Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
zata nunawa Haris, shima ranar daya zabi yayi mata, yana daga muryarshi tata take dishewa babu shiri. Ita duk fadanta bata da riko, da tayi magana shikenan, amman banda Haris, bata dogon fushi, Haris na iya sati biyu akan dan karamin abu, sai ta bashi hakuri kamar harshenta zai tsinke, tunda in bata lallabashi ba, tana finshi shan wahala, zai fice ya barta, zai iya dauke Awwab su fice abinsu. Sai da yayi kusan wata maganar nan ta Ishaq bata wuce masa ba
"Na fada maka yanzun bana son tashin hankali, ba zaka daina mun fushi ba? Nace ka dinga mun fada a wuce wajen, ka daina mun fushin nan banaso.."
Amman yayi biris da ita kamar ko yaushe, sai da tayi masa kuka na gaske tukunna ya sauko, ya riketa yana fadin
"Bansan sau nawa zan gaya miki ba, ke tawa ce, ni kadai, in zan iya zan koma baya kafin ki sanni, in goge duk wani namiji da ba muharraminki ba Maryamm, yanzun, yanzun da kike tawa..."
Bai karasa ba, amman taji kashedin, tama kanta alkawarin kiyayewa. Tunda sukazo New York babu wanda taji dadin zuwanshi irin Alhaji Mustafa, kamar taga Alhaji Sa'id haka ta dingaji, kwananshi daya ya juya, harda hawayenta, kamar ta bishi lokacin, sai Anisa ma tazo dan batasan me yasa basu zo tare da Alhaji Mustafa kamar yanda Haris ya gaya mata ba, ita dai satinta daya, wasu kwanaki da Maryama tayi su cikin takura matuka, bawai Anisa na shiga harkarta bane ba, amman a lokacin duk abinda zatayiwa Awwab to saita kushe, saita fadi maganar da zata saka Maryama taji cewa ta gaza a matsayinta na uwa. Kuma tana maganar ne cikin sigar da babu yanda za'ayi kace da wata manufa tayi
"Sannu Maryam, gaskiya yaron nan ina tausaya masa, tunda naga babu abinda kika iya, kalli yanda kika matse masa ciki da diaper din nan, kila shisa yaita kuka dazun, saifa kin kula, kinsan kowa zai iya haihuwa, amman ba kowa bane zai iya kula da yaro"
Saita dinga kallon Haris, taga ko ita kadai ce taji kamar Anisa ta gaya mata magana, amman sai dai in tana kusa dashi ya kara riketa, abinda bayajin kunyar yi a gaban kowa, wani lokacin kuma zaice
"Ai zata iya hankali"
Idan abinci ne ta dafa Anisa zatayi order din wani abu
"Ki dauke kayanki fa, da baki wahala bama, ba kowanne abu nakeci ba, miyar ma kamar mai yaso ya kwace miki"
Komai, karamin abu da babba saita samu maganar da zata fada, ba karamin dadi taji ba lokacin da Anisar ta tafi. Ta dinga addu'a kar Allaah Ya sake saka wani cikinsu yazo mata gida, tunda ba zata iya ganin nata 'yan uwan ba, ta yafe nashi, kowa ya zauna inda yake, ita dashi su zauna inda ya kawota. Kadaici nema in ya dameta zata saka shi a gaba da roko
"Dan Allaah mu dan fita, kaji Ganja, dan Allaah...nima in sha iska"
Saiya girgiza kanshi
"Ki bude window, ni ina zan fita dake kije kina kallon wasu garada...ai kiyi zamanki a gida yafi samamun natsuwa"
Akwai randa ta gaji tace masa
"Ganja"
Ya kalleta batare daya amsa ba
"Gida nake so in koma, nagaji, ka mayar dani gida..."
Sai yayi murmushi
"Wallahi nagaji, Allaah nagaji, in baka mayar dani ba zan koma"
Dariya yayi, mai sauti, taji hawayen bakin ciki na neman zubo mata, da ma ta saka masa rikici saiya kamata yayi mata rikon da ko motsin kirki ba zata iya ba
"Kije ina? In kika bar New York da sunan zuwa gida to tare dani ne, muje mu dawo...ai yanzun ke banajin akwai inda zan iya barinki kije batare dani ba Maryamm, kije wani ya ganki? Ko ke ki ganshi? Kinaso zuciyata ta buga?"
