Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
yake kara matse bakin aljihunshi.
Ita kuwa wanda suka rabeta ma sunsan cewa hannun mijinta a bude yake, kyautar Haris 'yan uwa na nesa dana kusa ma tana isar musu. Yanzun ma Haris dinne ya shigo yana katse mata tunanin da ta fada ta hanyar rungumeta ta baya, ya sumbaci gefen fuskarta sannan ya saketa yana fadin
"An kara samo mun inda za'ayi borehole, can wani kauyene a garin Katsina, na daisa aje a duba a tabbatar tukunna..."
Ta kalleshi, tun rasuwar Aise, shekaru shidda kenan, Haris ya kasa samun cikakkiyar natsuwa. A ranar data rasu, duk yanda 'yan uwa sukaso ayi janaizar zuwa washegari saboda kowa ya samu yazo daga Maiduguri, haka ma 'yan uwan Aise din su Mu'adh, Alhaji Modu yaki
"Tun wajen karfe biyu ta rasu, sai a barta har gobe? Saboda me? A kaita yau, ta samu ta wuce kwanan yau ko zata samu salama itama, addu'a ce kowa idan yayi mata ko da baizo ba In Shaa Allaah zata risketa"
Hakan akayi kuwa, sai dai shi kanshi Alhaji Modu yayi mamakin irin jama'ar da suka halarci Janaizar Aise, saboda Alhaji Mustafa ya sanar, anan gidanshi akayi mata wanka, wajen karfe biyar aka kaita, lokacin Haris ya baro asibiti yazo gidan, dashi aka kama munkarar da akasa Aise, dashi aka zirata cikin kabarinta aka mayar da kasa aka rufe. A ranar ne ya tabbatar da maganar da ake fada ta dan adam ba a bakin komai yake ba. Muna tafiya ne batare da sanin mutuwa na zagaya fuskokinmu ba. Sai gashi ya kasa tsaida hawayenshi, inya gogesu sai wasu su kara zubowa, zazzabi yayi na wajen sati saboda tashin hankali, amman bayan sadakar ukun Aise haka ya lallaba yaje makaranta, saboda yana so yayi magana da Malam, kamar kuma Malam yasan abinda yake ranshi wa'azin ranar akan mutuwa ne, akan shiriya da ba kowanne yake samun Rahmarta ba.
"A kowanne hali anaso ka zagaye rayuwarka da mutanen kirki, mutanen da zasu dinga tuna maka da Ubangijinka, ba mutanen da zasu shagaltar dakai ba, a irin wannan ne zakaga kana cikin shagala Allaah Ya dauki ranka, sai anje filin qiyama kaga abokanka sunzo sun wuce aljanna sun barka, ka dinga mamaki, sai daga baya kaji ashe shiriya ce tazo musu bayan mutuwarka ta zame musu wa'azi..."
Wannan maganar ta tsorata Haris matuka, sai maganganunsu da Aise suka dinga dawo masa, duk lokacin daya dinga biye mata inta rike shi, lokacin daya amsa zai sameta a hotel kafin mutuwa ta gifta musu. Shi gashi nan yayima kanshi alkawari, ya dauki alkawari tsakaninshi da Allaah ba zai sake kusantar zina ba, Malam kamar yana misali ne dashi da Aise da mutuwarta ce ta zame masa wa'azi, to da kuma tashi mutuwar ce ta zame mata wa'azi fa? Dashi kenan ko? Ya shiga ukunshi ko? To Aise ce a ukun yanzun?
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Ya furta zufa na keto masa, saida kowa ya watse tukunna ya samu Malam da tarin tambayoyinshi, haka kuma bai boye masa komai ba, ya fada masa
"Allaah zai yafe mun kuwa? Ina da sauran rabo Malam? Ita kuma fa? Aise fa? Ya zanyi?"
Anan Malam ya dinga kafa masa hujjoji da Ayoyin Rahmar Allaah, ya dan sama masa natsuwa da cewar zunubin Aise tsakaninta ne da Ubangiji, Ubangiji kuma mai yawan Rahma ne
"Zan iyayi mata sadaka? Ladan zai sameta?"
