Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
rigar da ta zaba da ya bude baki da nufin magana tace masa
"Ni zaka dinga sakawa, dan Allaah tunda kai ba jemage bane ba, in muna tare kasa in ganka a wata kalar kayan bayan bakake"
Ya karbi rigar yana juyawa
"Meye jemage?"
Ya tambaya
"Bat"
Ta bashi amsa, yayi dariya
"Jemagenki ne, I'm your batman"
Itama dariyar ya bata, ta gefenta budurwar tazo wucewa, tunda tana jikin kofar ne, ba zatace ga yanda abin ya faru ba, a girman jiki, da tsayi duka budurwar nan ta fi Maryama, haka jakar da take rike da ita ma batasan ina ta bulla ba, ta daisan gangar jikinta ta motsa, ta kuma ji hannunta cike da gashin budurwar da ta janyo dashi, taga karasowar Haris da kiciniyar da yakeyi da ita, amman batajinsu, batajin duk abinda suke fada
"Ta cire, wallahi saita cire rigar nan"
Dakyar Haris ya karbeta, fuskarta duk tayi ja, koma me take fada bai damu Maryama ba, haka shima abinda yake fada, ita da batama jinsu
"Kace mata ta cire"
Tayi maganar idanuwanta cikin nashi, kuma haka akayi, da ta cire rigar saita wullowa Maryama a fuska, ta cireta ta rike a hannunta, sannan ta juya, tana shirin rigan budurwar ficewa daga dakin, da Haris ya riko mata hannu yanda tayi amfani da duka karfinta ta hankada shi saida yayi baya kamar zai fadi
"Karka tabani, da zunubinka, karka tabani da daudar da take jikinka..."
Satin da Maryama zata taho New York ya fara duba inda zata zauna, gidan da zai ajiyeta, haka kawai yaji yana bukatar tazara mai yawa a tsakaninsu, nan din, inda yake, wajene da yakeyi masa dadi, wajene da yakeyin duk abinda yaga dama babu wata fargaba, to duk wanda ya sani anan suka hadu, sannan babu ruwan wani da abinda zakayi, itace mutum ta farko da zatazo inda yake, ta farko da bayaso taga wannan bangaren nashi. Shisa ya kaita can unguwar, shisa ya zabi ya dinga zirga-zirgar tsakanin nan din da can. Kuma sau nawa yake so ya dauko Maryama yazo da ita makarantar nan amman yake fasawa?
Akwai wajeje da yawa da idan ya wuce sai yaso ace tana zaune a wajen, shikuma ya haskata da camera dinshi, amman kuma yana daga cikin sanannun mutane a makaranta, saboda yanda yake a wajen mata, yanda suke bibiyarshi, yanda kuma yayi kaurin suna wajen kin saurarar kowa da sunan soyayya
"Mr no strings attached"
Haka yaji ana masa lakabi, in kinyi masa, inya kulaki to karki tsammaci wani abu daya wuce neman juna, koya yaga kina neman wuce hakan ba zai sake kulaki bama. Akwai tarin matan da suke kullace dashi, suke jin haushin shi, ko ba'a fada ba ya sani, kawo Maryama ba karamar barazana bace ga Labulen dayake lullube da wannan sirrin nashi. Idan aka tambaye shi zai rantse kai tsaye, abinda wannan matan kawai zasu nunawa Maryama shine kwarewa, shine jure ma yanayin shi, amman haka yake tsintar kanshi da hasashenta, ace dandanonta ne ya hadu da gogewarsu, kuma ita taki bari ya gogar da itan, taki sakin jikinta gabaki daya dashi har yanzun.
Jiya, wayar da sukayi, ya samu sukunin daya kwana biyu bai samu ba, da safen ma sunyi magana, kafin ta fita da Awwab, washegari yayi niyyar zuwa, shisa ya tsara clearing din duk wani abu da yake kanshi a yau din, amman akwai wani yanayi a muryar Maryaman daya hautsina masa lissafi, ta sake, yana zaunen ya dinga hasaso duk wani abu da zai gifta a tsakaninsu, cikin yanayin daya kwana biyu rabonshi dashi saboda fadan da sukeyi, yana kwancen ya kasa tashi yayi komai saiga Autumn, yarinya daya daya san tana sonshi, amman da yake bata fito da maitarta fili ba sai alakar tasu ta jima, kuma a yanayin da yake sai kawai ya biye mata.
