Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
duka suka kwashe da dariya, Lalaye na zaginshi
"Kaman baku san ba'a cin mutuncin aure a gabana ba ko?"
Shi ko kishiyar mahaifiyarshi da ta basu wahala baya fatan ace ga ranar da mahaifinsu zaiyi mata wani abu na rashin jin dadi, kawai yana da wani rauni ne akan mata, kuma a yanzun a cikin su hudun shine baya bin mata, zai sha komai, amman wannan harkar bata taba burgeshi ba, su Haris dinma inda zasu ji maganarshi da sun daina, ko yau akwai matan da Lalaye ya kira musu shi da Barde, daya daga cikinsu da ta tunkari Haris shi yayi mata wani irin kallo da yasa ta natsu waje daya, kuma da suka fito zai raka Haris din saida yace masa
"Kayi hakuri da matarka ta gida, idan tayi maka kadan ka kara, ka cike hudun tunda kana da halin rike su, amman kayi hakuri da biye-biyen nan Ganja bashi da amfani"
Murmushi Haris yayi
"Wai wa'azi zakayi mun Pac?"
Ya girgiza masa kai
"Ni da Malami ha ya zanyi maka wa'azi, gaskiya na fada maka, in kaga damar dauka kenan"
Haris din yayi gajeriyar dariya kawai, sukayi sallama tunda sunce masa washegari zasuje su gaisa da amarya, kuma ya amsa musu. Ba zakace Haris mutum bane da baya magana, inka kalle shi sai kayi zaton zaiyi miskilanci, yana da wahalar sabo, sannan bashi da saurin sakewa da mutane, amman yana magana, yana hira sosai da sosai. Sannan abubuwan da suke boyewa juna shi da abokanshi ba masu yawa bane ba, tunda su duka sunsan a shekarun baya bashi da wata kyakkyawar fahimta da Alhaji Mustafa, sai dai banda 2Pac din babu wanda yasan yana tare da Aise
"Ba abu bane na sauri Pac, ina sonta, tana sona, banajin son zaije ko ina, so zamubi a hankali ne, tunda duk muna da inda muke da burin kaiwa kafin muyi tunanin wani aure..."
Kuma yana da yakinin 2Pac ba zai taba zancen da wani ba, shi mutum ne mai matukar sirri, shisa Haris zai iya cewa abotar da take tsakaninsu tafi ta sauran, saboda yana iya maganar da yake kasawa da su Barde da 2Pac, ya fada masa Alhaji Mustafa ya karba masa auren Maryama, kafin yace wani abu ya dora da
"Bana son yin maganar, ya daura auren, na karba, iya abinda na sani kenan"
2Pac saiya sauya akalar hirar tasu a ranar daya gaya masa din, kuma bai sake tayar masa da zancen ba, yasan in bashi da kanshi ya sameshi ba, haka zasu cigaba kamar bai fada masa ba. Tunanin shi yanda zai gayawa Maryama cewa abokanshi zasu zo su gaisa da ita, tunanin da ya dingayi kenan da yake tuki, har ya karasa gidan, ya sameta zaune a falo tana kallon wani Indian, da yake DStv yasa aka saka mata, duk sanda zai ga tana kallo India ne, idan ma ta taba canzawa zuwa wata tashar shi dai baigani ba
"Nagode sosai sosai, naga DStv aka sakamun, zan cigaba da kallon films dina"
Haka tace masa ranar hakoranta a waje, dan zai rantse har turamenta saida suka bayyana, kuma yanzun daya shigo gidan in dai zata ganshi sai tace masa
"Sannu da zuwa..."
Ko ta gaishe dashi, jiya ma daya dawo da daddare data gaishe shi kafin ya amsa ta dora da
"Farfesun nama nayi, na hada da shayi, yayi dadi shine na rage maka tunda naga kaima kayi mun kirki... harda biredi na ajiye maka, amman na kusan cinye biredin fa saura guda uku...kanaci dashi ko in cinye kayana?"
Ya girgiza mata kai, shi kuwa me zaiyi da biredi yanka uku? Taso ma ta bashi dariya
"Na koshi duka...ki dai bani shayin"
Ta mike da saurinta
"Insa maka madara sosai?"
Ya daga mata kai
"Kisa komai sosai banda sugar, shi kadan"
Har ta kusan kofar kitchen din ta juyo
"Da yawa shayin?"
