Advertisements
Chapter 27 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   27 / 51

78K to 81K   out of 151K words

zatace ga fassararshi ba

"Fararen maza kadai kike kallo kenan?"

Da yake akwai tarin kuruciya da kuma wauta a tare da ita sai ta daga masa kai, ita fararen ne sukeyi mata kyau, in basu ba me zai kaita kallon wasu?

"Fararen ai sune masu kyau..."

Yaja numfashi, a hankali, ya kuma sauke a hankali

"Idan baki tashi daga gabana ba saina kwada miki mari"

Kuma da gaske yake, dukan mace na daga cikin abinda bai taba hangowa kanshi ba, to ka daketa kaji dadin me, amman yau, yanajin in taci gaba da magana tsaf zai kwada mata mari, farare take so ashe, shisa bata gajiya da ganin bakinshi, shisa bata taba nuna alamar yayi mata kyau ba, wani zafi yakeji a duka jikinshi, shi bama bakin nashi da take gani bane matsala, yanda take karewa wasu mazan kallo shine yake sakawa yanajin kamar kirjinshi zai rabe biyu.

"Sai ka mareni? Haka kawai? To ni me nayi"

Ya jinjina kai

"Karki tashi daga gabana, kar kuma ki rufe mun baki"

Yanda yake kallonta ne yasa ta matsa, yaja tsaki yana rabata ya wuce, to ita me tayi masa? Me tayi zaice zai mareta? Saita cire hijabinta kawai, ta kwashe komai takai kitchen tana ajiyewa inda ya kamata, ta fito zuwa dakinta, alwala tayi tana gabatar da sallar Magriba, data idar kuma sai tayi zamanta a wajen tana danne-danne a waya har akayi isha'i, saida tayi ta fita zuwa kitchen, salak dinta ta dibi rabi, ta yanka ta wanke tas, ta yanka timatiri harda su koren tattasai, tayi kwadon, ta zuba sauran taliyar da tayi da miya, ta dawo falo ta zauna taci kayanta a tsanake. Sai wajen karfe tara, lokacin da tasan Haris na shan shayin shi tukunna ta tashi ta shiga kitchen din, ta dauki kofi kenan taji shigowarshi, baiyi mata magana ba ya dauki wani kofin, ta kalle shi, sai taga shayin yake kokarin hadawa

"Yanzun zan hada maka"

Ta fadi, amman ko kallonta baiyi ba, ya gama hadawa ya fice daga kitchen din

"Ikon Allaah"

Tace a fili, amman bataji dadi ba har ranta, dan da sanyin jiki ta fita daga kitchen din, abu kamar wasa, Haris ya daina mata magana, editing dinma in taje dakinshi a rufe yake, gashi baya fitowa falon, haka zata kwankwasa ba zai koyi magana ba balle ya bude mata, kwanansu hudu a haka, taji gidan ya isheta, komai baya mata dadi, ta kuma rasa yanda zatayi, da safe har hawaye tayi tunda yanajin tanata masa magana amman ya wuce ya fita abinshi, ta kasa hakuri, Khairi na kiranta sai hawaye suka balle mata, dan dakyar ta iya ce mata

"Baya mun magana, haka kawai ya daina mun magana"

Ta karasa cikin sheshheka

"Haka kawai ba zai daina miki magana ba Maryama, me kikayi masa? Kunyi fada ne?"

Harta girgiza kai, sai ta tuna tun randa suka dawo daga kasuwa ne bai sake kulata ba, ta kwashe komai ta fadawa Khairi

"In bashi ba, babu abinda ya faru, banyi masa komai ba"

Khairi taja tsaki

"Ai nasan baki da hankali daman, amman ban zata zaki iyayin irin haukan nan ba, taya za'ayi ki fadawa mijinki kina kallon fararen maza? Ki kuma nuna masa wani kice yayi miki kyau? Ke yanzun in kuka fita tare sai ya kalli wata ya tabaki yace miki Maryama kinga waccen hadaddiyar ya zakiji?"

Sai da ta zabura daga zaman da takeyi, taji zuciyarta ta lailayo wani zagi da bakinta ba zai iya furtawa ba, wani duhu-duhu na neman rufe mata ido

"Ashe zan dirza kan yarinya cikin kasa"

Khairi tayi murmushi, tana tuna kishi irin na Maryama, kishin nan da Hajja take yawan damuwa akanshi

"Na rantse da Allaah sai nayi mata dukan da ba zata sake giftawa ta kusa dashi ba, kafin muyi tashin hankali dashi"

Dariya mai sauti Khairi tayi

"Dan yaga hadaddiya ya fada miki? To ina ruwanki? Sonshi kikeyi?"

