Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
duk bincikensu ba zasu iya ganowa ba balle su dauka. Yanzun ma maganar turaren sukeyi, suna ja mata Hadith din da ya haramtawa mata fesa turaren da wani zaiji kamshin shi idan zasu fita
"Ke saurayi ya kawo miki, shine kika shanshara kika fito"
Cewar Asiya, har sukazo gida, ta tafasa batace musu ba, meatpie dinma da aka gaji dayi mata kwalele aka bata, gutsira daya tayi masa dakyar ya wuce makoshinta, saita ajiye ta kwanta, a ranta take fatan Allaah Yasa ba zazzabi zatayi ba, ta kasa gane yanayin jikinta gabaki daya. Batasan bacci ya dauketa ba saida taji ana tashinta
"Baccin yamma Maryam, sai kinyi zazzabi...ke Khairi kina ganinta maimakon ki tasheta"
Cewar Hajja, Maryam din ta tashi tanajin kanta yayi mata nauyi
"Kije ki wanke fuskarki kizo Abbanku yana kira, yana falo"
Kai ta daga, kamar ma bata gama fahimtar abinda tace ba, haka ta shiga bandaki ta wanke fuskarta, ta fito tana nufar falon
"Abba sannu da zuwa"
Ta fadi da murmushi a fuskarta, ya kalleta yana ganin yanda fuskarta ta kumbura saboda baccin da tayi
"Me ya sameki?"
Tasa hannuwanta duka biyun tana taba fuskarta, wani abu daya fito masa da kuruciyarta, shekarunta sha shida suka haska a idanuwanshi kamar jiya ya riketa yayi mata huduba. Sai yake jin rauni na kara dirar masa
"Bacci nayi, anyi rasuwa shine aka tashi da wuri a Islamiyya, da muka dawo sai nayi bacci, Abba ka kawo mana dublan?"
Maganarta tasa shi yin gajeran murmushi
"Dublan dai Mairama?"
Ta daga kai
"Na bikin da kukaje fa"
Tayi maganar tana karasawa cikin falon ta zauna a kasan kujerar da yake zaune, kusa da kafafuwanshi, yanda ta saba, ko wani ne ya zauna a wajen nan in tazo saita saka rigimar da zatasa Alhaji Sa'id yace a tashi a bata wajenta
"Ai wajen daurin aure ba'a bada dublan, sai dai goro, gashi nan in kinaci"
Ta girgiza kai da sauri
"Bana cin gori ni kam Abba, bansan me yasa mutane suke cinshi ba duk dacin shi, naga kun kwana ne shisa na dauka an baku dublan"
Shine ya girgiza mata kai wannan karin, ya kalleta
"Mairama"
Ya kira, daman in yana waje kacokan hankalinta akanshi yake, yanzun ma kara natsuwa tayi tana kallonshi kafin ta amsa, shikuma ya cigaba da magana
"Kinsan waye Alhaji Mustafa a wajena?"
Ta daga masa kai
"Abokinka ne, babban abokinka, ka bamu labarin yanda kuka hadu dashi"
Ya numfasa, kalamanshi yake ta tattarawa suna neman bajewa
"Yau ya rokeni alfarma Mairama, bai taba rokona komai ba tunda na sanshi..."
Ta kalli yanayin Abban nata, zuciyarta na neman karyewa, saita tsinci kanta da furta
"Kayi masa mana Abba"
Cikin karamar murya
"Nayi masa, alfarmar ce mai nauyi, yanzun kuma nake kara jin nauyinta dan ta hada dake"
Ya kamata ace zuciyarta ta buga, amman bataji komai ba, kallon Alhaji Sa'id kawai takeyi
"Yau na bayar da aurenki Mairama, ina ba duka yarana zabine, ina ba kowa dama ya kawo mun mijin daya nutsu dashi, haka kuma nayi addu'ar kuma inyi muku, shisa na rasa ta inda zan baki hakuri Mairama, ban baki wannan zabin ba"
Ko kadan bugun zuciyarta bai canza ba, batama san hawaye takeyi ba saida taji duminsu akan kuncinta, ta kuma gane ta fahimci duk abinda yace saboda labbanta da suka furta
"To Abba..."
Irin kallon da yakeyi mata ne yasa tayi saurin saka hannu ta share hawayen da kamar ta bawa wasu kofar zubowa ne
"Kingane me nake fada?"
