Advertisements
Chapter 39 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   39 / 51

114K to 117K   out of 151K words

abinda Allaah Ya halatta ne, yana mun wahalar karba...ya zanyi da na waje? Ba guda daya ba Adda...ko matan da suke auren mazinata zan samu in tambayesu yanda ake suke zaune tare dasu zuciyarsu bata buga ba?"

Maryama ta karasa maganar muryarta na karyewa, hawayen da take ta rikewa suna zubowa

"Hakuri, hakuri sukeyi Maryama, hakurin da suka zabarwa kansu, wasu su hada hakurin da addu'a har Allaah Yasa su dace"

Ta daga ido ta kalli Khairi

"Anya wannan hakurin baifi na mutuwa wahala ba?"

Tunda hakuri a yayin rashi abune daya zama dole, har mamakin dalilin da zaisa a dinga tambayar mutanen da akayiwa rashin ya hakuri takeyi, ko a dinga jaddada musu suyi hakuri, kamar dai akwai wani abin da zasuyi bayan hakuri. Wannan hakurin da zatayi, hakurine da take da zabi a cikinshi

"Kina son mijinki Maryama, kina sonshi"

Kallon Khairin dai takeyi, tana kuma maimaita abinda ta fada cikin kanta, kamar wadda take laluben inda son yake

"Wannan shine son daman?"

Ta tambaya tana kallon tafukan hannayenta yanzun, kamar wadda zata ganshi a rubuce a jiki, ita dai tasan an aura mata Haris, kuma ta jima da karbarshi a matsayin mijinta, amman in ba ranar da zata taho ba, bai taba cewa yana sonta ba, itama kuma bata taba tunanin ta furta masa ba, duk yanda take jin kalmar

"I love you"

Tana tashi a kasar New York kamar gaisuwa, ita tunanin amfani da ita tsakaninta da Haris ma bata taba gifta mata ba, ko ranar daya furta mata din kuwa, zuciyarta ta dinga bugawa tana sake maimaita mata kalaman Khairi

"Maryama kina son mijinki, kuma alamunki sun nuna ko kusa bakya tunanin rabuwa dashi, saboda haka dogon bacci ba naki bane ba, dole zaki kara rike addu'a..."

Ai ta jima da sanin dogon bacci ba nata bane, tunda ta kalli Awwab tayi tunanin wayar gari ta riski yana aikata kwatankwacin abinda Haris yakeyi ta rage bacci, ina zatayi bacci bayan wannan amanar da Allaah Ya bata ba zata iya sauketa batare da taimakonShi ba?

"Ki fara komawa, kafin ya dawo zamu san ta inda zamu bullowa lamarin In Shaa Allaah"

Wannan shawarar ita Maryama ta dauka, ta fara shirye-shiryenta na komawa gidansu da yake cikin wata unguwa can gaban Millennium City, Dan honu, ita duk zamanta a Kaduna ma bata tabajin sunan unguwar ba sai wannan lokacin. Ana gobe zata koma dinne Hajja ta biyota har dakinsu, tana kwance ne tana danna waya, ganin shigowar Hajjan yasa ta tashi zaune, saita zauna gefen gadon

"Maryama"

Daga yanayin yanda Hajja ta kirata sai taji wani rauni ya fara shigarta

"Nasan kina da damuwa, tun kafin ki dawo kasar nan, nakeji a jikina kina da damuwa, kina shigowa kuma na ga wannan damuwar da dukkan wani motsi naki, kowanne aure baya rasa matsala ko da guda daya ce kuwa, sannan a cikin kowanne aure akwai sirri, kuma naji dadin ganin yanda kika zabi ki rike sirrin naki auren..."

Hajja ta numfasa

"Musulunci yayi mana gata mai yawa, babu wani abu dangane da rayuwa da bai koyar damu yanda zamu gudanar dashi ba, cikin tsarukan da zamuji dadin duniyarmu da lahirarmu, shi kanshi auren ba'a barmu haka ba, sai da aka koya mana matakai na zama a cikinshi"

Ta kalli Maryama da ta tattara hankalinta tana saurarenta

"Anason idan sabani ya gifta tsakanin ma'aurata to suyi kokarin ganin sun sasanta kansu batare da wani ya shiga ciki ba, amman Maryama akwai sabanin da sakko iyaye a ciki shine maslaha, kamar yanda musulunci ya samar da rabuwa a matsayin maslaha. A zamanku da Haris akwai abinda ya kamata ace mu iyayenki mun sani?"

