Advertisements
Chapter 29 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   29 / 51

84K to 87K   out of 151K words

bayan ta shiga, tana kokarin karbar doyar data dauko, nan suka dinga musu dan Maryama taki bata, bata ga ta inda zata iya sakar mata aiki alhalin lafiyarta kalau ba, ita kunya ma taji

"Dan Allaah Mama kibari zan fere"

Haka ta hakura dole sukayi aikin tare, ta kara nuna mata komai da cewar ko da bata tashi da wuri ba sai ta karya abinta. Matar ta kwanta mata a rai, daga gani ba zatayi matsala ba, kuma bata da matsalar, dan sosai suke zamansu da Maryama, kafin ta fito ta gyara ko ina, tare suke girki, suyita hira tana ba Maryama labarin kauyen da sukayi rayuwa ita da mijinta, wani kauye ne na Inyamurai can yankin Calabar, kauyen mai cike da abubuwan mamaki, haka Maryama zata dinga tunani. Wata rana taji tsoro ya shigeta ainun.

Akwai tashin hankali ace kana zaune da mijinka sai mutuwa tazo ta rabaku, har tausayin Mama Sadiya takeyi, ta dinga tunanin to kewarshi bata hanata sukuni? Ko dan Allaah Yana saukarwa da bayinShi Rahma ta hanyar mantuwa da kuma dangana. Kullum sai suyi waya babu adadi ita da Haris, amman kewarshi nukurkusarta takeyi ba kadan ba. Ya dai saka anzo har gida, ita da Mama Sadiya suka tafi ma akaje inda za'ayi mata passport din, Haris babu kashedin da baiyi mata ba

"Duk wanda yayi miki wata magana data wuce ta abinda kikaje yi ki kirani, karki kalli kowa, in aka cika kallonki kibar wajen ki sake wani, ki zauna kusa da Mama Sadiya kinji?"

Ita dai da to ta dinga amsa shi. Haka a wajenma ya dinga faman kiranta, dakyar suka gama abinda zasuyi suka dawo gida tukunna ya barta ta numfasa. A wannan tsakanin ne kuma Minal ta haihu, yayar Khairi. Haihuwar tayiwa Maryama dadi, tunda tasan duk su Adda Zahra zasu zo suna, harda Khairi. Tun ranar take fadawa Haris anyi haihuwa

"Yarinyar Mummy ce itama...inaso inje barka, inga baby"

Ta fada masa, sai yace mata

"Ba za'ayi suna ba?"

Tunda yasan ana taron suna idan anyi haihuwa, ta daga kai

"Eh za'ayi, su Adda Zahra ma duk zasuzo"

Ta karasa cike da zumudi

"Me zaki kai? Mace ta haifa ko?"

Haris din ya tambaya, ita tunanin abinda zata kai ma baizo mata ba

"Nima ban sani ba, banyi tunanin ba, gashi gobe idan Allaah Ya kaimu nake so inje barkar, daman Mama Sadiya tace zataje gida ta duba yaranta, ko kawai in kwana gidan Mummy?"

Da saurin shi yace

"Saboda baki da hankali? Sai kawai kije wani gida ki kwana, ga gidanki, sau daya zaki fita gaskiya, sai dai ko kije barkar, ko kije sunan, zansa a kawo miki kayan da zaki kai musu"

Ta dauka wasa Haris yakeyi, da gaske hanata yayi, har kuka tayi masa tunda tasan bai kamata ace ya hanata zuwa abu irin wannan ba, sai kawai ya kashe kiranma gabaki daya, kuma daya kira zata dasa masa magiya sai ya sake kashe wayar, haka ya dingayi saida ta hakura bayan ta gayawa Khairi tana share hawaye

"Sai kiyi hakuri tunda inda Allaah Ya kaiki kenan, muma ana gobe suna zamu taho In Shaa Allaah"

Ta dingajin kunyar Mummy, da yake sun saba waya, tana yawan kira ta duba lafiyarta, itama kuma tana kira ta gaishe da ita. Danma haihuwa ta uku ce Minal din tayi, duk da haka taji babu dadi, an kawo kaya, saida tayi mamakin yawansu da kuma tarin tarkacen da ta dinga budewa tanata kallo, komai ya burgeta, kayan jarirai akwai kyau, batasan.ya akayi bata taba ganin hakan ba sai yau, ko dan basu taba zuwa hannunta haka bane ba?

