Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
gudun karya saka mata ciwon ciki yasa ta tattara taje ta adana.
Ta dafa ma Haris shayi, ta dai saka Fa'iza ta fere mata dankali tabarshi a cikin ruwa, in dai Haris ne sai yayi wanka inya sauka ta sani, to inya shiga wankan saita soya masa kafin ya fito. Su dai ta dafa musu shinkafa da miyar kifi da taji tana marmari. Sai salad, sai da Fa'iza taci tukunna ta wuce Islamiyya, gidan yayiwa Maryama shiru fiye da kowanne lokaci, batasan ko dan kirjinta da yake ta bugawa da dawowar Haris bane, tunda Awwab na wajen Hajiya Rumana, yanzun in ta dauke shi sai yayi kwana biyu, ido ta dauka ta saka musu, so take ta gama hidimar bikin nan, ta kuma sauka lafiya, makarantar Islamiyya take so a fara saka Awwab din, idan ya samu ko shekara dayane sai a hada masa da boko, dan wannan Islamiyyar ta kusa dasu taga suna da kokari matuka.
Tana nan kwance kan kujera, cikin kwalliya mai sauki, lace ne irin marar nauyin nan, ja da aka dan yiwa adon golden, dinkin doguwar riga bubu, hula ce ja ta saka dan dankwalin zai dameta, ta dan goga jambaki, sai ta murza hoda, tayi kyau dan kalar lace din ta kara mata haske, danma cikin nan taga pimples ya fito mata, fasawa takeyi, sun bar mata dark spots waje-waje kuwa. Tana nan kwancen taji ana horn, duka ba'a dade da samo musu maigadi ba, ta dai ganshi sarkin shiririta ne, can yake tafiya wata majalissa da suka samar ta masu gadin unguwar su zauna sunata labari, haka ta mike ta leka ta window din falon, sai taga anci sa'a yana nan, ya bude gate din.
Luguden da kirjinta yakeyi ta karu, taje ta bude kofar da take da mukulli a jiki, ta dawo ta zauna kan kujera, har abinda ke cikinta ma motsi yakeyi kamar yana tayata taradaddin da ta shiga. Kwankwasawa Haris yayi sau biyu, kafin ta numfasa tayi magana ya murda kofar dakin ya shigo da sallama a bakinshi, sallamar da saida tayi da gaske sannan ya saba da yinta in zai shigo gida, yanzun kuwa har bedroom wani lokacin sai taji yayi in zai shiga ko da kuwa babu kowa a ciki, ta daga ido, ta sauke cikin nashi, zuciyarta ta buga. Rigace mai dogon hannu a jikinshi, ruwan toka mai duhu, in bata manta ba ita ta daukar masa rigar, sai bakin wando, bata kalli kafarshi ba, tasan bakin takalmi ne, sneakers.
Taji sautin numfashin daya sauke kamar matafiyin daya wuni gararamba sai yaci karo da ruwan sanyi, a hankali ya tako har inda take, ya kama hannayenta yana mikar da ita tsaye, bai damu da cikinta daya fito ba kawai ya rungumeta a jikinshi, Maryama taji kanta ya hautsina, tsikar jikinta ta tashi, data lumshe ido ta shaki kamshin turarenshi mai sanyi kuwa sai hoton nan ya dawo mata
"Sau nawa nace miki nayi kewarki?"
Ya fada yana dagota daga jikinshi, ya sumbaci kumatunta, idanuwanta taji sun cika da hawaye, zuciyarta ta takure waje daya tana mata zafi, tayi addu'a, tayi kuka, ta kara addu'a ta nemi Allaah Ya sassauta mata, ko da hoton nan ba zai goge ba, to tasirinshi ya rage, kuma a hankali tana samun saukin zuciya, sai dai ganin Haris, hadata da yayi da jikinshi yana neman warware mata komai
"Nayi kewarki, da yawa"
Ya kara fadi yana sake rungumeta, ta dan motsa cikin kokarin danne zuciyarta dan karta hankade shi, kar suyi fada daga dawowarshi. A hankali ta zame jikinta
"Sannu da zuwa"
Ta furta muryarta na dan rawa, bai amsa ba, sai idanuwanta daya kalla, ta danyi murmushin karfin hali, yatsanshi yasa yana taba goshinta, ba waje daya ba, waje waje
"Meye wannan yayi miki spots"
A hankali ta amsa da
"Pimples"
Ya sake saka yatsan nashi yana taba kumatunta
"Sunyi miki kyau...kinyi kyau...zo nan"
Ya karasa maganar yana shirin sake rungumeta, ta matsa baya tana dan ware masa ido
"Kai ko"
Yayi dariya
"Nayi kewarki da yawa ne"
Dan matsawa ta karayi
"Ina kayan?"
