Advertisements
Chapter 41 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   41 / 51

120K to 123K   out of 151K words

bakinta, Haris da bai taba ganin abinda ya bashi tsoro irin wannan ba, ya yunkuro har yana hadawa da rarrafe daga kan gadon da niyyar kwacewa, ta matsa baya

"So nake inji abinda kakeji ne da ka kasa bari..."

Ta fadi da wiwi din rike a hannunta, yasha ganinta a hannun mata a kasashen da yake zuwa, kai a cikin matan da yake bi ma anan gida Nigeria ba zaice yaga masu sha ba, amman yaga masu shan shisha sosai, kuma abin bai taba saka shi yaji dar ba, wiwin nan a hannun Maryama, wani abune da baya fata Allaah Ya sake nuna masa makamancinshi

"Maryamm..."

Tayi wata dariya da yaji sautinta ya hargitsa masa ciki

"Wai mu hadu mu kashe kanmu tare, tunda na karbi kaddarar aurenka, naji zan zauna da kai da abinda kake aikatawa, kuma baka shirya bari ba, gara kawai mu dingayi tare, randa abin ya isheka sai kayi mun magana mu bari tare, in kuma kayi nasarar kashe mu gabaki daya shikenan duk mun huta"

Daya kara takawa saita daga wiwin tana kaiwa bakinta

"Dan Allaah..."

Cewar Haris muryarshi na rawa

"Cikine a jikinki"

Ta dan daga masa kafadunta

"Ka damu da cikin ne? Cikin da kake shirin mayar da abin cikinshi maraya?"

Cikin saurin da baisan yana dashi ba ya karasa ya fisge wiwin, bai damu da zafin daya ratsa masa har tsakiyar kai ba saboda ya murje wutar ne sa yatsunshi biyu, ya rike Maryama da ta kamashi da kokawa tana kokarin karbar wiwi, da ta fisge jikinta saita nufi kan gadon inda ta zube wadancen, ya rufa mata baya, yanda suke kiciniya yana fadin

"Kibari, Dan Allaah, kar in buge miki ciki, Maryamm cikine a jikinki"

Amman taki saurarawa, dambe takeyi sosai dashi, saida yasa karfi ya kwantar da ita a gadon, kamar wadda batajin nauyin cikinta, ko ta manta dashi haka tayi yunkurin hantsilawa, ya rikota shima yana hawa gadon, sai kawai tabi ta zauna a cikinshi, ta kuma janyo pillow daga kan gadon tana fara maka masa, hawayenta na zubowa, kokarin karewa yakeyi, yaji ta danne masa kai da pillow din

"Bari kawai in karasa ka da kaina Ganjaa..."

Yasan Maryama bata da hankali, yasan in tana jin rigima batada hankali, amman yau ya kara tabbatar da wannan rashin hankalin nata jin tana neman toshe masa malumfasa da gaske, dakyar ya iya janye pillow din nan ya wullar dashi gefe yana maida numfashi, tayi masa wani irin kallo

"Kana tsoron mutuwa daman? Kana tsoronta kake so ka kashe kanka?"

Numfashin dai yake mayarwa ga tarin da yakeyi da bashida alaka da danne masa kai da Maryama tayi, jijjiga jikinshi da yayine tunda huhunshi yana da rauni, da kanta ta tashi daga jikinshi, sauka daga gadon tayi niyyar yi, ya riko hannunta

"Maryamm"

Ta fisge, ya sake rikowa

"Wallahi in dai zaka sha wiwi a cikin gidan nan, zamu sha tare ne Ganjaa, idan kuma zaka fita ka dawo inji warinta a jikinka, zan nemi inda ake siyarwa ko ina ne in fara siya nima"

Ko bata rantse ba yasan zata aikata

"Maryamm"

Ta watsa masa harara, hawaye na zubo mata

"Ban zabi zama da kai in ganka kana kashe kanka duk rana ba Ganjaa, ba zan kalleka kana kashe kanka ba, ko mu sha tare ko kabari...saika zabar mana wanda kake ganin yafi dacewa damu"

Ta karasa tana fisge hannunta, a zatonshi sauka zatayi daga gadon ta fice daga dakin, sai yaga ta matsa gefe ta kwanta, ya dafe kanshi da hannuwanshi biyu, wani abune yake kai kawo a cikin kirjinshi

Baisan ta inda zai fara ba,
Ya dai san yaune ranar farko, kuma rana ta karshe da zai kara ganin wiwi a hannun Maryama, kome zai faru kuwa!