Maryama taji kirjinta na wani irin rugugi, sai kyafta ido takeyi tana kokarin maida hawaye, cikin rawar murya tace

"Ba...ba...babu komai Hajja, 'yar matsala ce kuma In Shaa Allaah ma komai ya wuce"

Hajjan ta zuba mata ido na wasu dakika, kafin ta numfasa tana fadin

"Allaah Yasa hakan, Allaah Ya kara dai-daita tsakaninku Ya kade muku fitina, karkiyi wasa da addu'a kinji ko?"

Da kai ta amsa saboda tanata danne hawayenta. Aikuwa Hajjan na fita ta koma ta kwanta tabarsu sunata zuba, su suka zame mata abokan hira har bacci ya dauketa. Daman sunyi magana da Haris dan tana so a samar mata mai aiki da zata dinga kwana, Hajja ce ta bada shawarar a duba a cikin dangin Alhaji Sa'id da suke kauye

"Nifa wani lokacin gara a dauko mun bare, yanda in wani abin yayi mun zan saita masa hanya, akan ace 'dan uwa ne, inka kore shi dangi su nemi wutar jefaka"

Adda Zahra ta fadi lokacin da ake maganar, ta bawa Hajja dariya kuwa

"Ku duk masu aikinku ba kwana sukeyi ba, zuwa sukeyi su kama muku abinda zasu iya su tafi, ita kuwa wannan tare zasu kwana su tashi, ina ganin komin lalacewar da bama fata, gara ace 'yar uwarta ce take zaune da ita, ansan daga inda ta fito, ta kuma san wa take zaune da ita, sannan fargabar dawa zata dinga barin yaranta in bukatar hakan ta taso ma zai ragu"

Dan Hajjan a tsorace take da lamarin masu aiki, tasan maita batazo a musulunci ba, sai dai kambun baka, sai dai akwai tsoratarwa, nan makotan su Hajiya Sahura kawarta akace ta dauko mai aiki mayya, ta cinye mata yara har uku, ta kama karamar ta hudun ne asirinta ya tonu, kuma ance tana tsallaka yarinyar sai gata ta mike. Sai ta kara tsorata da batun masu aikin nan. In dai ba'a samu a 'yan uwan Alhaji Sa'id din ba, to ba zata bari Maryama ta dauki kowacce yarinya suna kwana gida daya ba, bayan ba'a san irin abinda zatazo dashi ba. Kuma da yake yawa ne da dangin Alhaji Sa'id din, gashi kowa so yakeyi ace nashi sun rabesu, ba'a sha wahala ba aka samo Fa'iza. Duka shekarunta sha biyu, wai da aure ma zasuyi mata, sai mijin da akayi baikon dashi yayi jinya ya rasu, to jin Kaduna za'a taho da ita yasa babu wani dogon tunani suka tattara mata kayanta.

Tunda Maryama ta ganta taji yarinyar ta shiga ranta, dan batayi mata kama da mai rawar kai ba, haka kowa yakeyi mata fatan ace zaman ya dore, kuma Fa'izar tayi musu bazatan zamarwa Maryama alkhairi. Washegari da zugar 'yan uwanta suka rakata, da ta saka rikici ma sai dai Alhaji Sa'id ya kaita

"Abba bafa ka taba zuwa gidana na Kano ba, ai yanzun kai ya kamata ace ka kaini"

Ya dinga dariya

"Zanzo Mairama, idan nazo kuma har girki zakiyi mun in zauna inci abincin gidanki"

Saida tayi masa tsaye tasa shi yayi alkawarin zuwa tukunna suka tafi, yanda su Adda Zahra da suka fara zuwa gidan suka kai mata kayan kitchen sukaita zancen tsaruwar gidan, sai taga yafi haka ma, mazan gidansu ma sunje, tunda Alhaji Sa'id ne da kanshi yace suje suyi mata addu'a a gidan. Komai ya burgeta, basu tafi ba sai yamma, aka barta daga ita sai Fa'iza da kuma Awwab da dan kwana biyun da yake ganin Fa'iza acan gidan Hajja ya saba da ita. Tana da duk wani na'u'in kayan miya da zata bukata a cikin fridge din kitchen dinta, zata kwana biyu tasan bata bukaci wani abu ba.

