Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
da ita.
Falon ta koma ta samu Maryama ta daga akwatin nan tana shirin sake kwantarawa Haris saboda takai kofa ya riko mata Hijabi
"Kashe shi zakiyi Maryama?"
Tayi maganar da madaukakin mamaki
"Wallahi ka sake tabani saina buga maka shi, ka kyaleni, gidanmu zan tafi"
Cewar Maryama da hawayenta ke zuba kamar an bude famfo, ganin Haris din na shirin sake riketa yasa Hajiya Rumana ta karasa da sauri tana watsa masa zagi
"Dan ubanka saita kwala maka ta kasheka tayi mana asara ko?"
Ta karasa tana hararar Maryama
"Ka rabu da ita ta tafi gidan nasu mana, sai me? In bama tsinannen naci irin naka ba, sai kace ita kadaice mace a fadin duniyar nan, daka dauki shawarara tuni har zata tsaya tana maka wannan barazanar ne"
Cikin wani yanayi yace
"Dan Allaah Mami, nine nayi mata laifi"
Hajiya Rumana taja tsaki kamar harshenta zai rabe biyu
"Dan Allaah ki bata hakuri, kice ta tsaya muyi magana"
Tsakin ta sake ja tana masa kallon takaici kamar tana gab da kwada masa mari, badan tana gudun kar Maryama ta kassara matashi ba, data matsa ai ta barta ta kwantara masa akwatin nan
"Laifin me kayi mata? Ko laifin kayi mata saita nemi kasheka?"
Wannan maganar tasa wata dariya da kuka suka kwacewa Maryama a lokaci daya, tsaye take waje daya, amman ji takeyi dakin na zagayawa da ita
"Me kayi mun? Ka fada mata"
Idanuwanshi ya saka cikin nata, wannan maikon yau na roko ne, ta kai hannu ta share hawayenta da sauri, wasu na kara zubowa
"Ka gaya mata Ganjaa, wallahi inka bude bakinka ka fada mata abinda kayi mun zan zauna muyi magana..."
Wani irin shiru ya ratsa dakin, irin shirun nan da akewa lakabi da kwatankwacin na ratsen mutuwa, kafin karar akwatin da Maryama taja ya kawo karshen shi
"Maryamm"
Ya kira muryarshi na rawa, ganin harta daga labulen dakin yasa shi fadin
"Hotel naje..."
Da sauri idanuwanshi akan Maryama da tayi tsaye, sai kuma ta juyo, kallonshi ta sakeyi, shima ita yake kallo, Hajiya Rumana kuma tana kallon su duka biyun
"Kaje kayi me?"
Cewar Maryama cikin wani irin rauni da yayi barazanar kayar da Haris din
"Mami hotel naje...I....I cheated on her"
Tayi wata dariya mai sauti, wai yaushe ne aka fara yiwa zina kwaskwarima?
"Fassaramun I cheated on her"
Cewar Hajiya Rumana cikin tashin hankali, inda ma sun saurara da sunji yanda cikinta ya kwaso wata kara, ya kalli Maryama, yasan kafiyarta, ya dawo da idanuwanshi kan Hajiya Rumana, Maminshi, Maminshi da laifukanshi kullum masu saukine a wajenta, Maminshi da ko zai muzanta a idon kowa yasan in yaje wajenta zai samu mafaka, zata lulluba masa bargon suttura
"I...I slept with someone"
Yayi maganar yana jin nauyinta bayan ya furta, kuma nauyin ne ya danne Maryama har saida ta dafa bangon da ke kusa da ita tana dan runtsa idanuwanta, ji take kamar zata yanke jiki ta fadi, karar da taji ce tasa ta bude idonta tar, mari ne, marine Hajiya Rumana ta wanke Haris dashi, da alama kuma mamakin marin yakeyi shi kanshi da aka wankawa balle kuma Maryama da take jinta kamar tana yawo a mafarkine
"Ai dama shaye-shayen yakeyi da sauki, amman kinsan girman daudar zina Rumana? Shine zan dauki 'yata in bashi"
Maganganun Alhaji Modu suka dawo mata ranar da sukayi abinda zata kira da uwar-watsi. Kuma maganar tayi mata zafi matuka, harta kwanta tana share hawayenta ranar, ashe Modu zaiqi jininta haka? Harya danganta mata Haris da mafi daudar aiki, saboda baya son bashi Aise. Ita kuwa meye zai hada jininta da zina? Ba'a shaidar mutum amman ko Qur'ani aka bata zata dafa kan cewa Alhaji Mustafa bai taba ko da kusantar zina ba, balle kuma ita, duk yawan kasashen da tayi ko gaisawa bata tabayi da wani da ba muharraminta ba, haka tayi aurenta cikin mutunci, to meye zai hada zuri'arta da wannan daudar? Dan a lokacin ta manta da wata kaddara balle kuma jarabawar da babu mahalukin da yafi karfinta, ta dai san babu wani abu da zai taba wanke mata wannan abin da Modu ya fada mata.
