Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
tuki ba ai sai a diga musu ayar tambaya, tunda dai mota ba matsala bace a wajensu. Kusan ko yaushe ma cikin sake motocin gidan ake, dan kamar Alhaji Mustafa baya gajiya da hawan kalolin motoci, ba kuma ya gajiya da son ganin suma ya sabunta musu.
"To sai ki fadamun idan kina son wani abin kawai"
Wannan dai ba zaiyi wahala ba, ta daga masa kai batare dama tayi tunanin basu da lambar juna ba, haka shima Haris din
"Ana tafiya da abinci ne? In dafa maka wani abin? Zaka iya jin yunwa kafin ka sauka, awa nawa ne?"
Ya girgiza mata kai
"Ki dai hadamun tea in sha kafin in fitan, awa biyar ne da wani abu"
Yayi wanka, kayan jikinshi kawai zai canza, anan kitchen din yayi tsaye yana kallonta harta dafa shayin, ta hada masa yace ta kara, sai da kofin ya kusan cika, ta mika masa kofin da cokalin a ciki, ya sake juyawa ya kurba, sai yaji zakin yayi masa kadan
"Saikin kara mun sugar kadan..baiji ba, kinji"
Yayi maganar yana dibo shayin a cokali ya hura da bakinshi ya mika mata saitin nata bakin, saita kurba kadan batare da ta gane komai ba, kuma sauran daya dan rage a cokalin sai kawai Haris ya karasa shanye shi kafin ya saka cokalin cikin kofin ya mika mata, inda ya kalleta sosai watakila daya ga yanda bugun zuciyarta yake kada sauran gangar jikinta, ko ita kadaice takejin hakan na faruwa?
Sikarin ta dan kara masa ta mika masa, ya karba, daya kurba saiya daga mata kai alamar yayi, ya fice daga kitchen din ya koma falo ya zauna yana kurba a hankali, ya bar Maryama tsaye da yanayoyi mabanbanta, ta fi mintina biyar cikin kitchen din kamar ta manta abinda zatayi, dankaline ta dan dibo zata fere ta soya, amman kuma cikinta ya cika taf da wani abu da batasan menene ba, ta tabbata ko ta soya bata da wajen zuba shi yanzun, gashi tafi son dankalin turawa daga kasko sai faranti, sai cikinta, ta tsani ya huce, ta kuma tsani a saka shi a cikin kula, zufa ya koma masa. Shisa ta fito daga kitchen din, lokacin Haris harya kusan shanye shayin shi, ta samu waje daga can nesa da kujerar da yake ta zauna. Tana danna wayarta, harya karasa ya tashi, tana nan zaunen ya shiga dakinshi ya fito da jakunkuna guda biyu, daya na da girma dan nan ya zuba duka cameras dinshi da ma abinda zai bukata na aikin.
Karamar itace take dauke da kayan sakawarshi, ya canza kayan daya saka dazun, in ba kula kayi ba sai ka dauka kaya daya Haris yake dashi, sai kasa ido ne zaka dinga bambance da yawa daga cikin bakaken wandunan shi, dazun jeans ne, yanzun kuma ba jeans bane ba, wani wandone mai laushi, sannan a karo na farko yau ta ganshi da riga ruwan toka, duk da mai duhu ce kalar, ta kalli fuskarshi, rigar dai bata haska shi kamar yanda take hasashe cikin kanta zai faru inya saka wasu kalar kayan banda bakake, bakin shi yana nan, sai taga wani lokacin na kamar kara baki yakeyi, kila kuma idanuwanta ne, maikon fuskar shi ya hadu dana idanuwanshi yayi mata wani iri yau, ita in kayi fari to kafi rabin kyau a wajenta.
Bakaken harda danginta dama wasu a gidansu ba kare musu kallo takeyi ba balle taga wani kyau da suke dashi ko muni, in ba wani bane yace mata wane na da kyau a cikinsu, shine in ta koma gida ranar zata tai kallo tana neman wannan kyan, kamar abinda takeyi yanzun akan Haris, a idanuwanta matashin saurayine, dogo, bakikirin, shikenan, babu ragi babu kari, tasan da zai matso kusa da ita zataji kamshin turarenshi mai sanyi. Babu yanda za'ayi kaji turaren Haris in ba yazo gab da kai ba, kamar daga kayan shi har turaren yana amfani dasune wajen ragewa kanshi attention din mutane, har wanda yake tare dasu.