"Za'a kawo miki mota Maryama"

Tunda bata jima da binshi New York ba yace mata an siyar da motocinsu, kudin na account dinshi, sai sun koma saiya siya musu wasu, in kuma tanaso ya saka mata nata kudin a account dinta ne kuma sai yayi hakan, to da ya saka mata ma dai tasan babu abinda zatayi dasu, yanzun kuma gashi ta dawo, ko da tasan motar haka zata dinga daukar kura taji dadi, kamar wata babbar alama ce na sake samun waje ta mike kafa a Kaduna. Washegari kuwa tunda sukayi sallar asuba, duk bacci suka koma harda Fa'iza, dan gidan ma yana nan a gyarenshi sai dan abinda ba za'a rasa ba.

Ringing din wayar Maryama ne ya katse mata baccin da yakeyi mata dadi, ta ga bakuwar lambace, sai dai abinda yasa ma ta daga shine sanin babu wani da yake da lambar banda 'yan uwanta, duka yaushe ta siyi layin? Mamaki tayi matuka jin muryar namiji, saida ya fada mata Hajiya Rumana ce ta bashi lambar zai dauki Awwab ne, yana so tayi masa kwatancen gidan. Ta girgiza kanta kawai, ta kuwa yi masa, har kofar gidan yazo, ta saka hijabinta ta fita tana bude gate din din ta mika masa Awwab da saida yayi mata rigima sosai na tashin shi da tayi, fuskar nan a hade ma suka fitan, ya gane direban shine ma ya ruga wajenshi yana dariya.

Data koma ta kwanta, bacci tayi niyyar komawa, sai kuma Haris ya kira, kamar karta daga

"Bacci kikeyi?"

Ya tambaya jin muryarta can kasa

"Eh, Mami ce ma ta aiko aka daukar mata Awwab, kiran direban nema ya tasheni"

Da mamaki da wani abu daban a muryar Haris yace

"Direba kuma? Direban ne ya kiraki?"

Dan shi Hajiya Rumana ta kira tace ya bata lambar Maryama zatayi mata kwatancen gidan za'a dauko Awwab, to akan me zata dauki lambar Maryaman taba wani gardi

"Eh ya kirane nayi masa kwatance"

Tayi maganar kanta tsaye

"Shi direban ne ya kira, kika dauki wayarshi da wannan muryar taki da take cike da bacci Maryamm?"

Yanda yayi maganar ne ta gane abin nashi ne ya motsa masa

"To akan me da kikaji namiji ne ba zaki kashe ba? Ita Mami me yasa zaya ba wani kato lambarki, ni haka tace mun zata kiraki...ina zuwa bari in kirata"

Sanin zai aikata yasa ta saurin ce masa

"Ka kirata kace mata me? Dan Allaah, bafa wani magana mukayi ba banda kwatancen gidan da nayi masa, kuma yanzun tunda yaga wajen ai kaga babu wata magana da zata sake hadamu"

Yayi shiru

"Ganjaa"

Shirun dai ya sakeyi mata

"Zanyi blocking dinshi"

Ta fadi

"Better"

Murmushi yaso kwace mata

"Karka kira Mami dan Allaah, kar kuma kayi mata maganar ko da kiranka tayi"

Ya amsa da

"Hmmm"

Kuma kafin ta kara magana yace

"Kiyi baccinki"

Ya kashe wayar, ta girgiza kanta kawai, fushi yayi ta sani, wannan rigimar kuma ba zata iya mata ba a yanzun. Baccin ma ya riga ya bar idonta, sai kawai ta tashi ta shiga wanka. Ta fita falon ta ga Fa'iza ma ta tashi, tana goge tv stand, ta gaishe da Maryaman cikin ladabi da kuma sanyin muryarta na halitta, ko kitchen ma tare suka shiga, tana so Fa'iza ta dinga ganin yanda takeyin abubuwa, sannan kuma zata samu Islamiyya ma ta sakata, bataji dadin yanda taga tayi sallar isha'i ba jiya, ta kudirta a ranta, da kanta zata fara koya mata yanda zatayi sallah kafin ma ta shiga Islamiyyar.

