Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
Ta sakashi ya kwaso har mutum uku suka taho neman auren da an riga an gaya mata ba za'a basu ba? Kuma cikin taro irin wannan? Wanne irin muzanci ne wannan ta janyo masa? A yanda ma yaji Alhaji Modun na magana da bacin rai, kamar Haris din bai kai namijin da zai iya daukar 'ya ya bashi ba, da ya duba sai idanuwanshi suka sauka akan na Alhaji Sa'id, saiya tsinci kanshi da furta kalmomin da zai shafe shekaru masu yawa yana dana saninsu
"Ma Shaa Allaah, ai a musulunci ma shari'a ta hana nema cikin nema, da tayi mun bayanin nan, ko nayi magana da kai Alhaji Modu da ba'a samu akasi ba, amman tunda neman aure mukazo, ai ba za'a fasa ba, Sa'idu ina nemawa Haris auren daya daga cikin yaranka..."
Ya karashe maganar idanuwanshi cikin na Alhaji Sa'id da yaji zuciyarshi ta buga, ta sake bugawa sanin kowa shi yake jira ya amsa, ya kalli Alhaji Mustafa, yanajin nauyin idanuwan mutanen dake dakin, amman babu abinda yake hangowa sai lokuttan da yayi tuntube da rayuwa, Alhaji Mustafa ya tare shi yana jingina shi da jikinshi batare daya bari ya kai kasa ba, sai yanda tun yana da shekaru kasa da goma a duniya, babu wani shafi na rayuwarshi da za'a bude batare da sunan Alhaji Mustafa ya fito a ciki ba, sau nawa yake rokon Allaah Ya nuna masa ranar da zai kamanta masa wani halacci badan ya rama wanda yayi masa ba, sai dan ya nuna masa shi din dan halal ne wanda baya manta alkhairi komin kankantarshi
Sa'idu kaine fa zaka kulamun da abin nan
Sa'idu ga kudi nan nasa a sakamun a account dinka in sun shigo ka fadamun
Sa'idu cikin kudin nan na wajenka ka dauki kaso kaza
Sa'idu
Sa'idu
Sa'idu
Muryoyin Alhaji Mustafa suka dinga dawo masa, wasu na ture wasu, kuma dukkansu na wani alkhairi ne da adadin nauyin shi zai danne shi da ahalinshi gabaki daya, yau a karo na farko wannan muryar ta Alhaji Mustafa da wasu zasu fassara cike da iko da izza, tayi laushi, ta cika da rokon da bai taba giftawa a tsakaninsu ba, ta ina zai fara tankwabeta? Ai aminantaka zatayi Allaah wadai dashi, zaman tare zai tsine masa, ya tabbata duniya duka zasuce
"Sa'idu baka san halacci ba"
Sai dai cikin yaranshi da suka rage wa zai bawa Haris? Sauran su uku, Asiya yasan akwai yaran da yake zuwa wajenta, tana level 2 a yanzun, sai Khairiyya data gama rubuta jarabawarta ta aji shida, in ba irin yanzun ba, mantawa yakeyi bashi ya haifeta ba, yar kaninshi ce, yana da cikakken ikon bayar da aurenta batare da mahaifinta ya daga masa kai ba, amman anya yayi adalci idan ya tsallake Maryama ya bayar da Khairi? Inda ace daga Asiya sai Khairi ne, to saiya bayar da Khairin da hujjar Asiya na da wanda take so
"Maryama, na ba Haris auren Maryama"
Yayi maganar yanajin wani nauyi ya danne masa zuciya ya kara sanyaya masa jiki
"Da alama dai yau aure bakwai za'a daura kafin taron nan ya tashi"
Fadin Alhaji Kabir, sai kuwa Alhaji Jibril ya karbe zancen da
"Alhamdulillah, Ma Shaa Allaah, ni zan bada sadaki kuwa..."
Ya mike kafin ma wani ya fadi wata kalma, baiyi mintina goma ba ya dawo, a shekarar 2013 ce, kowa yasan darajar dubu dari, haka Alhaji Jibril ya dauko, ya kuma karasa ya kama hannun Alhaji Sa'id ya damka a ciki
"Ga sadakin Maryama..."
Cikin kasa da mintina goma aka daura auren Haris da Maryama,
Auren da kaddara ta rantse akanshi,
Auren da kowa zaice rabo ne kawai,
Auren da zai canza rayuwar mutane da dama...