Anan gidanta su Adda Zahra suka sauka, ta rasa inda zata sakasu don farin ciki, komai da take dashi ta dinga kwasowa tana kawo musu

"Wallahi nayi kewarku Adda, kamar na shekara irin biyar banganku....ashe haka nake sonku da yawa bansani ba?"

Suka dingayi mata dariya, kuma basu tashi gaya mata da Hajja akazo ba sai da daddare

"Kai dan Allaah, kai dan Allaah Adda"

Ta kira Hajjan harda kukanta

"Yanzun Hajja ba zakizo kinganni ba, ba zaki zo gidana ba"

Tasan bata bakinta takeyi, dan zaka rantse Hajja irin fulanin dajin nan ce saboda kunya da kawaicinta, gidajensu Adda Zahra ma zasu iya kirga sau nawa ta taka, shima a bisa lalura, ko haihuwa sukayi sai dai a biyota da yaran nan tazo ta gansu. Taji kamar ba zata iya hakuri gari ya waye ba, Haris na kiranta tace masa

"Ashe da Hajja akazo, tana gidan Mummy, dan Allaah inje in ganta tun yau? Ba zan dade ba wallahi, sai muje ni da wani cikinsu Adda"

Ya danyi shiru kafin ya amsa da

"Dare ne yanzun anan Maryamm, dare yayi kiyi hakuri sai gobe, sai ki fita da wuri, kuma saiki wuni sai yamma wajen karfe hudu haka ki dawo"

Ta fara gane akwai yanayin da idan yayi magana cikinshi komin roqon da zatayi masa ba zai canza ba, shisa tayi masa saida safe, kafin ya amsa ta kashe wayarta gabaki daya. Kuma washegarin haka ta jefata a jaka batare data kunna ba, yau tana cikin 'yan uwanta, balle kewarshi tasa ta kunna wayar batare data shirya ba, sannan ba zata koma gidan da yamma ba, sai dare, tare zasu koma dasu Adda Zahra tunda sai washegari su zasu koma, Hajja dai wajen azahar ita direban da ya kawota ya dauketa, Maryama najin kamar tabita, sai rungumeta takeyi tana tureta.

Wajen karfe tara da rabi, lokacin ma suka shiga mota zasu koma, kuma wayarta bata kunna ba, Khairi da ta lallaba zata bita gidanta, tunda jiya ta sauka gidan Minal ne ta mika mata wayar data daga

"Mijinki ne"

Haka kawai taji gabanta ya fadi, kamar karta saka wayar a kunnenta, ganin yanda Khairi take kallonta yasa ta kara wayar a kunneta tanayin sallama cikin karamar murya, sallamar da Haris bai amsa ba yace

"Ina wayarki?"

Ta dan tura bakinta gaba

"Tana cikin jaka"

Tambayoyi ya jero mata

"Me yasa kika kashe? Kina ina? Baki koma gida ba?"

Sai kawai ta zabi amsa guda daya cikin rawar murya jin yanayinshi

"Bani da caji"

Kai tsaye yace

"Karyane. Karfe nawa nace ki koma gida?"

"Da yamma"

Ta bashi amsa

"Da yamma karfe nawa?"

Tayi shiru

"Karfe nawa?"

Ya sake maimaitawa

"Hudu"

Ta amsa kamar an saka mata tsumma a baki

"Yayi kyau"

Ya furta yana kashe kiran, ta cire daga kunne tabi wayar da kallo, wani abu na danne mata makoshi. Kuma daga wannan sunan, saida Maryama ta lissafa watanni uku bata leka ko kofar gate dinsu ba

"Ni zance ga lokacin da zaki koma gida, ki kashe waya kiyi zamanki sai dare Maryamm? Saboda muna wasa da juna ne inaga, ni na barki kika fita shisa"

Ta jera masa magiya da ban hakuri kamar zata ari baki, a wata ukunma zazzabi tayi, sukaje asibiti, ta dinga kallon gari kamar wata bakuwa, haka ta karbo alluran da aka rubuta mata tas, kuma tayi su saboda kullum zasu fita suje ayi mata, ko babu komai taga gari. Sai dai ta dauka a yanda tayi kewarshi, zataji wani doki na daban idan yace mata ga lokacin da zata bishi, amman sai zuciyarta ta buga, har tana ce masa

"Yaushe zanzo ganin gida to idan na taho? Kuma ni kadai zan hawo jirgi? Ba zaka dawo mu tafi tare ba?"