An riga an saba duk sanda za'a dauki Awwab, to duk inda karfe biyar tayi zuwa shida na yamma an dawo dashi, amman yau har an idar da sallar Magriba shiru, abin yana ran Maryama, danma batajin dadin jikinta, wannan cikin babu wani laulayi da takeyi banda cin abinci kamar gara, sai abinda ba'a rasa ba, kamar dai yau da ba wani aiki tayi ba amman jikinta ko ina ciwo yakeyi sai kace wadda tayi surfe. Da tayi isha'i kuwa taci abinci saita shige dakinta tabar Fa'iza da take kallo a falo. Data kwanta sai zuciyarta ta dingayi mata zillo da tunanin Awwab, haka sukayi waya da Haris da saida ya karanci rashin walwalarta, ya dinga tambayarta ko wani abu ya faru tana ce masa

"Babu komai fa"

Daya matsa mata ne tace masa

"Ciki fa gareni Ganjaa, ba kullum yanayin yakeyi mun dadi ba, yau irin ranakun nan ne"

Kuma wannan yasa ya daina tambayarta, saima yayi mata sallama yace ta kwanta ta huta, tayi masa kissing din Awwab, ta amsa da

"To"

Haka ta kwanta tanajin kewar Awwab din da take turewa gefe idan ya nanike mata wani lokacin, amman yau gadon ma yayi mata fadi sosai. Abin kamar wasa, kwana biyu Awwab shiru, kamar tayiwa Haris maganar saita kasa, saida kanshi da yace ta bashi Awwab din a waya tace masa

"Bafa a dawo dashi ba, yana gidan Mami"

Bai jira abinda zatace ba ya kashe wayar, ya dauki kusan mintina ashirin kafin ya sake kiranta

"Kinga rigimar Mami ko? Ashe wai Maiduguri suka tafi da Awwab din, sai sati mai zuwa zasu dawo"

Maryama taji kamar ya kifa mata mari, Maiduguri? Da Awwab din? Kuma harna sati? Ita bawai tafiyar bane matsalarta, kenan bata da darajar da Hajiya Rumanan zata gaya mata? Ba dan ta isa ta hana ba, amman dai ai sai a gaya mata

"Uhm, to madalla"

Ta iya cewa wani abu yayi mata tsaye a makoshi

"Bama a daukar masa kayanshi ba"

Haris ya danyi dariya

"Haba, kaya dai, ai nasan zata siya masa duk abinda yake bukata, wai taje kaishi ya gaisa da 'yan Maiduguri, Allaah Yasa kar yayi mata rigima sosai"

Da alama shi kanshi Haris din baiji cewar ba'a kyauta mata ba kenan?

"Nifa bawai banyi murna da zaki zauna a Kaduna ba, kawai ina jiye miki waccen bakar matar da fitinarta ne, kar tazo ta dinga tsiro da wasu abubuwan, Allaah Kanon saita fiye mana"

Khairi tace mata kamar mai duba, ita a lokacin bata hango wani abu ba sam

"Karta dinga zuwa miki gida kamar wadda ta samu aikin sintiri"

Abin dariya ya bata, ko kadan bata hango Hajiya Rumana zata dinga zarya a gidanta babu wani kwakkwaran dalili ba, tunda ta kula in ba dole ba, kamar ko ganinta Hajiya Rumanan batason yi. Ashe ba sai tazo bane zata samu hanyoyin da zata dinga cusguna mata, ita kadai tasan wahalar da tasha lokacin da take koyon saka Awwab din kan schedule, musamman ma na bacci, da suka dawo din nan ne baccin ya dan hargitse masa, amman a hankali a satin ya fara dai-daita, tana ta jin dadi, yanzun kuwa in suka dawo ta tabbata sai abinda ta gani

"Akwai aikin da zan karasa, in danyi karatu kuma, muyi magana anjima?"

Ta daga kai tana amsa shi da

"Allaah Ya kaimu"

Sauke wayar tayi a hankali, ba zatayi karya ba, taji zafin abinda Hajiya Rumana tayi mata, in ta fadawa Khairi ko da tayi mita, zata bata hakuri ne, ita kuma bataso a bata hakuri, a wannan auren nata da Haris, hakuri daya takejin zata iya,ko kadan bata hango tayi hakurin zama da Haris, sannan ta hada dana danginshi ba

Ai ko kaddara ce sai dai ta zabar mata daya...