Ya ajiye komai, ya taka zuwa inda take zaune, sai lokacin ma taga ba dogon hannu kadai rigar jikinshi take da ita ba, harda hula a hade. Mukulli ne ya bata guda daya, a jikin wata key-holder mai kyau
"Akwai kudi a cikin drawer din gefen gadona...kome kike bukata ki dauka a ciki, ko nawa ne..."
Ta jinjina masa kai, saboda wani abu da yayi mata tsaye a makoshi, ita bataso taga wanda ta sani zai tafi wani wajen, ta tsani bankwana, shisa zai wahala kaga anyi rakiya da ita, ko da kofar gidane kuwa. Ko wata Umrah dasu Hajja suka tafi bata bisu airport ba, batama fito daga dakinsu ba, babu wanda ya matsa mata tunda sun san halinta, kafin ma tace wani abu su duka sunji hon din da ake dannawa da alama a kofar gidan ne, Haris yasan Lalaye ne, ba zai shigo da motar ba, sai dai shi ya fita ya same shi, wayarshi da tayi kara ya ciro daga aljihu ya daga da fadin
"Gani nan fitowa"
Ya sauke yana kallon Maryama data sadda kanta kasa
"Zan tafi"
Ta sake jinjina kai, cikin karamar murya tace masa
"Allaah Ya tsare Ya bada sa'a, Allaah Yasa maka albarka a abinda zakaje yi Ya dawo da kai lafiya"
Addu'ar tayi masa dadi matuka, sai kawai ya taka ya kama hannunta ya dagota, kafin tayi wani yunkuri ya rungumeta a jikinshi, ya sumbaci saman kanta
"Amin thumma amin, Nagode. Ki kula da kanki sosai, karkije ko ina kinaji?"
Kai ta daga masa, duminshi da kamshin shi nayi mata rumfa, daya saketa sai taji wani irin sanyi ya tsirga mata, tana kallonshi ya juya ya dauki jakunkunan shi, ya fice daga gidan, ta koma ta zauna tana goge hawayen daya zubo mata. Kan one sitter din taja jikinta ta kwanta da mukullin nan rike a hannunta, sai wani abu yace mata ta tashi ta shiga dakin Haris din yau taga ya yake. Da saurinta ta mike, harda hadawa da gudu, taje ta bude dakin. Ta shiga da sallama a bakinta, sai taji dariya na kwace mata, zanin gadon da yake shimfide akan gadonshi bakine, sai duvet dinma daya linke ya ajiye a gefe, filallika ne a saman gadon sun kusan guda takwas a iya ganinta tunda ba kirgawa tayi ba, sune ma rigar jiki wasu bakake, wasu kuma ruwan toka, har karamin kafet din da yake gefen gadonshi baki ne.
Dakin qal-qal, dan ko nata bai kaishi kimtsuwa ba, babu wani abu a wani waje da bai dace ba, ga kamshin shi nan mai sanyi a cikin dakin da saika natsu zakaji shi, kawai saita karasa cikin dakin, kafet din nashi mai laushine sosai, ta dauko pillow daya ta sauke a kasan ta kwanta. Ta rufe idanuwanta, kuma bata jima ba bacci ya dauketa. Bacci tayi sosai, baccin da bata samu tayi sosai ba da daddare saboda tanata sakawa da warwarewa akan tafiyar Haris din da yanda zatayi idan Abba bai bar Khairi ba. Ringing din wayarta ne abinda ya tasheta daga baccin da takeyi
"Bacci ma kikeyi? Ni ki dafamun wani abu gamu nan mun kusan karasowa cikin Kano, yunwa nakeji ban karya ba na fito"
Cewar Khairi bayan ta daga wayar, da saurinta ta mike
"Me kike so? Zakici dankali? Ko indomie? Ko in soya miki doya?"