A mugun tunani, a mummunan mafarki bai taba hango Maryama zata tako inda yake ba, kuma inta tako din tazo ta bude kofa ta shigo ta samu wata a samanshi, a tsayin shekarunshi na duniya, yaune ya fahimci kalmar nan ta
"Humiliation"
Yau yaji ya muzanta ta sigar da baisani ba, yaji kunya irin wadda baisan da ita ba a rayuwarshi, kuma kamar abubuwan basu isa ba, sai ya kara da wani irin tsoro da firgicin ganin yanayin dake fuskar Maryama, da ta riko Autumn kuwa wannan yanayin na cikin idanuwanta ya bala'in firgita shi, haka na yanzun
"Maryamm"
Ya kara kira, cike da roko, da wani abu na daban, kuma kamar yanda kiran nata ya rufe mata jinta, haka ya sake dawo mata dashi yanzun, ta kalle shi, itafa wani abun nan daya tarwatse a cikin kirjinta ne takeji yana bin kafafuwanta, kuma kamar shine yake sakata jiri, saita kalli kafafuwan nata, suka kalla tare da Haris da yabi abinda take kallo shima, zuciyarshi ta buga, ta sake bugawa
"Jini...jini kike zubarwa"
Tasan ta dago, ta kuma ga labbanshi sun motsa, sai fatanta na dazun ya samu karbuwa, ganinta ya dauke tare da jinta...!
*
So takeyi ta tashi, ta bude idonta, saboda yanzun da yake rufe babu abinda take gani sai Haris da budurwar nan akanshi, kuma kirjinta zafi yakeyi, zafi na gaske, kamar an kara mata garwashi, shi ta fara kai hannu ta murza batare da ta bude idanuwan nata ba
"Maryamm"
Haris ya kira, duk da saida yayiwa likitanta alkawarin ba zaiyi ko kwakkwaran motsi ba bayan sun kawota asibiti anyi nasarar tseratar da cikin jikinta da yake barazanar zubewa, haka suka sakashi a gaba da tambayar abinda ya firgitata, daya san ba zasu kyaleshi ba sai yace musu an kirasu daga gidane aka fada musu mutuwa. Sannan suka sama masa lafiya. Yau kwananta biyu ko motsi batayi ba, da kanta take numfashi babu taimakon kowacce na'ura, amman taki tashi, kallo daya zaka yiwa Haris kaga yanda ya kara duhu, yake kuma a firgice
"Maryamm"
Ya sake kira a hankali, sai kuwa ta bude idanuwanta, akanshi, kallonshi takeyi kamar tana neman wani abu a jikinshi, sai kuma ta shafa cikinta
"Babu abinda ya same shi"
Ya fada da sauri, inda cikin nan ya zube bayajin zai iya dauka, zai iya yafewa kanshi
"Kema babu abinda zai sameki"
Sai taji dariya ta kamata, amman kuma bata da karfi ko kadan
"Ganjaa"
Ta kira da karamar murya, ya matsa kusa da saurinshi
"Awwab...yarona fa?"
Sai yace mata
"Yana daycare dinshi, zanje in dauko shi in lokacin tashi yayi..."
Ta danyi kokarin daga masa kai, lokacin ne kuma likitanta da wani Nurse suka shigo, dole Haris ya fita, suka sake duba Maryamm, wata allurar baccin suka karayi mata, a cewarsu jininta da yayi sama har yanzun baiyi saukar da suke fata ba, ga jinin da ta zidda, daga ita har abinda yake cikinta basu gama fita daga hadari ba. Yaji hankalinshi ya kara tashi, dakyar ya tafi dauko Awwab, saiya samu ya mikashi wajen da ake kula da yara kanana na cikin asibitin ya koma wajen Maryama. Lokacin data sake farkawa kiranshi ta karayi, ya amsa
"Ba mafarki nayi ba ko?"
A hankali ya daga mata kai
"Kaine, kaine da wata..."
Ya sake daga mata kai
"Me yasa?"
Yayi shiru, bashi da amsar wannan tambayar, ko yayi kokarin amsawa bashi da amsa, yama kasa hada idanuwa da itane saboda abinda yakeji
"Tun yaushe?"
Da sauri yace
"Maryamm"
Ta sake maimaitawa
"Tun yaushe?"