Dan ko a yanzun zumuncinsu yaja baya matuka, sai abu ya zama dole ne yake hadasu, tun yana kokarin shi harya hakura. Kenan gaskiya ya fada mata? To wai laifukan Haris guda nawa ne da soyayyarshi ta rufe mata ido daga gani, ta gabansu Maryama da take cira kafa dakyar tazo ta wuce ta shige dakinsu, ai ta rantse masa, duk da batayi zaton zai bude bakinshi ya furta wannan maganar a gaban Hajiya Rumana ba, kuma marin da tayi masa taji shi har zuciyarta, muzancin da take gani ya mamaye ilahirin jikinshi kafin ta shige daki, irin shine sak ya mamaye ta
Wai fa wannan Labulen da Haris yaja musu yayewarshi a gaban mahaifiyarshi ne...
A gaban matar da take da yakinin idan da mutane zasu taru su nemi kalle mata Haris a wannan halin tsiraicin zata cire mayafin jikinta ne ta rufa masa, su raba tereren tare...
To ina ga ace a idon sauran mutane ne?
Anya akwai kaddara mai nauyi irin Allaah Ya jarabeka da zama da mazinaci?
43
MARYAMA
Tun ranar da abin ya faru, tasan lokacin da Haris ya shiga dakin dare yayi sosai, duk kuwa da bata duba lokaci ba. Daya hawo gadon sai ta mike daga kai ta dauki pillow dinta
"Maryamm"
Batare data kalle shi ba tace masa
"Ba zan iya kwana waje daya da kai ba, dan Allaah, kabarni, yau kabarni dan Allaah"
Kuma a taurin kai irin na Haris, musamman idan fada takeyi dashi, a wannan ranar ba zatace ga abinda yayi aiki ba, yanayin muryarta, ko yanayin fuskarta, sai da ta kalle shi ta kara kallonshi lokacin da yace mata
"Ki dawo ki kwanta"
Sai shi ya dauki pillow din, tana kallonshi ya bude cikin wardrobe dinta inda take ajiye zannuwan gado, ya dauko guda daya, ya shimfida a kasa, ya ajiye pillow din, sannan ya kara dauko wani ya kwanta. Sai dai duk yanda tayi kokarin ganin tayi bacci, abin saiya gagareta. Akance kuka shi yakeyin kanshi, in yazo baka sanin sanda zakayi, to ita dai yau tanajin alamar kukan, tun daga kasan zuciyarta inda wani abu yake ta kaiwa da kawowa, amman idanuwanta sunki ba wannan abin hadin kai balle ta samu tayi kukan. Da yake ba bacci tayi ba, akan kunnenta aka kira sallah, saida ta tashi ta shiga bandaki ta gama abinda zatayi ta dauro alwala ta fito tukunna ta tashi Haris
"Lokacin sallah yayi"
Ya jima a kwance, tanajin dai idanuwanshi na mata yawo a jiki, wannan idanuwan nashi. Sannan ya tashi, da yayi alwalar fita yayi. Tana idar da sallolinta da duk wani azkar da zatayi saita fita zuwa kitchen. Kwanansu tara a haka, ya gwada yayi mata magana babu adadi amman batace masa komai, bawai bataso tayi magana dashi bane, kawai ko ta bude bakinta babu abinda zata iya cewa, kanta yayi nauyi, wani irin nauyi na ban mamaki, amman duk nauyin da yayi batajin komai a cikinshi, bata iya wani baccin kirki, zata tashi da safe, tayi duk wani abu data saba, har wanka zatayi sai dai batajin karfin yin wasu abubuwan bayan wadannan, ko yaran sun san wani abu yana damunta, dan haka Fa'iza saita janye su, su bata space din da suke tunanin tana bukata.
Wata safiya ta tashi saiga kiran Alhaji Sa'id, ta saba kullum saita kirashi ta gaishe dashi, suyi hira sosai, amman kwana wajen nawa, wayar ma ba dauka takeyi ba
"Abba..."
Ta furta bayan ta daga
"Mairaman Abba, kina lafiya dai ko?"