40

Bata taba sanin mutum zai iya yana zufa yana jin sanyi a lokaci daya ba sai a kwanakin nan, AC din dakin a kure take, haka fankar da tunda sukazo gidan bata ma tababi ta kanta ba ballantana ta kunna, yau ta hada masa

"Ina jin zafi Maryamm"

Ya fadi daga kasan barguna biyun data jibga masa, ta kai hannu tana goge hawayen daya zubo mata

"Dan Allaah mu tafi asibiti Ganjaa...kabari muje asibiti ko in kira wani yazo ya taimaka mana"

Idanuwanshi ma basa buduwa da kyau, a haka yayi mata wata dariya da ta kara mata tsoron da take tare dashi

"Ke kikace in zabar mana, me yasa zamu saka wani a tsakiya?"

Haka yake ta ce mata tun shekaranjiya, tasani, abune data bude bakinta ta fada, ko da sukayi fadan ranar, ko tace tayi fadan dashi, dauke masa wuta tayi, ta danyi mamaki data tambayeshi shi zuwa gida yace mata

"Ki gaishe dasu, kibi a hankali, karkiyi gudu, kuma daga gida karkije ko ina"

Ta duba wayarta yafi babu adadi, musamman da taga anyi la'asar, amman bata ga kiran Haris ba, sai taji ta kasa samun sukuni, sakewar da take tunanin zatayi cikin 'yan uwanta ma bata samu ba, wajen karfe shida ta kirashi, saida ta kusan yankewa tukunna ya daga hadi da kiran sunanta

"Da anyi Magriba zan dawo fa"

Ta tsinci kanta da fadi

"Alright, kiyi kula da tuki"

Ya karasa maganar cikin yaren Italian, bai dora da komai ba ya kashe kiran, tasan itace ta fara shareshi tun shekaranjiya, amman komin fadan da sukeyi, in zata fita, Haris na iyayi mata kira goma. Shisa data koma gidan, ta dinga kallonshi, shayi ma bai bukata ba, itace ta hada masa, ya karba yana furta

"Nagode"

A hankali, ta kalle shi, tagan shi yana rashin lafiya sau babu adadi, ta ga Haris ma a lokuttan da baya iya numfashi da kanshi, amman bata taba ganinshi a irin wannan yanayin ba, batama san akwai wani kyalli cikin maikon da idonshi yakeyi ba sai yanzun da bata ga wannan kyallin ba

"Me yake damunka?"

Ta tambaya, saiya daga mata kafadunshi kawai batare da yace komai ba, ta kyaleshi duk da zuciyarta batayi mata dadi. Haka suka kwanta, baiko matso kusa da ita ba. Washegari ya kama ranar alhamis ne, kuma ranar ne za'ayi kunshin bikin Khairi, juma'a za'ayi kamu anan cikin gidansu kamar yanda aka saba, washegari asabar a daura aure. Lokacin da ta gama shiryawa Haris na bacci, ta tabashi a hankali, ganin har tara da rabi

"Inaso in tafi gida, kasan yaune akeyin kunshi dan a gama mun nawa da wuri"

Kai kawai ya jinjina mata batare da yace komai ba, ta dan tsaya jim, sai taga ya sake rufe idanuwanshi, dole ta tafi cikin sanyin jiki, har Khairi saida ta tambayeta me yake damunta

"Ganjaa ne Adda Khairi, amman ba wani abu bane na tashin hankali"

Khairin bata matsa ba, to ko da taso ma ina take da lokaci anata hidimar bikinta? Ga dai yanda take so ta samu, kar Haris ya hanata zuwa gidansu ayi shagali da ita yanda ya kamata, musamman ma da Awwab na gidan Hajiya Rumana, sai ita da katon cikinta da takejin shine kawai abinda zai rage ma bikin armashi, ashe harda yanayin Haris. Haka akayi kunshin nan, yamma likis ta kama hanya, dan ana kiraye-kirayen sallar Magriba ne, har Fa'iza nace mata

"Anty dama mun tsaya munyi sallah sannan"

Ta amsa da

"Ai kam, sai muyi idan munje gida"

Tana kallon Fa'izar tana hura inda bai bushe ba a kunshin da akayi mata na bakin lalle da bakinta. Ta dibo musu abinci daga gida, yanda bayanta yake a riqen nan batajin zata iya dafa wani abu. Haris na daki a kwance, da tayi masa maganar sallah ya tashi yayo alwala, anan cikin daki yazo ya kabbara. Ta hadiye wani yanayi da yake taso mata, saida tayi isha'i tukunna tayi karfin halin hada masa shayi, ta zubo masa da samosa din da sukayi order wajen Zainab Kerau, amman shayin ma rabin kofi yasha, ya ajiye sauran, ba'ayi mintina biyar ba ya mike ya nufi bayi, jin yana amai yasa ta tashi da sauri ta same shi a bayin tana jera masa sannu

"Baka da lafiya?"

