Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
cimmasa ne. Tun ranar da yaji yana sha'awar ya ganshi a tsakiyar filin yaki yana daukar hotunan abinda yake da muhimmanci a game da yakin yana nunawa sauran mutanen duniya ya fara bin duk wata hanya data dace da zata saukaka masa hakan, a yanzun haka idan zai fadi adadin mutanen dake bibiyar blog dinshi da yake dora hotuna sai a zata idan akwai yiwuwar kudi su siya maka wannan mutanen abinda yayi kenan, workshops kuwa na sanannu a wannan fannin baisan adadin daya halarta ba, haka adadin mutanen da yayiwa email, wasu suka bashi hakuri cewa ba zasu iya taimaka masa da wani abu daya wuce 'yan shawarwari ba, wasu kuma suka yarda suka hadu har suka duba portfolio dinshi.
Burinshi ya samu manyan mentors ko guda biyune da zasu zame masa tsani wajen cimma wannan burin nashi. Ba wai rashi bane kawai Haris bai sani ba a rayuwarshi, harda tashin hankali, ranar farko da ya fara gane ma'anar kalmar shine randa Aise ta kirashi a waya tace masa tana cikin makarantarsu, da dokinshi ya fito, zuciyarshi shimfide akan fuskarshi saboda wannan ziyarar bazatan, amman kallo daya yayiwa rinannun idanuwanta da fuskarta da take a kumbure wani abu ya kulle a kasan cikinshi da baisan abinda zai kirashi ba.
Kuma ko da ta mika masa wasu hotuna yasa hannu ya karba, yanayin shi bai canza ba, tunda fuskarta ta sanar dashi ba lafiya ba daman
"Ni ne"
Ya fadi, yana cigaba da amsa duk wata tambayarta da
"Eh"
Tunda meye amfanin yayi mata musu? Aise ce fa, sonta yakeyi, son da yake fatan su kare rayuwarsu a karkashin inuwa daya, ko ta binne shi koya binneta, ai ya riga yasan dole zata sani wata rana, daman kuma bashi da niyyar boye mata cewa yana shan wiwi, matan dai, matan ma saboda wannan wutar da yake gani tana kara ruruwa cikin idanuwanta ne kawai zaisa ya boye mata, idan fatanshi ya kai mizani ma, da sunyi aure saiya daina, inya sameta me ya rage masa? Ai matan da zasu burgeshi bayan ta zama mallakinshi yana da yakinin ba masu yawa bane ba.
"Me yasa?"
Ta tambaya, yayi shiru kamar ba zai amsa ba, kafin ya dan daga mata kafadunshi duka biyun
"Ban sani ba Aise, haka kawai..."
To meye zaice dalilin da yake dashi? Rana daya ya kalli 2Pac yaji yana so ya zuki abinda yake zuka kawai dan yaji ya yake ji, wannan kuma zai iya zama dalilin da zaiyi amfani dashi ne? Matan kuma lokacin da zai gane amfaninsu a rayuwar kowanne namiji ne ya faru dashi da wuri, kuma tun lokacin saiya kasa dauke kai, ko da ba zaiyi komai da mace ba, shikam yana son yaji laushin jikinta a kusa dashi. Ba zaiki ace duk mirginar da zaiyi a wajen kwanciya su mirgina tare da mace kwance a kirjinshi ba, adadin soyayyar da ya keyiwa mata mai yawa ne, shisa yake so ya mallaketa ai, ta zama tashi, bai ko motsa ba ganin hawayen da suke zubar mata tana saka hannu tana gogesu
"Idan nace kabarsu duka ka zauna dani kadai zaka iya?"
Ya saka idanuwanshi cikin nata, saboda yana so taga gaskiyarshi, in zata iya ta leka zuciyarshi ko zai samu saukin harhada kalaman da zaiyi amfani dasu
"Sai kin taimaka mun"
Ta kalle shi tana son gane abinda yake nufi
"Saikin taimaka mun kin zama tawa Aise, zanyi kokarin bari idan kin zama tawa"
Da alama abinda take kokawa dashi mai nauyine, sai ajiyar zuciya takeyi
"Yanzun ba zaka iya ba ko? Ba zaka iya barin matan nan ba sai na zama taka"
Ya zabi yayi shirune tunda bayason kara mata ciwo akan wanda takeji, shima zuciyarshi zafi takeyi masa
"Shikenan..."