Ta girgiza kai, ba sonshi takeyi ba, ai Khairi tafi kowa sanin bason bakaken maza takeyi ba, amman ai ya aureta, mijinta ne, kuma bata hango zama da wani namijin bayanshi ba tun ranar data tako kafarta cikin gidan, kenan an bata Haris, Haris ya riga ya zama nata, ita kuma sanin kowane duk wani abu da yake nata bata son rabashi da kowa, 'yan uwanta ma tana bakin cikin ta bude ido taga suna son wani daban, yanzun kuwa zuciyarta har zafi takeyi

"Ni ba sonshi nakeyi ba, amman babu wata banza da zatayi masa kyau muna tare bataji kanta cikin kasa ba"

Cikin dariya sosai Khairi tace

"Sai kece zaki ga kyan wasu mazan ki gaya masa kuma kiyi tunanin za'a zauna lafiya ko?"

Ita dai har yanzun bata ga wani abu ba

"Balarabe ne fa, kuma gaskiya na fada ni, meye dan na fadi gaskiya dan Allaah? Shima in zai fadi gaskiya ai ba zaice balarabe bashi da kyau ba, kuma iya kyan nagani, ko magana yayi mun ba kulashi zanyi ba ni da nake da aure..."

Fada Khairi tayi mata sosai, tace mata ta dinga kiyaye bakinta kan fadar irin wannan maganganun a gaban Haris, kuma inya dawo taje ta bashi hakuri. Sai dai a maimakon ta bashi hakurin, tunda tasan ko ta kulashi ba amsata zaiyi ba, sai kawai tayi timing din shigarshi kitchen, taje ta fisge kofin daya dauka, tasha gabanshi

"Wallahi saika kulani, ka kulani in baka hakuri"

Kallon nan da bataso yayi mata

"Dan Allaah, kayi hakurin, ai ba zan kara ba, kaji, ka daina fushi dani, dan Allaah nace, ba zan kara ba"

Ya girgiza mata kai, dan ko idanuwanshi ya rufe saiya dinga ganinta a motar nan tana karewa wani tiqeqen banza kallo

"Ni me zakice mun? Muna tare, ina zaune a gefe kike kallon wani? Da aurena akanki kike kallon wani katon banza?"

Da sauri tace

"Na daina, ba zan kara ba"

Kai ya sake girgizawa

"Ai kin daina fita, babu inda zan kara zuwa dake, kema kina cikin gida, ba sai kin fita bane zakije kina kallon maza"

Jin maganarshi yasa ta rude, tasan zai iya hanata fitar gabaki daya, kuma babu yanda zatayi

"A'a dan Allaah, wallahi ba zan kara ba, dan Allaah kayi hakuri...dan Allaah, ai kaga ban tabayi maka laifi ba sai yanzun, kuma na baka hakuri"

Yana ganin hawaye sun cika mata ido, amman takaicin da ya shaka ya kasa barin shi

"Dan Allaah kayi hakuri, kaji....dan Allaah fa nace"

Ta karasa maganar tana riko hannunshi da nata duka biyun

"Ba zan kara ba, dan Allaah kayi hakuri

Wani abu ya hargitsa cikin kanshi da yanda ta rike hannuwan nashi, kuma batasan ma tana kara dumtsa yatsunshi ba, ya dan kwana biyu rabonshi da mace, kusan sati biyu, hannuwan Maryama da suka rike nashi sai yaji yana neman susucewa, baisan lokacin daya daga dayan hannun nashi ya sake rike hannunta ba, yanajin laushinsu, yanajin layukan da suke jikin kowanne yatsa, a hankali ya dagasu yana sumbatar bayan hannunta

"Me yasa? Me yasa zaki kalli wasu mazan? Saboda ni ba fari bane?"