Dan fargaba ce ta lullubeta, sai tabar kasar? Duka? Shi yanzun watanshi nawa da tafiya baizo ba, in kuma ta bishi sukaqi zuwa da wuri ya zatayi? Daga ita saishi a wata kasa mai nisa haka. Dokin tafiya kasar wajen yanzun daya tabbata zataje sai ta neme shi ta rasa, turawan ma da zata gani kala-kala taji duk sun fice mata daga rai. Satikan uku suka dinga mata wani irin sauri. Ba karamin dadi taji ba da Haris yace mata zataje Kaduna tayi kwana biyu, sai da tayi hawaye da sukayi sallama da Mama Sadiya, sun saba, matar na da kirki, shisa Maryama bataji komai ba, duk wani kayan abinci da suke dashi raba musu tayi da maigadin gidan da kamar zai tsugunna saboda godiya, ita kanta Mama Sadiyan harda hawayenta.

Lokacin da Maryama ta shiga gida, Alhaji Sa'id na nan, daga mota da gudu ta nufi bangarenshi, yanda tayi kewarshi

"Abba na"

Ta dinga fada duk wani motsi da zatayi a cikin gidan

"Abbanki a ina? Sai kace naki ke kadai"

Cewar Khalifa da ta fada yana wajen, ai ba karamin dadin saka masa biki da akayi taji ba, duk da bata gidan ta taya yan gidan murna, kowa sai taji sakat, inama wata uku akasa ba shida ba. Sai kuma taji babu dadi data tuna ba lallai ayi bikin tana nan ba. Abubuwa nawa zata rasa? Muhimman abubuwa nawa za'ayi bata nan? Aure ya dauketa ya mikawa Haris, shikuma zai dauketa ya bar kasar da ita. Wata sabuwar nasihar aka bude babin yi mata, kowa da akwai kalar shawarar da zai bata, da yake zuciyarta a karye take sai kuka, duk abinda suka dinga fada sai taji hawaye ya balle mata.

Hajja ce tasa ta tambayi Haris din zataje ta gaishe da Hajiya Rumana, akasa direba ya kaita ita da Khairi da tayi mata rakiya, yaji dadi har a muryarshi

"Da gaske zakije ki gaishemun da Mami na?"

Har saida taga wautarta da batayi tunanin yi masa kara ba, kuma wannan murnar itace ta takaita mata bakin cikin wulakancin da Hajiya Rumana tayi musu, tunda suka shiga falon, taga sune, ta amsa gaisuwarsu da

"Lafiya"

Ta tashi ta shige ciki, haka suka karaci zamansu, turarukan wutar da Hajja tayi asarar kudinta ta siya ma anan suka gaji da zama suka bar mata kan kujera

"Ni dana sani ma na dauko turarukan wutar wallahi, kilanma ta zubar a bola tayiwa Hajja asara"

Duk da Khairi ta fita jin zafin abinda akayi musu din, dannewa tayi tace

"Ita ta sani, ai dai an samu ladan kyautata mata, ke dai nasanki da kaikayin baki, kamar ba'a gasa miki shi da kyau ba, saura ki gaya masa ga abinda ya faru, kawai kice masa mun gaisheta"

Kuma har ran Maryama tayi niyyar gayawa Haris abinda ya faru, yanda in gaba bataje gaisheta ba, ba zaiji haushi ba, sai dai ko Hajjan ma saida ta kara ce mata karta fada masa

"Kiyi hakuri, kiyi kokarin tayashi ya zauna lafiya da mahaifiyarshi Maryama. Itace fitilarshi, kuma a yanzun shine naki fitilar, idan baya tare da haskenta, tare zaku hadu ku dishe, ki koyi hakuri, tunda ba sosai zaku dinga haduwa ba, ko da kasar kuka dawo ba gari daya kuke ba"

Haka dai ta daga kai, Alhaji Sa'id ma ya kara mata da tashi nasihar, har saida ta fara tunanin yaushe zata fara yin hakurin nan da ake ta kira mata? Shin bayan hakuri sai kuma wanne abu akeyi ne a zaman auren? Kamar dai hakurin fa yafi komai rinjaye shisa aketa jaddada shi har haka. Taci kuka da zasu koma Kano, da duka yayyenta mata suka tafi, aka kara share gidan, aka nade komai, kujerunta ma kira akayi akayi musu leda da duk wani furnitures, dakin da suka kwana ne sai washegari da sassafe akazo akayi masa kamar sauran daku nan. Jirgin karfe goma sha daya ne zata hau, abinci daga gidan Mummy aka kawo musu na safen, tunda duk sun tattare komai, ita ruwan shayi ta iya sha, cikinta ya cika fal da fargaba.

