleta yace "Ummi wai Aunty ta tafi Abuja?" Ba tare da ta kallesa ba "Ai na
xata xaka fi kowa sani tunda kun fi kusa" Ya sunkuyar da kansa yace "Aa bamu yi magana ba" Ummi tace
"Ayyo" yace "Yaushe tace xata dawo?" Ummi tace "Baka da lambarta ne?" bai kuma cewa komai ba kuma
bai dago ba, Jiddah dai sai kallon Ummi take, Bayan few seconds Abuturrab ya dago yace "An kawo lefen
Ramlah ne?" Ummi tace "Bakwa magana da Ahmad din ne?" Yace "Shekaranjiya mun hadu a Abuja da na
sauke jirgi a airport din can" Da sauri Jiddah ta kallesa, suka hada ido ya hade girar sama da ta kasa yana
kallonta, turo baki tayi, Ummi dai tv kawai take kallo, Ya dauke kai yace "Amma yace min xai shigo kadunan
yau, kilan xanje daukosa a tashan jirgi anjima" Ummi tace "Allah ya kawosa lafiya" yace "Ameen" Ummi
tace "Idan kaga xaka iya sai ka bar ta nan har bayan bikin, tunda ranan talata xa su fara shagalgulansu"
Abuturrab ya d'an yi shiru, can ya daga kai ya kalli Ummi yaga kallonsa take, suna hada ido tace "Ranan
bikin sae ka kawota" Da sauri yace "Aa Ummi gobe xan kawota tunda bata xo da kaya ba" Ummi tace "Aa a
bari ranan bikin dai" Yace "Uhn xan kawota goben in sha Allah" Ummi tace "Baxa ka siya mata ankon bikin
ba?" Ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Nawa ne?" Ummi tace "Kala uku ne, daya na family, sai general one
da xa a saka ranan yini, sai kuma na dinner, although naji yan matan sun fidda wani da xa su saka ranan
talata" Yace "Nawa ne duka" Ummi ta hada masa kudin gaba daya tace "Gaba daya 40k ne" Yace "A dinke
xa a siyo kayan?" Ummi tace "Ehh, da yake kayan dama a kyauta aka samosu daga kasuwa, iyakar kudin
dinkin ne dubu arba'in" Abuturrab ya bude ido ya fara dariya yace "Ummi tambaya fa kawai nayi" A takaice
tace "Nima amsa na baka" Ya shafa kansa yana murmushi bai ce komai ba" Ummi na kallon Jiddah tace "Su
Ramlah na can daki kije ki samesu tunda naga baki son magana" Tayi murmushin karfin hali ta mike ta nufi
kofa, Abuturrab ya mike yace "Ai bata san dakin ba, i will back Ummi" Da ido kawai Ummi ta bisa da kallon
mamaki har suka fita. Dakinsu Ramlah ya kai ta, Ramlah na xaune da Siyama sai wata kawarta da Aisha
step sis dinta, tana ganin Jiddah ta mike tana welcoming dinta da fara'a, bai amsa gaisuwan yan dakin ba
banda na kawar Ramlah da bai sani ba, sannan ya juya ya fita ya koma bangaren Umminsa....

Karfe hudu saura yace da Ummi xai je dauko Ahmad a train station, Ummi tace "Toh Allah ya tsare" Yace
"Ameen" Daga haka ya fita daga parlon, dakin su Ramlah ya nufa, Jiddah na xaune tana ma Siyama tsifa, su
Ramlah suna ta labari a dakin ganinsa duk suka yi shiru, yana kallon Siyama yace "Ke tsifan sai an maki??"