Kai ya sake daga mata. Ta hado masa, kuma baisan dame-dame ta saka ba, yanata kamshin daya wuce ace na madara da milo ne kawai, yayi masa dadi sosai, sai gashi kofin da ta kusan cikawa yake tunanin inda zai kaishi ya shanye duka. Yau ma ya ce mata
"A bani shayi, irin na jiya"
Data tashi ta shiga kitchen din, saita hada masa harda cin-cin din kayan gararta a wani dan karamin bowl, ta tsaya ta kwankwasa masa kofa, ta dauka zaice bayacin cin-cin din saiya karba duka yace mata
"Nagode"
Ya mayar da kofar ya rufe, zataso ta shiga dakinshi, taga yanda yake duka, bawai iya inda idanuwanta suka hango mata jiya da yau ba, wannan laptops din nashi da wasu abubuwa da ta gani baje kan gadon dakin take so ta ga menene, ta kuma tambayeshi duk abinda bata gane ba. Amman zatace masa ya bar mata mukulli ta share masa dakin wata rana, sai ta karayi masa kirki tukunna dan kar yayi zaton wani abu. Ba karamin dadin DStv din nan tayi ba, kuma tasan Haris dinne ya fadawa maigadi da an dauke wuta a kunna generator, saboda haka kallo saita gaji, babu maice mata ta tashi, babu zuwa makarantar boko balle ta Islamiyya, abincinta inta dafa sau daya har dare, ta rage kadaicin nan, in sukayi waya da Khairi ta dinga bata labarin wani film data gani kenan. Da dai tace mata
"Ke ba zakiyi girki ba kika zauna kallo ko? Saiya dawo baki gama abinci ba"
Shine ta amsata da
"Abinci na nakeyi ni kadai fa, da nace in dafa indomie dashi rannan haka yace baya cin jagwalgwalo"
Khairi tace mata
"In dai kin dafa ki dingayi masa tayi, ko ba zaici ba, kiyi masa tayi Maryama, wata rana sai kiga yace ki zuba masa, hakane zai gane ba jagwalgwalo bane, kinga babu dadi ace mutum yayi cefane kuma ba za'ayi girki dashi ba"
Cikin kare kai Maryama take fadin
"Nifa ban hanashi ba nace miki Adda, shine yace ba zaici ba daman"
Kuma shawarar Khairin ta dauka takeyi masa tayi, sai gashi taji dadi daya karbi shayin jiya, yau ya nema da kanshi, ya kuma karbi cin-cin din bai gwasaleta ba. Ta koma ta kwanta akan doguwar kujera tana cigaba da kallonta. Haris kuma shayin yasha, ya dauki cin-cin din daya ya gutsira, sai yayi masa dadi, duk ranar shine abu na farko mai kama da abinci da ya saka a cikin nashi, ko da su Barde suka tsaya siyayyar abubuwan da zasuci dazun ba'a siya dashi ba tunda sunsan hali, kuma duk tarin lemukan nan ruwa yasa hannu ya dauka ya bude ya sha rabi. Yana gama shanye shayin yaji gajiya ta saukar masa, jikinshi duk ya mutu. Aise ta fado masa a rai
"Ya jikinka ba zai mutu ba in kaci abinci bayan ka wuni da yunwa? Yanda ciwo baya kamaka ma abin mamaki ne"
Dariya yayi a wancen lokacin, yanzun kuma yayi murmushi yana jin kewarta kamar ace tana gabanshi, ganin tunani zaiyi masa yawa yasa ya mike yana fitowa da kofin da dan bowl din zuwa kitchen, ya riga ya saba in yayi amfani da kofi haka saiya wanke yake ajiyewa, yanzun ma abinda yayi kenan tukunna ya fito falon ya sameta a kwance tana kallo
"In karo maka shayin ne?"
Ta tambaya data ga ya tsaya jikin kujerar da take kwance akai ta baya
"Ya isheni, Nagode"
Ta jinjina kai
"Abokaina zasu zo ku gaisa gobe...."
Ita ta karasa masa da
"Idan Allaah Ya kaimu"
Dan tanajin wani iri duk lokacin da zataji wani yace, anjima zanyi kaza, gobe zanyi kaza, batare da ya hada da idan Allaah Ya bashi iko koma Ya nuna masa lokacin ba, sai ta dingajin kamar ya aikata babban sabo, kamar rashin fadar zaisa yaki ganin goben, abin da zaiyi din yaki yiwuwa ko da yaga goben ma tunda ai komai na Allaah Ne.
