Advertisements
Chapter 43 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   43 / 51

126K to 129K   out of 151K words

ta sauke hannunta data mikawa Maryaman

"Dan ka?"

Ta tambayi Haris, ya amsa yana nunawa Awwab ita hadi da fada masa wacece, Awwab ya gaisheta a takaice, kuma shiya daukewa Maryama hankali da abinda yake bata labari wanda bama ganewa takeyi ba, ta dai biye masan ne dan batason tunaninta yayi tasiri akanta. Daren dai basu kwasheta dadi da Haris ba

"Cikine da ita Maryamm, ko baki gani ba, da auren wani akanta, wani ta aura, ni me zanyi da ita bayan ta auri wani?"

Harara ta watsa masa kamar idonta zai fado

"Saboda ta auri wani kenan shisa ko? Inda zata fito tsab zaka kara da ita, har yanzun kana nacinta kamar yanda naga tana naka, tunda ku duka kuna makale da sunayen juna a yatsa, to bari kaji wallahi duka biyu zaka sha Ganja"

Ya zauna a gefen gadon yana kallonta

"Ga dukan sabawa Allaah nayin tattoo, ga kuma dukan sunan matar wani da kake dako, na tabbata bayan an kumburawa Mala'iku kai dai-dai yanda zasuji dadin duka, yatsan nan ma sai an hura shi sau dubu saba'in sannan mala'iku dubu saba'in su zagaye shi kowa ya samu inda zai jibga..."

Yayi dana sanin dariyar daya kwashe da ita, dan itace tasa Maryaman ta fashe masa da kukan da tasan yana rikita masa lissafi, kusan raba dare sukayi yana aikin lallashi

"Ni wallahi rabona da ganinta harna manta, tun a Italy, sai yau...kuma ai a gabanki, kinsan inda nayi magana da ita ko ba zatayi miki dadi ba zan gaya miki yanzun da kika tambaya"

Dakyar ya lallabata, su da sukazo da niyyar yin sati daya kamar sauran, saboda yanda taki kwantar da hankalinta, kwanansu hudu, ya cewa Hajiya Rumana anyi masa kiran gaggawa zaiyi clearing wasu kaya da aka kawo masa, dole sai yana wajen, suka barta da Awwab da Rauda, ya dauki Maryaman suka koma Kaduna. Kuma ya kara faranta mata bayan ya bar kasar ya dawo, abu na farko daya farayi a bakin kofa data tare shi shine mika mata hannunshi, daga farko bata kula ba, sai daya ware mata yatsunshi, ta duba, ta kara dubawa, ta daga kai ta kalle shi

"Na cire Maryamm...na cire kuma nayi Istigfar kamar yanda kike cewa inyi idan banyi sallah a masallaci ba saboda Allaah Ya yafe mun ya duba lamarina"

Batayi magana ba, hannun ta sumbata, ta juya bayanma ta sumbata, sannan ta rungumeshi duk da katon cikinta kuwa

"Zaki latsemun yarinya"

Tayi dariya tana sake rikeshi, tana maida numfashi saboda da gaske ta matse cikin nata, dole ta dago ta sake kama hannun tana kallo

"Nagode"

Saiya kashe mata ido daya

"Ban yarda da wannan godiyar ba Maryamm, kibari inyi wanka in natsu sai kiyi mun godiyar sosai"

Ta nuna masa cikinta da hannu

"Karki bari yarinyar da bakiyi wata bakwai da sani ba ta shiga tsakaninmu"

Tayi dariya, a lokacin tana jin kamar babu wata mace da ta kaita farin ciki, kamar babu wata mace da tayi dacen miji kamarta, mijin da yake barin komai saboda farin cikinta. Ko kadan bata san a wannan lokacin kaddara nayi mata lissafi bane ba

Wata bakwai Haris yace,
Kaddara kuma ta kara mata uku akai daya rage komai ya birkice musu