Ita wannan ma duka abune da ta fara sabawa dashi, kadaicin, da kuma da yawa daga cikin halayen Haris, dashi dinma gabaki daya. Tashin hankalin farko data fara fuskanta shine wani irin tari da Haris din yakeyi da sassafe, da asuba idan ta tashe shi sallah, haka in yana dariya. Sai takai ta kawo idan zai dauki Awwab su fita to haka zai shigo yana numfarfashi
"Mura ce tayi maka wannan kamun haka? Anya ba zaka ga likita ba?"
Ta tambaye shi cike da damuwa da taji yana tarin cikin dare, dan sai da ta dafe masa kirjinshi jin yanda yake dagawa, kusan sati yana fama, ita har alamun zazzabi takeji a jikinshi, amman yaki bari suje asibiti
"Tari ne kawai, zai daina, kilan sanyin dana kwasa ne a wajen aiki rannan dana fita ban wani saka kaya masu kauri ba sosai"
Dole ta kyaleshi, sai ranar wata alhamis, tana kitchen tana hadawa kanta cereal dan taji kamar alamun yunwa ne, kuma batajin yin wani girki, yunwar yamma dai, ita ko kafin ta yaye Awwab yunwa bata damunta haka, yanzun kuwa kamar gara, daga ta ci abinci sai taji kamar an kwashe mata shi, anan ta tsaya ma tana sha, tana kallon yanda Haris ya biyewa Awwab yana binshi da gudu suna ta zagaye falon, shi in za'a wuni ana wasa baya gajiya, sai dai kai ya barka da ciwon jiki, tarin nan Haris ya fara, ta ajiye bowl din hannunta tana jera masa sannu, ruwa take kokarin dauko masa taga ya durkushe ya rike kirjinshi, batasan lokacin data bar fridge din a bude ba ta karasa wajenshi.
Numfashi yake fitarwa kamar mai ciwon asthma, ga hannunshi da ya dafe kirjinshi dashi, a durkushe yake amman yanda yake fitar da numfashin a wahalce dole ya karasa kwanciya kawai, gabaki daya Maryama ta rikice, dakyar dabarar kiran 911 tazo mata, ta rike Haris, ta dago masa kanshi ta kwantar a cinyarta kamar yanda sukace tayi ko kofofin iskar shi zasu bude, kuka kawai takeyi, Awwab da baisan meke faruwa ba, ganin dai tana kuka shima ya fara, lokacin da suka karaso kuwa suka janye shi daga jikinta, suka saka masa abin numfashi a hanci, suka dorashi kan gadon daukar marar lafiya, wasu suka wuce dashi zuwa wajen motar asibiti, ita kuma daya a cikinsu yake tambayarta ko akwai wanda zasu kira mata.
Ta girgiza masa kai tanata kuka, da Awwab data dauka, haka taja kofar gidan suka shiga motar asibitin, suka wuce da Haris. Allaah Ya taimaketa kafin su fitan taja wani babban showel da take goya Awwab dashi, dan bacci yayi mata a waiting area din nan, ta kuwa goyashi, tana ganin yanda har Nurses din suke ta kallonta, wasu suyi mata murmushi, daman ko Chloe sai ta dinga ce mata ta koya mata yanda akeyin goyo, haka zasu shiririce wani lokacin ana abu daya, kamar goyon ne da basu saba gani ba yake basu mamaki. Ita dai banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, ko waya ma bata dauko ba, tunda babu amfanin da zatayi mata.
Inta dauko wa zata kira? Nan ba kamar Kaduna zuwa Kano bane, tasan sai dai ta daga musu hankali kawai, watakila kuma ta janyo musu 'yan uwan Haris suzo su kara dagula mata lissafi. Hankalinta bai kwanta ba sai da taga Haris, duk da har lokacin akwai abin da yake taimaka masa wajen yin numfashi, taji dadi da suka barta ta ganshi. Abinda akace yana damunshi ne bata tabajin ko sunanshi ba, saida ta tambaya sau biyu, ta kara sa cewa likitan ko zai rubuta mata tagani
"Chronic bronchitis"
Ta karanta tana haddace kowacce kalma, bayani yayi mata gamsashe, ta dinga goge hawaye, ta rasa ya zatayi da Haris, ya zatayi dashi da wannan Wiwi din da yaki ya taimaki kanshi ya kuma taimaketa a yanzun da rayuwarsu take waje daya ya daina sha, so yake ya kashe kanshi. Wasu hawaye suka sake balle mata jin cewa cutar ba wadda za'a iya warkewa gabaki daya bace ba, asalima in har bai daina bankawa cikinshi hayaki ba zata iya kai matakin da ba'a fata, ta hangota da Awwab, babu Haris, irin kadaicin da take shiga in ya tafi makaranta da aikinshi, to ace babu shi gabaki daya fa? Wani abu ya rufza cikin kirjinta, tashin hankali nayi mata dirar mikiya, kamar itama nata numfashin zai dauke.