Ya tsinci kanshi da fadi yana saka idanuwanshi cikin nata, kuma kamar wadda ya rike, kamar wadda ya rike da wannan abin na cikin idanuwanshi saita kasa ko kwakkwaran motsi

"Ba zan sake ba, na daina, kayi hakuri"

Ta fadi kowacce kalma da dukkan zuciyarta, kila abinda ya gani kenan, saiya daga mata kai

"Zaki daina fita daga gidan Maryamm, zan iya hanaki daina zuwa ko ina idan na sake gani"

Ta daga masa kai da sauri, sai ya jata yana riketa a jikinshi hadi da sauke numfashi, ba kuma karamin kokari yayi ba lokacin daya rabata da jikin nashi, ya kai hannu yana ja mata kunne saida tayi 'yar kara

"Ai saina cire kunnen"

Ta tura lebenta na kasa, har lokacin akwai alamar hawaye a idanuwanta

"Ki hadamun shayi"

Murmushi tayi masa, murmushin daya kasa dannewa saida ya mayar mata, yanajin kewarta kamar ya shekara bai ganta ba, kamar bata gabanshi, baima taba sanin zaka iya kewar mutumin da kake gani kullum ba sai yau, sai yanzun da take tsaye tana ta kokarin hada masa shayi, kuma ta zuba komai, ta ajiye kofin zata dauki flask ne, ta bude wani dan bowl tana saka hannu ta dauki dankalin data soya ta mika masa

"Ci kaji, jan dankalin ne, iri dayane fa da wancen, kawai wannan yafi zaki"

Ganin ya kalleta yasa tace

"Dan Allaah kaci kaji, dankaline fa, bashi da nauyi"

Saiya karba, yaci, yayi masa dadi, tunda data kwashe saita kara mai, ta barbada maggi da dan yaji, ta yanka albasa ta rufe shi, sai kamshi yakeyi, bata ko tambayeshi ba bayan ta hada shayin ta zuba masa dankalin, yau ya zauna a falon, ya sha shayin suna kallo tare. Kuma da ya gama ci haka ya sauko kasa suka zauna da laptop din da bama karba yakeyi ba yanzun, ko yaushe tana wajenta.

Fada na biyu...

Da daddare ne ranar, wajen karfe takwas, ta gama maimaita duk wani abu da ya koya mata a satin kan wasu hotuna, sai kawai taji tana so tayi abinda bata tabayi ba, bude tarin folders din dake cikin laptop din tana kallon hotunan cikin kowacce folder, ta bude wajen guda hudu, sai kawai tayi scrolling can kasa, idanuwanta suka tsaya kan wata folder da aka rubuta "Vita Mia" a jiki, sai taji tana so ta bude, hotuna ne a ciki sunfi guda dari, ta bude na farko, zuciyarta tayi wata irin bugawa, ita bakake ba kyau suke mata ba, amman wannan bakar tayi mata kyau, a kallon farko da tayi mata tsaye cikin shigar riga da wando, ta saka hannunta a kumatu tayi dariya har fararen hakoranta sun bayyana tayi mata kyau.

Data danna na gaba ma itace, kusan hotuna ashirin, sai kace anyi mata dole, a na gaban ne tayi zaton ma mikewa tayi tsaye, saboda ita da Haris ne, tana kwance a jikinshi suka dauka, ta ga hotuna sunfi guda goma sha duka babu inda bata manne da Haris, ko ita bata tana ruqunqume shi haka ba, sai numfarfashi takeyi, lokacin data bude wani hoto tayi tsaye a kanshi, Haris dinne rike da hannuwan Aise, irin rikon da yayiwa nata hannun, haka kuma ya kai bayan hannunta ya sumbata irin yanda yayi mata, ta tabbata tiririn da takeji inda wani na tsaye kusa da ita watakila da yaga hayakin da take fitarwa, a lokacin ne Haris yayi sallama ya shigo gidan dan ya fita ne, kuma saiya zagayo, yanda ta dago ta kalle shi da idanuwanta da suka canza kala yasa shi kallon screen din laptop din.

Wani yanayi ya saukar masa, wani abu da yaketa dannewa, wani abu da bayaso ko a mugun mafarki ya gani, a tunanin shima dannewa yakeyi, Aise da wani kato, Aise a yanda suke a hoton nan da wani

"Wacece wannan?"

Ta tambaya muryarta na fitowa kamar anja kwano a kasa

"Aise"

Ya amsa a hankali, sai wani abu ya gilmawa Maryama, itace taga sunanta a jikin yatsanshi a asibiti, Aise, itace kuma suke ta qaqamar juna, itace yake ta dakon hotunanta kala-kala

"Wacece Aise?"

Ta sake tambaya batare da ta kalle shi ba, yayi shiru, kamar ba zai amsa ba, sai kuma a hankali yace

"My ex"

Da wani irin yanayi, wai yau shine yake kiran Aise da Ex dinshi, tsohuwar budurwarshi, har sun faru sun kare, ashe zasu kare shi da ita?

