Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
Awwab na da passport ne?"
Kafin Haris ya amsa ta rigashi da cewa
"Eh"
Dan anje anyi masa, saboda lokacin suna saka ran yin tafiya kafin tazo ta samu wani ciki
"To Alhamdulillah"
Wani murmushin takaici ne yake neman kwacewa Haris
"Baba babu fa inda zataje"
Kallonshi Alhaji Mustafa yayi
"Ni ka tashi ka dauko mun passport dinsu ita da Awwab din kafin ranka ya baci"
Alhaji Sa'id ne ya saka baki
"Daka tsaya anbi abin nan a hankali Mustafa"
Cikin bacin rai yace masa
"Nasan kai ka haifi Maryama, amman daga randa ka na karbawa Haris aurenta na karbeta ne duka daga hannunka, saboda haka babu ruwanka, kafata kafar 'yata zamu bar New York, ba kuma shawarar wani nake nema ba"
Haris daya mike tsaye yace
"Amman dai gaskiya Baba idan akayi mun haka ba'a kyauta mun ba, saboda nima bana ce ba zataje gida bane ba"
Kokari yakeyi karya fadi duka abinda yake ranshi, saboda Alhaji Sa'id
"Ba zan sake maka magana ba, kaje ka daukomun passport dinsu, idan kuma ban isa ba saika nuna mun"
Yayi tsaye, kusan mintina uku, saida yaga Alhaji Sa'id ya daga ido ya kalle shi, wani kallo da baisan ya akayi yaji kafafuwanshi sun motsa ba, sai gashi a daki, inda ya adana duka passport din biyu, ya dauko yazo ya mikawa Alhaji Mustafa, zuciyarshi na tafasa kamar zata kama da wuta
"Ma Shaa Allaah, bari muzo mu koma masaukinmu, ki karasa shirya komai dai, dan zan duba mana yiwuwar mu samu tikitin safe"
Cike da murmushi take daga kai tana kuma amsawa da
"To Baba, ai kayan Awwab ne ma kawai, nagode, Allaah Ya kara lafiya"
Wannan karin itace ta rakasu har kofar gida, data dawo kuma sai ta samu Haris a tsaye inda suka barshi
"In dai a karkashina kike ban yarda ki taka ko ina ba Maryamm"
Ko inda yake bata kalla ba, ta koma ciki abinta, kuma tun yana hargagi, harya koma lallashi, amman Maryama taki tayi masa magana, da daddare da ta kwanta a falo kan kujera yazo yayi yunkurin mayar da ita daki saita saka masa ihu tana kokarin ja makota su kirawo musu 'yan sanda
"Meye haka? Meye haka wai Maryamm"
Ta watsa masa harara
"Wallahi inka sake ka hadamun jikina da wannan bakin jikin naka mai dauda saina maka ihun da makota zasu kira maka 'yan sanda, in bakayi wasa ba kana police custody zamu bar kasar nan, dan ba zan fadawa kowa kana hannun 'yan sanda ba"
Yayi tsaye yana kallonta, ta murguda baki ta sake watsa masa harara
"Yanzun ba zaki nutsu muyi magana ba, ashe zaki iya tafiya kibarni, ashe zan miki laifin da ba zaki bari in baki hakuri ba balle ki yafemun"
Ta kwanta kawai tana juya masa baya, hakurin me zai bata? Wanne irin hakuri? To inya bata hakuri zai goge mata abinda ta gani ne? Ko zai wanke mata cutar da yayi na gauraya mata jiki da nashi da yake cike da daudar zina? Ganin ta juya masa bayane yasa shi karasawa ya zauna a kujerar, cikin zafin nama kuma yasa hannunshi yana toshe mata baki, ta kuwa gartsa masa cizon daya sakashi sakinta babu shiri, filon kujera ta dauka ta shiga maka masa duk inda hannunta yakai, kuka takeyi, irin kukan nan mai gunji
"Dan Allaah Maryamm"
Yake fadi cikin karyewar murya, duk da baya wani yunkuri na kare kanshi daga dukan da take kai masa, in dai zata huce
"Dan Allaah karki barni, karki bari Baba ya tafarmun dake, bansan ya zanyi ba"
Da kanta tagaji ta jefar da pillow din, ta sauka daga kujerar tana komawa kasa kan kafet ta kwanta, har lokacin kuka takeyi sosai, wani irin zafi kirjinta yakeyi mata, ita batama taba sanin wani ciwo makamancin wannan ba. Daya sauko kasan karfinta ya riga ya kare, shisa ta kasa hanashi ya dagata ya hada da jikinshi