Dan tana tambayar ne tsikar jikinta na tashi, wata irin dauda takeji tana rufar mata, daudar da Haris ya dade yana goga mata, datti, dattin zina, tana so ta san ko tun yaushe, watakila ta iya hasaso irin wankin da zatayiwa jikinta, to inta wanke jikinta ya zatayi da zuciyarta, ita tafi jin daudar a ciki fiye ma da gangar jikinta, ko dai tunda tana asibiti yanzun magana zatayi musu, su bude kirjinta su ciro zuciyar su tsomata a ruwan hydrogen, in tayi wannan kumfar da ciwo yakeyi in an zuba masa, sai su bita da clean da hypo? Ta dan kalli jikinta, wai ko zata ga yana fitar da hayaqi, ko tiririn da takeji ya fito har waje.
"Zafi nakeji Ganja, babu AC a dakin nan?"
Ta tsinci kanta da amsa masa
"Zafi?"
Ta daga masa kai
"Zafi nakeji, ka kunna mun AC, ka qureta duka, zafi nakeji har cikin kirjina"
Ya mika hannu da niyyar taba jikinta, yanda ta mirgina inda babu makangi a jikin gadon ya tabbata saita fada kasa, har saida ta cire karin ruwan da akeyi mata
"Karka tabani, dan Allaah karka tabani"
Ta karasa cikin wata 'yar karamar murya, dole ya mike ya kira mata Nurse, aka goge mata hannunta da yake jini, sukace masa zazzabine mai zafi a jikinta, dan a gabanshi akayi mata allurar da ta sake komawa bacci, a karo na farko a rayuwarshi da wani abu ya same shi yaji ya furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Kalmomin sukayi masa nauyi a harshe, nauyi na gaske, nauyi na rashin sabo, ya saka fuskarshi cikin tafukan hannunshi, ya sake furtawa, ya cigaba da furtawa wani irin abu yana ratsa shi, kuma a lokacin ne wayarshi da ya dauko tayi kara a cikin aljihunshi, daya fito da ita sai da yaji ta nemi subucewa ganin Alhaji Sa'id ne, ya kasa dagawa saida kiran ya yanke, wani ya kara shigowa, tukunna ya dauka yana kasa cewa komai, sai daga can Alhaji Sa'id yayi masa sallama, ya amsa a hankali
"Haris, kuna lafiya dai ko? Inata kiran wayar Mairama ba'a dagawa, daga bayama sai najita a kashe"
A hankali yace
"Muna asibiti ne Abba, bata da lafiya, amman da sauki..."
A cikin addu'o'in Alhaji Sa'id yakejin tsananin damuwa, shisa yace
"Zazzabine Abba, sunyi mata allura dan ta samu bacci sosai, idan ta tashi zan kira saiku gaisa"
Ya amsa da
"A'a kabarta ta huta sosai, in ta kara warwarewa saimu gaisa. Allaah yayi muku albarka, nagode kwarai"
Rabon da yaji alamun kuka harya manta, lokacin kuruciya ma anya zai tuna sanda yayi kukan karshe? Amman yanda Alhaji Sa'id ya ajiye kalmar godiyar nan saida yaji yana so ya fashe da kuka, to me yayi da zaiyi masa godiya? Ko godiyar neman kashe masa yarinya? To yama akayi komai ya jagule masa lokaci daya? Me zai kawo Maryama inda yake? Me yasa zataje? Ga abinda zuwan nata ya janyo musu. Ko da sukayi masa suggesting rike Maryama dan tana bukatar absolute bed rest da gudunshi ya yarda, data tashi dai haka tace masa
"Ka kaini gida Ganja, ka mayar dani gida"
Cikin taushin murya yace mata
"Sun baki bed rest ne, kiyi hakuri tukunna, ko da inaso in kaiki ba za suyi clearing dinki fit to fly ba"
Ashar ne dankare da makoshinta, ashar din da tarbiya ta nade harshenta daga furtashi, ashar din da tasan in Hajja tasan ta taba jinshi ma saita san yanda tayi ko ta kunnenta ne ta dura ruwan sabulu ta daurayo mata shi tas, so takeyi ta hada shi fit to fly din da bed rest din a waje daya ta maka musu shi
"Gida nake so in tafi"
Ta kara maimaitawa
"Zamu iya rasa Babynmu Maryamm, dan Allaah ki kwantar da hankalinki, zan kaiki gida, I promise"
Sai taji taja tsaki
"Inya bare ai ya huta, nima na huta, duk mun huta"
To me zaizo yayi a duniyar? Rabon ya fito yaga zabin da kaddara tayi mata, tayi musu? Na auren dan wiwi, mazinaci, wai itace tayi zaman aure da mazinaci, itace Haris ya birkida da matan waje yazo ya birkida da ita, suka hadu cikin daudarshi, ita fa, wannan tiririn takeji yana kara gauraye mata jikinta, daman biyya tayi ai, ta aureshi.
