Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
bashi abubuwa, watakila sai nan gaba kadan idan ya samu kudinshi zai fara yi mata irin wannan siye-siyen, harma ya bude bakinshi yace mata
"Maryam ina sonki"
Ta karayin wani murmushin mai cike da nishadi, aikuwa da kowa bai huta ba, da tayi kawaye masu tarin yawa dan suzo wajen bikinta suga irin mijin da zata aura, ta karayin wani murmushin kawai. Kuma kamar Ishaq ya hangi zuciyar Maryam a wannan ranar, daya sake zuwa sai gashi da wata babbar leda shakare da kayan marmari, falon nasu a cike yake, amman haka ya karasa ya mikawa Maryam yana fadin
"Kanwata ki cire duka guava din dake ciki taki ce, nason kina sonta saiki basu sauran"
A kasa ta ajiye ledar bayan ta karba saboda wani irin nauyi na musamman da tayi mata, duk wani surutu da akeyiwa Ishaq din baya karasawa kunnenta, saima da Khairi taso karbar ledar ne ta janye, haka ta saka hannu tayi abinda yace cikin sanyin jiki, idanuwan Hajja yasa ta raba guava din nan gida biyu ta ba 'yan gidan rabi, tanajin kamar ta raba wata kulawace da Ishaq din ya wareta ita kadai ya damka mata tare dasu, zuciyarta tayi mata nauyi matuqa, data kwashi sauran sai tayi daki, bata ma ko tuna ya kamata ace ta wanke ba, ta daga guda daya takai bakinta ta gutsira, irin manyan nan ce koraye da ba zakayi tunanin zasuyi zaki ba, idan ma babu zakin Maryam bataci ba
Asalima tunda take bata tabacin guava da tayi mata dadin wannan ba
Ishaq ne ya kawo mata, da tunaninta ya siya
Akwai wani zaki da take bukata bayan na kulawarshi?
7
Kaso mafi yawa na iyaye, tun kafin amsa sunan suke da tarin burika akan yaransu, a cikin wadannan burikan bai wuce ace a taron yara dubunnai nasu su kasance sune taurarin da haskensu zai dishe na kowa. Musamman uwa da in tayi aure, sai aka wayi gari tasan da shigar ciki a jikinta, duka rayuwarta take tsaya, a wannan lokacin ko faduwa tazo yi ko wani abu na cutarwa ya tunkarota, zuciyarta zata fara sanar da kwakwalwarta, abu na farko da zata farayi shine kare cikinta da hannayenta, cike da fatan koma menene ya tsaya akanta ita kadai, karya taba abinda yake cikinta, sanda zai fito duniya kuma saiya zama kamar bata taba wata rayuwa kafin zama uwa ba.
Idan ma ta zauna tana tunanin rayuwarta kafin ta haihuwa, takanji kamar wani lokaci ne mai tsayi, wani lokaci daya shude yake neman bacewa har a cikin tunaninta. A wajen iyaye irin Hajiya Rumana, wanda suka samu haihuwar a lokacin da suka fara karaya, suka fara hangen zasu mutu batare da dacewa da irin wannan rabon ba, ba iya rayuwarsu suke mikawa yaransu ba, da yawansu harda wani kaso na ruhinsu, ita dai wannan kason ne yafi yawa akan Haris, Munira tayi aurenta, tasan ko da yaushe Anisa ma ko da yaushe miji yazo aurenta zatayi, ana cewa 'ya'ya mata sune na iyayensu har abada, ita batajin haka.
Da wayonta ta rasa iyayenta, kuma ko suna da rai, a halin yanzun, a yanda takeji ita din ta iyalanta ce, mijinta da yaranta, ko da iyayenta na da rai kyautatawa ce a tsakaninsu da ziyara lokaci zuwa lokaci, mata ai rayuwarsu tare da iyaye tana farawa ne daga haihuwa, ta kuma kare daga ranar da aka damkawa mijinsu, suna kara nisanta da wata rayuwa ne duk rana, balle idan sun fara tara yara, to a tsakanin hidimar yara data miji sun nemi kansu sun rasa, ita tanajin babu ma wani abu da yayi saura, me ake tsammanin zata ba wani? Ai a wajen Hajiya Rumana, a kuma tunaninta, Haris shine nata, shine nata har abada, ko aure yayi matarshi ta haihu yaranshi sune zata bugi kirji tayi iko dasu batare da wani ya daga mata hankali akan hakan ba.