Ta furta tana goge fuskarta hadi da mikewa
"Shikenan zaki zama tawa?"
Ya tambaya da saurinshi shima yana mikewa, saita daga masa kai da wani irin rauni da bai taba gani a tare da ita ba, tunda in zai lissafa jaruman mutanen daya sani zai kira sunan Aise a farko-farko, ya kama hannunta, ta fisge, ya sake kama ta sake fisgewa
"Dan Allaah, zuciyata na ciwo"
Saiya kyaleta
"Tafiya zakiyi?"
Ta daga masa kai
"In rakaki?"
Ta girgiza masa kai, haka ya tsaya ya kalleta harta bacewa ganinshi, ko da yayi magana da ita yaji ta koma makaranta lafiya saiya dan samu natsuwa, baiyi zaton abin ya dameshi sosai ba sai lokacin da yaje kwanciya bacci, ya dinga juye-juye, duk hayakin daya bankada baiyi masa amfanin komai ba. Yana son Aise, kuma Aise tana sonshi, to soyayyarsu kadai zata isa kuwa? Shi ta bangarenshi yasan babu wanda zaiyi fada dashi akan samunta, Hajiya Rumana tana son abin, ko da Alhaji Mustafa bayaso yasan tasirin hakan ba wani mai yawa bane balle ya daga masa hankali, in yaja, ya turje zai barshi da zabinshi ne kamar yanda yasan yayiwa Munira, tunda kamar Hajiya Rumana a lokacin akwai wanda yaso ta aura, ita da take mace ma ba'ayi mata auren dole ba balle kuma shi namiji.
Amman Aise fa? Ina ma ta samu hotunan nan? Ya kamata ace ya tambayeta tunda yasan ba zata taba sakawa a bishi ayi masa bincike ba, sai ya kasa hakuri ya tashi zaune daga kwancen da yake ya dauki wayarshi, sako ya fara tura mata
Kinyi bacci?
Kamar itama shi take jira ta dawo masa da amsa
Na kasa...
Ya sauke ajiyar zuciya
Waya baki hotunan nan?
Amsa daya ta bashi
Mu'adh
Yaji wani abu ya hautsina a cikinshi
Ya bani, ya ba Mamma.
Sai yakejin kamar zaiyi amai, amman babu komai a cikinshi duk yinin ranar banda hayaki da black tea, da yake baya daga cikin mutanen da suka damu da abinci, in dai zai samu shayi saiya wuni yana gararambarshi
"To ya za'ayi kayi kiba Haris? Ka zauna kaci abinci ba zaka zauna ba? Jika dan Allaah sai tsayin"
Haka Hajiya Rumana take yawan yi masa mita, sai dai yayi dariya, shi dogo ne tabbas, amman yana da kirar jikin da bature yake kira da lean, ba rama yake da ita ba, kawai dai ba zaka kirashi da mai jiki bane ba, kuma da yake baya wani abu na motsa jiki daya wuce zirga-zirgar da ta zame masa dole, babu wani kwanjin daya tara, sau nawa yabi Logan gudun da yake masa tayi duk safiya yaji yana neman shekawa barzahu, ya kuma gane cewa huhunshi bashi da lafiyar da zaiyi wannan iyayin, ya tattara ya watsar. Kamar yanda yasan a lokacin ko tashi yayi ya shiga bayi babu abinda zai amayar, ko dan ruwan shayin ma ya jima dayin fitsarin wanda baibi jikinshi ba.
Meya tarewa Mu'adh da zaiyi masa haka, ina ruwan Mamma da wannan maganar, idan akwai wanda ya kamata ya sani ai Aise ce, tunda itace za tayiwa kanta zabi, a karo na farko da yaji an taba masa mutuncinshi a idanuwan da bayaso hakan ya faru, to ta ina zai fara zuwa gidansu Aise yanzun? Duk da zagi baya cikin dabi'arshi saida ya lalubo wani ya makawa Mu'adh a zuciyarshi. Sosai abin ya dinga damunshi na kwanaki, bai fara samun sauki a ranshi ba saida yaga Aise ta warware, sun fara hira kamar yanda suka saba, sai dai akwai abinda ya canza, a da ko muryar mace Aise taji tayi masa magana bata damuwa, za dai tace masa
"Ka fada mata kana da budurwa ko? Ka fada mata kai din na mace daya ne? Naji kamar tana makale maka murya"
In yayi dariya sai itama tayi dariya, tunda sai suyi watanni, banda kalmar ina sonka, ina sonki da suke rufe duk wata wayarsu dashi, haka in sun hadu, wani zancen soyayya baya hadasu, hirarsu sukeyi cike da shakuwa, son yana nan, duk sun sani, meye amfanin ayita magana akan abinda babu inda yaje? Amman yanzun da wahala su kare waya lafiya in dai zataji muryar mace a background, ko da bashi tayiwa magana ba, ya dinga jadda mata kenan, har saida ya biye mata sukayi fadansu na farko
"Ina sonki Aise, hakan baya nufin zaki dinga tsaramun abinda zanyi ko yanda zanyi da rayuwata, ban zama naki ba balle kice ba zan kula mata ba, idan na kulasu zanji tsoron gaya miki ne? Na taba miki karya?"