Saida su Adda Zahra suka rakata har airport, suma sai gasu suna hawayen duk kuwa da tsokanar da suka kwana sunayi mata, haka suka dinga rungumeta daya bayan daya kamar masu bankwana. Ita dai idanuwanta har yaji sukeyi mata saboda kukan da tayi, daga ita sai akwatinta guda daya, akwatin da Khairi ce ta hada mata shi saboda ta kasa, ta rasa abinda zata dauka, tunda duk wani abu da take so ta dauka ba zai yiwuwa ya shiga akwatin nan da takeja ba, sai karamar jakarta. Ta juya ta daga musu hannu, haka ta dinga juyawa har ta bace musu, tukunna ta sauke numfashi mai nauyi, tana tunkarar rayuwar da take jiranta batare da tasan cewa yanzun ne asalin labarinta zai fara ba

Ita da Haris...

30

Yasan ko karfe nawa jirginsu zai tashi, saboda haka a lissafe yake da lokacin daya kamata su sauka, amman baisan me yakeyi a airport awa biyu da kusan rabi kafin lokacin saukar jirgin ba, kuma a zaune yake sai earpiece din daya saka a kunnenshi yana sauraren wani podcast da akeyi akan yakin duniya na biyu, yana sauraren ne yana kuma duba lokacin da yaga kamar da gayya yaki yi masa sauri, kwakwalwarshi ma ta kasune waje uku, daya na duba masa lokaci, daya na kokarin fahimtar abinda yake saurare, dayar kuma tana masa tunanin Maryama, yanda zai ganta bayan watannin nan, ta kara kiba? Ko tana nan da wannan sirantakar tata? Ta kara haske? Duk da dai kai tsaye mutane da yawa ba zasu kirata da fara ba, amman in zata tsaya kusa dashi yasan farar za'a kirata.

Wanne kaya ta sako? Ko tasan a wannan watan na January a kasar ta New York lokacine na tsananin sanyi? Ba suyi maganar ba, bai fada mata ba, yace mata ko da bata saka rigar sanyi ba lokacin da zasu taho to ta riketa a hannu saboda zata bukaceta, shi bakin wando ne a jikinshi, takalminshi ma da yake sneakers bakine, sai ya dora leather jacket akan farar tshirt din da ya ganta sabuwa cikin kayanshi, bama zai tuna lokacin daya siyeta ba, kuma yau ya sakane saboda yanaso Maryama taga yana saka wasu kaya da ba bakake ba, har hasashen mamakin da zai cika fuskarta yakeyi, ya saka hular sanyi baka da ya danja baya, gashin shi da yake bakikirin fiye da sauran jikinshi na bayyana, da yake ba tarawa yakeyi ba, yayi ma sabon askine, kana iya ganin yanda edges din suka nuna alamar kwarewar wanda yayi askin.

Lokacin kuma da agogo ya buga karfe sha daya da kwata na safe agogon New York, sai gashi ya mike tsaye, ya zare earpiece din dake kunnenshi, ya hada har wayar ya saka a aljihunshi, zuciyarshi na tafiya tare da agogon yana jiran sauran mintina sha biyar din da zasu cika, idanuwanshi kafe a hanyar da yasan Maryama zata bullo, zuciyarshi cike da fatan shine mutum na farko da idanuwanta zasu tsame mata a cikin tarin mutanen da suke wajen. A wannan lokacin, da Haris yake jiran Maryama, a lokacin ne kuma jirgin nasu ya sauka.

