Advertisements
Chapter 32 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   32 / 51

93K to 96K   out of 151K words

na boyemun? Kamar wani abin arziki"

A hankali yace

"Ke kikace bakyason jin Mami, duk wani abu in dai ya hada da Maryamm, shisa ban fada miki ba"

Tsakin da tayi ya tabashi har kasan zuciya, shisa ko haihuwar nan ma ya riga yayiwa kanshi alkawari sai dai taji a bakin ko Alhaji Mustafa din kosu Munira. Dan ya kirasu daya bayan daya ya gaya musu, harda su Mukhtar kuwa, addu'o'in da suke tayi na kara sanyaya masa zuciya. Sanda ya gama wayoyin ya koma basu tashi daga baccin ba, saiya sake fita ya nemi abinci yaci. Saida suka kwana a asibitin tukunna aka sallamesu. Wani sabon kukan ya kwacewa Maryama bayan sun koma gida, taga daga ita sai Haris, shiya karbi Babyn, ita ta shiga wanka, wankan data saka towel tayi shi sosai kamar yanda Adda Zahra ta kwatanta mata.

Wai yau itace ta haihu a wata kasar, daga ita sai miji, babu wani dan uwanta ko guda daya, ta tuna irin taron dangin da akeyi a asibiti idan wani na gidansu na nakuda, Hajja ce kawai bata zuwa, amman ko haihuwar farko ta Adda Zahra, ba zata manta ba harda Alhaji Sa'id a wajen

"Yanzun kai sai ka bisu asibiti? Dan Allaah sai kaje kayi tsaye 'yarka na nakuda?"

Hajja tace masa

"Ai idan na samu waje zan zauna, in ban samu ba kuma haka zamuyita tsayuwa tare har Allaah Ya sauketa lafiya"

Kuma Hajjan data dauka da wasa yakeyi ta kwashi mamaki, dan tare da yaranshi kaf da suke nan suka dunguma zuwa asibitin, suka cika, danma na kudine, duk da haka saida aka korasu waje, dan sunki yin shiru, kuma duk bayan mintina sai wani cikin mazan yaje ya samu Nurses da duk wani likita da zai gani ya addabeshi da tarin tambayoyi. Da ta haihu kuwa, tunda mijin yace ba zataje gida wankan jego ba, haka dangi suka cika gidanta anata kai kawo. Amman ita nata yaron ma batasan ranar da zasu ganshi ba

"Adda Munira tace zata zo, kilan gobe ko jibi...zata zo ta ganku"

Kai kawai ta daga masa da yake fada mata a hanyarsu ta komawa gida, kuma kukan da ta dingayi a bandaki ne yasa ta dade, har saida Haris ya kwankwasa mata kofar tukunna, ta fito, ta samu doguwar riga ta zira a jikinta, ko mai bata shafa bama, ta dai murza turare, shima saboda sabone, ta kwanta, Haris yazo ya kwantar da jaririn a tsakiyarsu, shima ya kwanta

"Sannu..."

Ya fadi a hankali, idanuwanta yake kallo

"Me ya sakaki kuka?"

Ya tambaya

"Ba kuka nayi ba"

Ta amsa

"Karya ne..."

Saita sauke kanta saboda wasu hawayen da taji suna neman balle mata

"Me ya sakaki kuka?"

Ya sake tambaya

"Mu kadai, babu kowa, mu kadai, inka tafi kabarni ya zanyi?"

Ya dan sauke numfashi

"We will figure it out, ni da ke, bama bukatar kowa, bakya bukatar kowa Maryamm, ina nan, ni kadai na isheki"

Tayi shiru, ganin ba zata amsa ba yasa shi cewa

"Baki tambayi sunan babyn ba"

Har mamakinta ya dingayi da cikin yana girma bata tabayi masa maganar sunaye ba, da yayi mata ma saita dan daga masa kafada

"Kowanne suna yayi maka fa"

Dan ita dai bata ma taba wannan tunanin ba, kuma a ganinta abu mafi wahala dai ka samu yaran, dan suna, ai ba zaka taba rasawa ba

"Ya sunanshi? Kayi masa huduba daman?"

Ya daga mata kai, ya gyara kwanciyarshi yanda zai kalleta sosai

"Sa'id, sunanshi Sa'id"

Kuma shirun daya lullube dakin bayan maganarshi, irin shirun nan ne da yafi duk wata tarin hayaniya tasiri, shiru ne da zaka iya karanta, shirune mai cike da abubuwa masu yawan gaske, idan aka tambayi Haris kai tsaye zaice

Ba saboda Maryamm bane,
Ba saboda ita bane,

Zai kara da

Sabo da Baba ne
Saboda shi kawai.