Tayi sanyi da yawa, itama ta sani, Haris yasa tayi sanyi da yawa, a halin yanzun kuma ba wannan Maryaman yake bukata ba, dole ta bude ido daga rufewar da suka fara, kamar yanda yake fada ne, daga ita sai shi a kasar New York, yana bukatarta kamar yanda take bukatarshi
Watakila kaddara ta hadasu ne dan ta taimake shi
Amman ai kaddara na da fuskoki da yawa, kuma a tata rayuwar, kaddara tazo mata ne da fuskar Haris Ganja...
34
Kwanansu tara a asibiti, ba zatace ga sau nawa ta kalli kanta a mudubi ba a cikin wadannan kwanakin, amman tasan ta kara ramewa, tayi haske sosai, amman ta rame, kuma abinci take ci da har mamakin kanta takeyi, sai dai idan akayiwa Adda Maimunatu maganar kibar da takeyi sai tace
"Ku rabu dani, bafa abinci bane kawai, abincin ne ya hadu da kwanciyar hankali, inda hankalina ba'a kwance yake ba yaushe abinci zai bi mun jiki harku isheni da magana"
To Maryama tasan abinda yake faruwa da ita kenan, rashin kwanciyar hankali, ciwon Haris yayi mata tsaye, ba'a asibitin take kwana ba, wannan zirga-zirgar kadai ba karamin jigata takeyi ba, danma Chloe ta taimaka mata ta samu babysitter, sai take bar mata Awwab, saukin data samu kenan. Kawai inta kalli Haris sai ta dinga tunanin tarin dokokin da suke tattare da wannan ciwon da shine ya jawa kanshi, dokokin da take ta tunanin hanyar da zatayi amfani da ita wajen ganin ya bisu. A wannan kwanakin, a rana ta biyar da aka cire masa abin taimakon numfashi, ya koma yi da kanshi, daya tashi daga bacci, idanuwanshi akanta, wandon jeans ne a jikinta, sai riga mai dogon hannu, daga yanda take zaune ma yana ganin girman rigar, dan ta sanyi ce mai laushi, kalar yellow, sai ta saka karamin hijabi, tayi masa kyau.
"Ka tashi? Ya jikin?"
Ta tambaya muryarta cike da gajiyar da takeji
"Kin rame, zo, matso in ganki sosai"
Batayi masa musu ba, taja kujerar da take kai har gab da gadon, dan ta matsa ne tana dan kallo a laptop din da take zuwa da ita asibitin, ya mika mata hannunshi da yatsanshi guda daya yake makale da wata na'ura. Saita saka nata hannun a ciki, ta kuma kama karamin yatsanshi
"Bana son ganin sunan nan"
Ta fadi a hankali, batasan sau nawa taso ta gaya masa ba, ta tsani ganin sunan Aise a jikin yatsanshi, kamar ta saka reza ta kankare haka takeji, idan ma ya jita ya zabi yaki amsawa ne
"Kin rame, anya ba zasu dubamun ke ba"
Numfashi ta sauke
"Zirga-zirgar da nakeyi ne kullum, ga damuwarka"
Idanuwanshi cikin nata yace
"Kiyi hakuri"
Ta sauke nata idanuwan
"Inyi hakuri dame? Kokarin kashe kanka da kakeyi? Inyi hakuri in fara shirin yi maka takaba? Inyi hakuri ni kadai zan raini Awwab? Inyi hakuri wata rana inya tambayeni meya kashe Babanshi in masa bayani? Inyi..."
Yayi saurin katseta
"Maryamm"
Ta kalle shi
"Meye? Kar in fada masa? Ince wiwi ka zaba akan ka zauna damu?"