Ta tambaya, ya kalleta da wannan abin da batason gani a cikin idanuwanshi, wannan disashen abin

"Lafiyata kalau"

Ya amsa yana rabata ya wuce bayan yayi brush, ta biyoshi tana karayi masa sannun da bai amsa ba, a daren ne kuma taji yanda yake zabura, da farko ta dauka ma mugun mafarki yakeyi sanin in bata tsaya akanshi ba, ba addu'a yakeyi ba in zai kwanta, yau kuma da kanta ta tofa masa kawai. Data kunna kwan dakin sai taganshi ya hade jikinshi waje daya, akwai wani yanayi da ake fassara farar fata dashi, ace fuskarshi tayi fari tas, ya dashe kamar wanda bashi da jini, to a madadin wannan farin sai taga fuskar Haris tayi mata kamar ya kwaba toka da mai ya shafa, zuciyarta tayi wata irin bugawa.

Data girgiza shi a hankali ya motsa, ko tace ya kara zabura ne, fuskarshi ta taba, tayi sanyi, ga zufa yana hadawa, wannan daren yana daga cikin darare masu tsayi a wajen Maryama, tunda ko daya bude idanuwanshi ma ta tambayeshi ko wani abu nayi masa ciwo haka yace

"A'a, ki kyaleni dan Allaah"

Yana janye hannunta daga jikinshi ya juya mata baya. Washegari kuwa har karfe goma da rabi ta kasa fita daga gidan, sai da taga ya shiga yayi wanka ya fito wajen sha daya lokacin, tukunna ta tafi. Ta ari karfin hali tun a hanya ta sakawa fuskarta, ta dinga murmushin da takejin har kumatunta na amsawa, anyi mata kwalliya mai sauki, tace bayanta ya riqe saboda batajin zata iya wani kai kawo, waje daya ta samu tayi zamanta. Hajja ce ma tasa aka kirata wajen biyar da rabi

"Kinga kina fama da kanki, gara kizo ki tafi gidanki ki huta, Addarku tace kina waje daya a zaune tun dazun, kuma yanayinki ya nuna bakyajin dadi"

Bata tafin ba saida suka karayin hotuna sannan, ta nemo Fa'iza data shige cikin 'yan uwanta da suka zo biki, silalewa sukayi, motarta daman tana waje, akwai wanda sukace zasu bita gidanta su kwana, sai dai gidan nata na cikin yanayin da bata bukatar wani bako, Fa'izar ma dan tayi mata shara ne da wanke-wanke data kyaleta ta kwana anan gidan nasu. Karfe 11 na safe ne daurin auren Khairi, kuma ko a mafarki Maryama bata hango wai tana garin Kaduna, amman ace bata gefen Khairi a zaune ba a wannan ranar da take da dimbin tarihi a rayuwarta. 'yan gidanma sai kiranta sukeyi a waya

"Haris ne bashi da lafiya Adda"

Ta tsinci kanta da fadawa Adda Zahra da ta sake kiranta

"Wallahi kinganmu haka muka kwana, tun shekaranjiya ma..."

Tayi maganar muryarta na rawa

"Subhanallah, shine kuma kikayi shiru saboda baki da hankali, ki tashi ku tafi asibiti dashi, in kina bukatar wani ya biyo bayanku saiki kirani, Allaah Ya bashi lafiya"

Asibitin itama take so su tafi, amman Haris yaki

"Babu inda zanje fa, kuma wallahi karki kiramun wani"

Ita babban tashin hankalinta ma batasan abinda yake damunshi ba. Bata iya taje gidansu ba ranar asabar sai karfe biyu, lokacin da za'a tafi kai Khairi gidanta da yake unguwar dosa, kuka biyu Maryama tayi, dana Haris da kuma wanda ta taya Khairi, tare suka tafi aka kaita bayan sallar la'asar. Ta danji sauki da Adda Zahra tace mata ta tashi ta tafi gida wajen karfe shida. Haka ta koma ta samu Haris yanda ta barshi, suka sake kwana lahadi, ga yau likitinin, inta mike itama jiri take gani. Dan haka ta samu ta dafa bango ta fita falo da wayar Haris din a hannunta, tunani takeyi Alhaji Mustafa zata kira ko Hajiya Rumana, ko su biyun zata hada dansu hadu su saka Haris din zuwa asibiti.