Tayi shiru, so take ta amsa, tace masa tana lafiya, amman labbanta sunyi mata nauyi da wannan karyar tun kafin ta furta
"Banajin dadine Abba, amman bansan me ya sameni ba"
Shima shirun yayi na wasu dakika, kafin a hankali yace
"Kina addu'a Mairama?"
Ta daga kai
"Inayi, kullum inayi"
Dan babu wani abu da ta fasa ko a kwanakin, duk wata addu'a da nafila da takeyi bata fasa ba
"Zan fito ba jimawa, zan biyo in dubaki In Shaa Allaah"
Ya kuwa biya din, kamar yanda yayi alkawari, dakyar ma ya shiga cikin falon, duk abubuwan da ta kawo ta jera masa, ruwa kawai yasha, tanajin yanda yake ta kallonta, kuma a tunanin Maryama ta aro murmushi ta dora saman fuskarta, sai dai idanuwanta fayau suke, sai kace wadda bata da wadataccen jini.
"Allaah Yayi miki albarka Ya sanyaya miki Mairama"
Cewar Alhaji Sa'id cike da damuwa, zuciyarshi ta takure waje daya, a karo na farko da yayi dana sanin wannan sadaukarwar da yayi, a karo na farko da soyayya hadi da tausayin Maryaman ya danne girman abotarshi da Alhaji Mustafa, a yau bayaji baya kuma tunanin komai sai 'yarshi. Har bakin mota Maryama ta rakashi yanata tsokanarta sai dai ta kasa mayar masa yanda ta saba, kamar an sauya masa ita haka yake gani, ya shiga mota, harya kunna, ita kuma ta juya da nufin ta koma cikin gida, sai kawai taga wani duhu ya gifta mata, batasan takai kasa ba, duhu ne daya gifta, bai bata damar sake bude idanuwanta ba balle tasan cewa yanke jiki tayi ta fadi, balle kuma ihun Alhaji Sa'id da fitowarshi daga mota.
Shiya dauketa ya saka a bayan motar, ya manta da cewa tana da aure balle kuma yayi tunanin akwai jaririn da bai rufa watanni hudu da haihuwa ba a cikin gidan, baya ganin komai sai 'yarshi da tsoron ta rasa rayuwarta. Su Maryama Dialogue suke zuwa, can suke da kati, amman shi Alhaji Sa'id da nashi iyalan a 44 da kuma Frontiers suke da kati, sai kawai ya nufi 44 din da ita. Sai bayan yaje an karbeta dan bata taimakon gaggawa tukunna ya samu ya kira Hajja yana fada mata abinda yake faruwa
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un, meya sameta?"
Cike da damuwa ya girgiza kanshi
"Bansani ba, faduwarta kawai nagani, tana numfashi, naga kirjinta na dagawa, amman duk da haka...na kashe 'yata ko Asma'u? Me yasa na aura mata yaron nan? Na kashe 'yata na raya dan wani ko?"
Bata amsa tambayoyin shi ba, sai tace masa
"Ina Naadir din?"
Cikin rashin fahimta yace
"Naadir?"
Da sauri tace
"Eh..."
Har lokacin dai bai gane me take nufi ba
"Bansani ba, dauko ta kawai nayi muka taho"
Sai yaji ta sake yin wani salatin kafin ta kashe wayar. Ya dade a tsaye a wajen, dan sai bayan ita Hajjan sun iso asibitin harda Khairi da take goye da Naadir din da itace ta biya ta dauko shi, dan har sanda taje yanata bacci ne.
"Ina Maryaman?"
Khairi da har fuskarta ta kumbura da alamun kuka tasha ta tambaya
"Tana ciki"
Alhaji Sa'id ya amsa, sun kuma sake kwashe wajen awanni biyu a asibitin nan, banda jinin Maryama da yayi wani irin hawa, sai kuma yanayin bugun zuciyarta da suka kira da palpitation, su kansu ba zasuce ga abinda yake damunta bayan wannan ba, dan ko motsi batayi ba, sun kara mata da alluran bacci a cewarsu tana bukatar hutun.
"An gayawa mijinta kuwa?"
Hajja tayi tambayar
"A fada masa yazo yayi mata me? Ko ta farka ta ganshi ya karasamun ita?"