Ko da ba Maryamm yake aure ba, wannan sunan shine yakeyi masa yawo duk lokacin da yayi hasashen samun yaro namiji tunda alakarsu ta gyaru da Alhaji Mustafa, idan macece kuma zai saka mata Rumana, zai saka sunan Maminshi. Amman namiji kam Sa'id ne, daya duba abinda sunan yake nufi saiya kara kwanta amsa a rai

Sa'id
Aminin mahaifinshi
Dan uwan da kaddara taba mahaifinshi.

Mutumin da ya tabbatar Alhaji Mustafa yana kauna fiye da 'yan uwanshi na jini ko da bai taba bude baki ya fadi hakan ba

"Sunan Abba na?"

Cewar Maryama tana so ta tabbatar

"Sunan abokin Babana"

Ya amsa mata, sai tayi dariya, tayi dariya hawaye na kwace mata

"To me zamu kira shi? Takwaran Baban Tudun Wadan?"

Da dukkan zuciyarshi yace mata

"Ke zaki zaba, kome kika zaba zaiyi mun"

Ta dan numfasa, duk wani hali da take fatan jaririn da yake tsakiyarsu ya dauka na Alhaji Sa'id na gifta mata

"Awwab, zance masa Awwab"

Maryama ta fadi zuciyarta na budewa waje-waje da tarin soyayyar Awwab din

"Zamu ce masa, zamu kira shi da Awwab, yaronmu Awwab"

Haris ya gyara mata, yana kara maimaita sunan a kasan numfashin shi, yayi masa dadi

"Awwab"

Maryama ta maimaita kamar tasan abinda Haris din zai fadi, sukayi dariya a tare. Kuma da Alhaji Mustafa ya kira yana tambaya

"Ina bakon duniya? Ni banma tambayi sunan abokin nawa ba"

Cikin farin ciki Haris yace

"Sa'id, sunanshi Sa'id Baba"

Alhaji Mustafa ya danyi jim, kafin yace

"Nagode Haris, Allaah Yayi maka albarka, Allaah Ya karramaka ninkin karamcin da kayi mun, Allaah Yayiwa abokina albarka, zuwa New York ya kamani, dole inzo inga Aminina"

Haris yayi dariya

"Maryamm tace zamu kira shi da Awwab"

Alhaji Mustafa ya jinjina kai daga dayan bangaren

"Mai yawan ibada, aikuwa abokina ma'abocin ibada ne, Allaah Ya tabbatar dashi akan ma'anar sunanshi da kuma sunan da kuka zabi kuyi masa alkunya dashi. Allaah Yayi muku albarka Haris"

Wannan kalmomin, na Alhaji Mustafa, sune suka rike shi, su ya dinga jujjuyawa a cikin kanshi yana amfani dasu wajen goge bacin ran da Hajiya Rumana ta saka shi a ciki

"Sa'idu? Haris ubanka ko mutuwa yayi ai banyi zaton idan sunanshi baiyi maka dadi ka sakawa danka ba zaka tsallake dangina da nashi ka dauko sunan bare ka maka, to wai ni daman Sa'idu da 'yarshi na haifawa kai? So kakeyi aga na yanke jiki na fadi? Bakin cikinku kai da ubanka ya kassarani?"

Abinda bata sani ba, abinda inda ta nutsu zata gane ya faru, yanda Haris yayi shiru yana shanye duk abinda take fada batare daya kashe wayarshi ba, ai tasan ko fada takeyi masa zai kashe wayarshi gabaki daya, idan ma a gabanta yake zai fadi abinda yake ranshi ne, koya tashi ya bar mata dakin. Amman sai da ta gama tas tukunna yace mata

"Kiyi hakuri..."

Cikin sanyin murya kafin ya kashe kiran. Zuciyarshi na bugawa saboda bacin rai, dan saida ya shiga gidan, yaji dadin ganin Maryama da Awwab na bacci, ya duba inda yayi ajiyarshi ya nada wiwin ya busa tukunna ya dan samu kanshi ya fara sauka. Shifa Maryama ce tasa ya daina kashewa Hajiya Rumana waya, shima ranar irin ihun da takeyi har Maryaman da take gefenshi saida taji, daya kashe saita bishi da kallo

"Kashe mata waya kayi Ganja? Mamin? Tana magana ka kashe wayar?"

Ya kalleta shima

"To me zanyi idan ban kashe ba?"