Tana shirin kiran Alhaji Mustafa ne taji shigowar mota cikin gidan, inda zata iya data tashi ta leka ta hango waye, sai dai batajin zata iya mikewa. Da aka kwankwasa tace waye, bata gane muryar ba, ta kwalawa Fa'iza kira, ita tazo ta bude, ta gaishe da Hajiya Rumana sannan ta koma daki abinta, Maryama kuwa tayi mamakin ganin Hajiya Rumana matuka, Awwab ya rugo yana fado mata, ta dan runtsa idanuwanta tana kokarin dagashi daga jikinta dan ya buge mata ciki.

"Sannu da zuwa"

Maryama ta furta a hankali, muryarta cike da bacci da gajiya, Hajiya Rumana tayi mata wani irin kallo

"Ina Haris?"

Dan yau kwana hudu biyar kenan bai kirata ba, idan ta kirashi ma baya dagawa, jikinta ne ya bata ba lafiya ba, musamman da Alhaji Mustafa ma yace mata ya kirashi bai daga ba

"Bashi da lafiya, yana ciki"

Daman bata zauna ba

"Bashi da lafiya? Shine saboda rashin hankali ba zakiyi tunanin kira ki sanar ba?"

A yanda Maryama takeji, hayaniya ma bataso, sai kawai ta koma cikin kujerar ta lafe batare da tace komai ba, tana kallon Hajiya Rumanan ta wuce dakin da Maryaman ta nuna mata, ta tura a hankali da sallama, ai batasan lokacin da kafafuwanta suka karasa da ita cikin dakin babu shiri ba. Kuma maganar duniya da tayiwa Haris banda hakoranshi dake haduwa babu abinda yace mata, ta taba jikinshi a maimakon zazzabin da tayi tunani sanyi yayi kalau, ta yaye bargunan da yake rufe dasu tana kokarin dagoshi, ya kwace, ta sake kamoshi tana watsa masa zagi

"Bari zakayi ka mutu matarka da ubanta su samu abinda suke so..."

Da taga ya sake komawa ya kwanta, duk abinda ta fada ba tasiri yakeyi ba, saita fito falon tana cewa Maryama

"Wai meye ya same shi? Sannan kunje asibiti"

A takaice tace

"Nima bansani ba, ba muje ba"

Hajiya Rumana taja wani tsaki mai karfin gaske, ta sake komawa dakin

"Wai dan ubanka Haris ba zaka tashi mu tafi asibiti ba?"

Zuciyarshi bata masa dadi, duniyar ma duka batayi masa dadi, kamar wanda wani abin firgici ya biyo ya kasa gudu haka yakeji, ga wasu abubuwa sunayi masa yawo cikin kai, maganar da Hajiya Rumana takeyi ma bayaso, bayason komai sai a barshi yaji da abinda yakeji, kuma babu asibitin da zaije, haka Maryama take so ta ganshi, to kowa ya fita ya barsu ta zauna tana kallonshi haka din. Ganin da gaske yake ba zai tashi ba, sannan ita ba zata iya dagashi ba yasa ta zauna a gefen gadon kamar zata rusa kuka, ta kirawo Alhaji Mustafa tana fada masa abinda yake faruwa. Duk da yace mata gashi nan, kuma bata san daga inda yake tahowa din ba, agogo ta dinga dubawa tana jan kananun tsaki, ya kusan mintina arba'in tsakanin wayarsu kafin ya shigo, kuma tana jiyo shi ya tsaya magana da Maryama kamar bata fada masa halin da danshi yake ciki ba.

Da taimakon Alhaji Mustafa, da Haris ya kasa yiwa gardama suka dunguma zuwa asibiti, Maryama hijabi ta zirawa jikinta, Fa'iza ta dauki Awwab, suka zauna a tata motar. Tashin farko aka karbeshi aka soma bashi taimakon gaggawa, ita kanta Maryama yanayinta da likitan ya gani yasa shi tirsasa mata kwanciya aka daura mata ruwa, da yake akwai gajiya sosai a jikinta, sai bacci ya dauketa. Bata san abinda yake faruwa ba sam, irin zirga-zirgar da Alhaji Mustafa da Hajiya Rumana sukeyi ganin likitocin kansu kamar canki-canka sukeyi da abinda yake damun Haris din, saida suka jira wani specialist da yake zuwa asibitin daga Shika, sunci sa'a ranar na daga cikin ranakun da yake zuwa. Shine bayan ganin Haris kanshi tsaye ya cewa Alhaji Mustafa

"Danku yana shaye-shaye?"