Ta tambaya
"Suna mota fa...ina zan tsaya dauko wasu kaya banganki ba"
Tunda direban ya riga ya bashi mukullin motar ya tafi, sai kawai yabar kayan a ciki, harda gudunshi ya hada wajen shigowa cikin gidan, ganinta da yayi kawai zuciyarshi ta samu wata natsuwa ta daban. Da ya riketa a jikinshi kuwa sai yakejin komai daya hargitse masa yana dai-daita. Gajiyar ma ya nemeta ya rasa, yanajin yunwa dai
"Yunwa nakeji fa...amman ina so inyi wanka"
A hankali Maryama tace masa
"Akwai shinkafa da miyar kifi"
Ya dan hade rai
"Shinkafa? Ba wani abin?"
Kallonshi takeyi
"Saika hada da shayi"
Yayi shiru na wasu dakika
"Shayin dai da wani abu, kinsan ba son kifi nakeyi ba"
Yanda yayi maganar ne yasa ta fadin
"Sai in zuba maka shinkafar da mai da yaji ai, ka hada da shayin"
Ya kalleta da wani firgici cikin idanuwanshi, kwakwalwarshi na harhada masa shinkafa da mai da yajin data kira, yunwa yakeji da gaske, yunwar kwana biyu, tun washegarin tahowar shi, abinda ya saka a cikin nashi ba wani mai yawa bane ba, yasan shayi kadai ba zai ishe shi ba
"To kiyi mun order din wani abu mana, ko cake din nan ne wajen Kerau din nan, tunda kinga muna Kadunan"
Nauyin da kirjinta yayi ne yake ta sauka a hankali, shi dai ya kasa manta wannan cake din, ita ta manta dashi ma, amman yanzun kam dole zata lalubo lambarta 09057866631.
"Zan mata magana inji idan akwai, kaje kayi wankan"
Ya daga mata kai, hankalinshi yana dan kwanciya, amman shinkafa da mai da yaji, shi abinma ya kasa haduwa a cikin kanshi. Harya wuce saiya dan dawo
"Ina ne dakinmu?"
Da hannu ta nuna masa inda ta ware a matsayin nashi, nata daban, dayan bedroom din Fa'iza ce take kwana a ciki, duk da sai tayi bacci a falo sau nawa saboda kallo. Kitchen ta wuce, tana jin Haris ya sake fitowa yaje ya bude mota ya dauko kayanshi. Kafin ya gama wankan ta soya masa dankalin, haka kawai dai ta soya masa kwai da tayi scrambling, yasha yankakken tattasai da albasa, tasan ba lallai ya burgeshi ba duk yanda ita yayi mata kyau a ido, fata takeyi dai yaci.
*
Tunda ta tabbatar babu wani abu da zai bukata ta tafi dakinta, amman saiya kwashi komai ya bita can din, batayi masa magana ba, ta cigaba da danna wayarta, dan kuwa ko ba tayi chatting ba, tana samun abubuwan da suke debe mata kewa a Instagram dinta, sannan taci karo da wani shafi, Hausaroom, inda mutane suke tura labarin matsalolin rayuwarsu sai ayi musu posting ana bada shawarwari, zatace taji tsoro matuka, ganin yawan matan da suke fama da maza mazinata, amman kuma ta wani fannin sai hakan ya dan sama mata natsuwa, sanin ba ita kadai bace ba, ta karanta, wasu ma bayan zinar mazan harda tarin wulakanci, wasu ga talauci, ga mazan ma ba dadin zama dasu sukeji ba, tarin matsaloli birjik, ta dinga jinjina lamarin aure.