42

Har gobe Maryama ba zata taba bace lissafi ba, idan ranar ta fado mata, sai ta tuna cewa kwananta talatin da daya da haihuwar Naadir. Tana zaune akan gadon dakinta, ko tace dakinsu ita da Haris, dan dole suka mayar dashi nasu, sai daya ya koma na Awwab, dayan kuma Fa'iza da Rauda. Yanzun dinma Fa'izar ce tayi sallama, saida ta bata izini tukunna ta shigo, inka kalli sanyinta, yanda take komai a nutse zaka iya cewa zatayi san jiki, kuma hutun da take samu ya fito da hasken fatarta sosai. Yarinya ce da Maryama take kara godewa iyayenta da suka basu rikonta, a shekarun nan ba iya islamiyya ba, har boko saida ta tsaya aka mayar da Fa'iza, aka daukar mata lesson teacher, da yake itama tana son karatun kuma saita maida hankali sosai. Yanzun haka tana ss2 ne, sai dai iyayenta aure suke so tayi, karfin hali na Haris harda zuwa ya samesu yace suyi hakuri ta kammala ko da ssce dinta ne, Maryama ta dinga kallonshi tana kasa hadiye mamakinta a lokacin.

Sai kuma ta ga daga duk wani abu da Haris zai karba, to yana karbane da dukkan gaskiyarshi

"Kanwarmu ce kanan?"

Ya tambayi Maryama, ta dan jinjina masa kai

"Ta wanni fannin kuma 'ya ba, tunda rikonta aka bamu"

Nashi kan ya jinjina mata a lokacin, sai a hankali ta kula da rikon 'ya yakeyiwa Fa'iza, yanda su Awwab suke ce masa Papa, haka ya hanawa Fa'iza kiransa Kawun data nemi kakaba masa itama take kiranshi haka. Sanda ta fara tsayawa da Auwal da yanzun iyaye suka shiga maganarsu, kamar Haris zai daketa, ya dakatar da zuwan Auwal gidan sai bayan da yayi bincike ya gamsu da tarbiya da kuma inda Auwal din ya fito, asalinshi dan zamfara ne, zama ya dawo da iyayenshi nan Kaduna, sai dai shi din jami'in tsaro ne masu yaki da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA. An tsayar da magana sai ta gama zana jarabawarta sannan za'ayi bikin, haka kuma Haris yake jadda masa ko bayan auren Fa'iza zata cigaba da karatunta.

A maimakon haushi ma sai abin ya dinga ba Maryama dariya, yanda ya rufe ido ita ya hanata tayi nata, gashi yanata hakilo akan Fa'iza, ai addu'a takeyi Allaah Yayi mata tsahon rai dan taga yanda za'a kwashe dashi akan Rauda. Yau ma Auwal dinne da yake aiki a Minna yanzun yazo Kaduna, to baiga Naadir ba, shine Fa'iza tazo zata daukar masa shi. Itama ganin yayi bacci da ta cewa Maryama a barshi

"Ammi banaso ya farka ya dinga kwala ihu, kyau kema ki dan kwanta ki huta fa"

Maryama tayi dariya, Naadir ba dai kuka ba, ita babu ma wanda yayi rigimarshi, kuma da alama zaiyi qwiya, dan tun yanzun duk wanda ya dauke shi saiya dinga kure masa kallo kamar yana so ya gane wanene kafin ya yage baki, kuma shi da alama ba zaiyi duhun fata kamarsu Rauda ba, ta ganshi har yanzun da haskenshi, su kam kafin ayi arba'in duk sun rine.

"Kinsan Naadir dai inya tashi rigimarshi zaiyi ne, ki dauke shi ki kai masa shi ya ganshi"

Bayan Fa'izar ta dauki Naadir ne ta fita, sai kawai ta kishingida, tasan ko zancen suka gama ma, Fa'iza goyashi zatayi, ta dauki wayarta ta tafi open diaries tana karanta matsalolin mutane, a gefe daya tana godewa Allaah da nata matsalolin, wani abin inka gani dole ma ka godewa Allaah, dan sai kaga taka matsalar na matsala bace ba, iya wannan rufin asirin da take ciki abin ta duba ne, tafi karfin komai na bukatar rayuwa, harma tayiwa wasu batare data takura ba. Tana cikin dubawa ne kuma taci karo da wani abu daya sakata tashi zaune. Ta sake karantawa daga farko

"Malama yau kwana hudu da mutuwar mijina, wayarshi na hannuna tun rasuwar, bukatar kudi ta taso da yasa na bude wayar tunda nasan pin dinshi, aka cire kudin, wallahi Malama na yarda da mijina, akwai yarda sosai a tsakaninmu da soyayya da in zan bada labarinta sai wasu sunce karya nakeyi, lokacin da aka kawomun gawarshi da yake hatsari sukayi sumana hudu, har aka rufoshi bansan inda kaina yake ba, amman kinganni yanzun haka naci na koshi harma na hau social media. Kewa ta sakani bude social medias dinshi harna fada Snapchat, na gano abinda ya tsaida mun hawayena ya busar mun da zuciyata. Allaah Ya isa tsakanina da mutumin nan, wallahi ko darajar yara banajin zan iya karayi masa addu'ar samun Rahma, maha'inci, makaryaci..."