Itama cikin hargowa tace
"Amman gaskiya nawa ka boyemun?!"
Ranshi yayi kololuwar baci, yaja tsaki ya kashe wayar kawai, bata sake kiranshi ba, kuma lokacin daya huce ya dinga jera mata kirama bata daga ba, duk sakon daya dinga tura mata na lallashi dama barazana babu wanda ta amsa, daga baya ma saita kashe wayar gabaki daya, sai gashi da bada uzurin karya na rashin lafiya dan akwai wani assignment da zaiyi submitting, ya kama hanya yana nufar makarantarsu. Ya dinga yawon nemanta, tunda wayarta a kashe take, yafi awa daya da wani abu, kawai ya hangota cikin abokanta, maza guda biyu sai mace daya, su hudu, sunata dariya alamar shi kadaine hankalinshi yake a tashe, nata a kwance yake, ko da ya hangi abokinta daya ya kaiwa kafadarta duka cikin wasa, ta bangaje shi da rabin jikinta, sai duhu ya gilma masa, jiri ya nemi ya tikashi da kasa saboda wani irin kishi daya taso masa.
Tunda yazo kasar wani abu bai taba hadashi da jami'an tsaro ba, idan ya tsaya yau tabbas babu abinda zai hanashi kwana cell, in su Aise suka karaso zai jibgi abokinta, zai dake shi irin dukan da rabonshi da yayiwa wani shi tun yana makarantar kwana, saiya juya ya koma inda ya fito. Wannan shine sanadin da suka ba juna iska na wata daya shi da Aise, baisan daga bangarenta ba, amman a nashi bangaren kwanaki ne daya san irin girman son da yakeyi mata, kwanaki ne da yayi karamin hauka a cikinsu, har saida ya kasa hakuri ya kara komawa makarantarsu, daya kirata saiya sameta kuma ta daga, ya fada mata inda yake.
Tana zuwa tayi tsaye tana kallonshi, idanuwanta cike taf da hawaye
"Mi manchi tanto...(Nayi kewarki, sosai...)"
Yayi maganar yana jin kamar zuciyarshi zata bude, inta bude kuma ace Aise da take tsaye a gabanshi zai dauka ya kara duba mata wani sabon wajen ya zaunar da ita, hawayen da suka zubo mata yasa shi karasawa inda take ya tallabi fuskarta da hannuwanshi duka biyun
"Ni zaka fadawa kai ba nawa bane ba? Ni?"
Ta karasa tana ture shi, ya sake rikota, ta kai masa duka tana kukan da yake fitowa tun daga kasan zuciyarta, sai kawai yasa karfi ya rungumeta yanda duk mutsu-mutsun data dingayi ta kasa kwacewa, sai kawai ta kara fashewa da wani kukan, ji yake kamar ace yau Aise ta zama tashi, akwai lallashin da yakejin su duka biyun suke bukata. Numfashi kawai yake saukewa yana maimaita mata kalmomin ban hakuri da kuma yana sonta. A ranar suka shirya, sai kuma labarai yayi musu yawa, kowa nason ya fadawa dayan abinda ya faru a wannan wata dayan da sukayi basa tare.
Shi ta bangarenshi ba wani abu bane daya wuce cigaban daya samu a karatu da burinshi, a nata bangaren ne yaji wani abu da yake neman kara birkita masa lissafi, Mamma tace mata ta rabu dashi
"Bata sona dake ko? Mu'adh ya batani a wajenta"
Ya fada cikin wata karamar murya kamar ba tashi ba
"Zanyi magana da Papa, zaiyi mata magana, abinda nake so shi Papa yake so..."