Hajiya Rumana ta kalle shi da sauri, zuciyarta na wani irin bugawa, wanne irin shaye-shaye. Wai me yasa duk lokacin da zata ga Haris a nutse, sai a nemi dawo da wannan maganar?

"Eh gaskiya nasan yana shan wiwi, amman bayan ita bansan ko yana hadawa da wani abu ba, sannan bansan koya bari ko bai bari ba"

Cewar Alhaji Mustafa cikin wata irin murya. A karo na farko da Hajiya Rumana taji idanuwanta sun cika da kwalla akan wannan matsalar ta Haris, shikenan? Ya dai tabbata, duk yanda take gudun wannan gaskiya gata nan a gaban idonta, danta shaye-shaye yakeyi. Haris dinta, kuma abinda take ta gudu da karbar gaskiyar shine inda ya koyi shaye-shayen, tasan a Boarding ne, can zuciyarta ta dauketa ta wulla, ranar da aka gaya musu a ofishin shugaban makarantarsu, ta rufe idonta da zuciyarta taki yarda. Ko meya faru daga wannan makarantar ne, makarantar da Alhaji Mustafa ya nuna mata bayaso, amman tayi fatali da bukatarshi ta dauki Haris din ta kai, kenan in aka zagaya aka zagayo itace sanadi, ita ta jefashi a wannan mummunar dabi'ar.

Yaron da yanzun yake da iyali, Haris din da kowa ya kalle shi zaiga kimtsatsen mutum da natsuwa ta saukarwa, duk da batajin dadin yanda ya kasance tare da Maryama ne ya samu wannan natsuwar. Amman idan wani yaji, tasan abune da zai zubar masa da mutunci

"Yaronku yana fama da abinda ake kira withdrawal effects ne, da alamu dai iya wiwi din yake ta'ammali da ita, dan da akwai wani abin zaifi haka shiga yanayi"

Alhaji Mustafa ya sauke wani numfashi da baisan yana rike dashi ba, har saida ya dafa bangon da yake gefenshi

"Kana nufin ya daina sha kenan?"

Hajiya Rumana ta tambaya da saurinta

"Bai shaba kwana biyu shisa yake wannan abubuwan, muna fatan kuma ya dore da hakan, sai dai yana bukatar taimakon duk wani na kusa dashi, saboda abu dan kadan zai iya sake mayar dashi..."

Bayanai yayi musu sosai, bayan ya fita Haris ya motsa, ya sake motsawa. Hajiya Rumana ta karasa wajen shi

"Maryamm"

Ya kira, ya kuma sake maimaitawa duk da idanuwanshi a rufe suke

"Me yake cewa?"

Alhaji Mustafa ya tambaya, fuska a hade Hajiya Rumana tace

"Wai wata Maryama"

Ya dan girgiza kai kawai, shi wannan kiyayyar marar tushe da Hajiya Rumana take yiwa Alhaji Sa'id da ahalinshi ta daina bashi mamaki ma, ya karasa wajen Haris din ya zauna a gefen gadon, ya kuma riko hannunshi a hankali duk da karin ruwan

"Maryamm"

Ya sake fadi a hankali, sai Hajiya Rumana taja kujera ta zauna, ta matsa jikin gadon sosai, wajen kan Haris

"Haris, ga Maminka"

Dariya taso kwacewa Alhaji Mustafa

"Maryamm"

Yace yana dan bude idanuwanshi, sambatu yakeyi, yawanci duk cikin yaren Italian ne, banda sunan Maryamm din da yake kira yana maimaitawa kamar karatu babu abinda Hajiya Rumana take ganewa, saida yace

"Ina so in sha, amman na kasa, saboda ke, na kasa Maryamm"

Wani irin kishin Maryama da Hajiya Rumana batayi zato bane ya taso mata

"Kai Alhamdulillah, Madallah da Maryaman Sa'idu, madallah da 'yar albarka, ashe itace zata zame maka haske Haris"

Alhaji Mustafa ya fada da biyu

"Ruma kinga abin Allaah ko, kinajin me yake fada?"

Ta kauda kai gefe, cikin dabara tana dauke kwallar da take shirin zubo mata, batace komai ba. Alhaji Mustafa dinne ma ya mike ya nufi dakin

41 / 51