Ba ita ta zaboshi ba, zabo mata akayi, ta karba, bata nemi wani dalili da zaisa a zabo mata shi ba ta karbeshi, yanzun kuma zata mayar dashine, kuma tana fatan kar wanda ya tambayeta dalili, suyi mata wannan adalcin
Sai dai wata kaddarar ai bata ma fara ba...
36
Haris ba zaice ga ranar daya zauna yayi addu'a akan wani abu ba, tunda in ya idar da sallah ma mikewa yakeyi ya kama harkokinshi, gara ma bayan zuwan Maryama, ko da baije masallaci ba, in yayi sallah a gabanta yana kokarin mikewa zatace masa
"Bakayi addu'a ba, dan azkar din nan na bayan Sallah, wallahi randa wata bukata ta taso maka zaka sha mamaki, sai ka tsinci kanka da kunyar Allaah..."
Dariya take bashi duk inta fadi hakan, wata rana dai yanayin Azkar din bayan sallar tunda ba mai yawa bane ba, da yatsun hannunshi ma saiya kirga talatin da uku sau nawa, amman bayan hakan bayajin yana da wani abu da yake so ya roka, a tunanin shi komai yana tafiyar masa lafiya kalau. Sai gashi washegarin kawo Maryama asibiti daya idar da sallar asuba ya daga hannayenshi sama, bakinshi yayi masa nauyi, wani irin nauyi da bai taba sanin akwaishi ba a duniya, to me ya kamata yace? Ta ina zai fara?
"Allaah nine Haris..."
Sai kuma yayi shiru, tunda haka Maryama tace
"Randa zakaje da bukatarka sai kaba Mala'ikun mika addu'a mamaki, zasuce wannan kuma daga ina? Yau kuma?"
Amman akwai ranar da tace masa
"Sai dai Allaah Mai Yawan Rahma ne, sai kaga Ya karba maka rokonka, amman da kunya gaskiya"
Shisa ya kara gyara zamanshi
"Allaah Ka ba Maryamm lafiya, Allaah cikin jikinta, babynmu...Babyn daka bamu, Allaah Karkasa Ya zube, Dan Allaah karya zube, nine nayi laifi, batayi komai ba"
Hankalinshi bai kara tashi ba sai da tayi kwana uku bata bude idanuwanta ba, ga Awwab sai yake ganin kamar wani irin kallo yaron yakeyi masa, kallon
"Ina ka kaimun Ammi na? Me kayi mata?"
Gabaki daya a firgice yakejin shi, kallo daya zakayi masa kagane wannan firgicin, duk kuwa da yana komawa gida yayi wanka, ya sake kayanshi, amman bashi da natsuwa, ko lokacin da suka rabu da Aise bai tsinci kanshi cikin irin wannan rashin sanin abinyi din ba. Yau kwanansu takwas, ta tashi, ta kalle shi tace masa
"Gida zan tafi Ganja, ina barin asibitin nan gida zan tafi, bansan taya ba, amman ba zan zauna ba, ba zan zauna da kai ba...ka dauko mun wayata"
Wayar na jikinshi, yaje ya dauko mata acan gidan, amman bai sakata a caji ba, da ita yaketa yawo, kuma duk da babu cajin saiya kasa bata, haka kawai yakejin tsoron bata, abinci ma daya ya samu take karba
"Ka taba, hannunka da dauda, ka tabamun abinda zan kai cikina da hannunka"
Baisan sau nawa ya dirje hannuwan nashi a bandaki ba, har sanitizer saida ya saka jiya yazo ya daga mata
"Na wanke Maryamm, dan Allaah"
Wani irin kallo tayi masa
"Waye ya gaya maka kaf kasar nan akwai sabulun da zai wanke dattin da kake yawo dashi? Dattin daka cuceni ka goga mun"
Ya rasa yanda zaiyi da ita, har dadi yakeji idan yaga ta koma bacci, fata yakeyi su cigaba da riketa a asibitin nan harta haihu, watakila kafin nan ya samu zuciyarta tayi sanyi, dan a yanda take din nan tsoron ace an sallamesu sun koma gida yakeyi. Ko yanzun ma bacci takeyi, wayarshi ce taketa vibrating da wata lamba da baisanta ba, an jera masa kira har hudu, shisa ma ana biyar din ya yanke hukuncin dagawa yaji waye zai dameshi haka, sai gashi yanda zuciyarshi ta buga a kirjinshi da yaji muryar mai kiran saida ya tashi tsaye
"Ba...Baba"
Ya furta da madaukakin mamaki
"Ina zamuce a kawomu? Ga Uber mun samu, ina zamuce?"