Ya kalleta da idanuwan nan nashi da yau suke haskawa da kyallin tashin hankali
"Idan ya hanani aurenki fa?"
Ta girgiza masa kai
"Ka daina irin maganar nan"
Numfashi ya sauke
"Ya zanyi idan shima yace baya sona? Ba zan iya hakura dake ba Aise"
Idanuwanta suka sake cika da hawaye, yanzun haka dakyar Mamma take magana da ita akan Haris din
"Ba zai hana ba, ko kana tunanin ni zan iya hakura dakai?"
Ya dumtsa hannunta da yake cikin nashi wani abu na dukan zuciyarshi, duk wani tsari da lallashi da takeyi masa da karfafarshi akan cewa babu abinda zai samesu, ita dashi, sunki zauna musu, haka suka rabu bashi da wata walwalar kirki. Ga jarabawarshi ta karshe da yake shirin rubutawa a cikin watanni hudu masu zuwa amman hankalinshi fiye da rabi yana tare da Aise, kuma jarabawar na da matukar muhimmanci a wajenshi, yana bukatar fita da sakamako mai kyau, in son samunshine ma ya zamana yana daga cikin mutum biyar din farko a shekararsu, ko dan kara samun chances na cikar burinshi tunda shi ba dan kasa bane ba, visar shima in ba aiki ya samu ba, ko ya kara dora karatunshi ta fara lissafa masa lokacin karewa. A karo na farko hanyar shi daya hango babu komai ta cika da tarin tudu da gangaren da yake neman afkawa.
Ya tabbata akwai abinda yake faruwa lokacin da yake tsakiyar jarabawa da Aise ta kirashi tana ce masa
"Akwai biki, a Maiduguri, bansan wanne biki bane ba, Papa zaije, ka aika a same shi ayi masa maganarmu..."
Yanda ta sauke duka maganganun nata kusan a numfashi daya yace mata
"Wani abu ya faru ko? Wani abu ya faru..."
Yayi tambayar yana ba kanshi amsa, tayi shiru
"Zan ba Baba lambar Uncle din ya kirashi"
Da sauri tace
"A'a maganar waya ba zaiyi ba, yaje ya same shi, dan Allaah yaje ya same shi, ba zan iya rasaka ba, amman bani da wani karfi mai yawa tunda Mamma na tsakiya"
Saiya daga mata kai kamar tana ganinshi, sai da ya tabbatar mata da zaiyi masa magana, tukunna yaji hankalinta ya fara kwanciya, tambayar duk da yayi mata akan ko me yake faruwa, sai tace masa bashi da wani amfani, in dai Alhaji Mustafa zaije yayi maganarsu da Alhaji Modu shikenan. Kyaleta yayi, a lokacin da suka gama waya dare ya riga yayi sosai, shi damuwa da fargaba ma ita ta hanashi baccin kirki, sai kawai ya tashi ya cigaba da rage wasu abubuwan da suke gabanshi ko zai ragewa kanshi damuwa.
Da safe kuwa ya kira Hajiya Rumana yake fada mata yana so ayi maganarsu shi da Aise, yanda ta dinga murna saida murmushi ya kwace mata
"Ba wai mun shirya bane mu duka Mami, akwai 'yar matsala ne, shisa nake so a tambayar mun auren, manya su shiga maganar"
Da mamaki tace
"Wacce irin matsala?"
Yayi shiru yana tunanin ta inda zai fara, to haka zaice mata Mamma ta san yana shan wiwi yana neman mata, bata sonshi da 'yarta?
"Matsalar me, kayi shiru ina tambayarka"
A raunane yace
"Mu'adh baya sona da Aise din, haka kawai tun randa ya fara ganinmu nagani a fuskarshi, to yanzun Mamma ma bataso"
Hajiya Rumana taja wani tsaki
"Shi Mu'adh din ubanta ne? Ko ita Bintar ce zata bada auren Aise din, harta isa tace bata sonka da 'yarta, dadin abin ai ba itace take da iko da ita ba, wannan ma zancen banza ne da bai kamata ya dameka ba, kabar komai a hannu na kawai, kamar ka auri Aise ne kagama tunda dai kana sonta"
Ya sauke wata irin ajiyar zuciya, to sau nawa Hajiya Rumana nayi masa alkawari tana cikawa? Tama taba ce masa zata sama masa abu ta saba kuwa? Me yasa tuntuni bai fada mata ba ya tsaya yana ta damuwa? Tun ranar da Aise ta gaya masa Mamma bata sonsu tare bai samu natsuwa ba sai yau, wani abu daya kulle a cikinshi bai saki ba sai yanzun nan
"Shisa nake sonki Mami Na"
Tayi dariya.