Ta daga masa kai
"Ba auren kawai na bada ba, an daura, an daura aurenki da Haris yau...ga sadakinki nan"
Ya karasa yana daukar kudin da Hajja ta ajiye masa ya mika mata, batasan ya akayi tasa hannuwa biyu ta karba ba, sai shima ya tsinci kanshi da mayar da hannunshi cikin nashi aljihun ya dauko mata goro guda biyu ya sake mika mata
"Goron ne...kiyi hakuri ban baki zabi ba"
Ta girgiza masa kai tana kasa cewa komai, sukayi shiru su duka
"Nagode, Allaah Yayi miki albarka"
Muryarta na rawa ta amsa da
"Amin Abba..."
Kuma sai ta mike, da kudin, da goron, harta tafi ta dawo tace
"Me zanyi dasu Abba? Kudin? Da goron?"
Yaso ya kakaro murmushi, hawayen da take tayi ne suke kara karya masa zuciya
"Naki ne duka"
Saita mika masa da hannuwanta biyu
"Ka ajiyemun to"
Baiyi musu ba ya karba, saita juya ta nufi hanyar dakinsu, ta tura ta shiga, ta karasa, amman akan gadon Khairi ta zauna batare da tasan tayi hakan ba, yanayinta yasa Khairin tashi zaune
"Maryama? Lafiya? Kuka kikeyi...meya faru?"
Ta share hawayenta, ta kalli Khairi, wasu hawayen suka sake zubo mata
"Zazzabi nakeyi...jikina zafi yakeyi mun"
Data taba jikin Maryam din sai kuwa taji akwai zazzabin
"Kiyi hakuri, bari in kira Hajja sai ta baki magani, in kuma asibiti zamuje saimu tafi, amman kece kike yiwa ciwo kuka Maryam..."
Khairi ta karashe da damuwa a muryarta, saida ta kai kofa sannan Maryam tace
"An daura aure na yau, Abba ya fadamun ya bada aurena, wai ya ba Haris"
Sai khairi tayi saurin dafa kofar saboda kanta da taji ya sara, babu shiri ta koma cikin dakin tana kama kafadar Maryam din ta girgizata
"Bangane an daura aurenki yau ba"
Ta saka idanuwanta da suke cike da sababbin hawaye cikin na Khairi da suke cike da firgici, dan tunda take bata tabajin wani abu da yake neman birkita mata tunani lokaci daya ba irin wannan
"Haka Abba yace, ya bani kudi da goro sai nace ya ajiyemun"
Cikin Khairi ya murda
"Wai wanne irin aure? Aure fa kikace, kinsan meye aure?"
Maryam taji dariya ta kwace mata
"Aure yace mun"
Khairi tayi tsaki tana sakin kafadar Maryam din ta wuce ta fita daga dakin, kanta tsaye ta wuce dakin Hajja ta kwankwasa, saida ta bata izinin shiga tukunna ta tura da sallama a bakinta
"Hajja kizo, Maryam bata da lafiya, tana zazzabi, gashi tana wasu surutai wai an daura mata aure...kizo a kaita asibiti, kuka takeyi ma"
Sai Hajjan ta mike
"Ina Asiya?"
Khairi ta amsa da
"Tana dakinta inajin, bari in kirata, tare zamu tafi mu duka?"
Batama jira amsar Hajjan ba ta juya ta fita, sanda suka koma dakinsu ita da Asiyar sun samu Hajja acan, tana zaune, ta rike Maryam a jikinta da take wani irin kuka har jikinta na bari, a cikinsu babu wanda zaice ya taba ganinta tana kuka haka
"Wai zazzabin ne Hajja?"
Asiya ta fadi cikin rawar murya
"Ku zauna"
Cewar Hajja, babu wanda yayi musu, a kasa suka zauna
"Yau an daura auren 'yar uwarku, Abbanku ya bada aurenta a Maiduguri da sukaje, ya ba Haris din Babanku na Tudun Wada..."
Hajjan suke kallo kamar tayi musu wani yare
"Aure kuma Hajja? Maryam din? To saboda me?"
Asiya ta tsinci kanta da tambaya
"Saboda ya isa...ko idan ya daurawa wata a cikinku zatayi masa musu ne?"
Hajjan ta fadi tanayi mata wani kallo da yasa ta sadda kanta kasa, hawaye na balle mata, zuciyarta sai bugawa takeyi, ta rasa ta inda zata fara daukar wannan abin, anfa daurawa Maryam aure ake ce mata, da Haris din da a cikinsu babu wanda ya taba ganinshi, to yaushe ma aka fara haka? Yaushe Abban nasu ya fara haka? Wa aka taba yiwa irin wannan auren? Ishaq din fa? Ita kanta Maryam din ta ina zata fara? Tana jin yanda hawayenta suke zuba, Khairi ma kukan takeyi, 'yar uwarta take tayawa kuka, dan ita ko dukan Maryam akayi tare suke kukansu, kome ya samu Maryam tare suke rabawa, a yau dai tanajin wani abu ya samu Maryam wanda ba zasu iya rabawa ba, wani abu da Maryam din ita kadai zata dauki abinta.