Tace masa

"Bakomai"

Amman ga mamakinshi saita dauke masa wuta, sosai ya kasa gane kanta, saida sukayi rigima sosai tukunna tace

"Me zance maka to? Kasan hakkokin uwa akan yaranta? Kana kashe mata waya so kakeyi ka jefamu a matsala? Ko bakasan yanzun rayuwarmu hade take ba? Abinda zai sameka zai sameni?"

Hajja ma haka tace mata, idan bata tayashi yayiwa Mamin biyayya ba su dukane zasu sha wahala, rayuwarsu ta riga ta hade waje daya, dole ta saka shi yayi mata alkawarin ba zai sake kashe wayar Hajiya Rumana ba duk fadan da zata dingayi, kuma zai dinga yin shiru in tagama ya bata hakuri. Wani abin ma mamaki yake bashi idan yaga wai shine Maryama take sakawa a gaba tana balbalewa da fada, gashi in tana cikin irin wannan yanayin sai dai duk abinda zaiyi mata yayi, ba zatayi shiru ba, har tsalle takeyi kamar zata kama shi da kokawa, yar yarinyar da zai iya rabawa gida biyu.

Kamar yanda Munira tace masa zataje, kwana uku da haihuwar Maryama ta sauka a kasar New York, da akwatinta shakare da siyayya, amman ko kadan baiji dadin yanda tayiwa Maryama dibar karan mahaukaciya ta watsar ba, muryarta can kasan makoshi ta amsa gaisuwar da Maryaman tayi mata, dan cikakken kallo ma baiga tayi mata ba, data dauki yaron sai ta wani sauke numfashi

"Kasan addu'ar da muka dingayi da Anisa, Allaah abinda za'a haifa karya yo mana kwashe-kwashen wasu kamanni can, sai gashi yayi kama da kai"

Shi dai Haris daya kalli Awwab baiga kamannin da tace ba, da alama dai yaron zaiyi baki, amman fuskar Maryama yake gani a tare dashi

"Nikuwa fuskar Mamanshi nake gani fa"

Ya amsa kanshi tsaye, Maryama tana jinsu

"Allaah Ya kiyaye...inji wa? Kai kasan kamanni ne"

Taso tayi shiru, amman zuciyarta tafasa kawai takeyi, ai daman itama bawai sunyi mata ba, Haris dinma sai da tasan shi, ya fara mata kirki tukunna ta tsame shi daga jerin masu bakar zuciya kamar bakaken fuskokinsu

"Ai ba sai yayi kama dani ba, tunda ba zai canza cewa daga jikina ya fito ba, to Alhamdulillah, fatana dai ya dan haska, kar yayi bakikirin din nan...shine bana so"

Haris yayi murmushi mai sauti

"In Shaa Allaah baki zaiyi, duka yaranmu bakake zamu haifo, tunda kike mun wulakanci"

Munira taji ta shake har makoshi

"Dariya maganar ta baka? Wannan ai zagi ne"

Kuma wannan fadan da Haris ya biyewa Munira sukayi ne yasa tace ba zata kwana a gidan ba, ta tafi ta kama hotel, dan ta daga akan Maryama ta zagesu, shikuma yace baiji sanda tayi zagi ba yana dorawa da

"Babu fa yanda za'ayi kizo gidanta kice zakiyi mata hayaniya, ba zan dauka ba"

Ta kara harzuka, Maryama tayi zaune, dan Haris ya gama wanke mata bakin cikin Munira, sai dai ko awa biyu da tafiya batayi ba sai ga Hajiya Rumana ta kirashi ta rufe shi da zagi

"Yar uwarka zaka wulakanta? Ai bansan ka gama mallakuwa ba sai yau Haris, wallahi ban yarda ba, da bana yarda da abubuwan nan..."

Sai kawai ya zabi ya karya alkawarin da yayiwa Maryama, ya kashe wayarshi, dukanta, Munira bata dawo gidan ba, daga can ta wuce, bai kuma nemeta ba, kamar yanda ya fadane, in ma Anisa da tace masa tare da Alhaji Mustafa zasu zo in zaizo niyyarta kenan, tazo tace zatayi wa matarshi hayaniya, yana fatan Munira ta gaya mata, zasu kwashi 'yan kallo

"Na karba Baba, na karbi auren"

Haka yace, kuma yana nufin kowacce kalma, a cikin wannan karbar akwai mallakar Maryama, a cikin karbar aurenta akwai kareta daga dukkan abinda zai iya, ko da abubuwan nan sun hada da 'yan uwanshi

Hajiya Rumana ce kawai zai cire daga wannan lissafin, ita kadaice zaiyi hakurin dole da ita, tunda wadda zaiyiwa fadan ma in taji ba zasu kwashe da dadi ba

Hajiya Rumana ya cire,
Ya manta da kanshi, a jerin abubuwan da ba zai iya kare Maryama daga su ba...