A tsayin shekarun aurensu, in ta daga hannunta zata kirga adadin lokuttan da taga bacin ran Alhaji Sa'id, kuma kullum sai tayi addu'ar Allaah Ya kara masa hakuri, saboda mutum ne shi da bai iya bacin rai ba, ko dan ance daman haka mutane masu hakuri suke
"A'a karkace haka, tunda ita dai batace sunyi fada ko makamancin haka ba"
Wani irin kallo yayi mata
"Saiki fadamun wata matsala da zata sakawa Mairama hawan jini banda kaddararren auren nan dana dora mata..."
Shiru tayi, sai ta kalli Khairi da ta dan daga mata kai a hankali, itama kuma da yake tasan halin Abban nasu, sai da tabar wajen tukunna ta kira Haris
"Muna asibiti da Maryama bata da lafiya"
Ya danyi shiru kafin ya tambayeta wanne asibiti, ta fada masa, saiya kashe wayar. Fa'iza ya barwa message tunda akwai waya a hannunta, yasan direbansu zaije ya daukesu daga makaranta, karsu koma gidan suga babu kowa. Tukunna ya nufi asibitin, zuciyarshi ta buga, ta sake bugawa da yanda Alhaji Sa'id ya kalleshi, kuma rudanin daya shiga bai hanashi gane bai amsa gaisuwar da yayi masa ba. A cikin wannan tsoron ne ya kira Alhaji Mustafa ya fada masa suna asibiti da Maryama, duk kuwa da a ranar Alhaji Mustafan yana Abuja, haka ya jerawa Alhaji Sa'id kira har hudu bai daga ba.
"Na kira Sa'idu har sau hudu bai daga ba...lafiya kuwa Haris? Ko dai jikin nata yayi tsanani ne?"
Akan idon shi Alhaji Sa'id ya amsa kira dazun da suka fito sallar la'asar daga masallacin da yake wajen asibitin, sai gashi yana shirgawa Alhaji Mustafa karyar da baisan daga inda tazo masa ba
"Kilan wayar bata jikinshi ne Baba, ko tana mota, ko bai fito da ita ba...nasan da yaga kiran zai sake kiranka, nima na fito siyan wata allura ne da aka rubuta, jikin da sauki bacci take tayi"
Duk da haka akwai yanayin damuwa a muryar Alhaji Mustafan har sukayi sallama, ko a wanne irin yanayi, tun bayan shigowar wayar hannu, bai taba jerawa Alhaji Sa'id kira har hudu bai daga ba, anya yama taba katarin kiranshi baya kusa da wayar kuwa? Haka kawai abin yake ta damunshi. Washegari kuwa sai gashi a garin Kaduna, kuma har lokacin Maryama bata tashi ba, su kansu likitocin sun fara damuwa, dan duk wani kokari da zasuyi wajen ganin sun farkar da ita ya gagara, ga jinin nata ya fara sauka ba kamar sanda aka kawota ba, haka babu zazzabi a jikinta, amman taki tashi. Abu kamar wasa, kwanan Maryama hudu a cikin wannan yanayin, 'yan uwanta mata kuwa babu mai lallashin wani, har Hajja duk karfin halinta sai gashi tana share hawaye.
Kallo daya zakayiwa Haris kasan kwanciya ce kawai baiyi a asibitin da sunan marar lafiya ba, amman tare suke wannan jinyar da Maryama, ya fita hayyacinshi gabaki daya, musamman yanda kowa yake masa wani kallo, kallon da yasan duk da basu da cikakkiyar hujjar yi masa, kallo ne daya dace dashi, kallo ne na tuhumar laifin da yasan ya aikata, duk yanda za'a zagaya a zagayo shine sanadin wannan kwanciyar ta Maryama
"Kayi mata wani abinne Haris?"
Alhaji Mustafa ya tambayeshi a safiyar ranar
"Tunda nake da Sa'idu irin wannan shirun bai taba gifta mana ba, ko fadan kuruciya Sa'idu bai taba biyemun munyi ba, ko matana basa hakuri dani yanda yakeyi...me kayi Haris?"
Kanshi kawai ya sake saddawa kasa, to me zaice? Aiko hauka yake yana buge-buge yasan ba zai taba bude bakinshi yace wa Alhaji Mustafa ga abinda yayi ba, shirun nashi ne yasa shi fadin
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...me kayi haka Haris? Wanne abu mai girma kayi da ya kure kawaicin mutum irin Sa'idu?"