"I'm sorry, dan Allaah kiyi hakuri"
Shine abinda yake furtawa yana sake maimaitawa, yana rocking dinta a jikinshi, har baccin wahala ya dauketa, ya mike da ita yaje ya kwantar a gefen Awwab, shima ya hau gadon ya kwanta, yana fatan gari ya waye musu da sauyawar zuciyarta. Sai kawai ta karya masa tashi da safen data shirya, ta kuma shirya Awwab ta fito musu da akwatina guda biyu matsakaita, nata dana Awwab, ta kuma sake karya masa zuciya lokacin data mikawa Alhaji Mustafa akwatinan bayan sunzo da mai taxi
"Maryamm"
Ta juya, ta kalle shi, idanuwanta cike da hawaye, sannan kuma ta sake juyawa ta murda handle din kofar, dan Alhaji Mustafa ya dauki Awwab ne ya barsu
"Ga wayarki"
Ya fadi cikin wata murya data kasa ganewa, saita tsaya ta sake juyawa ta karbi wayar, ya karasa hade takun da baifi uku ba daya rage a tsakaninsu, ya sumbaci gefen fuskarta
"Kiyi mun alfarma ki zauna a gida, a gidanmu, dan Allaah, zan taho dana gama exams dina...ki kulamun da kanki, karkije ko ina"
Harta bude kofar saita sake juyowa, hawayenta suka zubo, tasa hannu ta gogesu, zuciyarta zafi takeyi, zuciyar nan dai da akace guda daya kowa yake da ita, amman kuma a yanzun ba ko ina bane taji yana mata tururin, akwai wani sashi da yayi sanyi da yanayin Haris, da abinda take gani cikin idanuwanshi
"Zanje gida, Kaduna"
Ta tsinci kanta da furtawa cikin rawar murya, ya daga mata kai
"Karki dade, dan Allaah Maryamm, karki dade acan"
Batace masa komai ba ta taka kafarta waje
"Maryamm"
Ta juyo
"Ti amo..."
Tasan batajin yaren Italian, amman wannan matsala ce data shafi kwakwalwarta, dan kuwa zuciyarta a bude ta karbi abinda ya fada, ta kuma fassara mata
"Ina sonki"
Ya dan dafe kirjinshi da hannu, ya bubbuga a hankali
"Da yawa...."
Ya sake fadi, a karo na farko, yana ba kanshi mamaki, saboda kalma ce da bata taba giftawa a tsakaninsu ba a shekaru hudun nan
Sai yau
Sai yanzun...
Kamar kuma zuciyarshi ce bata gama tabbatarwa ba din sai yau, da ta bi bayan Maryama data shiga taxi din nan, kuma ko da suka bacewa ganinshi, ya riga yasan ta tafar masa da kanta ne, a yanda yakejin kamar bashi da komai a kasar New York, yasan ba iya zuciyarshi Maryama ta tafi da ita ba...
Harda wani sashi da Haris baisan sunanshi ba!
37
KADUNA
Tasan daga zuwanta, a cikin kwana biyun nan inda akwai wani adadi na hawaye da ake warewa kowanne dan adam a cikin kowacce rana, ace in bakayi amfani dashi ba shikenan, to tabbas da ta gama karar da nata, Hajja ta fara gani lokacin da suka isa gidan, tana dora idanuwanta akanta, taji shekaru goma sha daga cikin nata sun murmushe sunbi iska, a wannan lokacin, ta manta da wani abu wai girma, ta manta da auren da yake kanta, ta manta da ta haihu, ta manta tana shirin sake zama uwa a karo na biyu
"Sufa iyaye ba'a girma da bukatarsu Maryama, ko shekara 100 zakayi a duniya babu wata rana da zaka wayi gari a cikinta kaji baka bukatar iyayenka"
Haka Khairi ta taba fada mata lokacin da suka jewa Malaminsu na Islamiyya gaisuwa taga idanuwanshi duk sun kode, kamar wanda yayi kuka, take mamaki, tunda shi kanshi zaiyi shekara arba'in da wani abu, kuma akwai wanda tagani a wajen da ta sukayi kama dashi, kuma tasan sun girmeshi, to a ganinta kukan me zaiyi? Shi da ba yaro ba? Sai yanzun ta gane, kana kara hankali ne kana kara gane muhimmanci iyayenka da rawar da suke takawa a cikin rayuwarka, dan a ranar so tayi ta ruga, da gudunta ta fada jikin Hajjan, amman nauyin kewarta daya danneta sai ya sauka har cikin kafafuwanta yana hana mata yin wannan gudun, kuma nauyin ne ya tunkudo hawayenta wani na biye da wani.