*
Lokacin da suka tafi, tun daga Kaduna har Kano hira sukeyi, wajen dawowa kuwa daga filin jirgi da aka dauke su, hirar tafi yawa ne tsakanin su Alhaji Kabiru, daga Alhaji Mustafa har Alhaji Sa'id kamar an liqe musu bakuna, kowa da abinda yake sakawa a ranshi. Alhaji Kabiru aka fara saukewa, sannan aka sauke sauran, tukunna suka direban ya nufi gida da Alhaji Mustafa, wani abu da Hajiya Rumana ta jima batayi masa ba, ko yace tunda ya kara aure, shine ta tareshi a harabar gida da taji motarshi inya dawo daga tafiya, tasha kwalliya cikin wata doguwar riga ta leshi kalar ruwan toka daya amshi bakar fatarta, tayi shar da ita, daya fito daga motar, murmushinta da kuma tarbar da ta fito tayi masa ya tabbata saboda tasan abinda tayi ne, tun azahar take kiranshi tana tambayar ya ake ciki, yayi wani murmushin takaici yana cewa
"Saurin me kikeyi ne Rumana? Ba gidan zan dawo ba"
Watakila murmushin ne yasa tayi dariya, ta kuma dauka anyi nasara, ramin data hakawa Alhaji Modu bata bar masa wani zabi daya wuce fadawa ba, aikuwa itace mutum na farko da zata fara kiran Haris ta gaya masa, tayi masa albishir din da take fatan har karshen rayuwarshi karya manta dashi
"Sannu da zuwa..."
Ta fadi tana kokarin kama hannunshi, bai bata kunya ba, shima nata hannun ya kama suka karasa har bangarenshi
"Amman kunyi sauri..."
Yayi murmushi kawai, ya zauna kan kujera, ita kuma ta shiga cikin dakin sosai, in dai karamin fridge dinshi yake ta dauko ruwa, ta dauki kofi a wajen da ake ajiyewa tana kawo masa ruwa, ya sha har saida ya nemi kari, ita ta karbi kofin ta ajiye, ta zauna a gefenshi, ya kamata ace tana Maidugurin tasani, sai kiranta sukeyi ta langabe tayi musu karyar bata da lafiya, in taji dadin jikinta, a yanda ta fada washegari zata isa Maidugurin, ranar Lahadi kenan, tunda akwai sauran shagulgulan da za'a gabatar, kuma ba wani abu ya hana mata dokin bikin ba duk kaunarta da hidimar biki, sai gujewa Alhaji Modu da takeyi, bataso su hadu sai ta tabbatar an gama wannan maganar, ita dashi sai dai su bada labarin halayen juna.
Kuma ko da shekaru suka ja a tsakaninsu, ai ance hali zanen dutse, akwai halayen da ko lokaci baya raba mutum dasu, daga cikin wannan halayen tasan Alhaji Modu ya bita har cikin gida ya damko hannunta zuwa inda zasu sake suyi fada ba wani abu bane ba, inma taki hankalinshi kwance zaiyi fada da ita a gaban kowa, su biyun anyi musu shaidar rigima a kaf ahalinsu, tun tasowa, kuma wannan rigimar shekaru basu raba kowanne a cikinsu da ita ba. Ta numfasa da niyyar tambayarshi yasa hannu a aljihunshi ya zaro goro, irin goron da tasan ana rabawa ne a lokacin daurin aure, manya-manya, ja da kuma fari, guda biyune ya mika mata, ta karba idanuwanta cike da tambayoyi
"Ga goron auren Haris..."
Ta dan zaro idanuwa, ta bude baki, ta rufe, ta sake budewa amman duk wasu kalamai nata kamar sunbi iska haka takeji, ta rasa abinda ya kamata ta fada, sai kawai ta kai goron nan bakinta ta gutsira ta tauna
"Alhamdulillah, Allaah Yasa an daura alkhairi..."
Ya amsa da
"Amin thumma amin"
Da yake kafin su juyo, Alhaji Modu da kallo daya zakayi masa kaga yanda kunya tayi masa dabai-bayi ya rantse ba zasu bar Maidugurin ba sai anyi duk wata siyayya daya kamata ace bangaren maza sunyi dangane da aure, babu inda zasu dauko wannan kayan su taho dasu, sai goron yasa hannu ya diba ya mimmika musu, harda Alhaji Sa'id
"Kayan nan zasu biyo bayanku zuwa Kaduna In Shaa Allaah..."