"Me za'a dafa musu? Su nawa ne?"
Haris ya dan tattare girarshi duk biyun, yana tunanin abinci kuma?
"Zaku gaisa ne kawai"
Ta tashi zaune tana kallonshi
"A'a fa anayin girki, ko Adda Maimunatu ma da akayi bikinta sanda abokan mijinta zasu zo mune mukaje muka tayata aiki ta dafa musu abinci"
Ya girgiza mata kai
"Ba abinda za'a dafa fa, zasu sha ruwa da lemo su tafi in kun gaisa"
Itama abin bai zauna mata ba, dan yana ganin gardamar da take so tayi masa
"Maryamm"
Ya kira da wani yanayi da yasa kalamanta bacewa
"Ba abinda za'a dafa, ke ina zaki iya wani girki, ki basu ruwa da lemo. Akwai cin-cin din da kika bani dazun?"
Ta daga masa kai
"Tam ki basu dashi, shikenan ya isa"
Kafin tace wani abu kuma ya wuce ya koma dakinshi, amman dai tasan anayin girki, haka ma ake cewa za'aje gidan amarya aci taliyar amarya. Sai ita zaice ba zata dafa komai ba, ta kuwa yiwa Khairi text tana fada mata
"Saiki hada musu harda dublan dasu alkakin ki basu lemon da ruwa kamar yanda yace, idan basu ci bama in zasu tafi kiyi masa magana a zuba musu a ledoji su tafi dashi, in kina da kaza kiyi peppering irin yanda Abba yake so din nan, wanda Hajja ta koya mana sai kawai ki hada musu dashi"
Sai lokacin taji ta dan samu natsuwa, kamar taje ta kwankwasa masa daki ta tambayeshi su nawa ne, sai kawai ta kyale shi. Jin idanuwanta sun fara yaji yasa ta hakura da kallon ta kashe komai taje ta kwanta. Washegari kuwa tun wajen karfe tara ta kara share ko ina, ta dauko gawayinta ta kunna ta saka turaren wutarta a ko ina na gidan, tama manta dashi, amman da yake mai kyaune tun wanda aka turara gidan kana jin alamar kamshin nashi har lokacin, sai taji ko ina yayi mata dadi sosai. Lallai shisa Adda Zahra ta nacewa wannan Meens Incense din (08036387204).
Da yake bata zauna kallo ba, kuma farar shinkafa ta dafa wadda zataci, zuwa azahar ta gama komai, tayi wanke-wanke, kaji biyu ne tayi amfani dasu. Ta zuba abincinta taci ta koshi, ta riga tayi wanka, kuma ruwa dai ba wani shiri takeyi dashi ba, in ba tsananin zafi akeyi ba, ko ta kwaso gajiyar da takeji har kasusuwanta, wanka biyu sai dai taga su Khairi na wannan fi'ilin yanda take kiranshi. Ita ko Novel take karantawa taga ance wai matar tayi wanka kafin miji ya fita aiki, ta cancada kwalliya sai kawai ta sheke da dariya, dan bata hango kanta a wannan lamarin ba, to dame zataji, tsakanin share-sharen gidan da akace tayi da girki kala biyar duk kafin mijin ya fita, sannan kafin ya dawo ta sakeyin wasu girke-girken, wani wankan da wata kwalliyar.
Kenan ba zatayi baccin rana ba? Ba zatayi komai da rayuwarta ba, yaushe zatayi kallo duk ta gama barbadewa tsakanin kitchen da bandaki. Inda ma taga ina aka zuba mata abayoyinta da ita zata saka, sai kawai ta samu riga da skirt na lace marar nauyi tasa, harta fito da mayafi saita fasa ta dauko hijabi ta ajiye a hannun kujera, kafin ma ayi la'asar ta cire dankwalin data kima, dan ya isheta, tanayin sallah kuma saita daura shi simple ta ajiye hijabin tana sauraren ta inda su Haris din zasu bullo, da zai fita yace mata da yamma zasu zo. Ta dauka da anyi la'asar zata gansu.