Wato kowacce mace dai kaganta da mijinta, abinda take fuskanta in bata bude baki ta fada ba, ba zaka sani ba, kuma abin da ya kara bata mamaki, yanda kowanne case akayi posting da yake da alaka da neman matan da maza sukeyi sai kaga mata da suke magana da sunan bada shawara suna fadin
"Yar uwa kina gyara kuwa? Kinsan mazan yanzun sai dai gyara"
Haka zaka ga wasu ma na dorawa da
"Ai zagewa zakiyi ki dinga yi masa bajinta a yayin mu'amalar aure, ki koyi abubuwan da zai dauke masa hankali daga matan waje, kinsan suma karuwan da abinda suke janye su kenan"
Kamar a kowanne comment da zata gani, a yanayin maganganunsu, sun manta cewa haka tace mijinta na bin mata, mijinta na aikata daya daga cikin manyan laifukan da aka fada a musulunci, shisa ma har suke hango cewa matsalar daga itane, laifin daya zabi ya aikata, shine aka juya aka mayar kan matar data kawo kara, aka nuna gazawarta ce ta janyo haka,dan ko jiya da daddare da Maryam taga wani, saida masu comment din nan suka sakata dogon tunani, to ko dai itama itace take da matsalar? Ko da gaske in kana yawaita gyaran yana hana mazan biye-biye? Tunda acan New York ina ma taga wasu kayan mata?
Tun wanda Adda Zahra ta batane, wasu ma zubarwa tayi saboda taga sun dade sosai, ko sun lalace, sannan tasan Haris na da yawan bukata, tana iya kokarinta, amman wani lokacin yana kureta ne. Yanzun ma data dago ta kalli Haris din sai da abin ya fado mata a rai, wani sashi na zuciyarta kuma yana fada mata, ai koma me tayi ba uzuri bane da zai saka shi bin wasu matan, a karo na farko da taji gara ace aure ya kara, da kazantar zina gara ace auren yayi, sai yafi mata sauki. Addu'a ta dingayi duk wadda tazo ranta, tana fatan Allaah Ya saukaka mata abinda takeji, Allaah Ya dubata ya shirya mata mijinta. Hira suka danyi sama-sama, saida taji dawowar Fa'iza daga islamiyya ne ma ya fita, ta kuma sake komawa dakin. Da aka kira sallar Magriba ta kalli Haris da yake kwance akan gadonta
"Ana kiran sallah fa"
Ya dan kalleta
"Zan tashi, nagaji ne, da naci abinci kuma sai naji na kara gajiya"
Ta jinjina masa kai
"Ka dai tashi ka tafi masallaci kar a tayar da sallar, in ka samu kayi, ka koma isha'i shikenan sai ka kwanta gabaki daya"
Saida ta fara ganin musun da zaiyi a yanayin fuskarshi kafin yace
"Zanyi a gida ai, idan na mike zan hada da Magribar da isha'in"
Bayi ta wuce, dan fitsari ma na damunta, ta farayi sannan ta dauro alwala, Haris yana kwance inda ta barshi. Ta shimfida darduma tayi sallar wani abu tsaye a makoshinta, ko azkar dinta bata iyayi ba, ta sake kallonshi, uzurinshi lokacin da suke New York shine babu masallaci a kusa dasu ko guda daya, to ita in ba lokacin sallah ba da sukaje idi dashi, saida tayi tunanin ko babu masallacin nema gabaki daya, kamar zasu wani gari haka suka sha tafiya.
"Ganjaa"
Ta kira, bai amsa ba, ya dai kalleta
"Kasan meye abu na farko da ake fara dubawa idan mutum ya mutu?"
Bata jira amsashi ba taci gaba
"Sallah...sallar mutum itace abu na farko a cikin ayyukanshi da ake fara dubawa, shisa zakaga a islamiyya ana fada mana cewa idan sallar nan ta gyaru, to akwai kyakkyawan yakinin cewa sauran ayyukan ma sun gyaru..."