"Tsohuwar budurwarka, ba tsohuwar matarka ba? Tsohuwar budurwarka itace kuke aikata wannan zunubin kuma harka adana? Akan me? Saboda me?"

Ta karasa tana kallonshi kamar zata rufe shi da duka, takai bayan hannunta tana dirje shi a jikin skirt dinta, tana so ta goge sumbar da yayi mata da wannan bakin nashi da yaje ya sumbaci Aise, da bakin bakinshi, kuma kan idonshi tayi baya ta rufe folder din kafin ya hangi zata danna delete, baisa lokacin daya karaso yana rike hannunta ba

"Ka sakeni, ajiyar me kakeyi musu to? Ka sakeni in goge..."

Take fadi tana kiciniyar kwace hannunta, sai ya dauke lapton din daga cinyarta yana rufeta, ta kuwa mike tana kai mata wawura itama, daya janye hannunshi sai kawai ta saka nata biyun ta hankade shi, abin yazo masa a bazata saida yayi baya, kuma ga madaukakin mamakinshi sai kawai ta dan ware kafarta tana dunkule hannuwanta kamar wadda take a filin dambe

"Maryamm"

Ya kira da murmushi, kafin dariya ta kwace masa

"Dambe zakiyi dani?"

Cikin harzuqar da tayi, hawayen bakin cikin yanda ya hadata da kirjin da Aise ta gama kwanciya a jiki tace masa

"Eh din, kuma ko da kake ganin ka fini girma ba anan abin yake ba"

Ya girgiza kanshi kawai mamakinta na kara kamashi, sai kawai ya juya da niyyar tafiya da lapton din a hannunshi, yaji ta kawowa kafafuwanshi wawura

"Na rantse sai an goge hotunan nan... duka sai an goge su"

Ya kasa daina dariya yake fadin

"Ki sakeni Maryamm, wai saikin kayar damu, meye haka? Ina ruwanki da hotuna na? Me yasa zan goge"

Tana kaima kafafuwanshi duka take fadin

"Da ruwana, ka aikata Haram, wallahi Mu'allim dinmu in da zai ganka sai yayi maka wa'azin 'yan wuta kala-kala..."

Kokarin bambareta yakeyi amman takiya, sai kara rikeshi takayi tana so ta kayar dashi, shisa yasa karfi yaja baya, ya ajiye lapton din da ta sakeshi da sauri zata dauka, ya kamata yana janyota baya, data juya sai kawai ta kamashi da dambe na gaske, da duka karfinta

"Me yasa ma zaka sumbaci hannuna da bakin bakinka?"

Cewar Maryama wasu sababbin hawayen bakin cikin na zubo mata, yaji abinda tace, sai yayi mata wani irin riko data kasa ko motsin kirki, lokacin ne kuma yayi wani abu da ya kashewa Maryama jiki, ya sumbaceta, ko tace yayi iya bakin kokarinshi wajen ganin sunyi musayar labban ma gabaki daya, yanda duk taso ta kasa kwacewa, sai da ya gaji ya saketa da kanshi

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un, ni? Ni? Ganja ni? Ni kayiwa haka?"

Take fadi tana maida numfashi, bakin nan fa taganshi dazun, wajen kunnen Aise, dai-dai bayan kunnenta, bakinshi, watakila ma da sauran dauda a wajen tunda ba gane daudar bakaken mutane akeyi ba, nan ya dankara labbanshi ya kwaso dauda kala biyu, ta Aise din da kuma ta zunubi, sannan yazo ya manna mata a nata bakin

"Ni Ganja..."

Ta sake fadi wani abu na tsirga mata, tabbas ya gama cutarta, batajin yayi Istigfar, balle ya wanke masa dauda daya, shine ya dankara mata akan nata leben

"Wannan baqin bakin kasa akan nawa?"

Ya daga mata kai yana murmushi

"Ki kular dani, kiga adadin wajajen da bakin nawa zai taba yau, da baqin nashi da komai..."

Taji hawaye sun zubo mata, sai kuwa ya tako yana rikota

"Ka sakeni, wallahi ka sakeni, ka daina tabani da hannuwanka"

Jikinshi ya jata sosai

"Ganja bana so, bana so"

Dan haka kawai yaji yana so ya sake sumbatarta, baisan me taci ba kafin ya dawo, ko menene yana da yaji, akwai sauran dandanon a bakinta, dandanon da ya saka shi jin son cin koma menene, sai dai inya sake komawa ba lallai ya iya mallakar kanshi ba, kawai saiya sumbaci gefen wuyanta yana sakinta

"Ni ko?"