Amman basu shigo gidan ba sai wajen biyar da wani abu, haka suka gaisa a mutunce, sunayi mata Allaah Yasa alkhairi, sai taji kunya ta kamata, ta kasa daga kanta, ta mike kawai tayi hanyar kitchen
"Shege ashe 'yar jinjira ka aura, wannan yarinyar ma ta wuce sha biyar?"
Lalaye ya fada yana wata dariya, kawai wannan maganar tasa wani abu ya tsirgawa Haris, kallo Lalaye ya karewa Maryaman kenan? To akan me? Kafin yayi magana 2Pac ya rigashi da furta
"Lalaye..."
Saiya daga hannyenshi biyu alamar surrender
"Nayi shiru Pac...kafin ka sakani a gaba"
Sai Haris din ya mike yana rufawa Maryama baya, ya sameta tanata kiciniya da kwanuka da fillatai, yabi siraran hannayenta da kallo, idanuwanshi suka dira kan yatsunta da ke da alamar jan lalle har lokacin, sauran lallenta na biki, babu a jikin faratanta da suke farare qal kamar bata da wadataccen jini, yatsun nata suma sirara ne, amman dogaye, sai sukayi masa kyau, sai yaji yana auna laushinsu a idanuwanshi, yanda basu da tsokar nan ko inya rike zaiji alamar kasusuwanta jiki? Yanda ta daga wata kula yaga kamar sun lauye yasa shi karasawa da sauri ya karba
"Saikin karya wannan hannuwan naki hankalinki zai kwanta"
Ya bata dariya
"Na fada maka ina da karfi fa, Allaah kuwa, kaki yadda ne kawai"
Ya tabe bakinshi
"Ki tsaya anan inzo in dauki sauran"
Kuma gudun kar tayi masa gardama yanda tayi randa suka dawo daga siyayya yasa yace mata
"Ki tsaya anan"
Cikin umarnin da ta tsinci kanta da daga masa kai, tsayuwae tayi, shi yazo ya karasa kwashe duk abubuwan data hada
"Ki koma daki abinki tunda kun gaisa"
Ta sake daga masa kai
"In basu cinye ba ka juye musu su tafi dashi dan Allaah, ga ledojin dana fito dasu nan"
Ya dan kalleta, da yake an zuba mata irin ledojin nan da zaka iya sakawa mutum kayan gara, wai ko da zata ba wani, to tunanin yanda zatayi da wannan bokatan ma takeyi, tunda ita dai ba kawaye ne da ita da zasu zo ba, shima kuma sai yau ya kawo abokanshi, amman zatayi masa magana taji ko akwai wanda yake so yaba, kuma zata dibarwa mai gadi da yawa in yana da iyalai sai ya kai musu.
"Kaji, kafa juye musu komai...kaji"
Ya daga mata kai kawai, dan bayaso ta koma falon nan Lalaye ya kara ganinta. Sanda dai shiya koma duk sun sauko kasa suna cin dublan din, ga kular daya kinkimo an bude, nama ne yake ta tashin kamshi, dan shi Barde da yake abinda yake sone naman yake ci
"Wallahi naman nan yayi dadi sosai"
Yake fadi yana dorawa da
"Anya ba zanyi auren nan ba in dai za'a dinga mun irin wannan? Ko zaka tambayar mun Madam in akwai kanwarta da ba'ayi wa miji ba"
Sukayi dariya su duka, Lalaye yace
"Kanwarta fa kace? Amman Barde tabbas rashin imaninka ya shahara, irinku ne kuke shan kunun marar lafiya...kanwar wannan ai ko wanka ba'a daina yi mata ba"
Barde ya harareshi
"Ina ruwanka, kaine zakayi mun hanya ko Ganja?"
Haris kai kawai ya girgiza, duk maganganun da sukeyi bai tanka musu ba, da yaji zasu ishe shine ma yayi zagi. Sun gama ci, 2Pac yace su tashi ana kiran sallah
"Ka kira Madam muyi mata sallama..."