A kasalance yace mata
"Ai inayin sallar nima"
Tunda komin gajiyar da zaiyi, ko da baiyi kowacce akan lokaci ba, baya yarda yayi bacci bai rama duka sallolin nashi ba
"Kanayi sanda kaga dama, bawai lokacin da akace kayi ba"
Ya sauke numfashi
"Maryamm...zanyi fa, ba sai kinmun wa'azin nan naki da baya karewa ba, barin tashi"
Ta girgiza kai kawai, to taya za'ace mutum zai tsallake tarkon shaidan? Ita sallah ga mace da namiji in dai zasu tsareta akan lokuttanta, to shaidan zai sha wahalar yin galaba akansu. Anan dakin yayi sallah, tanata kallon shi, kuma yanayin kallon ne yasa lokacin da aka kira isha'i sai ya fita, tare da maigadin gidan sukaje masallaci, baiyi wani nisa dasu ba, layi biyu ne sai a karya kwana. Daya dawo yace mata
"Naje masallacin, shikenan? Ki daina kallona kamar na aikata miki wani abu"
Batayi masa magana ba, ta fita ta zuba abincinta taci, abincin da bai barta ba saida ya bita har kitchen din, tayi masa tayi, kamar yanda ta tsammata kai ya girgiza mata. Data gama cin abinci ta zauna anan, dan Fa'iza tunda ta fito ta gaishe da Haris, saita koma dakinta ta zauna, dakin da take din akwai tv, amman dai basu taba kunnawa ba, sai taje dakin ta hada mata kayan kallon da yake ciki, dan tasan zaman kadaici ga babbama bashi da dadi, balle kuma yarinya mai shekarunta. Bataso ta koma dakinta, amman bayanta ya gaji, bata jure zaman kujerar ko kwanciya akai yanzun da tayi nauyi, in kuma ta zauna akan kafet to tashin saiya zame mata wani babban aiki. Haka babu yanda zatayi ta tashi
"Zamuje mu kwanta ne? Nagaji sosai"
Cewar Haris, bata amsa shi ba, data nufi daki dai tanajin yanda yake binta a baya, tana kwanciya kuma shima ya cire dogon wandon jikinshi ya bar boxers din, ya kuma cire rigar, sannan ya hau gadon. Yanda tsikar jikin Maryama take tashi har wani amai takeji yana mata barazana, ta rufe idonta lokacin da taji Haris ya rikota a jikinshi, sai gashi ta fashe masa da kuka, ya kuwa rikice yana dagota gabaki daya
"Maryamm...menene? Meya faru? Wani abu na miki ciwo ne?"
Yana tambayar ne yana tattaba jikinta ko zaiji alamar zazzabi, ba karamin tsoron kukan nata ya bashi ba
"Me yasa? Akan me? Me yasa? Ya zanyi hotonka da yarinyar nan ya gogemun?"
Yayi tsam, bawai ya manta da ta gansu bane bane ba, tunda duk sanda zai rike wata macen bayan data tafi saiya tuna Maryama tasan wannan sirrin nashi, tasan cewa he's cheating on her, kawai ganin yanda suke waya lafiya kalau duk watannin nan, saiya dauka komai ya wuce mata, ta hakura, ta yafe masa, tunda ma ai zai kara yin taka-tsantsan ne
"Maryamm"
Ta kalle shi da rinannun idanuwanta
"Menene bana maka? Me zan gyara da zaisa kabari? Tun yaushe kakeyi? Wai me yasa ma?"
Baisan taya zai amsa mata tambayoyin nan ba, tanayi masa komai dai-dai gwargwado, kuma zaice natsuwar da yake samu a wajenta baya samunta a waje, bambancin shine bata iya dauke masa duk bukatarshi, ji yakeyi tayi masa kadan, wannan rashin kunyar ta sauran matan da yake bi, yanda zai rikesu yayi yanda yake so babu wani tausayi ko soyayya, ita ko da zata barshi bayajin zai iya mata haka. Babu wani abu da zata gyara, tunda daman ba ita tasa ya fara ba
"Kiyi hakuri, dan Allaah kiyi hakuri"
Yake fadi yana kara riketa jin irin kukan da takeyi, gefen kanta kuwa da duk inda bakinshi zai samu haka ya dinga sumbata yana bata hakuri, kuka tayi, irin kukan nan da mai yinshi yake neman rage damuwa, tayi kuka har bacci ya dauketa, Haris najin ajiyar zuciyarta har kasan tashi zuciyar. Ya sake riketa da kyau, yana sumbatar idanuwanta da suka kumbura har kana ganin jan da sukayi saboda kukan da tasha, bayason haske mai yawa haka in zaiyi bacci, amman bayaso kuma ya cika motsi ya tasheta, dole ya hakura ya rufe nashi idanuwan har bacci ya dauke shi. Karfe uku da rabi ta bude ido, ta dinga mamaki yanda fitsari bai dameta ba yau, tana tashin alarm din wayarta ma na fara bugawa, tayi saurin latse shi, ta yunkura ta mike ta nufi bayi.