Wani sanyi ya daki fuskarta tun da kafarta ta taka matattakalar farko ta sauka daga jirgin, kafin kuma sanyin ya ratsa ko ina na jikinta, riga da wando ne a jikinta ruwan kwai, a cikin lefe ta gansu, wandon irin pallazo din nan ne, haka rigar ma bata kamata ba, sannan ta sauka har kusan gwiwarta, kayan ba cutton bane, amman yadin da akayi su dashi mai laushi ne, hannun rigar dogo, shisa sai ta saka jersey scarf da kuma mayafin farare, wata iska taji tana kadata har hanji, ga kamshin iskar cakude yake da wani abu mai kama da kofi da kuma sabuwar rayuwar da Maryama tasan ta shigo, duk ya cakude waje daya, tasan yanayin safiya ce ko tace ma rana zatayi, akwai fitilu sosai a filin jirgin na John F. Kennedy International Airport, ga kuma wani abu nan kaman allo da aka rubuta Welcome to new york da manyan baki.

Ta tsaya tana kallon rubutun, zuciyarta na harbawa da sauri, hannunta na rike da jakar da ta dauko tun daga gida, jakar da kuma ko a cikin jirgi tana makale a kafadarta. Sai kuma katon akwatinta da take rike dashi a dayan hannun tana ja a hankali. Maryama ta lumshe ido na wasu dakika. Wata irin fargaba ce ta tsaya mata a kirji da ba zatace takamaimai ta mecece ba, a gefe daya kuma akwai tsoro dokin ganin fuskar da ta shafe watanni tana tunanin canzawarta, fuskar Haris, labbanshi sun kara duhu ko suna nan a wannan kalar mai yanayi da ruwan toka mai cizawa da kuma zanen layukan baki da watakila ita kadai take gani, a hankali take takawa inda taga mutane nabi da tasan zata sadata da inda Haris yake tsaye yana jiranta, ko da ta karasa wajen kuma sai taji ta diririce, bakunta da rashin sabo na shiga ko ina ita kadai ya dirar mata, ta fara waige-waigen nemanshi

"Maryamm…"

Muryarshi ta shiga kunnenta, ta zarce cikin zuciyarta da wani irin karfi, duk da a hankali yayi maganar, ta juya, da saurinta, tsaye a cikin shigarshi, sanyin daya ratsata wannan karin bashi da alaka da kayan jikinta, kuma Haris yaga yanda jikinta ya kada, daya matsa gab da itama zai rantse yaga wasu kananun goosebumps a kan goshinta, wani abu da bai taba gani ba

"Sanyi ko?"

Ya tambaya yana kallonta, idanuwanshi cike fal da kulawa, wannan maikon na cikinsu yayo kasa kamar zai zubo, a wannan lokacin Maryama taji ta manta da gajiya, ta manta da hayaniyar mutanen dake wajen, shi kawai take kallo, ta ga lokacin daya cire jacket din jikinshi, farar rigarshi ta bayyana, farinta na shiga idanuwan Maryama tana kuma kara haska mata bakin Haris da har kyalli yakeyi

"Farar riga, kasa farar riga yau"

Ta tsinci kanta da furtawa, sai kawai yayi dariya yana zagaya da rigar kan kafadunta ya gyara mata zamanta sosai, kamar tace masa ya karayin dariyar, kewar sautin dariyar tashi ya saukar mata da kuma dumin da jacket din tayi, dumin da tasan na jikinshi ne, jakar hannunta ya karba, ya kuma sake mika dayan hannunshi ya karbi akwatin, yana mamakin yanda ya iya rike kanshi bai rungumeta ba har yanzun, ya dai hada jakar da akwatin waje daya, ya riko hannunta da yaji yatsun sunyi sanyi karara, ya kuma dan murzasu a hankali, kafin ya rike shi sosai yana janta, kafafuwanta suka bashi hadin kai, suka fara takawa, da suka fita daga airport din, sai taga yana rike da ita sun wuce sun dan tsaya kafin suka tsallaka titi, wani dan karamin waje ya nufa da ita, ya tura kofar gilas din suka shiga, taji yayi magana, yayi turanci, amman accent din da kuma saurin da yayi maganar baisa ta fahimci komai ba.

Kofi aka miko masa, ya karba yana mika mata, saita karba taji duminshi a hannunta, da sauri ta dago dayan hannun ma da yatsunta da suka kandare saboda sanyi, ya biya kudi suka sake fitowa

"Kisha, zaki danji dumi kafin mu karasa, mantawa nayi ince miki ki dauko rigar sanyi saboda in kin sauka"

Da straw din ta fara zuqa, taji gardin har

29 / 51