"Yanzun za'a kira sallah nasan, ke Asiya ki bata paracetamol tasha, sai kuyi sallah...bance ku zauna kuna kuka kamar anyi mutuwa ba, ku kula da 'yar uwarku"
Suka daga mata kai, tasan lallashinsu ya kamata ta zauna tayi, amman inta kara mintina biyu kukan zata tayasu, batason suga rauninta akan wannan auren, sai ta fice tana barinsu. Suka kuwa tashi suka koma kan gadon inda Maryam take kwance, ita fa in zasu tambayeta a halin yanzun bata ma san kukan me takeyi ba, gabaki daya batama san me takeji ba, kukan ne yake ta zuwa da kanshi, ta kasa tsayar dashi, batayi gardama ba tasha paracetamol din da Asiya ta bata, ta kuma yi alwala, amman sallar takeyi tana kuka, harta idar bata daina ba
"Kar kanki yayi ciwo Maryam, dan Allaah kiyi hakuri haka, ai nasan Abba zai kara yi mana bayani...kuma ba wani abu bane In Shaa Allaah, ba zaiyi abinda yasan zai cutar dake ba"
Asiya ta fadi a tausashe tana share hawayen itama
"Na sani"
Maryam tace cikin shesheka
"To ki daina kuka"
Saita kalleta
"Na kasa"
Aikuwa da gasken ta kasa, a haka sukayi isha'i, sun karbi abincin da Hajja ta zuba musu, babu wanda yaci na kirki, Maryam da suka matsa mata loma daya tayi ta fara yunkurin amai, haka suka tattara abincin Khairi ta mayar kitchen ta dawo, yau a gadonta suka kwanta ita da Maryama, Asiya kuma ta kwanta akan na Maryam din, suka kwana anan gabaki dayansu, bayan wani baccin wahala ya dauki Maryam din, dan zazzabine a jikinta ga kuma ciwon kai saboda kukan da tayi.
Sai dai su sun samu bacci, ita kuwa Hajiya Rumana yanda taga dare haka taga rana, musamman da a karo na farko bayan ta kira Alhaji Jibril da kukanta riris ya kware mata baya
"Haba dai Rumana, kinsan muna da halaye da yawa, za'ayi mana shaida akan abubuwa kala-kala, harda son kanmu da muke dashi, amman kowa zaice dattako halin gidan nan ne, a jininmu yake, iyayenmu da kakanni ba kananun mutane bane, sannan munsan halacci, to abinda Alhaji Sa'id yayiwa mijinki kenan, halaccin daukar 'yarshi ya ba Haris batare da wani dar ba, bayan naki dan uwan, uwa daya uba daya yace hana..."
Kuma ya cigaba da fadin
"Mun zauna ni da Modu, saboda zancen shi bai zauna mun ba, ni na rutsa shi da tambayar dalilin da zaisa ya hana Haris auren Aise ya gayamun, a ganinki a irin amincin da yake tsakaninsu da kike yawan korafi akanshi shi Alhaji Sa'id din zai rasa sanin halin Haris din? Ina kaunarku, kinsan bana shakkar nunawa, ina kuma kaunarku da duk ahalinku, amman koni ba zai wahala in dauki 'yata in ba Haris, ki karbi auren nan da rufin asirin da nake hangowa tare dashi..."
Bata jira ya kara dora kowacce kalma akai ba ta kashe kiran tana kara rushewa da kukan bakin ciki, wanne so Alhaji Jibril yake magana yanayi mata? Aita dauka ko a gidan gala ta tsinci Haris din ta dauke shi tace ya zama nata su masu yi mata kara ne, masu rufa mata asiri ne. Sannan ko da gaske ne Haris nayin abinda Modu ya lika masa, suna nufin ba zasu iya daukar 'ya su bashi ba? Ta share hawayenta, tana kissima shikenan, zatayi shiru, ai ba zata bari Alhaji Sa'id yayi nasara biyu akanta ba, tana da yakinin ba wani abu bane yasa ya dauki Maryam ya ba Haris sai kwadayin abinda zai kara samu sanadin hakan, abinda 'yarshi zata yago musu.