Har dogayen riguna guda uku da hijabai uku ta ware nayin sallar dare, da kanta take wanke su ta goge, ta feshe su da turare, tana jin dadin zuwa da bukatunta wajen Ubangiji jikinta tsaf-tsaf, tunda fatanta wadannan ibadun Allaah Ya karbesu ya wanke mata zuciyarta da ruhinta, amman yau a maimakon addu'o'in ma kuka ta dingayi a sujjadar ta, data idar ma hawayen ta zauna tayi saida taji ta wasai, ta mayar da raka'atanil fajr, sannan ta cigaba da Istigfar kafin aka kira sallar asuba, saida ta fara tashin Haris, taga ya shiga bandaki tukunna ta tayar da sallar asuba, kawai batayi zaton dayan dakin Haris ya koma yayi tashi sallar acan ba maimakon ya tafi masallaci. Kuma da yake taji ta hakura, har kasan ranta ta karbi wannan kaddarar ta Haris, daya dawo dakin ya nemeta bata hanashi ba, bata da wani karsashi yanda ya kamata, amman bata hanashi ba, kuma kukan da tayi zaton zatayi ma batayi ba.
*
A ranar yaje gidansu, yana fada mata da Awwab zai dawo, da yake bata saka rai ba, daya dawo shi kadai ko tambayarshi batayi ba, shima baiyi mata maganar ba. Da tayi waya da Hajja ne take fada mata Haris din yaje ya gaishesu, ba zatayi karya ba, taji dadin hakan da yayi har ranta. Zata lallabashi, so takeyi tun saura kwana uku bikin Khairi, ko da ba zai barta ta kwana ba, to tun safe inta tafi sai dare zata dawo. Ta dan farayi masa maganar yayi wata gajeriyar dariya. Sai ta kyaleshi, tunda ya fita yaje gidansu din nan bai sake fita ko ina ba, tare suke wuni dashi a gida, ya dawo da ayyukane masu yawa, aikin da take ta kama masa yana rage yawansu.
Anan dakinta ya yada zango, yana shiga dayan ya ajiye abubuwanshi, amman dai a nata din suke wuni. Yanda ya shigo daga sallar asuba daya fita yana tari ya tabbatarwa da Maryama wiwi dinshi yasha, gashi nan ma ya sake kaya, ba wannan kayan ya fita dasu ba, rigar daya fita da ita bata da collar, kuma yana saka turaren da inya giftaka zaka jishi farat dayane in yanaso ya boyewa hancinta shakar hayakin wiwi dinshi, yanda ma yake ta kokarin danne tarin yana kallonta ya gama tona masa asiri. Ta rasa dalilin da yasa Haris ya rantse saiya kashe kanshi, wasu hawayen takaicine takejin suna neman balle mata, data mike daga dardumar batace masa komai ba. Fita tayi daga dakin, ta nufi dayan, wani abu da bai sani ba shine ta riga ta gane duk wani sako da lungu da yake boyonshi, ai yau da gobe bata bar komai ba.
Kuma tana daddaga inda take zato din ta ga abinda take nema, wasu ma ya nannadasu a jikin takarda, wanda ya nannada din wajen guda hudu, su ta kwasa, ta dauki lighter guda daya cikin wadanda tagani, ta kuma kwashi wasu daga cikin wiwi din da suke a kananun ziplock ta koma dakinta. Yana nan kwance, har lokacin tari yakeyi kasa-kasa, tana ganin yanayin idanuwanshi daya canza alamar tarin na damunshi, dan wiwi ta kula komin yawan da zaisha sai dai idanuwanshi su rage girma, basa canza launi, sai ace idon 'yan shaye-shaye in sunyi shaye-shayensu yayi jajur, banda na Haris, in baka san yanayi ba zaka dauka ko bacci ne bai wadace shi ba. Kan gadon ta ajiye abinda ta kwaso, banda lighter da kuma karan wiwi din guda daya, yanda ta kyasta lighter dinne yasa Haris ya kalleta da sauri, mamaki ya hanashi mikewa.
Kunnawa tayi, ta ajiye lighter din akan gado, sannan takai wiwi din bakinta tana zuqa, hayaqin ya karasa kirjinta yana rarrabuwa cikin kanta hadi da qulle wasu abubuwa da yasa ta fara tari, amman saboda karfin hali saita kara kaiwa