Ta dinga kallon 'yan uwanta da yanda suka cika gidan washegari, masu auren, yara daga makaranta duk an kawosu nan, kuma wai saboda su ganta, suyi mata barka da zuwane sukayi wannan taron, itafa, Maryama, karamar kanwarsu da a cikinsu babu wanda baya gajiya da gaya mata rashin hankalinta a lokutta mabanbanta, amman yau sune suka jingine komai na rayuwarsu suka zo don ita, kowa kuma da abinda ya riko naci ya taho mata dashi, harda mazan kuwa, ta dinga fakar idanuwansu tana share hawayenta, tarin kaunarsu na sake samun sababbin wajaje a cikin zuciyarta
Cikinta rabon da taji shi ya cika irin na ranar harta manta, saboda kowa mika mata wani abu yake
"Meatpie din nan yayi dadi Maryama, kinji kuwa?"
Saita karba, kome suka bata, saita karba ta saka a bakinta, Awwab kuwa ba zatace waye ya fice dashi a cikin mazan gidan ba. Ko kadan baiyi musu kwiya ba. Duk basu fara barin gidan ba sai bayan isha'i, ita dai sun zauna a falo suna cigaba da hira har wajen goman dare, kafin ta yiwa Hajja sallama, suka shige nasu dakin ita da Khairi, da suna shiga ta rufe kofar ta juyo tace mata
"Ki fara magana yanzun nan"
Abinma sai yaso ya bata dariya, duk da wani abu daya taso mata, wani abu da ganin kowa ya danne
"Adda Khairi..."
Ta kira sunan muryarta na karyewa, wannan tiririn da ta taho dashi tun daga New York yana tasowa ya sake rufar mata, sai Khairi tazo ta kama hannunta ta jata suka zauna a gefen gadonsu, wasu hawaye masu zafin gaske suka tasowa Maryama
"Bansan ta inda zan fara ba, inajin kamar maganganun da nake ta adanawa in cigaba da rike su..."
A hankali Khairi ta jinjina mata kai
"Idan kina so ki rike, kinsan zan fahimta, ko a tsakaninmu, ni da ke, dole zai zamana muna da sirrikan da zamu adana, amman nice Maryama, sirrinki har abada nawa ne duk lokacin da kika zabi ki rabashi dani"
Nata kan Maryama take jinjinawa, ta sani, data kalli Khairi sai tace mata
"Kinsan me yasa ake cewa Haris Ganja?"
Khairi ta girgiza mata kai, itama zuwansu New York ne ta saka shi a gaba da tambaya
"Me yasa ake ce maka Ganja? Kaji? Dan Allaah"
Yayi murmushi
"Kin tabbata kina so ki sani?"
Da saurinta ta daga masa kai
"Eh mana, sunan yana mun dadin fada, dariya yake bani kuma"
Sai shima ta bashi dariya, yana son wannan barin zancen nata, yanda take fadar duk wani abu da yake zuciyarta batare da ta tsaya ta juyashi ba
"Lokacin da na fara...dana fara shan weed, mu duka muna sha, Ni, Barde, Lalaye, 2Pac...saiya zamana babu wanda yake shan yawan da ni nake iya sha batare da yasa sun zama high sosai ba, yawan wanda zan sha inyi hidimata batare da kowa ya gane nasha wani abu, in su suka sha tsaf za'a gane harma ya iya zame musu matsala, shisa suke ce mun Ganja..."
Haka ta maimaitawa Khairi, abinda Haris ya fada mata, tana dorawa da
"Sai dai na dauka shine kawai matsalarshi, wiwin, tunda yace mun wani abu daban na maye bai taba burgeshi ba...kuma na yarda, ko da zai boyemun, dana tambaya, tunda ya bude bakinshi ko ba zaimun dadi ba zai gayamun gaskiya"
Ta numfasa saboda zafin da zuciyarta takeyi, saboda abinda ya dawo mata
"Bashi kadai bane Adda, harda mata.."