Kasa karasawa Maryama tayi saboda jikinta da taji yana rawa, wanne irin masifa ce wannan taje ta ganowa kanta? Anya wannan matar tasan mutuwa kuwa? Anya ba dimuwar mutuwar bace ta sakata wadannan maganganun? Ta ajiye wayar ta kwanta, sai kuma ta dauka wani irin tsoro na ratsata, saboda yara take sakawa wayarta Pin, musamman ma Rauda, tayi fadan harta duka ta hada dashi, amman data ajiye wayar saita dauka taje tanayi mata game, yanzun nema ta huta da Haris ya siyawa Rauda din wasu irin games tunda ya kula abinda tafi so kenan. Ta kalli wayar, tasan bata da wani abu da zatace tana gudun a gani.

In ba hirarsu da Khairi ba, shima kuma sirrikane da suka shafesu, sune zatace bataso wani ya karanta saboda sirrinsu ne, abune daya shafesu, kuma ko gulmace bata da abokiyar yinta sai Khairin. Yanzun idan itama mutuwa tayi fa haka za'a samu wani cikin 'yan uwanta koma Haris ya iya zama ya bude chat din nan ya karanta ko? Ta karewa dakin kallo, da gaske ne da akace mutuwa mai tonon silili, har dakin ma haka za'azo ayi masa filla-filla, idan akwai wani abu da take boyewa ma sai an bankado shi, tunda mutuwar ita ba sallama takeyi ba balle ace zata baka lokaci kasan ya zakayi da duk wani abu da bakaso a gani.

A zamanin da muke kuma, wayoyinmu sune wani abu guda daya da yake dauke da sirrikanmu fiye da komai, fiye ma da kowa namu. Suma ba zasu tsira ba, koyane za'a samu mutum daya da yasan mabudin sirrin wayar, idan an bude, iya inda za'a tsaya da bincikenta Allaah ne kawai zai sani

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Maryama ta furta a fili, sai gashi tana goge chatting dinsu da Khairi, tana tanin kamar itama mutuwar na iya yi mata dirar mikiya. Haka ta dinga juyi tana tuna mutumin nan kamar ta sanshi, sai take hasashen idan iyayenshi basu da rai kuma fa? Yaranshi ko sunyi girman da zasuyi masa addu'a? Su roka masa yafiyar Allaah a cikin koma menene matar tashi ta binciko daya sakata yi masa wannan tonon sililin? Ko zata huce wata rana ta yafe masa? Kai in akace mutuwa ma ya kamata fa ta kori komai, wanda ya mutu meye ya rage masa? Tashi ta kare fa kenan, komai ma daya aikata anan ya tafi can inda zai tarar dashi, ya kamata a tausayawa mamaci a nata tunanin.

Wannan abin ya tsaya mata matuka, dan har Haris saida ya kula da rashin kazarniyarta a ranar, yayi mata magana tace masa babu komai, sai bai dameta ba, yasan takan shiga irin wannan yanayin in tana jego, yana dai saka mata ido sosai saboda ko zaiga alamomin postpartum depression da mata da yawa kanyi fama dashi. Washegari da safe yana sauri ya fita, ya ajiye su Fa'iza a makaranta, sai lokacin ne ta kula daya bar wayarshi a gida, yana barinta sau babu adadi, amman yau dai tasan mantawa yayi. Wayarshi ko password babu, yanda ta kada Haris ta rayashi yaki harkokin social media din nan. Instagram ma ita ta bude shi a wayarshi sai take tayashi posting din wasu cikin ayyukan hotunanshi. Daga karshema ta mayar da account din kan tata wayar, dan yafi mata saukin managing, yake cewa dole ne ya dinga bata albashin wannan aikin suna dariya.