Zatayi shiru taga abinda Alhaji Mustafa zaiyi,
Haris dai bayan dakon cikinshi da tayi babu wanda ya tayata nishin fito dashi,
Gasu gata, zata ga ta inda za'ayi wannan zaman auren in dai jininta na yawo a jikin Haris...
12
Idan ya daga yatsunshi zai kirga abubuwan da ya damu dasu, dama wanda ya taba sakawa a ranshi, tunda baya lissafawa da iyayenshi balle kuma 'yan uwa, su wannan babu wanda ya bashi zabi akansu, sai sauran abubuwan suka zamana yan kadan, idan kuma auna 'yan kadan din zaiyi akan sikeli, a yanda yakeji a halin yanzun, Aise ce zata zamana a saman komai, tunda in ya duba gaba, yayi tunanin inda yake fatan rayuwa ta kaishi sai yaganshi tare da Aise din, hannunta cikin nashi, ko hannunshi cikin nata, idan kuma ya hangi rayuwar, baiga Aise din a ciki ba sai yaji komai ya hargitse masa, kamar wani gini da ba rushewa yayi ba kawai balle yayi tunanin tsintar wani abu da zai harhada, murmushewa yayi, iskar da batayi niyya bama zata iya kadar da abinda yayi ragowa.
Shisa daya amsa wayar Alhaji Mustafa, suka gaisa yace masa
"Ina so muyi magana Haris, ba zai yiwu ta waya ba, inaso inzo..."
Sai yace masa
"Zanzo Baba, ni zanzo, nan da kwana biyu In Shaa Allaah"
Ya gama exams, akwai mentor dinshi, asalinshi bature ne amman kuma haihuwar nan kasar Italy din, ba alkawari yayi masa ba, ya dai fada masa akwai yiwuwar ya sama masa clearance ya bishi aikin sati biyu a kasar Syria, dan yana daga cikin tawagar masu kawo labaran kai tsaye game da yakin da ake tayi tun shekarar 2011, in yaso sai Haris din ya zama cikin wanda zasu dauki hotuna, dama ce da zata bude masa kofofi masu yawa in har ya samu, sai gashi a karo na biyu yana addu'a akan wani abu bayan Aise, to yana da hutu kafin aikin dama wasu abubuwan da yake ta processing, haka kawai bayason wata hayaniya shisa yayi shiru yaki fadawa kowa ranar graduation dinshi, yasan daga Hajiya Rumana har Alhaji Mustafan zasu zo, haka ma 'yan uwanshi, Aise kadai ta sani.
Hajiya Rumana zatayi fada ya sani, amman zata hakura, ai ba iya nan zai tsaya ba, dorawa zaiyi da karatun, zai lallabata ne kawai. Dan haka Aise ce kawai a wajen, ganinta yasa shi jin yanda da gaske baya bukatar kowa bayan ita, bayama cikin yanayin kamar yanda itama ya kula babu wata walwalar kirki a tare da ita
"Ya zanyi wata kusan uku banganka ba? Ya zanyi?"
Ta tambaya muryarta na karyewa
"Zamuyi waya kullum Aise, zamuyi video call"
Ta girgiza masa kai, hawayenta na zubowa
"Ya mun kadan, komai zai iya faruwa a wata uku"
Ya tsinci kanshi dayin murmushi mai sauti
"Me zai faru? Sonki zan kara? Ko sona zaki kara?"
Ta juya idanuwanta da suke cike da hawaye, ya kama hannunta ya dora a kirjinshi
"Kina nan, tare dake zan tafi"
Tayi dariya ta kama hannun nata da yake rike dashi ta canza musu waje
"Ga inda zuciyar take nan fa"
Shima dariyar yayi
"Idan tawa ba irin ta kowa bace fa? Tawa a dayan bangaren take, shisa son da nake miki ma nakejin shi daban, kamar babu irinshi, kamar yayi yawa..."
Ya fadi yana saka idanuwanshi cikin nata
"Son da nakeyi miki baiyi yawa ba kuwa Aise?"
Da dukkan zuciyarshi yayi mata tambayar, saboda abin ya fara bashi tsoro, yanda tunanin rasata kawai yake birkita masa komai, yanda yake kasa samun natsuwa a tare da duk wata mace in yana cikin wannan yanayi, yanda har wiwin shi bata batar masa da damuwar Aise, kiris ya hanashi kwankwadar giya daren jiya, wai ko zai samu saukin nauyin da kanshi yayi masa, har zubawa yayi a kofi, sai dai aman da yake ganin masu shanta na shekawa bayan tambelen da take sakasu na daga cikin abinda yake kara masa kyamarta, bayason irin wannan kwamacalar.