Tayi dariya tace "Ita tace ta xata min Yaya" Yana kallon Jiddah yace "Kinci abincin ko baki ci ba?" Ramlah
tace "Yanxu muka gama cin abincin fa yaya" Wani kallo ya jefa mata yace "Nayi da ke?" Bata kuma cewa
komai ba, yana kallon Jiddah fuska daure yace "Tambayar ki nake" Tace "Mun ci" juyawa yayi ya fita, Sai da
Ramlah ta tabbatar ya tafi don har sai da taje ta d'an bude kofar taga babu kowa wajen sannan ta dawo
tana kallon jiddah da murmushi tace "Yaya yana ji dake kamar yanda yake ji da profession dinsa..." Jiddah
dai bata ce komai ba ta ci gaba da tsifar da take.... Bayan kusan awa daya da tafiyar Abuturrab Aunty ta
dawo gidan, alamar dai ita ma train din ta biyo daga Abuja ta dawo, tun da ta kyallara ido taga Jiddah taji
kamar taga mugun abu a gidan, ko gaisuwar Jiddah bata amsa ba, bata sake shiga damuwa ba sai ganin
wani haske da kyan da Jiddah tayi alamar kwanciyar hankali, ita Abuturrab xai raina ma wayo?? Ta kusa
minti ashirin xaune gefen gado a dakinta, ta saka wannan ta kunce wnn, ita Abuturrab ke son kunyatawa
gun aminiyarta? Takanas ta shirya yau ta tafi Abuja ba mahaifiyar Aneesah hakuri bayan sun sanar mata
abinda Abuturrab din yyi ma Aneesah a airport kamar yanda Aneesan ta gaya ma uwarta... Wani
murmushi Aunty tayi tana gyada kai. Jiddah na ta xaune parlorn Ummi ita kadai don su Ramlah da yan
matan gidan sun fita xuwa gun tailor, Ummi kuma ta hanata bin su tace mijinta bai sani ba, Jiddah na ta
juya furucin Ummi a kanta, wai mijinta, ai ba mijinta bane Aliyu, tunanin hakan kawai sai taji jikinta yayi
sanyi sosai, Ummi ce ta fito daga dakintaz ganinta xaune ita kadai tace "Ki shiga kitchen kiga ko aunty na
ciki ki tambayeta abinda xa ki kama mata Jiddah" Jiddah ta kalli Ummi a hankali tace "Toh" Mikewa tayi ta
fita bangaren Ummi, tayi hanyar kitchen din, jikin kofa ta tsaya tana lekan kitchen din don ita har taji tana
tsoron matar nan da ake ce ma Aunty, ganin Auntyn a ciki, cikin sanyin murya tace "Aunty me xan kama
maki wai?" Juyawa Aunty dake yankan cabbage tayi tana mata wani irin kallo tace "Me xa ki kama min?"
Jiddah ta gyada mata kai gabanta na faduwa, Aunty ta ajiye wukan hannunta ta kunduma mata xagi tace
"Ke a wa xaki kama min aiki?? Yanda kika samu wajen xaman yin iskanci gidan Aliyu kin xata nan ma haka
ne, toh bari kiji... Wllh ki saka a ranki cewar xamanki ya xo karshe a gidan Aliyu, sai dai ya dinga bin ki can
kauyen naku yana iskancin da yake dake, yau xai san ni mahaukaciya ce wllh" Jiddah dai kallonta kawai
take a ranta tana kara nanata kalmar da ta jefa mata wai iskanci, tana nufin iskanci suke yi da Aliyun
kenan? Muryar Aunty ya sake dawowa da ita, ciki tsawa tace "Baxa ki fita ki bar min kitchen ba mayya...."
Cikin sanyin murya Jiddah tace "Ni ba iskanci muke yi ba wllh...." Aunty ta fixgi roban cabbage din gaba
daya ta watsa mata ranta bace ta kunduma mata xagi tace "Kina shige da karuwar xaki ce min ba iskanci ku
ke ba, dama mace da namiji na xama gida daya tare babu aure? Fita ki ban waje kada in fasa maki ido
algunguma" Jiddah da ta rufe idonta da hannunta taji kuka ya taho mata ta juya da sauri ta bar kitchen din
jikinta duk cabbage da suka makale, dai dai nan Abuturrab ya shigo

32 / 108