Khairi tayi mata wani dogon kallo
"Tarayyar namiji da mata kala-kala ce Maryama, dan kinga wani chatting, ko kiran waya zai yiwu wayar ce kawai, chatting dinne kawai, ba zaki taba raba rayuwar kowanne namiji da wasu matan ba"
Maryama tayi wani murmushi mai ciwon gaske
"Kince inyi surprising dinshi, in bashi mamaki, inyi masa ziyarar bazata, naje, nayi masa ziyarar Adda amman nice na sha mamaki, bazatan da zanyi sai akayi mun, naga abinda nasan mutuwa ce kawai zata goge mun shi...ba chatting nagani ba, kafin kuma kice wani abu, a samanta naganshi, kuma baiyi musu ba, a karo na farko da naso ko karyace ya kalleni ya fadamun, bai musa ba Adda....mijina mazinaci ne....mijina"
Ta karasa hawaye na sake balle mata, wai kalmar da ko kiranta bata so ayi, ko a Islamiyya ake musu karatu da aka tabo zina da hukunce hukuncenta sai taji kamar kasa ta tsage ta shige ciki, in aka gama sai ta bude ta fito da ita saboda yanda take jin munin kalmar a kunnuwanta, littafi kuwa duk dadinshi ficewa yakeyi daga ranta in dai za'ace akwai mazinaci a ciki, saboda bataso ma ace yana da mata, balle kuma akai ga ranar da zata gane irin mijin da take aure, sai ta dinga jin kamar ita, ta dinga jin kamar numfashinta zai iya tsayawa, haka ma take hasashe cikin kanta, inta auri mazinaci ta gane, zuciyarta bugawa kawai zatayi ta sama mata hutun mutuwar da ta tabbatar zata bukata. Ashe wani abin hasashe ne kawai, wani abin baka sanin me zakayi saiya faru da kai.
Gata nan zaune, harma ta bude bakinta tana bada labarin cewar bawai zina kawai mijinta yakeyi ba, ita da kanta ta ganshi, ta ga wata akanshi a zaune. Kuma wai bata mutu ba har yanzun, numfashi takeyi, dazun ma da ita aka dinga tuntsira dariya a tsakanin 'yan uwanta, a cikinsu, da suka kalleta babu wanda ya gane tayi birkidedeniya da mazinaci, babu wanda yaga ko wata alama na cewa igiyoyin da suke kanta na aure, auren daya sama mata wannan datajar a wajensu yau, darajar da tasa suka taso tun daga gidajensu da sunan yi mata sannu da zuwa, daure suke gam da mazinaci, dan wiwi. Lallai ne da akace aure sirri ne dashi.
Har masu azancin magana ma sai suce ai shi auren Labule ne, labule kuma asirin mai daki ne, duk da a zahiri, kowa in yazo kofar dakin nan, ko babu neman izini zai iya saka hannu ya daga Labulen nan, amman kuma akwai wani Labulen na daban, wanda hannuwan da ba mammalakan dakin nan ba basu isa su iya daga shi ba, shine sirrin, sirrin mai dakin da ake cewa, babu kuma wata mace da zatace bata da wannan Labulen a gidanta na aure, ai yau da gobe babu wani abu data bari, ko da kuwa in ta zabi ta daga Labulen nan babu zina balle wiwi a cikinshi, amman akwai hakuri, hakurin yau da gobe mai zuwa da tarin sadaukarwa, hakurin nan da kowacce mace take kamanta shi a ranaku mabanbanta a zamantakewar aurenta.
"Maryama..."
Muryar Khairi ta kurda cikin kanta
"Nasani, baiyi kama da ko daya ba? Mazinacin, dama dan wiwi"
Sunanta dai Khairi ta sake kira, itama hawaye na zubo mata
"Kibari, ki daina...dan Allaah, mijinki ne har yanzun, ki daina jingina masa wannan kalmomin"
Takai hannu ta share hawayenta, duk da wasu sun sake maye gurbin wanda ta goge din
"Bani na jingina masa ba Adda Khairi, da abinshi na same shi daman, ban dai gansu bane ba sai daga baya...saboda siffarshi ta iya adana masa su"
A zaune Maryama take, amman ji takeyi kamar bakin cikin da yake taso mata zai iya kayar da ita
"Haka yace yana sona, da zamu taho, yace yana sona, bai taba fadamun ba, me yasa sai da naganshi da wata tukunna zai gayamun? Toni me zanyi da wannan son yanzun? Ya zanyi dashi Adda? Ya zanyi da zuciyata da ta karbarmun shi duk da bana so? Me yasa tunda ya fadamun muryarshi take ta dawomun? Ya zanyi? Na fada masa ba zan zauna ba, shisa nayiwa ba Baban Tudun Wada magana sai suka taho dani, tun dana fito daga gidan nake jin kamar ba gabaki dayana na fito ba, kamar akwai wani abu dana bari a wajenshi..."