Haris ya manta bai cire kanshi ba!

33

Da sunyi waya da 'yan gidansu sai suce mata

"Ya New York?"

Ba zatace ga adadin sau nawa akayi mata wannan tambayar ba, amman duk sanda za'a tambayeta sai ta dauki wasu yan dakika tukunna take iya amsawa da

"Alhamdulillah"

Tunda tasan abinda suke fatan suji kenan, kuma shi take fada musu, a shekarunta biyu yanzun a kasar, wani lokacin inta na kwance tare da Awwab su kadai a gidan, Haris baya nan, sai tambayar ta fado mata a rai, to ya zata amsata idan zata fadi dukkan gaskiyarta? Ta ina zata fara? Da kanta zata fara? Babu inda take zuwa saita kama dole, daga cikin dolen kuwa asibiti ne, yawanci ma Awwab ne, kuma bata taba zuwa ita kadai batare da Haris ba, sai kuma wani lokaci idan kadaicin ya isheta saita fito waje, a hakane ma suka saba da Chloe sosai, dan har yaranta tana barwa Maryama ta danje siyayya ta dawo.

Sai kuma wata rana sukan dan zagaya cikin unguwar, daga can kasa ma akwai wani dan park da zaka iya kai yara, to dansu motsa jiki sai suke takawa da ita da Chloe, ba karamin tashin hankali sukayi da Haris ba kafin yake barinta wannan fitar, sau daya a sati, tunda tsautsayi yasa sun fita tare take ce masa

"Nifa tunda nazo kasar nan banda kai banga baki ba, mazansu duk farare ne"

Kalar kallon da yayi matane ta gane cewa tayi kuskure, sai kuma da suka koma gida baiyi mata magana ba, lokacin ta fara ganeshi, ta fara karantar abinda ya zabi yayi mata shiru akai ta cikin idanuwanshi dama yanayin shi. Gabaki daya ta kasa sukuni, zuciyarta ta dinga bugawa, tana taradaddin zuwan dare, tunda wani hali data kula ya dauka idan yayi mata shiru haka shine ya huce haushin nashi akanta, ya gayawa jikinta abinda bakinshi bai furta ba, bataso, batasan wannan horon da yakeyi mata, tayi masa magana harta fara gajiya ma, sai kuma ya bude drawer din dakin nasu, batasan me yaje yi ta bangaren kayanta ba ya juyo yana ce mata

"Waisu wannan turarukan da kika zo dasu, meye amfaninsu idan ba zakiyi amfani dasu ba?"

Tunda bayan kayan sakawarta, spices din shayi, bata dauko komai ba sai turarukan da kuma turaren wutarta na Meens_incense, cancana shi takeyi sosai, tasan ita da sake samunshi sai dai in sunje ganin gida. Ta kalli daya daga cikin kwalaben daya daga, turarukan nan ne, wanda Ishaq ya bata, tun daga Kaduna ta dauki abinta har Kano, kuma bata taba fesasu ba, duk sanda zata bude wardrobe din kayanta zata ganshi, saiya zama wani abu data mallaka, wani abu nata. In zakace mata me yasa ta jefasu cikin kayan da zata taho dashi bata sani ba, kuma har kasan zuciyarta ta manta rabon da ko a tunani Ishaq yazo ranta, ko da kuwa taga turarukan nan ne. Yaushe ma ta samu lokaci? Tsakanin hidimar Awwab da bata karewa, danma Allaah Ya taimaketa bashi da rigima ko kadan.

Ga kuma hidimar Haris din in dai yana nan, naniqar da yakeyi mata ma bata barinta wani tunani, kusan ma zatace gabaki daya ita yanzun tanajin babu kowa a rayuwarta sai shi kadai, bata da wanda zata juya ta kira da nata sai shi da Awwab

"Zanyi amfani dasu"

Ta amsa shi cikin sanyi murya, sai kuma ya fesa a bayan hannunshi

"Karya ne"

Ya fadi yana dorawa da

"A ina kika siya?"

Dan kamshin wanda ya fesa din yayi masa dadi

"Bani akayi"

Bata taba son ace ta iya karya ko boye-boye ba sai da Haris ya kalleta yace mata

"Waya baki?"

Muryarta can kasa tace

"Hamma Na"

Kuma batasan ko wani yanayi ta nuna da ya saka shi tsayar da hankalinshi kacokan akanta ba

"Wanne a ciki?"

Taji muryarshi, tayi kasa, yanda takanyi idan wani abu na gab da bata masa rai

"Baka sanshi ba, gidansu daya da Adda Khairi..."