Shisa take da tarin burika akan Haris din, ita kadai idan ta zauna sai ta dinga tsare-tsare akan yanda take fatan bikinshi zai kasance, shagulgulan da zatayi, yanda zata tayashi zabin gidan da zai zauna, a yanda tasan Haris ma da son da yakeyi mata, idan ta nemi su zauna a Kaduna, kusa da ita ba zaiyi mata musu ba
"Anya Mami?"
Shine abinda yakan fadi idan ta nemi yayi wani abin da bayaso
"Haka nake so ayi Haris, ko ba zan samu ba?"
Wannan maganar, kalmomi goma kacal, wata rana sai yayi mata murmushi ya kada kai kawai, wata rana kuma fuskarshi babu walwala zaice
"To Mami"
Amman dai ko da bayaso, ko da yayi mata musu, karshe abinda take so dinne zaiyi. To haka zatayi masa magana akan zaman Kaduna, idan ma aikinshi wani gari ne ko wata kasa, iyalin ya bar matasu anan Kaduna shi saiya dinga zuwa, ikon da ya kwace mata akan Munira da wanda tasan zai kwace mata akan Anisa ko wanne lokaci, batayi wani yunkuri akai bane saboda tasan tana da Haris, zatayi yanda take so akan Haris. Wani abu da yake kara sanyaya mata zuciya shine kusancin da take gani tsakanin Alhaji Mustafa da Haris, shisa lokacin da yake fada mata Mukhtar zai tafi Madina sai ma tayi murmushi tana fadin
"Ma Shaa Allaah, abin ya tabbata kenan, Allaah Yasa albarka, yaushe zai tafi?"
A karo na farko a rayuwarta, da yayi mata tayin rakiyar Mukhtar din bataki ba, kuma bata damu da yanda zuwan nata yasa Fadime da yaranta duk suka sha jinin jikinsu ba, kamar ta takurasu, kamar ta tare musu wani kaso na walwalar da ya kamata ace sunayi, murmushi ma tayi, to aiko Fadimen ma tun da aka aurota take kiyayarta balle kuma yaranta da suka taso da tsoronta fal ransu, tunda ita tazo ta aure mata miji rana daya. Ita kam yanzun duniyar dadinta takeji, abunuwan da suke damunta kuma basu da wani yawa, watakila shisa ma kwanakin dake ta hadewa suna tashin wata, zuwa shekaru ba suyi mata wani tsayi na azo a gani ba.
Musamman da a cikin shekarun ta mika Anisa dakin mijinta, taso ace itama ta auri dan uwa kamar yanda Munira tayi, tunda akwai da yawa da suka nuna suna sonta daga bangaren Hajiya Rumanan, a wannan gabar ma har dan Kanwar Alhaji Mustafa da ya nuna yana so, inda Anisa ta maida hankali ba zataki ba, tunda yaron yana tashen kudi sosai, Anisa tayi tsalle ta dire kan cewa bata son auren zumunci, wanda sukayi Allaah Ya kara musu zaman lafiya, wanda suke shirin yi ma Allaah Yasa albarka, ita dai in ba kaddara ba, bata taba hango kanta a cikinshi ba, haka kawai baya burgeta. Bata kuma yin ba, Abuja aka kaita. Haris ne ya roki a saita bikin lokacin da zaiyi hutu saboda yana so yazo, yanda yaga album din bikin hoton Munira babu shi a ciki abin baiyi masa dadi ba.
Yazo din, shi ya kama hannun Anisa a wajen dinner dinta yana shigar da ita ciki, yaje ya zaunar da ita kusa da angonta. Yaji dadin zuwan, yaji dadin bikin. Shisa ma da Hajiya Rumana tace masa
"Allaah Ya nuna mun naka haka Haris..."