Ya kuma kara jin dadin da aka fada masa ayyukan alkhairi da ko bayan mutuwarka ladansu zai cigaba da samunka har kabari, saboda a cikin irin wadannan ayyukan alkhairin Aise tayi wasu daga ciki, ya san tayi, akwai kauyukan da tayi musu rijiyoyi saboda yanda matan suke shan wahalar zuwa dibar ruwa da kuma rashin samun ruwa mai tsafta alhalin suna da ciki, kar ayi maganar matan data taimakawa da magunguna da kudaden asibiti da makamantan wannan, kuma duk wanda ya samu lafiya ta sanadin taimakonta, yayi amfani da lafiyar wajen aikata alkhairi saita samu lada, haka wanda ta samawa tallafin sana'a don su dogara da kansu ma ba zasu kirgu ba. Sai Haris yace a ranshi
"Watakila, daya daga cikin wadannan ayyukan alkhairin na Aise ga bayin Allaah sune suka hana musu haduwa a ranar data rasu, watakila sune sukayi musu Katanga da jin kunyar duniya da lahira..."
Shisa ya daura damarar amfani da dukiyar da Allaah Ya bashi wajen nemawa kanshi da ma iyalinshi lahirarsu ba iya duniya kawai ba. Yanajin kamar zunubanshi suna da yawan da yake bukatar aikin alkhairan da yake fatan Allaah Ya karba Yayi masa Rahma ta sanadinsu
"Allaah Ya karba daga gareka..."
Maryama ta ce masa tana fadada murmushinta, har tausayi yake bata
"Akan mata, In Shaa Allaah na daina Maryamm, nagode da baki gaji dani ba, nagode da baki rabu dani ba, dan Allaah ki tayani, kiyi mun addu'a Allaah Ya karbi tubana, kiyi mun addu'a Allaah karya kara jarabani da kusantar zina, na dade a cikinta inajin tsoron sake komawa..."
Haka yace mata, saita rike hannunshi, tanajin wani sanyi na ratsa zuciyarta
"In Shaa Allaah, ba zaka sake ba, In Shaa Allaah, Allaah zai tsareka, ka kyautata tubanka, in ka kyautata tubanka Allaah Zai duba zuciyarka Ya kareka"
Ya dinga jinjina mata kai cikin yarda da kalamanta, yanzun kam sai yace
"Amin thumma amin... nagode"
Ta karasa tasa hannunta cikin nashi daya mika mata
"Da nayi me kuma?"
Saiya jata suka zauna gefen gadon
"Da kikayi komai ma"
Dariya tayi
"Kamar me da me?"
Ya daga mata girarshi guda daya
"Kamar dai auren baki irina bayan ke bakya son bakake ko?"
Dariya Maryama tayi sosai
"Ai ka karyatani Ganja...ka nuna mun bansan me nake so ba sai bayan na aureka, sai gani ba bakin namiji kawai nake zaune dashi ba, na goya bakaken 'yayanshi
Ya dan murda hannunta da yake rike dashi, tayi dariya, shima dariyar yayi
"Ba zaki daina ba ko..."
Dan kafin Aalim yayi wayau, haka yake binshi yana kiran Ganja Ganja, ta dinga tuntsira dariya
"Yanzun dan sunan soyayyar nan ma da mata take kiran mijinta ni na kasa samu"
Ta dan daga masa kafadunta
"Nafison Ganja dinne, dadi yake mun"
Sai kawai ya girgiza kanshi yana murmushi, dan shima inta ce Ganja din yanayi masa dadi, a gefe daya kuma yana tuna masa abubuwa da yawa da kullum ya kalleta suke zamar masa dalilin da zaice mata
"Nagode Maryamm, madalla da aurenki"
Haka kuma dalilai masu yawa da zasu hadu ita dashi suce
"Alhamdulillah..."
#LABULE...Asirin mai daki
#LubnaSufyan