Cewar Maryama cikin rawar murya, da yake kallonshi takeyi, tana ganin lissafin da yakeyi, yanda yasan kowa da kowa na gidansu, wanda suke uwa daya uba daya dama wanda suke abokan wasanta har mamakinshi takeyi

"Hammanki....kikace Hammanki Maryamm?"

Ta sauke idanuwanta

"Turaren wani kato kika dauko tun daga Nigeria har New York? To ajiyar me kikeyi musu ma tun daga farko? Akan me zaki ajiyesu? Yaushe ya baki? Ko Khairin ya aiko dasu bansani ba?"

Da saurinta ta girgiza masa kai

"A'a, sun dade, tun kafin aurenmu"

Sauran turarukan ya kwaso, tana kallonshi ya kama hanyar kofa, idanuwanta suka cika taf da hawaye, daga inda take tanajin karar fashewar kwalaben nan, kafin kuma shiru ya biyo baya. Ranar ya dauki mintina kusan talatin kafin ya dawo dakin, daya hawo gadon inda take, taji kaurin wiwi dinshi, sai dai bataso tace masa komai, ita numfashi mai karfi ma bataso tayi saboda dare ne, saboda a yanayi irin wannan Haris yana bata tsoro. Sai dai a karo na farko ya saka tazara a tsakaninsu, sai hakan ma yafi bata tsoro

"Kiyi mun shiru Maryamm, ni banyi kuka ba kece zakiyi kuka?"

Ya fadi saboda sheshekar da takeyi, kirjinshi zafi yakeyi, yasan yana da kishi, amman baisan cewa kishin nashi ya wuce misali ba haka, sai da yaso buga mata daya daga cikin kwalaben turaren nan

"Ya sunanshi?"

Tambayar ta kwace masa, taji shi, saida ya sake maimaitawa tukunna

"Ishaq"

Ta fadane saboda tasan tunda ya tambaya dole saiya samu amsar zai kyaleta
Ta fadane saboda bata hango hakan zai zame mata wata gagarumar matsala a shekarun da zasu zo ba

"Saurayinki ne?"

Ta girgiza kanta, ita ai batama tabayin saurayi ba, duk da 'yan gidansu sun sha kiran Ishaq din da saurayinta, amman tunda babu wata kalmar so data gifta a tsakaninsu ba zata kirashi da saurayinta ba

"To me yasa? Zaki ajiyemun abinda ya baki a daki? Me yasa ma zaki ajiye duk tsahon lokacin nan?"

Shiru tayi tunda bata da amsar da zata bashi, shima bai sake ce mata wani abu ba, washegari data gaishe dashi bai amsa ba, baiyi mata magana ba sai da ya gama shiryawarshi, tukunna yace mata

"Ki duba kiga babu abinda kuke bukata?"

Ta girgiza masa kai kawai, idan ma akwai tayi order din abinta a kawo mata har kofar gida

"Karki fita ko ina, ina nufin ko ina"

Kan dai ta sake daga masa tana kokarin kar hawaye ya balle mata tunda in bata fita ba ai ba zata mutu ba, karshen dai abinda zaiyi mata kenan ya kulleta cikin gida

"You are mine Maryamm"

Haka yasha fada yana maimaita mata, idan wani yaji yanda yake fadar kalmomin, sai yace zai tayata murna, saiya zata wata zazzafar soyayya ce taja hakan, kamar yanda itama tayi tsammani ranar daya fara furta mata, dan wani irin abune ya taso yayi mata rumfa, tayi kwanaki tana jujjuya kalaman suna kuma yi mata dadi, amman yanzun ta fara gane ba kalaman soyayya bane ba, na nuna iko ne, na mallaka ne, ita din tashi ce, yayi yanda yake so da ita. Shisa in wani abu ya hadasu saiya zabi ya kulleta cikin gida da kalamanshi, dan yasan baya bukatar amfani da mukulli dan yin hakan, bata isa ta fita babu izininshi ba.

Idan ya zauna gidan saiya kara janye mata kanshi, Awwab din da zaiga ta shiririce ta biye masa, saiya zo ya dauke shi yayi daki dashi, ko in suna dakin su fiti falo, ko suma fita su bar mata gidan. Wata rana mamaki ya kamata, in ta kyaleshi. Zata so ace zata iya ba Hajja labari inta tambayi ya suke, labarin Haris da taurin kanshi, in ta kare bada labarin ta rufe shi da fadin

"Hajja kinga wanda ya fini taurin kai ko?"

Tunda ita fadanta ma yafi kafiyarta, to fadan kanshi hayaniya kawai

32 / 51