Kamar ba zai kirata din ba, amman ganin 2Pac ne yayi maganar sai yaje ya kwankwasawa Maryama kofa yace tazo suyi sallama data fito, ta sake dauko hijabinta, sunata yi mata godiya
"Komai yayi dadi"
Ta kalli Haris ganin ko rabin abubuwan basuci ba
"Bari in kawo ledoji a juye musu"
Bata tsaya yace wani abu ba ta juya, saida ta karasu dublan din a ledojin tukunna ta fito, Haris ya karba ya juye sauran, ya karbi wata roba mai kyau data bashi tace ya juye musu naman a ciki, tana da murfi
"Ganja wato so kayi kai mana bakin hali, ashe gara da Madam ta fito, mikomun naman in rike"
Cewar Barde
"Ganja"
Maryama ta maimaita a cikin kanta tana kallon Haris da baisan ya akayi shima ya kalleta ba, kuma wani abu ya gaya masa tunda taji sunan sai tayi magana, a karo na farko kuma yaji cewa zata bashi dalilin da zai kama wannan siraran yatsun nata ya lankwasa yaji sautin karar da zasuyi, dan tun dazun sukeyi masa yawo a kai, in hannun Aise na cikin nashi haka zai ta lankwasa yatsun yanaji suna qaras-qaras, sai ta kai masa duka tukunna, so yake yaji bambancin wannan sautin, shisa ya fita raka su Barde da fata daya a ranshi, tsautsayi ya aiki Maryama ta kirashi da
"Ganja..."
19
Gidan bai taba yi mata girma ba duba da irin wanda ta taso cikin shi, amman duk girman gidansu ba'a taba rabashi da mutane, bayan su 'yan gidan kusan ko yaushe cikin baki suke, kuma kaso mai yawa na bakin nan kwana sukeyi. Shisa bata san ko tana tsoron zama waje ita kadai ba ko akasin hakan. Haris ba wuni yakeyi ba, sai sa'a suke haduwa sau daya a rana, danma yanzun ya mayar dashi dabi'a yasa ta bashi shayi kullum, ranar da abokanshi suka zo, bayan ya rakasu ya dawo. Washegari kuma daya fita da yamma ya shigo gidan, tana kitchen ma dan tashi tayi tana marmarin tuwo amman ta dinga mirgina akan kafet din falonta sai bayan tayi sallar la'asar tukunna ta shiga kitchen din, taga harda shinkafar tuwo a cikin kayan gararta, sannan tana da busashiyar kubewa ma dasu kuka da aka zuba mata a wasu containers.
Cikin nishadi take aikinta, tana kuma karanta Surah An Naml cikin Qira'ar Qaari Bilal Darbali, dan yana daga cikin mutanen da take matukar son karatunsu, musamman mashi, wata mp3 ce da Yayanta Ahmad ya bar mata, haka taje ta kafa masa naci saida yasan yanda ya samo mata karatun shi ya saka mata a mp3 din nan, ruwa ta subuce ta fada, har hawaye tayi lokacin saboda takaicin da taji. Duk yanda ake fada mata irin muryar da take da ita in tana karanta Al-Qur'ani bata taba yarda ba sai da Adda Maimuna tayi recording dinta batare data sani ba, ta wuni tana farin ciki, tana fatan ace wata rana ta samu damar recording muryarta, ta dinga kunnawa yara sunaji, kar girma ya kwace mata dadin muryar.
Tun da ya shigo daga falon yaji muryarta, wani abu ya tsirga masa, in ba randa yaje masallaci ba, ba zaice ga ranar karshe daya kunna karatun Qur'ani ya saurara ba, koma shi ya bude ya karanta. Daya matsa kusa da kitchen din kuwa zai rantse har yanayin numfashin shi saida yaji ya canza, kafafuwanshi kamar rawa sukeyi, tsikar jikinshi sai tashi takeyi, anya akwai abinda ya taba saurara da yaji ya ratsa har ruhinshi? Ita kuma Maryama ji tayi kamar ana kallonta, saita juyo, ta ganshi tsaye
"La tua voce e musica per le mia orecchie..."
Ya furta da yaren Italian cikin wata murya kamar yana jin bacci, ta jishi, duk wata kalma da yanda ya lankwasa harshen shi wajen furtawa
"Yare kayi ko? Wanne yare ne?"
Kowanne irin yare ne yayi mata dadi, ko tace yanda yayi shi yayi mata dadi
"Me kace?"
Ta sake tambaya, sai yayi gajeran murmushi, shima maganar ce kawai yaji ta subuce masa, amman ta ina zai fassara mata? Ya za'ayi ya gaya mata haka yace muryarta tayi kama da kida mai dadi cikin kunnuwanshi? Ko sauti ne ma, ko waka zaice, kamar ba kowacce kalma bace inka fadeta da wani yare zaka iya fassarata da wani yaren kaji fassarar