Sunanta ya sake kira, amman ya kasa kara wata kalma akai, saboda yasan gaskiya ta fada
"Kashe kanka kakeyi, kana kashe kanka Ganja, kuma rayuwarka ba taka bace kai kadai yanzun"
Karo na farko daya fara jin yana so ya bari, amman inya hanga cikin kanshi sai yaji kamar abune da ba zai iya ba
"Zan fadawa Baba, zan kira Mami, watakila in sukaji har yanzun baka daina yunkurin kashe kanka ba su zasu maka magana kaji"
Ya danyi murmushi, da dukkan zuciyarshi yasan ba zata iya ba, Maryama ba zata taba kai kararshi ba
"Yunwa nakeji"
Yace mata
"Ki siyomun tea"
Bata kara cewa komai ba ta mike, ta juya zata tafi ya kirata
"Maryamm"
Ta kalle shi
"Karki kalli kowa"
Sai yaso ya bata dariya ma, ita a kwanakin nan da yake kwance, inda zata iya ai da tasha yawonta ma ta huce takaicin kullen da yakeyi mata, to inta kira uber har kofar gida, zai kawota asibiti, in zata koma haka takeyi, duk wani abu da zata siya naci kuma akwai wajaje a kusa-kusa da asibitin dan ba saita hau abin hawa ba. Kawai sake juyawa tayi ta fice abinta, tunda itama yunwar takeji. Kuma tunda ya tashin dai, duk sanda zata fita saiya dinga jaddada mata karta kalli kowa, yanda ya addabeta da maganar
"In kinga an cika kallonki kawai ki bar wajen Maryamm, kinji"
Sai kawai take saka facemask, amman bata tsira ba
"Me yasa kika saka kwallin nan kika fito? Kinga yanda idanuwanki sukai kyau"
Gajiyar da ita yakeyi da irin abubuwan nan
"Kin rame da yawa, Allaah sai an dubamun ke zamu bar asibitin nan, kilan wani abin ne daban yake damunki"
Batace komai ba, sai kuma yace mata
"Ya kamata kina period, yau tara ga wata"
Tasani, ita bata kawo komai a ranta ba, ta dauka ko wannan stress dinne yasa ta samu delay
"Maryamm"
Haris ya kira yana wani irin murmushi
"A'a"
Tace tana girgiza kanta, ba dai ciki ba, to duka yaushe ta yaye Awwab? Kuma ita da ko numfasawa batayi ba sai ace harta kara samun wani cikin? Haka akeyi? Ita da suke shirin zuwa ganin gida ma kamar yanda Haris yayi mata alkawari nan da watanni uku
"Yes"
Shikuma yace cike da zumudi, wani cikin? Wani yaron ko yarinyar? Yana so, yana so sosai. Allaah Yasa wannan yayi kama dashi, saboda kowa ya kalli Awwab yanzun zaiga yanda yaron yake juyewa zuwa fuskar Maryamm duk da kuwa bakine, amman baya kama dashi, kalar kawai ya dauko. Haka sukaje ana dubawa kuwa ciki gareta, in tace tayi murna karya takeyi, asalima wani abune ya danne mata kirji, yanzun anan zata kara haihuwa? A wannan kasar ita kadai
"Banaso in kara haihuwa anan Ganja, dan Allaah ka mayar dani gida in haihu acan, in yaso sai in dawo"
Yanda yaga yanayinta yasa shi yin shiru, bayaso tayi masa kuka ta dagula masa lissafi, amman shi ina zai bari ta tafi batare dashi ba? Taje gida ta haihu, wata nawa kenan? Ba zai iya ba, ya kamata ta fara gane cewa ba zai iya bari tayi nisa dashi ba yanzun.
"Zamu san yanda zamuyi, karki damu"
Hawaye ya cika mata idanuwa, amman batayi masa gardama ba, asalima ta yiwa kanta alkawarin ba zata sake tayar masa da zancen ba, kyaleshi zatayi, suje gidan, sai taga idan a saman kai zai dauketa yasa ta sake binshi. Ko bayan an sallame shi suka koma gida, babu wanda ta fadawa maganar cikin, harda Khairi kuwa. Tunda batajin tama san me takeji, ta dai san batayi farin ciki ba, kuma tanajin bata shirya kara haihuwa da wuri haka ba. A wannan watan ne ta samu labarin da yayi mata dadi da dukkan zuciyarta, saka ranar Khairi, da Ibrahim Bakori.