Shi zamuce dinne ya kasa fahimta, bashi kadai ba kenan? Kuma bai gane sun samu Uber ba, zuwa ina? Uber a ina?
"Haris muna tsaye fa, kuma mun tsayar da mutum, kuna asibitin har yanzun?"
Da harshenshi da yakejin ya bushe lokaci daya har makoshi ya amsa dakyar.
"Asibiti Baba, muna asibiti..."
Kuma a hankali, cikin wani sabon bugun zuciyar ya fada masa sunan asibitin. Sai gashi a kofar asibitin yana raba idanuwa cikin jiran ganin ta inda zasu bullo, Baban da wa? Me yasa yanzun? Me yasa zasu zo yanzun? Me sukazo yi? Duk lokacin daya kamata, lokacin da suke lafiya kalau daga shi har Maryamm din, kamar dai bayan haihuwar Awwab da Alhaji Mustafa yazo, ai haka ya dinga yi musu addu'a harma bayan daya koma saida yace masa
"Naji dadin yanda na ganku Haris, naji dadi sosai"
Yanzun kuwa ko da bai kalli mudubi ba, ya tabbata bashi da natsuwa, sannan kallo daya zakayiwa Maryama ma kasan ciwon daya kwantar da ita ciwone da ba dukanshi asibitin nan suke da maganinshi ba. A karo na farko yaji yana so ya ruga da gudu, ya boye, ya boyewa Alhaji Sa'id daya fito daga motar nan cikin fararen kaya da suka kara haska tarin kamala da dattakonshi, wani mutum guda daya da ko a waya Haris yake tsintar kanshi da jin nauyi, dakyar ya iya tsayawa suka karaso, yana fatan abinda yake saman fuskarshi murmushi ne
"Haris, sannu da kokari"
Cewar Alhaji Sa'id bayan sun gaisa, Haris da kafafuwanshi har rawa sukeyi yayi gaba suna binshi a baya, dan a barsu su shiga ya fada musu cewa 'family' ne. Lokacin Maryama bacci takeyi, sai suka sake fitowa waiting area din, Alhaji Mustafa yake ce ma Haris
"Ina Awwab?"
Ya fada musu yana daycare, amman anjima zaije ya dauko shi
"Bafa muci wani abu ba, dan nikam yunwa nakeji"
Cewar Alhaji Mustafa, sai kuwa Haris yayi saurin cewa
"To ko zamu fita ne, in sama muku wajen kwana nan kusa, sai kuci abinci ku huta, kafin lokacin ma Maryamm din ta tashi"
Alhaji Sa'id ya jinjina kanshi cikin amincewa, kafafuwanshi duk sunyi dayi saboda zaman jirgi, kuma yanda yaga Maryaman na bacci saiya samu natsuwa, zuciyarshi tayi masa sanyi, yana so ya dan kebe ya kira Hajja ya fada mata ko itama zata samu kwanciyar hankali, kwanakin nan duk ba'a nutse suke ba, ita Hajjan ma harta fishi damuwa duk kauda kai da kawaicinta akan yaran
"Da Maryama nake kwana da ita nake tashi, tun kafin kace mun bata da lafiya din nan take yawan fadomun fiye da misali...dan Allaah kaje ka dubota"
Daman yayi niyya, sai kuma ta kara masa karfin gwiwar zuwan, kafin dai yayi magana ne Alhaji Mustafa ya kirashi yana ce masa
"Ka shirya fa muje mu duba yaran nan, wannan baccin da ake cemun Maryama nayi kullum bai kwanta mun ba"
Ba karamin dadi yaji ba, tunda dole shi zai yiwa magana daman, yana da passport dinshi, amman yana bukatar processing visa, gabaki daya baisan ta inda zai fara ba, sai gashi da yake idan kudi suna maka abubuwa da yawa, to sanayya ma tana aiki, sun samu visa cikin kankanin lokaci
"Kuje kai da Abbanka, ni kam zan jira har Maryamm din ta tashi, kawai ka fara samo mun abinda zanci"
Yanda yayi maganar Haris yasan babu wajen yi masa musu, sai kawai ya fara fita shi kadai, abinda yake tunanin Alhaji Mustafa zai iyaci shi