WhatsApp kuwa batasan me yasa ya bude ba, tunda sai kayi masa magana hamsin baiko duba ba balle kayi tunanin zai baka amsa, yafi sauki kayi masa text ma. Yau da ta dauki wayar sai abinda ta gani jiya ya fado mata, sai taji zuciyarta tayi wata irin bugawa kamar zata fado daga kirjinta, hannunta har rawa yakeyi lokacin da taga Snapchat din a wayarshi, duk wayoyi suna zuwa dashi, itama akwai a tata, tana ma dan shiga taita gwada filters din kai, amman bayan nan bata komai dashi. Tana budewa sai taga alamar Haris ya bude account ne, duk wani gargadi da kwakwalwarta takeyi mata, saita bar zuciyarta tayi mata fatali dashi, jikinta ya dauki dumi alamar zazzabi na kwankwasa mata kofa.

Sakkonni, sakonni da zatace sunfi dari, mata, dukka sakkonin sunayen matane, wasu asalin sunansu, wasu kuma wani suna ne daban, tasan zuwa yanzun ba iya jikinta da kayan cikinta bane suke kadawa, har ruhinta ma rangaji yakeyi, ta bude na farkon, maganganun karshen ta duba, maganar yarinyar ce da tayiwa kanta lakabi da "Lush"

"See you 4pm din"

Daga sama kuma maganar Haris dince, sunan hotel ne da kuma lambar daki. Ta fice daga chat din, bata san iya awannin data dauka ba, amman saida ta duba duk wani chat da yake kan Snapchat din Haris, zazzabi mai zafi ya rufeta, sai kawai hotonshi da Autumn ya fado mata, sai ta dinga harhada kwatankwacin wannan hoton da wannan kwamacalar da ta gama gani yanzun, tana kuma ajiye Haris a cikin kowanne, sai taji jiri na dibarta daga zaunen, data kwanta ma dakin wulwula mata yakeyi

"Ke dai babu ruwanki da wayarshi, ai in kina nemawa kanki zaman lafiya ki kiyayi wayar miji"

Haka tasha gani ana ba mata shawara, har karamin tsaki takeja idan tagani, musamman idan Haris ya bar wayarshi a gida. Ashe itace sakaran, basu da takewa kallon basu yarda da mazansu bane ba, ita data yarda Haris zai iya barin mata kamar yanda ya bar wiwi, zai barsu saboda ita, ya barsu saboda ita, haka take tunani, musamman da bai bar mata wata kofa da zatayi wannan tunanin ba. Tana nan kwance ko sallar azahar ta kasa tashi tayi taji alamar shigowar Haris din, da sauri taja jikinta ta shige bandaki, ta saka mukulli daga ciki, tana jinshi ya shigo dakin

"Maryamm zan fita, sai bayan Magriba zan dawo..."

Yayi maganar bayan ya jinjina kofar bayin nata yaji ta saka mukulli, saita bude famfo dan yayi tunanin wanka takeyi

"Sauri nakeyi"

Ya sake fadi, a zaune take kan sink, sai taji hawayen da taketa rikewa sun balle mata, tana nan zaune har aka kira la'asar, ta mike tayi alwala, data fito ma ta fara gabatar da azahar, harta idar da duka sallolin bata daina hawaye ba, dakyar ta samu ta tsayar dasu bayan ta saka hijabinta ta dauki mukullin mota, tunda Fa'iza ita ta dawo tun dazun, kuma alhamis ce ba Islamiyya ke akwai ba, su Awwab ma ta tabbata suna gidan Hajiya Rumana ne sai kuma Asabar zasu dawo saboda islamiyyar da sukeyi nan cikin unguwar ne, sai bayan ta shiga mota ta fice ne ta kira Fa'iza a waya tace mata in Naadir ya tashi ta hada masa madararshi, wani irin tsotso gareshi, ita kuma wannan haihuwar bata da ruwan nono sosai, dole tasa suke hada masa da madarar.