Ta sake fadi cikin yanayin nan da yakeji yana saka wasu notina kwancewa a bayan kanshi, ya girgiza kai, yana kallon yanda take goge wuyan nata, yayi dariya, ta jinjina kai tana sake matso hawaye, sai kawai ya dauki laptop din ya wuce yana barinta a wajen da tarin takaicinshi, a ranshi yana fadin

Wai duk akan taga hotunanshi da Aise?
Akan ya sumbaci Aise?
Tasan iya inda bakinshi yaje kuwa?

28

Fridge ta bude ta yanko cake dinta ta dora a plate, da ta koma falon ta zauna, tunda kallo take daman, sai ta dinga kallon cake din, Khairi ce ta aiko mata dashi har guda uku, idan kuma akace tun wancen birthday din nata take tara kudin ba zata musa ba, tunda ita dai Khairi tafi gane ta siyi kowanne irin cake a wajen Zainab Kerau (09057866631) kuma sai yayi watanni koya fridge yake da sanyi bai lalace ba, gashi babu ha'inci. Haris kanshi tayi mamaki daya kusan cinye guda daya shi kadai, da kanshi yake zuwa ya diba, kuma da yake taga wanda yafi so din, chocolate cake ne, itama shi tafi so, fushin da takeyi bai hanata bar masa shi ba.

Da yake shi yaje tasha ya karbo mata sakon, ko da Khairi ta kirata ranar tace mata

"Ki bani lambar mijinki"

Babu wani tunani ta tura mata, daya kawo saida yace mata

"Yaune birthday dinki? May 3rd, ban sani ba, me yasa baki fadamun ba?"

Saita harare shi tana fadin

"Tunda kasan na Aise ai lafiya lau"

Ya girgiza kanshi batare da yace mata komai ba ya wuce ya kyaleta. Kawai ta rasa yanda zatayi ne, ko zuwa yayi ya gifta ta gabanta sai ta dinga hango shi Aise a jikinshi, idan hannunta ya rike ma sai taji kamar akwai sauran wani abu na Aise a jikin nashi hannun daya hada ya riketa dashi yana shafa mata, ranar daya sumbaceta, batasan adadin brush nawa tayi ba, saida dadashinta ya dinga zafi. Ko baccin kirki kasawa tayi ranar, data rufe idanuwanta sai ta hangoshi da Aise, sai wani abu mai kama da zazzabi ya rufeta. To Khairi da taga ta kwallafa rai akan wannan saurayin nata bayan tace yana da mata ya zatayi? Anya ita zata iya auren mai mata kuwa? Watakila idan itace zata shiga zata samu sauki, amman tunanin ace wata zata shigo mata gidan miji sai takejin jiri daga kwancen da take.

Ko da Hajja take yawan magana akan kishinta tana ce mata

"Maryama idan kinyi sallah ki dinga addu'a kinji, kice Allaah Ya sassauta miki kishin da kike dashi, Allaah Yasa karya zame miki halaka, Allaah Karya jarabceki ta sanadin shi"

Tanayi din, duk da bata gane dalilin da yasa Hajjan take yawan ce mata ta dingayi ba, ita wanne kishine da ita? Dan batason wasu su kwace mata 'yan uwa? Bataso taga suna fifita soyayayar wasu akan tata? Ko dan gabaki daya ma so takeyi su tattara duk wani so da suke dashi akanta ita kadai? Laifi ne? Amman a ranar da taga hotunan nan ta gane daya daga cikin dalilan da yasa Hajja ke sakata yin addu'ar. A hakanma tanajin dan ba auren soyayya sukayi da Haris ba, ita ba sonshi takeyi ba, amman ai mijinta ne, nata ne, batason kowacce mace a kusa dashi tunda nata ne. Babban abinda yayi mata tsaye ma da yaki goge hotunan, me yakeyi dasu? Me zaiyi dasu?

Sakasu yakeyi a gaba ya dinga kallo yana debewa kanshi kewarta mana, wani tunanin ya bata amsa, yana sakata tashi zaune daga kwanciyar da takeyi. Ko randa ya shigo gidanma ya ganta tana cin cake din, tasan dan tayi magana ne yasa shi daukar plate

27 / 51