Shirun dai ya sakeyi, Alhaji Mustafa ya sauke wani numfashi cike da damuwa
"In Shaa Allaah ba zaka zama sanadin raba alakar da ta kullu tun kafin in san zan sameka ba, ba zaka rabani da abokina ba Haris, In Shaa Allaah ba zaka rabani da abokina ba"
Kuka Haris yake so ya fashe dashi, irin kukan nan da 'yan yara sukeyi idan sun fara gane yawo suka ga an fita an barsu, kukan da sai yayi juyi sannan ya tumu da kasa, ya mirgina daga farko zuwa karshen bango, kukan da kararshi zata kidima duk wani mutum daya damu dashi, yanda zasu rugo su rufu akanshi ana turereniya wajen dagoshi a lallashe shi. Sai dai a yanda kowa yake kallonshi din nan yasan babu wanda zai lallashe shi inma kukan yayi. Yana ganin irin kallon da Awwab yake binshi dashi a kwanakin nan
"Meya sameta?"
Haka yace masa
"Bata da lafiya ne Awwab"
Kai ya jinjina masa
"Eh nasani, meya sameta?"
Ya sake tambaya, kafadu kawai yadan daga masa tunda babu damar ya amsa da
"Ni, nine na sameta"
Ranar kwana na shida a asibitin Maryama ta bude idanuwanta, Hajja, Khairi da sai anyi da gaske take barin asibitin nan kullum, kuma da kuka itama tana dakin, sai Haris da a wajen Hajja ne kawai yake ganin sassauci, itace take amsa gaisuwarshi da fara'a, kuma take kulashi. Kuma yana ganin saita kalli Alhaji Sa'id yake amsa shi da
"Lafiya"
A halin yanzun ma Alhaji Mustafa fushi yake dashi, ko dan tunda Hajiya Rumana ta dauki wani irin fushi da bai taba gani ba, waye ma ba zaiyi fushi dashi ba? Yau ya tabbata inda akwai wiwi a jikinshi ba zai san lokacin da zai busa ba, ya manta rabon da ko tunaninta ya gifta masa sai da safiyar yau din. Sai kuma yanzun da Maryama ta kare musu kallo su dukansu, Hajja ta kira sunanta, ta kalleta tace mata
"Ina nake? Wacece ke?"
Da ta fita da nufin kiran likita Haris ya tashi ya riko hannun Maryama data fisge da sauri tana fadin
"Subhanallahi, meye haka? Waye kai? Me yasa zaka rikemun hannu?"
Wani abune mai kama da aradu yaji ya rikito masa yana neman danne masa numfashi, saima da likitoci biyu suka shigo suka korasu waje
"Ina Abbana? Ku kiramun Abbana"
Shine abinda Maryama take fadawa likitocin tana sake maimaitawa, babu shiri aka kira Alhaji Sa'id. Ta kuwa rikeshi tana sakin wani irin kuka daya kidima shi
"Kinganni nan Mairama...gani nazo"
Cikin kukan tace
"Wasu ne suke tamun magana tun dazun Abba, ban sansu ba"
Dakyar ya samu ya lallasheta, ranar ne kuma aka maida case dinta wajen wani babban likitan kwakwalwa saboda sai a ranar suka gane abinda yake damunta ciwo ne da yake da alaka da kwakwalwarta
"Maryamm bata ganeni ba Hajja, bata sanni ba tace"
Haris yake fadi cikin tashin hankalin da yake ciki yasa Hajja ta riko hannunshi
"Ba kai kadai bane bata gane ba Haris, baka ga harda ni ba"
Sai ya girgiza mata kai, kukan daya kwana biyu yana nema ya taho masa, hawaye wasu na ture wasu
"Haka tace waye ni Hajja, baki ga idanuwanta ba? Bata gane ni ba har idanuwanta sun nuna haka, riketa fa nayi ta tsorata..."
Yake fada cikin fitar hayyaci, gashi ya kasa tsaida hawayenshi, ita kanta Hajjan hawaye taji sun zubo mata, ta sharesu cikin dabara tana sake riko hannun Haris, sai kawai ya zame ya durkushe a wajen, ta tsugunna itama tana masa rikon da uwa zatayiwa danta, kuka yake har jikinshi na amsawa
"Kowa fushi yakeyi dani, muna fadanmu Hajja, mun saba fadanmu mu shirya, Maryamm ce, ta saba yafemun...amman kowa fushi yake dani, nina ja mata ciwon ko?"
Hajja batace komai ba, dan bubbuga bayanshi takeyi kawai, sun dauki kusan mintina ashirin kafin ya samu ya natsu
"Kaje gida kayi wanka Haris, saika kara samu natsuwa ka dawo...tunda kaga sun hana kowa ya kara shiga wajenta"
Ba karamin fama Hajja tayi ba kafin ya yarda ya