Babu wani tunani, da tambaya ta ganta a kofar hotel din nan, ta fito daga motarta da tayi parking daga tsallake, idanuwanta har sun kankance saboda kuka da tashin hankalin, inda ma za'ace me takeji ko kasheta za'ayi ba zata iya misaltashi ba. Tana ganin yanda yamma take karayi, ga kuma kafafuwanta da suke mata barazanar kasa daukarta har lokacin, amman haka ta cigaba da tsayuwa, sai ga abinda take jira din ta tabbatar, motar Haris ta danno kai ta fito daga hotel din, duk da gilasan a sama suke, kuma irin wanda na waje baya iya ganin na cikine

"Motar marassa gaskiya kenan"

Haka 'yan gidansu suke yiwa masu wannan gilashin lakabi, suyita dariyar abin, yanzun kuwa ko daya babu nishadi a ciki data tuno, tata motar ta shiga tana binshi a baya, hanyar gida ya nufa, itama kuma gidan tayi daman, tana kallon yanda ya kara rage gudun da yakeyi yanayi mata fitila alamar ya gane tata motar, sai kawai tayi overtaking dinshi ta wuce da wani irin gudu kamar zata tashi sama, batayi mintina goma da shiga gida ba shima Haris din da yake tunanin abinda zai fitar da ita batare da ta sani ba, kuma ta ganshi ta wuce tana sharara wannan gudun yana kara hauhawar bacin ranshi. Har kiranta yayi a waya ta karaci ringing bata daga ba.

Jikinshi har bari yakeyi sanda ya shiga cikin gidan, ya karasa har dakinsu inda ya samu tana birkito kaya, duk wanda hannunta yakai sama, daukowa takeyi tana jefawa kan gado, wasu na faduwa kasa batare data damu ba

"Maryamm...."

Ya kira, mamakin abinda takeyi din na danne bacin ran da ya shigo dashi, ya sake kiran sunanta amman bata kulashi ba

"Magana nakeyi miki fa, meye haka? Me kike? Kuma daga ina kike?"

Dan akwai hijabi a jikinta har lokacin, sai ta kalle shi da idanuwanta da suka rine, wasu hawayen na sake zubo mata

"Daga inda kake"

Ta amsa, da wani sabon mamakin yace mata

"Daga inda nake kuma?"

Bayan ta kara watso wasu kayan ta jinjina masa kai

"Eh daga inda kake, hotel din da kake, dakin dai daka shiga room 305 shine na kasa karasawa"

Yaji wani abu ya tsirga masa, musamman yanda ta tsura masa ido

"Maryamm"

Kayan data dibo shi ta watsawa wannan karin, ya taka har inda take yana kokarin kamata, ta hankade shi

"Karka tabani, wallahi zan iya maka illa inka tabani...mazinaci...mazinaci kawai...ashe baka daina ba? Da yaranmu, da girmanka, ni ina nan na killace kaina, inata tattalinka, ashe kana waje kana zubar mana da mutunci...."

Take fadi numfashinta na harhadewa saboda maganar takeyi cikin kokarin daga murya da shanye kukan da takejin kamar ta rusa hadi da ihu. Wani akwati ta juya ta janyo, batare data zuba kayan nan data fito dasu ba taja akwatin zuwa falo, Haris yayi yunkuri rikewa, ta juyo ta wulwula akwatin nan tana maka masa shi, ko yanzun daya biyota rike yake da hannunshi na haggu da ko bai karye ba to tabbas ya samu matsala, dan ya sage masa nan take, azaba yakeji har tsakiyar kanshi, tashin hankaline yasa yake biye da ita

"Dan Allaah Maryamm, ki tsaya muyi magana"

Ta juyo tana sake daga akwatin, ita kanta data janyo shi ba zata tuna meye a cikinshi bama, babu shiri ya matsa baya

"Dan Allaah"

Wani irin kallo takeyi masa hawaye na zubo mata, lokacin ne kuma akayi sallama, Hajiya Rumana ta daga labulen da yake kofar ta shigo, sabe da Rauda a kafadarta, ta kalle su, yanda suke tsayen, gidan ba bakonta bane ba, shisa ta wuce dakin Fa'iza ta sameta tsaye da goyon Naadir tana dan danna waya, bata ko amsa gaisuwarta ba ta kwantar da Rauda da take bacci. Tunda suka koma ta ganta tana ta kwanciya, saida ta tabata taji zazzabi a jikinta, dole ta dauketa zuwa asibiti, inda akace malaria ce amman babu yawa, saidai wata Nurse ta taimaka mata ta rike Raudan akayi mata allura, tasan ba zata iya sakata tasha magani ba, dan allurar ma kukan da Rauda tayi har yanzun tana jinshi har tsakar kanta, sai kawai ta dawo

43 / 51