Ya kuma san idan basu iso cikin daren yau ba, to gobe suna hanya
"Me yasa kikayi mun karya Rumana?"
Ya tambaya idanuwanshi fes cikin nata.
"Me yasa zaki turani neman auren da aka riga aka gaya miki ba za'a bayar ba? Saboda ki wulakantani a cikin taron danginki?"
Komai nata yayi tsaye cak da tambayoyinshi, harda hakoranta da suke kokarin tauna mata katon goron data gutsira
"Har yanzun ba zaki daina halin nan na aikata duk abinda zuciyarki ta saka miki ba ko? To Alhamdulillah, burinki bai cika ba Rumana, ban kunyata ba, na nemawa Haris auren Aise an hanani, amman bamu baro Maiduguri ba saida aka daura masa aure da Maryama"
Kuma a duk maganganun da taji, sai ta zabi tayi tsokaci akan kalmarshi ta karshe
"Wacce Maryaman?"
Yayi mata wani kallo kafin ya amsa da
"Maryaman Sa'idu"
Goron da yake bakinta ta furzo dashi waje har a jikin Alhaji Mustafa kuwa, batasan ta mike ba sai da taji ta akan kafafuwanta, zuciyarta na kadawa gangar jikinta wata ganga da ta kasa tantance ta bacin raice ko tsananin firgici
Haris din aka daurawa aure da 'yar gidan Alhaji Sa'idu?
Haris dinta?
Babu abinda kwakwalwarta take hada mata sai jininta da na Alhaji Sa'idu a waje daya, sai danta mafi soyuwa a cikin zuciyarta da jinin Alhaji Sa'idu, almajirin nan da mijinta ya dauka da muhimmancin da ta kasa gane tushen shi, wacce irin bakar rana ce
"Haris din? Haris din ka dauka kaba Sa'idu? Dana Mustafa?"
Tayi maganar wasu hawayen bakin cikin na wanke fuskarta
"Ko dai shi Sa'idun ya rufamun asiri ya dauki auren Maryama ya ba Haris ba"
Wasu hawayen ne suka sake zubo mata
"Allaah Ya tsinewa wannan rufin asirin Mustafa, in dai na Sa'idu ne Allaah Ya tsine masa...na rantse da Allaah ba'a isa ba, babu wanda ya isa yayi mun haka, akan me? Kai ka haifa mun dan ko shi Sa'idun?"
Da wani irin bacin rai yake kallonta
"Ke kika haifi abinki, amman ni nake da iko dashi a matsayina na ubanshi, kuma a karo na farko a rayuwarshi zan ga idan na isa in amsa wannan matsayin a wajenshi ko zaki hana ne Rumana"
Ta kai hannu ta share hawayenta tanajin yanda zuciyarta take zafi kamar zata kama da wuta
"To baka isa ba, kana jina? Kaima baka isa ba balle Sa'idu...zan kira Haris ya sakar masa 'yarshi a yau din nan ba sai gobe ba..."
Tayi maganar tana juyawa da saurinta, ta kai kofa kalamanshi suka tsayar da ita cak
"Idan kikasa Haris ya saki Maryama a bakin aurenki, idan maganar auren nan ta isa kunnen Haris daga bakinki a bakin naki auren Rumana..."
Kafafuwanta taji suna neman kasa daukarta, ta juyo da idanuwanta da suka sake launi
"Akan Sa'idu? Ni kakewa barazanar saki akan Sa'idu? Akan 'yar shi?"
Nashi idanuwan shima sun rine da bacin rai
"Eh akan Sa'idu da 'yar shi"
Ta jinjina kai, batare data furta komai ba ta fice daga dakin, yanajin yanda bugun zuciyarshi ya karu saboda bacin rai, akan wannan auren da sai bayan an daura shi yaji fargaba ta dirar masa, a shirye yake daya nunawa Rumana iyakarta, ya kawo karshen duk wani kauda kai da yakeyi mata akan yanda ta dauki Alhaji Sa'id, da bakinshi ya nemarwa Haris auren Maryama, kuma zaiyi tsaye wajen ganin ya sauke wannan amanar da ko dogon tunanin Alhaji Sa'idun baiyi ba ya mika masa ita. Ai daman yasan dole za su kwashi 'yan kallo da ita, tunda ta saba ita take iko da yankewa yaran hukunci, shi bai isa ba, wannan karin ya shirya mata tsaf tun da aka daura auren.