Yayi dariya mai cike da nishadi
"Allaah Yasa karka kwaso mana ta waje irin yanda Anisa tayi"
Ya jinjina kanshi
"Ba ta waje bace Mami"
Da sauri ta kalle shi, ya karayin dariya
"Aise ce, Aisen Uncle Modu"
Batasan lokacin data fadada murmushinta ba
"Waye zaice Haris zaiyi hankali haka? Kinsan maganar business mukayi jiya? Duk da ma mun kwana biyu da yayi mun maganar, amman yanzun yana cemun ya fara tsara business plan dinshi, Haris fa, da nace masa akwai kudin da nake ware masa tunda yayi mun maganar kinsan me yace mun?"
Alhaji Mustafa ya fadi cike da wani alfahari a muryarshi, kafin ma ta amsa ya cigaba da magana
"Shekarar karshe nake yanzun Abba, akwai ayyukan da nayi applying, idan na samu kudin babu laifi, ciki nake so inyi tarin shekara biyu inga idan zasu fara siyamun manyan motoci daya ko biyu, ko babba da kananu, inaso in fara daga wani waje, kamar yanda ka bani labarin yanda ka fara naka, ina so in fara da kudina ko da zaka bani wani abu inaso ya zamana a gaba ne, idan na kafu, sai mu zauna muyi magana..."
Ai ita duk wannan labaran na yanda Haris yayi hankali bataji dadinsu ba ashe, bata maga hankalin ba sai yanzun daya nuna mata shi, a cikin 'yan uwanta kaf, shakuwar da take tsakaninsu da Modu lokacin da suke tasowa ba 'yar karama bace ba, barin kasar da yayi da auren da tayi itama shine abinda ya fara disashe wannan shakuwar, amman yanzun, Haris zai dawo da ita sabuwa
"Aise fa Haris"
Ta fadi farin ciki fal muryarta, da kuma wani alfahari da ta kasa boyewa
"In Shaa Allaah Mami, itama tana makaranta ne yanzun, sanda dai zan zama stable sai ayi maganar komai In Shaa Allaah..."
Da saurinta tace
"Wanne stability kake magana? Kufa sai kun dauko abin hankali saiku rushe shi, ai ba wani wasa ko shiriritarku za'a biyewa ba, da wuri ya kamata manya su shiga maganar"
A lokacin zumudinta ma dariya ya bawa Haris, kafin ya koma sai da ta karbi lambar Binta a wajenshi, haka ta kirata suka gaisa bayan Haris din ya tafi, sai dai taji wata kunya da batasan daga inda ta taso mata ba, duka gani nawa tayiwa matar ta yanke hukuncin batayi mata ba, taso tun a wayar tasu ta farko ta kwaso mata maganar Haris da Aise, amman saita kasa, zata bari su kara gaggaisawa, watakila ma ita Bintar ta fara yi mata. Kuma kamar yanda Hajiya Rumana tasan da maganar, ko ace Haris ya fada mata, haka ya kasance a wajen Binta.
Ita Binta ranar da ta sani, tana kitchen ne, sai take juyo dariyar Aise din da tazo daga makaranta, tunda itama kamar Haris, tata makarantar tafiyar awanni biyar ce da inda iyayen nata suke, da tayi niyyar barin Italy ne, tana yawan maganar, rana daya kuma ta canza shawara, babu wanda yasan cewa tazara ce batason ta kara samarwa tsakaninta da Haris shisa ta zabi kusa da gida. A wayar, Binta taji kalamai da yawa da suke alamta soyayya, shisa ta tambayi Aise kai tsaye, batare data musa ba ta tabbatar mata, tunda ma basu saba irin wannan boye-boyen da iyayensu ba, a wajensu ba wani abu bane na tashin hankali dan wani ya burgeta ma tazo tana labarin da Binta, da mahaifinta ma hirar samari takeyi hankali a kwance.
"Ban fada miki bane ba saboda ba sauri mukeyi ba Mamma, inaji a jikina na samu miji ne, shisa, ba abin sauri bane ba"
Binta ta fahimta, duk wani bayani da Aise tayi mata, kuma har ranta, a lokacin bataji cewar tana da wata matsala da hadin Aise din da Haris ba, tana sonshi, kuma a lokacin ne ta kula da yanda in dai Haris yazo, idanuwanshi na kan duk wani motsi na Aise, cike da tarin kulawa da wani taushi cikin idanuwan nashi da ya kwantawa Binta a rai, Haris na son 'yarta, irin soyayyar nan mai wahalar samu. Ko da sukayi waya da Mu'adh yake kara jaddada mata maganar da tun wancen zuwan nashi har yau ya kasa natsuwa da ita, wato Haris, sai tayi dariya tana gaya masa ya kwantar da hankalinshi, Haris na son Aise ne, itama kuma tana sonshi, idan har komai ya tafar musu yanda suka tsara ma aure zasuyi.