Maryama take fada a numfashi daya, da Khairi ta riko hannunta sai ta kalleta, cikin idanuwa tace
"Na haukace ko Adda? Ganjaa ya haukata ni"
Kai Khairi take girgiza mata, idanuwanta cike taf da wasu sababbin hawayen, akwai kalmar da bature zaiyi amfani da ita a yanzun in da zaiga Maryama
"Broken"
Amman kuma a shimfide a kasan wannan kalmar, a dacin da yake fita a sautinta akwai soyayya, soyayyar Haris, irin soyayyar nan da maiyinta baisan da zamanta ba balle kuma girman wajen da ta mamaye a tare dashi
"To me na bar masa? Na taho da Awwab, ga cikina na taho dashi, kuma babu abinda nake so irin inyi nisa dashi, inyi nisa da New York, gani na samu abinda nake so amman bai nutsar dani ba, inajina a firgice tun jiya, bansan ya akayi nayi bacci ba saboda inajin ban taho gabaki dayana ba Adda, kirjina ciwo yakeyi mun, I don't feel whole, shisa nace miki na haukace, ya zan bar abinda ban san menene ba?"
Khairi ta goge tata fuskar, ta danyi gyaran murya saboda makoshinta da takeji a tokare da tausayin Maryaman
"Kinyi magana dashi? Kunyi waya tunda kika sauka"
Ta girgizawa Khairi kanta
"Ina wayar taki?"
Tana cikin jakarta, a kashe take ma, ko kunnawa batayi ba
"Tana cikin jakata, ban kunna ba...tunda mukazo ban kunna ba"
Jakar tana nan dakin nasu, Khairi da kanta ta tashi ta bude, tana kuma dauko mata wayar ta koma kan gadon ta mika mata
"Ki kunna yaji kin sauka lafiya"
Ta karbi wayar, tayi shiru tana kallonta, a hankali ta kunna, sau nawa a zuwanta Haris ya sauya mata waya, haka kawai ba dan tayi wani abu ba, inya bushi iska saiya karba ya sai mata sabuwa, kuma wayar tana gama loading, sai taga babu network, ta kuma tuna ba layin Nigeria bane a ciki
"Sai dai ki aramun wayarki inyi masa text"
Cewar Maryama a hankali, cikin muryar da zaka gane yawan kukan da tayi duk da bashi da sauti, wayar Khairi ta dauko ta bata, akwai ma lambar Haris din a ciki, dan haka ta tura masa gajeran sako
"Mun sauka, muna lafiya mu duka ukun"
Sai ta rubuta sunanta daga kasa, kuma sakon yana shiga kamar Haris yana jiranshi ne sai ga kiranshi na shigowa, taji zuciyarta ta mulmule tayi wata mirgina kamar tana neman hanyar guduwa, wayar tayi mata nauyi a hannu
"Kira yakeyi, shine yake kira"
Khairi ta danyi murmushi
"Ki daga"
Tayi maganar tana mikewa ta fice daga dakin, lokacin kiran ya yanke, amman harya wani ya kara shigowa, ta daga tana saka wayar a kunne kamar mai tsoron zata cijeta
"Maryamm"
Haris ya kira, a yanayin da sautinshi ya fita, numfashin daya sauke mata cikin kunne, da tarin tazarar da take tsakaninsu bata hanata jin gajiyar da take tare da muryar ba, bata hanata fahimtar abubuwan daya fada batare daya furta ba
"Nayi kewarku, nagaji, babu abinda ya shiga cikina banda hayaki, me yasa kika tafi? Me yasa zaki tafi? Ki dawo"
Duk wannan, dama wasu masu yawa, taji su, ta kara kankame wayar
"Me yasa bakaci abinci ba? Ba zaka daina bankawa cikinka hayakin nan ba ko Ganjaa? Ka manta me likita yace?"
Ya sake sauke numfashi
"Maryamm"
Ta girgiza kanta
"Bacci zanyi ni, dare yayi mu anan, kwanciya zanyi, kaje ka samu wani abu kaci, ba shayi