Sai dai shi Alhaji Sa'id din baiyi wannan shirin ba, asalima bayan kafafuwanshi da yake ja dakyar lokacin da su Alhaji Mustafa suka sauke shi gida. Aljihunshi ma rinjayarshi yakeyi, duka biyun, daya goro ne, dayan kuma sadakin Maryama ne. Haka ya shiga cikin gidan nashi da sallama cikin muryarshi da yaran suka dauka ta gajiya ce, ganin kuma yanda yake ta amsa sannunsu da kai kafin cikin irin muryar yace wa Khairi
"Ina Hajjanku?"
Ta mike da saurinta, bai ga Maryama ba, amman kafin Hajjan tazo ma duk yaran sun watse, sai kace sunga alamun magana yake so yayi da matarshi, magana mai muhimmancin gaske, dan itama Khairin dakinsu ta wuce, sai gata kuwa tana yi masa sannu, tasan yana hanya, yaran shinkafa da miya sukayi, shine bata sa kowa ba, ta shiga da kanta take soya masa funkason da taki karbar tayin kowa wajen yin aikinshi, tama gama ta hada komai, tana dauraye hannunta ne Khairi ta fada mata gashi nan ya shigo, kallo daya tayi masa tasan ba gajiya bace kamar yanda yaranshi suke tunani, damuwa ce kwance akan fuskarshi, ta zauna akan doguwar kujerar da shima yake zaune, bayan tayi masa sannu da zuwa ya amsa, yaja numfashi yana saukewa, ya kalleta na wasu dakika.
Hannu yasa a cikin aljihunshi ya fara dauko goro guda daya daga ciki, baima san guda nawa bane Alhaji Mustafa ya danka masa, ya kamo hannunta ya saka a ciki, duk da bata tare da ma'abota cin goro, amman ai ta ganshi sau babu adadi a rayuwarta, yau dai ne ganin wannan din da yake hannunta ya haifar mata da faduwar gaba mai tsananin gaske, kafin kuma tayi wani yunkuri ya sake saka hannunshi a aljihu ya zaro damin kudi ya kara kama hannunta ya dora akai
"Kudin menene wannan? Goron menene?"
Tayi tambayar cikin rawar murya, daga farko, kafin taga kudin sai zuciyarta take saka mata ko aure ya kara? Lokaci daya taji tana so ta fashe da kuka, ta kuma ji tanaso tayiwa kanta dariya
"Sadakin Mairama ne, goron daurin aurenta ne da akayi da Haris dazun a garin Maiduguri"
Ta zuba masa ido na dakikun da suka bace daga lissafinta, kallonshi takeyi kamar wani bakonta
"Nayi muku laifi ko? Na bayar da auren 'yarki batare da shawararki ba"
Hawaye ne taji sun zubo mata da watakila da tana da ikon hango kaddarorin da suke jiran Maryam din sai tace wasu a cikine ta hango, tausayin 'yarta ne ya kamata shisa, amman a yanzun kam ba zatace ga dalilin hawayen ba
"Ya zanyi in kalli Mustafa ince ba zan ba Haris auren 'yata ba?"
Ta ajiye kudin akan kujerar, ta kamo hannunshi da yake rawa
"Allaah Ubangiji Yasa albarka a auren, Allaah Yasa duka mu hadu wata rana muce gara da akayi, Allaah Ya basu zaman lafiya da fahimta irin wanda za'a bada labari a tsakanin jikokinsu wata rana"
Ya dumtsa hannunta cikin godiyar da ya kasa furtawa, duk da kalamanta sun nutsar dashi, amman ai ita yasan macece da baya gajiya da godewa Allaah da samunta, macece da bata taba bata fuska akan hukuncin da zai zartar ba, macece fa da ya kwaso mata yaran 'yan uwanshi ya cika mata gida dasu, ta karba ta rike kamar nata, bai tabajin korafinta akan yanda danginshi suke mata zarya akai akai ba
"Ina take? Ina Mairama?"
Ya tambaya, sai a lokacin ne kuma zuciyar Hajja ta buga, ita ta karbi auren da zuciyarta daya kamar yanda tasan Alhaji Sa'id ya bayar da auren da tashi zuciyar a wanke, amman ai daga ita harshi babu wanda zai taya Maryam din zaman auren.
Sannan ita tasan abinda shi bai sani ba,
Tasan Maryam na son Ishaq...
Da farko bata maida hankali ba, sai da taji yanda 'yan gidan gabaki daya, ciki harda mazan kuwa suke saka Maryam a gaba in Ishaq yazo
"Mutumin naki fa yazo..."