Shirun da Mu'adh yayi daga bangarenshi sai da tayi tunanin ko kiran ya katse ne, data duba taga yana tafiya ta sake masa magana
"Inaji Mamma..."
Ya furta cikin karamar murya, duk wani labarin Aise da Haris data bashi haka yace mata
"To"
Yana ma yi mata sallama da uzurin cewa ana masa magana zai sake kiranta. Kuma tun daga ranar bai kara yi mata zancen Haris ba, sai tayi tunanin ya fahimta ne, ya gane abinda itama ta gane, Haris ba zai taba cutar da Aise ba tunda soyayya ce a tsakaninsu ba wani abu ba. Wata goma akayi a tsakani kafin Mu'adh ya diro kasar Italy, kuma kwana daya da zuwanshi, ya fita, ya dawo da wata envelope a babba a hannunshi, envelope din daya ajiye a gaban Binta, idanuwanshi a cikin nata yace
"Bana son Haris Mamma, bana son Haris da Aise, tun kafin in samu dalili baiyi mun ba..."
Ko da ta dauki envelope din ta bude, hotuna ne masu yawan gaske, hotunan da a tashin farko ta rasa ma me take kallo, Haris cikin abokai, Haris cikin mata, Haris a club, Haris rike da mata kala-kala, Haris a tsaye da wani abu mai kama da sigari a hannunshi, hotuna ne sun kai guda dari
"Haris na shan wiwi, Haris na bin mata, Haris baiyi kama da mijin da nakewa Aise mafarki ba, ba anan ya fara ba, tun a can Nigeria, nasan ba zan iya hana Aise abinda take so tayi da rayuwarta ba, amman a matsayina ma dan uwanta, nayi abinda nake tunanin zan iya, na fara fada miki gaskiya, itama kuma zan fada mata, abinda zatayi da gaskiyar zabinta ne"
Ita shan wiwin ma bai wani dameta ba, aiko sanda ta auri Modu yana shan sigari, yana ta cewa zai bari, bai daina ba sai ranar data haifi Khamis, ranar, a asibitin yace mata ba zai kara ba, saboda lafiyarshi, saboda a ranar yaji yana da bukatar wannan lafiyar iya tsayin shekarun da Allaah Ya kadarta masa. Kuma har yau, shekaru ashirin da tara, Alhaji Modu bai sake kunna sigari ba, tasan idan har Haris yaso ya daina shan wiwi, zai bari, ai itama kamar sigari din ce a tunanin Binta. Amman mata? Wannan cuta ce da taga maza da yawa na fama da ita, neman mata cuta ce data ruguza aure da yawa har anan kasar Italy, tayi sanadin broken homes da batasan adadinsu ba, kuma yana daga cikin abinda yake bawa Binta tsoro.
Abinda har a sallarta in zatayi addu'a saita roki Allaah Ya kara mata mijinta da yaranta da duk wani da zai rabesu daga fadawa cutar neman mata. Sai kuma ta dauki 'yarta kwara daya tilo ta mikawa Haris bayan tasan abinda yakeyi? Haka ta wuni zaune batare da tasan takaimaiman abinda takeji ba. Sai dai kafin ta tashi abu daya ta sani
In dai tana numfashi, in dai karfi irin na uwa zai iya tasiri akan 'yarta, to ba zata taba barin Aise ta auri Haris ba...
Yanda Mu'adh ya fadawa Binta, haka ya kara daukar dayar envelope din ya samu Aise har cikin dakinta ya mika mata guda daya
"Kiyi hakuri, shine kawai abinda zan iya miki a matsayina na dan uwanki...kome zakiyi dashi, kome kika zaba, kowanne hukunci kika yanke, ina tare dake, kinaji?"