Dan ji tayi ta wartsake gabaki daya, sai yanzun murnar zuwan Khairin ma ta dirar mata
"Ni dai koma me"
Tana sauke wayar ta mike, ta dauki pillow din ta mayar masa kan gadon, saida ta kulle dakin da mukullin taje ta ajiye shi a nata dakin, ta wanke fuskarta sannan ta koma kitchen din, cefane ta gyara, tasan Khairin nason stir fry indomie, sai ta soya dankalin, tasan direba ne ya kawo Khairin, shima sai ta zuba masa, shisa ma ta saka da yawa, ta fara aikinta cikin nishadi, burner din gas biyu ta kunna dan aikin yayi mata sauri, ashe ma su Khairin na gab, dan ba'a rufa mintina talatin ba taji sallamarta, da gudu ta fita daga kitchen din suka rungume juna suna tsalle-tsalle kamar yara
"Wallahi nayi kewarku, kowa da kowa a gida"
Cewar Maryama, tana jan akwatin Khairin ta kaishi dakinta, ta dawo tana ce mata
"Bari in duba kar abincina ya kone, sai inzo in shigar miki da jakar"
Hijabinta Khairi ta cire, sai suka nufi kitchen din tare, suka karasa komai sunata hirar har kowa na rasa abinda zai ba dan uwanshi labari, saika rantse basa waya har katikansu ya kare, da aka zubawa direban, Khairi ta daukar masa ruwa da lemo ta fita ta kai masa, sukayi sallama dan juyawa zaiyi. Ta dawo ta zauna suka ci nasu ita da Maryaman sunata hira. A ranar kuma ta fahimci akwai wani a rayuwar Khairin, saboda tana yawan daukar wayarta ta danna, sai tayi murmushi ta ajiye
"Waye baki bani labarinshi ba?"
Murmushin kawai tayi mata batare da tace komai ba, aikenta ma Hajja tayi gidan Adda Maimunatu, daga can ta fita tayi mata cefane sai ta hadu dashi, ba yaro bane ba a idon Khairi da take da sauran 'yan watanni ta rufa shekara goma sha takwas, dan a hasashenta zaiyi shekara talatin da biyu, yace mata yana da mata da yaro daya, sai kuma cikin na biyu. Ma'aikaci ne shi yace mata a FIRS yake aiki, sunanshi Ibrahim Bakori, dan asalin garin Katsina, ita ko kadan babu wani maganar aure a ranta, tana so tayi karatu ne, shima ta gaya masa yace mata
"Matata ni na mayar da ita makaranta, yanzun haka tana aji uku a Bayero, inta gama degree dinta kuma zatayi Master's In Shaa Allaah...bani da matsala da karatunki, sai kince mun kingaji da kanki tukunna"
Ita ba zatace ma ga abinda takeji akan Ibrahim din ba, bata da dogon buri akan namiji, wanda duk ta samu in zasu zauna lafiya ya mutuntata da iyayenta bata da wani abu da take nema bayan wannan. Duka satinsu biyu kenan da haduwa, ta bashi lambar Yaya Ahmad, dan yaje yayi masa jagora wajen Abba saiya fara zuwa, akwai kasuwancin da yace mata yake shigo dashi Kaduna duk wata daya zuwa biyu, tunda iyalinshi suna Kano, haka iyaye da 'yan uwa. Wannan ne abinda yafi komai jan hankalinta harta ji ta amince ta fara kula shi su fahimci juna, a Kano yake, idan da rabon ya aureta a Kano zai ajiyeta, kusa da 'yar uwata, kusa da Maryama.
"Ba zaki bani labari ba"
Ta karayin dariya
"Sunan shi Ibrahim, kuma baiyi magana da Abba ba shisa ban baki labari ba, babu wani labari a yanzun har sai Abba ya amince"
Duk da haka saida Maryama ta kafa mata naci wai sai taga hotonshi
"Allaah Ya duba miki, Allaah Yasa ki aure shi, kinga da hasken shi, ba kamarni ba"
Khairi ta kwashe da dariya
"Wallahi kina da matsala Maryama, to wai uwarme hasken zaiyi miki? Saiki samawa Haris din man bleaching ai"
Maryama tayi shiru tana hasaso ta inda zai fara shafa man bleaching, dariya ta kubce mata, irin bakinsu ne mai wahalar sha'ani in ance za'a shafa masa mai, dan tana ganin 'yan bleaching din, sai yayi musu dabbare-dabbare
"Wa yaga Ganja yayi dabbare-dabbare"
Khairi ta kalleta
"Bana ce ki kiyayi kanki karkice masa Ganjan nan ba?"