Har ta fara saka ido, tana ganin yanda idanuwan Maryam yake cika da kunya da wani abu da yayi mata kama da fuskarta a cikin mudubi a lokuttan da take tsakiyar soyayyar Alhaji Sa'id. A zuciyarta, a lokacin tayi musu addu'a, idan akwai alkhairi a tsakaninsu Allaah Ya tabbatar, idan babu kuma yayi musu musaya da mafi alkhairi, dan kuwa Ishaq din yaro ne nutsatse, bata taba ganin yayi wani abu akasin haka ba, sannan mahaifiyarshi tana mutuntata, in zasu zo gidan nan, a kwanakin da zasuyi tare suke shiga kitchen, haka duk wani aiki da zata ga anayi ko ance tabarshi saita sa hannu anyi da ita.
Gashi basu da fargabar tsayawa bincike tunda ai na gidane. Kawai ta cigaba da saka ido ne akan motsin Maryam din dama na Ishaq din idan yazo gidan, da yake bashi da rawar kai, bata taba ganin sun kebe wani waje ba, duk hirar da zasuyi anan falo ne, wani lokacin ma tare da kowa da kowa, sai dai yanayinsu ya nuna maka akwai soyayya, irin soyayyar nan mai sanyi da ake ginata a hankali, soyayyar da babu wata gaggawa a ciki, ashe kaddara zata yayyafa musu ruwa kafin ma itacen nasu su gama bushewa balle suyi tunanin kunna wuta. Sai tausayin Maryam din ya danne zuciyar Hajja, a cikin yaran gidan kaf ma babu wanda akayiwa aure batare daya kammala sakandiri ba, kai Zahra mace kawai tana gamawa akayi bikinta, kuma a lokacin ko ita ta samu admission, sai ta cigaba da karatun a dakinta.
"Ke zakiyi magana da ita koni?"
Da sauri ta girgiza masa kai, ita uwace, kamar yanda ya kasance irin uban da kowanne yaro zaiyi alfahari dashi, amman a rayuwar yaransu, itace mai zafi, itace mai fada, itace take duka, itace in an tambayi abu takan hana a lokutta da dama, akwai damuwar yaran da yawa da sai dai taji labari a wajenshi, sunfi sakewa dashi da dukkan lamurransu fiye da ita, kamar dai akwai wani abu mai taushi a tsakaninshi dasu, abinda yake sakasu fada masa komai batare da fargaba ba, a gidaje da yawa, ko tsayayyen saurayi yara sukayi suke son mahaifinsu ya sani, mahaifiya suke tunkara sai ita kuma ta sanar, amman haka suke zagayeta suje wajenshi kai tsaye.
"Hajja zatayi fada, Hajja zata hana"
Haka suke cewa, batama jin tana da wasu kalamai da zatayiwa Maryam bayani, me zatace mata? Ta ina zata fara? Babanki ya bada aurenki? Yanzun ke matar aure ce? Ta inda duk ta kamo zaren sai taji ya tsinke mata
"Ki taimaka ki kiramun ita to"
Alhaji Sa'id yayi maganar muryarshi cike da rauni, sai ta mike, a wannan yammacin ma, ita Maryam din tana dakinsu, da wuri suka tashi Islamiyya, ko tace ma basu hada mintina talatin ba aka tashi, anyi rasuwa anan kusa da Islamiyyar, babban mutum ne, sai aka tashe su da wuri saboda Janaza, unguwar ma harta fara cika, haka suka ratso mutane suka dawo, bata ma damu dasu Asiya da suke tsokanarta ba, haka ta tashi da wani irin sanyin jiki, ko magana bataso tun safen, su kuma basu ga lokacin da zasu uzzura mata ba sai a wannan yanayin. Suna mata tsiya ne kan wasu turaruka da Ishaq ya kawo mata, guda hudu ne, tayi niyyar basu dai-dai saita fasa, tunda Asiya tace
"Na tabbata shekara yayi yana tara kudin turarukan nan, dan daga ganinsu zasuyi tsada, shima da iyayi..."
Ita kuma Khairi tayi dariya
"Haba ba zai shekara ba Adda, ai kinsan in yazo dole Abba zai bashi kudi idan zai koma..."
To ta fasa basu, gara ta fesa guminshi da hakurin da yayi da abubuwan dadi ya kashe mata kudin, tattalasu ma zatayi, ta boye inda tasan daga Asiyar har Khairi