Ta kalle shi idanuwanta cike da tsoro
"Ina tare dake, kome zaki yanke"
Kai kawai ta daga masa batare da ta iya cewa komai ba, tunda yace mata yana so suyi magana taji gabanta yana faduwa, take ta jan kafa kuma, saboda yanayin muryarshi tasan ko meye zasu tattauna abune mai muhimmanci, sannan haka kawai zuciyarta ta dinga gaya mata abune daya shafeta, sai gashi yanzun yazo ya tabbatar mata da cewa da gaske maganar ta shafeta, wacce gaskiya? Hannunta har rawa yakeyi lokacin data zazzage abinda yake cikin envelope din nan, sai zuciyarta ta taya hannuwan nata data fara duba hotunan nan, daya bayan daya, kowanne yana samun wajen daya zauna a tare da ita
Haris ne,
Haris dinta...
Fuskarshi ce, shigarshi ce daya saba, shigar da bakaken kaya sunfi yawa a cikinta, kalolin kayanshi da ta taba gani gabaki daya basu wuce guda hudu ba, baki, ruwan toka mai cizawa, koraye masu cizawa, sai ruwan kasa da batasan ma ko zata kirasu da wannan sunan ba saboda da duhunsu
"Me yasa baka son kaya masu haske?"
Ta taba tambayarshi, da mamaki ya kalleta
"Masu haske?"
Ya maimaita kamar bai gama fahimta ba
"Farare, ja, kala mai haske, ba baki ba, ko irin wannan na jikinka"
Sai yayi yar karamar dariya
"Inji wa? Ina sakawa mana, ko yanzun singlet dina fara ce, ko in daga rigata kigani?"
Itama dariyar tayi
"Baka amsa mun tambayar da nayi bafa, me yasa?"
Saiya numfasa
"Nima ban sani ba, watakila na jima inajin kamar babu mai ganina ne, sai wani sashi tare dani yake son kara boyewa, in zama iri daya da inuwata, sai ka matso kusa, sai kasa hankali zaka ganni"
Batajin ta gane inda kalamanshi suka dosa a lokacin, batama san me yasa wannan hirar ta dawo mata yanzun ba, tunda ai bata da alaka da tarin matan da suke tare dashi a hotunan nan, ko suna dashi? Ita Haris din data sani kama kawai yakeyi da wannan, Haris din data sani bata taba jin warin hayaki a jikinshi ba, kuma ai ta rungumeshi har in za'ace ta lissafa zata bace lissafi, duk matan nan, inda hannuwan Haris suke a jikin wasu ko da wasa basu taba kaiwa a nata jikin ba, Haris ne zata nanike masa, cikin dariya zai rabata da jikinshi yana fada mata
"Boundaries Aise, ba zaki so ki kunnamun abinda baki san kokawar da nakeyi don kashe shi a gabanki ba..."
Haris fa...
Haka Mu'adh yace kome zatayi da wannan gaskiyar yana tare da ita, data kai hannu ta share hawayen da babu komai a cikinsu sai wani irin kishi mai rufe idanuwa, sai soyayyar da take tabbatar da girmanta a yau, hukuncin da ta yanke shine
Tana son Haris
Zata cigaba da son Haris
Zata so shi har sai sonta yasa ya rike hannunta ya saki na kowacce mace...yanda take jinta ta Haris, to zata tabbatar da Haris ya kasance nata ita kadai...
8
HARIS
Tun tasowarshi, a labarai kawai yake jin menene rashi, kalmar a nesa ko kusa bata taba shafarshi ba, tunda sau nawa ma ya taba tunkarar Alhaji Mustafa da wata bukata tashi ballantana yace masa a'a? Watakila da yana yaro, lokacin kuruciyar da lokaci ya shafe masa daga kwakwalwarshi, shifa ko mutuwa, da girmanshi dai Kakarshi ce ta rasu, yana ma nan Italy aka kira aka fada masa, ko Alhaji Mustafa a waya yayi masa ta'aziyya, haka shine ya tura masa lambobin duk wadanda ya kamata yayiwa gaisuwa, kuma mutuwar ba shigarshi tayi ba, tunda ba sabawa yayi da ita ba, tun da aka fada masa yayi mata addu'a haka ya cigaba da sabgoginshi na ranar kamar babu abinda ya faru.
In dai yana son abu, to yana sonshi ne da duk zuciyarshi, sannan kuma idan ba zai yiwu ya sameshi a wannan lokacin ba, tabbas zai fara tsare-tsaren yanda zai