Tayi dariya
"To ai yanzun baya nan"
Dan ranar da taji an kirashi da sunan, saida ta kasa hakuri da daddare take ba Khairi labari, suka dinga dariya tare
"Ganjaa fa,anya kinji dai-dai kuwa? Wanne irin suna ne wannan"
Ta rantse ta maya haka taji ance, kuma sau nawa tun ranar take tauna harshenta in ta kusan subutar baki ta kirashi da Ganjan. Ba karamin dadi zuwan Khairi yayi mata ba, dan a washegari ne take ce mata ta kira Haris taji koya sauka lafiya, sai taji wani abu ya fado daga kirjinta zuwa cikinta
"Bamu da lambar juna ai"
Khairi tayi mata wani kallo
"Mantawa nayi bance ya bani ba"
Ta kara fada cikin rashin jin dadi da tunanin ko ya sauka, ko me yakeyi yanzun? Ko ya hada shayi? In bai hada ba ya fita ya siya?
"Inama kikace mun yaje?"
Da sauri ta amsa, Khairi tayi jim
"Anya ba Syria bace aketa yakin nan da Abba yake kallo a BBC?"
Maryama ta girgiza kai, saboda yanda taji daga zuciyarta har gangar jikinta basu aminta da karbar Haris na wata kasa da ake yaki ba, akan me to? Me zaije yayi acan din shida ba soja ba? Sai kuma ta tuna in wuka za'a saka a yankata a tambayeta aikin da yake sai dai a cire har kan, dan batasani ba, batasan aikin da yakeyi ba, babu wanda taji ya fada, kuma ita bata tambaye shi ba, idan kuma sojan ne bata sani bafa? Shisa yake ta fama da bakaken kaya
"Can ne fa Maryama, wallahi can ne ake yaki"
Khairi ta fadi dan ta dubane a wayarta ta gani, sukayi shiru na wani lokaci
"In Shaa Allaah babu abinda zai faru, ya sauka lafiya, kuma zai dawo lafiya"
Batayi magana ba, batace komai ba, jikinta abu daya ya bata
Haris ya sauka lafiya,
Zai kuma dawo mata, kawai dai batasan zai bar wani kaso na rayuwarshi a kasar Syria ba...
21
Khairi na wanka lokacin da aka kwankwasa kofa, ita kadaice a falon tana kallo, sai ta tashi kawai, ta murza mukullin kafin ta bude kofar, idanuwanta suka sauka kan bakar leather jacket dinshi da bai zage zif din ba, dan haka tana ganin t-shirt din ciki da itama bakace, da saurin gaske ta daga kanta tana kallon fuskarshi
"Ba dadewa zanyi ba, sati biyu zanyi In Shaa Allaah, amman zan iya biyawa wani wajen, ban dai sani ba, kaman dai ba zan wuce sati hudu ba"
Haka yace mata, kuma abinda ta dinga juya kenan cikin kanta babu dare babu rana, musamman da daddare da take tsintar kanta da kirga kwanakin da yatsunta, addu'ar da tayi ta bacci tana zame mata abu na biyu da takanyi kafin baccin ya dauketa, sati hudu, ba zai wuce sati hudu ba yace, kuma data lissafa bakwai sau hudun nan kwanaki ashirin da takwas ne a ciki, yau kwanan Haris hamsin da tafiya, karyar da Khairi tace mata tayi na fadin
"An kara musu lokacin aikin ne"
In 'yan gidansu sun tambaya, ita ta dinga maimaitawa kamar mai son ita ta yarda da karyar fiye dasu Abban ma
"To in dai bai dawo satin nan ba sai a samo miki wata da zata zauna dake dan su Khairi har an fara registration a makaranta"
Abban yace musu a jiya da sukayi magana, haka a jiyan Khairi ta sakata a gaba da zancen Haris na dawowa tayi masa maganar makarantarta, karta yadda ta zauna haka, ko kwalin sakandiri bata dashi, ta dinga amsawa da
"In Shaa Allaah"
Amman makarantar ce karshen abinda yake cikin kanta, ya dai dawo, ta ganshi, ta ga yana lafiya, babu abinda ya same shi. Tunda kara dagawa kanta hankali ta dingayi ta hanyar kaiwa labaran BBC tayi kur tana jiran ayi magana akan abinda yake faruwa a Syria, itace har tashar Al-Jazeera. Ranar da aka hasko din kuwa, wani babban gini ne aka jefawa bomb ya rushe, ance makaranta ce, dan ginin zaiyi hawa goma ko takwas, masu bada taimakon gaggawa da yan kwana-kwana nata aikinsu, ana daga fasassun ginin nan ana zaqulo gawarwakin yara da manya a kasan shi, wasu kuma masu rai, ita kadaice a dakin lokacin, Khairi taje gidansu, hawaye kawai take sharewa wasu na sake zubowa.