39

Shirin bikin Khairi sukeyi, ko tace akeyi saboda yanda Haris ya takureta a gida, ya hanata fita yanda ya kamata. Su Adda Zahra ne tsaye akan komai kamar yanda suka saba, amman Maryama zataso ace da ita ake yawon zuwa kasuwa siyayya, ko ace tana yawan zuwa gida yanda take so

"Me zakije kiyi ne wai? Kece zakije musu kasuwar? Bana son fitar nan Maryamm, kin sani kuma, bana so ko kadan"

Haka zaice, inta matsa masa suyi fada, koya kashe wayarshi gabaki daya. Ko kai Fa'iza Islamiyya ma haka yace a bari sai ya dawo idan babu wanda Maryaman zata samu ya kaita, ranta ba karamin baci yayi ba, sai dai babu yanda zatayi da Haris tasani tunda babu yanda zatayi dashi, cikin mazan gidansu ta samu akazo aka kai Fa'izar, da yake makarantar ma anan kusa dasu take, karfe uku na rana suke shiga, su tashi karfe biyar da rabi. Ya dameta akan me zasu ba Khairi gudummuwa, ita dai tasan abinda take so ta bata, Khairi na son tukwane, ko gidanta tazo ta dinga sauko kwalayen tukwanen da bata bude ba kenan tana budewa tana kallonsu, a waya ma haka zata dinga nunawa Maryaman

"Ki kalli tukunyar nan, in ina da ita ai a kitchen zan wuni, ko ba zan dafa komai ba, in jerasu ina kallo ina jin dadi"

Akwai Chef Maryam da take following a manhajar Instagram, dan zatace ma ita kadai takebi tunda bata jima da bude Instagram din ba, tana saka recipe na girke-girke kala-kala kuma Maryaman na karuwa da wasu abubuwan, a wajenta take ganin tallar tukwanen kamfanin Caraway, tun tana New York taso ta siya tunda Chef Maryam din a America take sai kuma tahowar da tayi bata natsuwa bace ba, amman ta dauki lambarta (+13177018261) sunyi magana, tana aikawa kowacce kasa kake, sannan farashin shipping din baiyi mata tsada ba, farkon zuwanta New York, kome suka siya saita tambayi Haris, nawa kenan a kudin Nigeria, inya fada mata saita dinga ganin yayi tsada matuka.

"Ki daina lissafi da kudin Nigeria, saboda ba dasu ake biyana albashin duk wani aiki da zanyi ba, da dollar ne, shine zaki dinga ganin saukin komai"

Haris ta turawa account din Chef Maryam ya saka mata kudin

"Sai kuma me?"

Tace masa babu komai, tana da kudinta, zata bayar ayo mata canji tayi duk wata hidima a ciki

"Ni me zan bata?"

Dariya ta dingayi masa

"Kaima kayi tunani da kanka..."

Saiya kyaleta, daya tashi kudine ya turawa Khairin wai ta siyi abinda take so, kudine da yawansu a har Hajja saida tasa aka kirawo shi tana masa fadan kudin yayi yawa

"Dan Allaah Hajja ki daina cewa haka...ko bana auren Maryamm, Adda Khairi ai kanwata ce da zanyi hidima a bikinta"

Dole Hajjan tayi masa addu'a sosai tare da godiya. Itama Maryaman ta karayi masa godiya, dan tayi mamakin yawan kudin. Saura kwana takwas bikin Khairi, Haris ya iso Nigeria, da yake Kano ya sauka, ya riga ya fadawa Alhaji Mustafa, aka aika da direba daya dauko shi zuwa Kaduna. Tun safiyar Maryama take tunanin abinda zata dafa, in da ace Haris kamar sauran mutane ne, ta tabbatar tana nan tana ta girke-girke, abubuwan da yafi so, to abincin ma ba damunshi yayi ba ballantana a samu abinda yafi so a ciki. Duk yanda Khairi ta matsa mata akan tayi kunshi kiyawa tayi

"Wallahi ba zanyi kunshi ba, kinsan ba fita zaiyi kafin biki ba"

Rantsuwar da tayi ne yasa Khairin ta kyaleta, ta dai dibo mata wasu abubuwa cikin magungunan gyaran da Adda Zahra take bata, har gida tazo ta kawo mata, ta dinga kallon ledar kayan, data bude ma ta duba sticker din jiki ta girgiza kai, wani abin saika rasa inda Adda Zahra take samo shi tana nan garin Kaduna, dan taga ansa Zee Herbal a jiki, kuma taga matar a garin Katsina take, gumbar da aka rubuta chocolate gumba ce ta dinga shigar mata ido, data gutsira ta saka a baki, sai gata ta sake duba lambar 08109343492. Abin yayi mata dadi sosai, ga kwakwa. A ranta ta raya wannan ai ba maganin mata bane ba, kayan kwadayine kawai aka hada, bata iya hakura ba saida taci kusan rabin robar,

39 / 51