Hajiya Rumana uwa ce,
Kuma uwa zatayi duk wani kokarin da zata iya wajen samawa yaranta abinda take so,
Amman duk karfi da tasiri irin nata babu yanda zatayi da kaddara...
9
A tunanin Hajiya Rumana, yanda labarin soyayyar Haris da Aise ya cika zuciyarta da farin ciki, haka abin zai yiwa dan uwanta dadi, to matarshi ta isa ta hanasu karfafa zumunci ne? Ko kuwa ikon bada auren Aise a hannunta yake? Rashin son da take yiwa Haris babu abinda zai tare. Shisa da karsashinta ta kirashi, haka kawai lokacin kuruciyarsu ya dinga dawo mata
"Modu..."
Take kiranshi kai tsaye, cikin tsokana, shikuma zai rankwasheta
"Ni sa'anki ne kike gatsa sunana haka babu rissinawa"
Lokacin da tayi aure ma, haduwarsu ta farko, haka ta kirashi, daya kawo hannu zai rankwasheta, da yake a gaban Alhaji Mustafa ne saiya rike masa hannu yana fadin
"Ayi hakuri a yafe mata"
Kamar karamar yarinya sai tayi masa gwalo, akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu a wancen lokacin, kuma tasan ba barinshi Najeriya bane silar nakasun da alakarsu ta samu, harda ita da ta fara janye jikinta tana rike Alhaji Mustafa, tana kuma fifita lamarinshi akan na kowa a rayuwarta
"Yayana"
Ta furta yau, tare sukayi dariya
"Ni kuma? Yaushe kika fara ganin girmana Rumana? Ai nasan kina daga cikin mutanen da ko furfura zata lullube duk jikina ba zaki bani girman da na dace dashi ba..."
Dariyar dai tayi
"Inji wa? Ni din? Ai tunda ma ina girmamaka, kawai ka raina adadin girmamawar ne ba wani abu ba"
Ya girgiza kanshi daga dayan bangaren kamar tana ganinshi
"Kuma kaga yanzun nice zan koma babbar ka koma karami"
Yayi murmushi mai sauti
"Amman dai ba anan duniya ba ko?"
Saida suka gama zolayar juna sannan suka gaisa sosai, lokacin ne kuma ta kara gyara muryarta saboda tana son ya dauki duk wani abu da zata sake furtawa da muhimmanci
"Ashe yara zasu kara mana zumunci Modu?"
Abinda bata sani ba shine, Binta ta fada masa komai, babu abinda ta boye masa dangane da dalilinta na kyamatar Haris din, kuma yama fita jin tsanar abin, ai son yaransu a jini ne, kuma shima bai hada nashi da komai ba a halin yanzun, bashi da sama da yaran nan uku rak da Allaah Ya bashi, sonsu yakeyi da gabaki dayan zuciyarshi, abinda kuwa zai cutar dasu in dai akan idanuwanshi ne sai inda karfin shi ya kare balle kuma ace wai shine zai daukesu ya mika inda zasu cutu, musamman Aise, yarinyarshi, yarinyar nan tashi da tafi kowa shakuwa dashi tun tasowarta, yarinyar da tun tana da shekaru biyar a duniya inya kalleta ya tuna wata rana zai mika kulawarta karkashin wani sai zuciyarshi tayi wata irin dokawa.
Data tasa sosai kuwa, labaran abokanta maza, da mazan da suke burgeta, inda ta numfasa ta kalleshi watakila da ta godewa Allaah da yasa bashi da lasisin mallakar bindiga duk ya harbesu ya huta da fargaba, a yanzun kuwa, kullum cikin tsara irin mijin da yakeyi mata fatan samu yakeyi, kuma Haris yasha bamban da wannan mijin, shisa yanzun ya nunawa Hajiya Rumana kamar bai gane abinda take nufi ba ta hanyar fadin
"To gashi dai Haris yana nan sunata zumunci abinsu, sai kiga sun taso basu watsar da nasu zumunci ya samu rauni irin yanda mukayi ba, balle su zamani ya saukaka musu komai"
Ta fadada murmushin