"Ikon Allaah Adda...Ibrahim din dai"
Tace cikin mamaki tana dorawa da
"Bakya tsoro Adda? Bakyajin kishi? Yana da wata matar fa"
Khairi tayi dariya
"To akanta zan zauna Maryama? Ni ina ruwana da matarshi? A Kano fa zamu zauna, kinga Abba ma yanata mun kokari in samu transfer tunda nan da wata uku zamu gama level 2, kuma kinga bikin wata ukun aka saka"
Dadi ya kara kama Maryamm
"Aikuwa zan yiwa Ganja magana sai kawai mubari ma sai watan bikin mu taho, inaso ayi komai a gabana, komai da komai"
Khairi ta sakeyin dariya
"A Kano din zaku zauna?"
Maryama ta tambaya
"Ai shine dalilina na aurenshi, saboda zai ajiyeni kusa dake"
Wata kewar Khairin ta danneta, bawai saboda su Mummy ba, ko sauran 'yan uwanta, saboda ita
"Ko kun fasa dawowa?"
Maryama ta girgiza kanta kamar Khairi tana ganinta, Haris bashi da burin zama a wata kasar da ba tashi ba, ta sani, ya fada mata da bakinshi
"Kimun addu'a, na siya truck dita ta farko"
Haka yace yana dorawa da
"Ta farkon da nake fatan ta budemun hanyar siyan wasu da yawa, ina son inyi kudi Maryamm, manyan kudi, irin kudin da ke da yaranmu ba zaku nemi wani abu ku rasa ba, kudin da idan na mutu na bar musu su cigaba da kula dasu suma subarwa nasu yaran"
Duk wani plan dinshi, akan wannan business dinne da baya gajiya dayi mata hirarshi, ko fada mata yanda ake ciki, shi ba kamar Alhaji Mustafa ba, ba motocin yake so ya dinga siye yana siyarwa ba, haya yake so a dingayi da motocin, manyan ana daukar kaya daga gari zuwa gari. Mafarkinshi babba ne, kuma tana yawan tunanin wannan mafarkin nashi, tana ganin wanne kudi yake nema banda wanda yake samu yanzun, ko ita idan ta tayashi aikin hotunanshi yana bata kudi, suna nan tana tarawa, a wata 'yar karamar jaka take sakawa tunda dalolin yake bata cash.
"To abubuwan hotonka fa? Zaka daina ne"
Ya girgiza mata kai
"Wancen business din, ina sonshi ne saboda ina hango tarin kudin da yake ciki, saboda kudinne kawai, hoto kuma, saboda ina so"
Ita dai ba zatace ta gane abinda yake nufi ba, ta gane bambanci, tunda hoton ma ai ba kyauta yakeyi ba, kudi yake samu, kudi masu yawa a wajen Maryama, tunda bata taba cewa ga abinda take so yayi korafi ba, abinda ma batace ba kwasowa yakeyi. Inya bata kudi duk sanda zai koma makaranta, baya taba tambayarta koya rage, itace ma in zai sake tafiya ya kara mata zatace
"Akwai fa, wancen bai kare ba"
Sai yayi dariya
"To duk ki hada, kici duk abinda kike so, kiyi order za'a kawo miki, kawai dai karki fita ko ina"
Yanzun da dukkan zuciyarta ta cewa Khairi
"Zamu dawo, daya gama karatunshi, zamu dawo In Shaa Allaah"
Tanajin Khairi ta sauke numfashi
"Alhamdulillah, Allaah Ya kaimu lokacin"
Suka cigaba da hirarsu, hirar ranar ma duk Maryama ce da take ta tsara abubuwan da zasuyi na biki, harda cewa kar Khairi ta sake ta bari wasu su zabi anko, sai tazo zasu je kasuwa su zabo tare, tanata mata dariya. Kuma ko bayan da suka gama wayar haka ta kalli Awwab tace
"Amminka ce, Ammi Khairi, kaima kana so kaje kaganta ko?"
Da tayi maganar sai taji kamar zatayi kuka, kewar gida da kowa ta kara danneta, wai ace ta haihu, yaronta har ya shekara biyu amman ko su Hajja basu ganshi ba sai a hoto, shekararta uku fa harda wasu yan watanni yanzun rabonta da gida, inda wani ma yace mata zatayi wata uku batare da taga kowa nata ba dariya zatayi. Dariya mai yawa dan tasan sai dai in mutuwa tayi, kuma ko da mutuwar tayi ai ba za'ace ba zata gansu ba, sune dai ba zasu ganta ba, amman zata kasance tare dasu a duk wata addu'a