Da an daga ginin nan ana kokarin zaqulo mutum daga kasanshi sai taji zuciyarta tayi wata irin tsinkewa, har daga kai takeyi tanajin kamar ta shiga ta cikin tv din ta tayasu, kuma a tarin mutanen da suke wajen nan haka ta dinga baza ido, karshe da taga wani ya gifta da bakin wando a jikinshi sai gata a gaban tv din tana lekawa ta gefe ko zai dawo, ko Haris ne, da ita aka dinga daga ginin nan, ita da masu taimakon kowa da abinda yake nema har aka dauke labaran aka fada wani, ko abinci kasaci tayi don tashin hankali, Khairi ta dinga yi mata fada
"To ke waye ma yace miki bangaren da ake yakin yaje?"
Sai ta dinga gayawa kanta ba nan Haris yaje ba, wani aikin ne daban ya kaishi, wani sashi na Syria inda hatsaniyar bata kai musu ba, watakila ma ya bar kasar ya wuce wata kamar yanda ya gaya mata. Amman meya tsayar dashi? Me yasa ya dade haka? Bata da mai amsa mata wadannan tambayoyin, sai Haris din da yake tsaye a gabanta yanzun, Haris din da a kallon farko ta ga ya kara yin baki a idanuwanta, sannan ya rame, duka fuskarshi ta rame, da ta saka idanuwanta cikin nashi kuwa sai taji kafafuwanta na rawa, sai taji irin yanayin nan da takanji duk lokacin da take kallo a tv aka hasko teku, ta hasasota a gefen tekun nan, kuma watakila da bata sauke idanuwanta daga cikin na Haris ba da ta gane me bature yake kira da drowning, data nutse a cikin abinda take gani a idanuwan nashi.
Sauran jikinshi take kallo batare da tasan abinda take nema ba, da jaka a goye a bayanshi, jakar nan tashi daya tafi da ita, sai dayar daya rike a hannunshi, dayan hannun nashi irin Stanley cup din nan ne
"Sono così stanco..."
Ya fadi cikin wata murya, kafin ya dan runtsa idanuwanshi ya bude su a hankali yace
"Nagaji sosai Maryama, nagaji...kin tare mun hanya"
Sai lokacin ta tuna tana tsaye ne a bakin kofa, ta kuma kasa ce masa komai, ta dai matsa. Ya shigo yana rabata ya wuce. Da yake kullum sai ta share masa dakinshi, ita ta cire babban abin rufar da taimakon Khairi suka ninke shi suka saka a wardrobe dinshi dan kar yayi kura
"Wai shi komai nashi baki ne? Sai kace jemage"
Khairin ta fada ranar, ganin kayan da suke cikin wardrobe din, kuma yau kwana hudu da sukai wanki ta shiga ta cire zanin gadonshi, da rigunan filallikan aka wanke su tas a injin wanki, da suka bushe saita ninke su suma, ta koma dakinta ta dauki wardrobe balls din da take dasu, taji suna da kamshi, kuma kamshine mai sanyi irin wanda takeji a dakin Haris din, tana fatan ba zai dame shi ba, duk ta jefa masa a cikin kayanshi, harda zanin gado. Yau taso tabi Khairi gidansu, gargadin Haris ne ya zaunar da ita, shi yace in ba rashin lafiya ba kar taje ko ina, duk da Mummy din tazo gidan sau biyu tana dubasu. Macece