"Ina so ka kara sona, kayi mun son da zaka rabu da kowacce mace saini kadai"
Ya sakeyin dariya, kuma a ranar da zasuyi sallama ya kasa hana kanshi yin abinda zuciyarshi da gangar jikinshi sukaso, ya sumbaceta, hawayen daya zubo mata yasa shi saurin fadin
"Kiyi hakuri, na kasa ne, na kasa sarrafa kaina"
Ta girgiza masa kai wasu hawayen na kara zubo mata
"Bashi bane, ba kai bane ba, bansan me yasa ba, tsoro naji ya kamani Haris, kamar kana mun bankwana ne, kamar...ban sani ba"
Sai ya sake sumbatarta, fiye da na farkon, har saida jikinta ya fara kakkarwa a cikin nashi
"Wannan yayi miki kama da bankwana?"
Yayi tambayar yana rike fuskarta cikin hannayenshi
"Babu inda zani babu ke, kina jina, inda duk zanje ina tare dake, a komai nawa"
Ta daga masa kai, amman idanuwanta cike suke da shakkun da baisan ya zai goge mata shi ba, sai kawai ya kara riketa a jikinshi, kewarta na dirar masa. Dakyar sukayi sallama kamar zata sakeyi masa kuka, har mamakinta yakeyi, yanda kuka bayayi mata wahala, a wajen Aise, abin murna ma kuka takeyi masa, ko abune yayi mata kyau zata iya fara hawaye, komai nata yayi masa, ko motsi tayi sai yaji ta burge shi. Haka ya hada duk wani abu nashi tunda makarantar dai ko ya kara dawowa dora karatunshi yasan wani dakin za'a bashi daban. Jirginshi na safe ne, haka ya kwanta babu wani karsashi balle dokin zuwan safiyar.
Ko kadan baisan ruhinshi bane yake yiwa zuciyarshi alamar abinda yake jiransu a Najeriya.
*
Kallon Alhaji Mustafa yakeyi kamar yaune rana ta farko daya taba ganinshi a rayuwarshi, kamar kuma akwai wani bakon al'amari da yake faruwa da fuskarshi gabaki daya, ko sabon kai ya kara fitowa kusa da wanda yake dashi sun zama biyu, amman ba anan matsalar take ba, bawai shi bane, abinda yake fada ne, ai Haris yasan bashi da wata matsala data danganci lafiyar kwakwalwa, kuma cutar da bature yake kira da "Amnesia" babu yanda za'ayi ace ta dirarwa mutum yana zaune, bayan ya gama cin abinci har da ruwa, maganar da sukayi a ranar Asabar din na daga cikin maganganunsu da ba zai taba mantawa ba
"...Yau zamu nema maka auren Aise"
Haka yace masa, da yace zasuyi magana, ya kawo abubuwa da dama a ranshi, ciki harda hana masa auren Aise, kuma ko daya zauna a dakin Alhaji Mustafa din, abinda ya tsammaci ji kenan, shisa yake ta gayawa zuciyarshi wannan bakomai bane ba, son da suke yiwa juna shida Aise wani abune da suka shirya nunawa duniya bama iyayensu ba, dole zasu hakura, dole zasu barsu da juna in suka ga da gaske ba zasu rabu ba, to meye hadin maganarshi da Aise da abinda yaji Alhaji Mustafa ya fada a karshen zancen shi
"A gaban mutane Alhaji Modu ya nuna mun ba zai baka Aise ba Haris, cikin taron mutane...tun tasowarka ban taba yanke maka hukunci ba, banajin ma akwai lokacin dana nuna maka matsayina na uba, yau ina so ka bude zuciyarka ka karbi abinda nayi, alfarma nake nema"
Alfarma yace
"Na nema maka aure, na karba maka auren a wannan ranar, na karba maka auren Maryama yar aminina Sa'idu...ina fatan zata maye maka gurbin Aise"
To daman anawa neman aure alfarma ne? Yasan ana bada labaran da akayiwa mata auren dole, duk da abin bai taba kama hankalinshi ba sam, to su suna me za'ayi musu auren dole? Basu san 'yancinsu bane ba? Ko iyayensu basu san me sukeyi ba da kawai zasu kakaba musu aure daga sama sai kace wani kaya da in sun ga dama zasu wurgar, to shi baima tabajin inda akayiwa namiji abinda yaji Alhaji Mustafa yana fadin yayi masa ba
"Kana jina Haris?"
Cewar Alhaji Mustafan yana