Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
tayi dai-dai da abinda kake nufi
"Me kikeyi?"
Ta kankance idanuwanta akanshi
"Ba zaka fadamun abinda kace ba ko?"
Ya daga mata girarshi
"To saboda me?"
Ya kara gyara tsayuwar shi yana jingina bayanshi da kofar kitchen din sosai, yasa hannunshi a aljihu ya zaro wasu kudi, yan dari biyar-biyar ne, watakila dan ba sababbi bane shisa ta gansu masu yawan gaske
"Ga kudinki"
Ta zaro idanuwa, jiyan su Barde suka saka masa su a account, dubu dari ne cif, wai su duka ukun ne suka harhada a bata, shikuma daya fita yau saiya tsaya banki ya cirosu gabaki daya
"Kudina? Ni? Yaushe?"
Tayi masa tambayar a rikice
"Su Lalaye ne suka baki"
Kai take girgiza masa
"Me yasa? Kudin ai sunyi yawa, Hajja ma sai ta iya mun duka idan ta sani...dan Allaah ka mayar musu da kudinsu kace nagode"
Maganar ta bashi dariya
"Wacece Hajja?"
Ya tsinci kanshi da tambaya
"Mamana"
Ta amsa masa, ya girgiza kai kawai
"Ya za'ayi ta dakeki? Ke da kina Kano ita tana Kaduna, yama za'ayi ta sani"
Cike da tsoro Maryama take kallonshi
"Hmm bakasan Hajja bane shisa...kuma ai dole zan fada mata idan aka bani abu"
Baisan shekararta nawa ba, yana bata sha shida zuwa sha bakwai, amman da tayi magana sai yaji anya kuwa? Anya ta kai wannan shekarun? Saboda shi dai ba zaice yaga kuruciyar kowa ba, yasan Aise tana karama, amman ba zaice akwai rana daya da yaga tayi wani abu na yarinta ba, sai dai ma ta saka tunanin anya bata girmi shekarunta da aka fada maka ba.
"Sai kice mata abokaina ne suka baki da suka zo, ba zatayi fada ba"
Ta girgiza masa kai
"Kinga ba zasuji dadi ba idan aka mayar musu"
Da saurinta tace
"To na bar maka, ka dauka"
Shima ya girgiza mata nashi kan
"Nima Mami zatayi mun fada ai, tace na karbe miki kudinki"
Ita dai bata ga wanda zaisa ta karbi wannan tulin kudin da suke hannunshi ba
"Ka ajiyemun zan dinga karba"
Yayi murmushi
"Ni zaki yiwa wayau? Ki karba ki ajiye a dakinki"
Itama murmushin tayi
"Da gaske zan dinga karba, ko yanzun ma bani dari biyar...sai ka ajiyemun sauran"
Dariyar da yayi mai sauti ce
"Me zaki siya da dari biyar?"
Batare da tunanin komai ba tace masa
"Flour"
Ganin yanda yayi da fuska yasa ta dorawa da
"Tayin cin-cin, meatpie zanyi"
Dan dazun sukayi maganar meatpie din da Khairi, tace mata taje gidan Adda Zahra ta tayata aikinshi da yawa, sai itama tayi tunanin inda tana da flour din da tayi, saita saka a fridge, ta dinga soyawa in zata hada masa shayi ta dinga bashi, da wani abin ma, tunda ta kula abincinta ne bayaci, rannan da ta zuba masa jalof din shinkafa da tayi a dan karamin bowl, jin tayi mata dadi, saiya dauki kofin shayin yace mata
"Na koshi, Nagode"
Abinda Maryama bata sani ba, ba abincinta din bane bayason ci, abincin ne gabaki daya bai dameshi ba, in dai zai samu irin cin-cin din da ta bashi ko kuma wani abin dai banda abinci, zaifi masa
"Ki rike kudinki, in dai flour ce zan kira Lalaye sai a kawo, suna siyarwa a shagon shi"
Da fara'a a fuskarta tace
"Dan Allaah? Yaushe za'a kawo?"
Ya raba bayanshi da jikin kofar
"Ko anjima ma idan na fita sai in taho miki da ita, flour kadai?"
Tana son doya ma inda zata samu, da dankali, bataso yaga kamar bata da hankali ne
"Bana so kaga kamar bani da hankali ne fa, tun rannan ina so ince ka siyo mun doya da dankali"
Kallonta yayi sosai, kallo ne na rasa abin cewa, ita kuma saita fassara shi da kallon rashin hankalin kamar yanda tayi tunani
"Ka dauka cikin kudin nan to"
Saiya taka har inda take tsaye, yayi abinda yake ta masa yawo cikin kanshi tun jiya, ya kamo hannunta, ya jishi da sanyi a cikin nashi, dan ta gama aiki da ruwa ne, nama ma ta wanke, kuma naman na da kankara a jiki, ya kalli yatsunta, kamar yanda itama ta kalli hannun nata daya rike, zuciyarta na bugawa kamar zata fito waje, yasa dan yatsanshi daya yana taba jan lallen da yake farcenta kamar mai son dangwalo shi, a hankali kuma ya dumtsa hannun nata cikin nashi, kuma a wannan lokacin sai yaji bai taba rike hannun macen daya ga kamar an halitta mata nata hannun ne saboda yayi dai-dai rikewarshi. Gashi hannun nata yayi masa laushi ba kamar yanda yayi tsammani ba, ya bude yatsun nata yana murza yatsanta manuniya da yaga kamar yanka ne a jiki
"Dame kikaji ciwo?"
Yayi mata tambayar kamar baiji bugun zuciyarta ba, kamar kuma baiga yanda jikinta yake kyarma ba, sai ta ganshi babba a gabanta, taga yana da tsayi tun a ganinta na farko dashi, amman yanzun da yake tsaye a gabanta, sai taga ba tsayi kadai yake dashi ba, babbane, babba sosai, ta yanda ta tabbatar inda wani zai shigo kitchen din a wannan lokacin ba zaisan tana tsaye a gabanshi ba
"Ya akayi kikaji ciwo?"
Ya kara tambaya yana murza wajen, yana kuma murza wani abu a cikin kirjinta daya kara gudun zuciyarta
"Da wuka..ina yanka albasa"
Ta iya furtawa cikin rawar murya, daya kalli idanuwanta kuma, yau sai taga wannan ruwan da take gani cikin idanuwanshi kamar hawaye yau sun sauya launi, sunyi wata kala da bata da suna a iya hasashen Maryama, tana jin da zata jure, da batayi saurin sauke nata idanuwan ba, da zata iya ganin fuskarta a cikin wannan maiqon da idanuwanshi sukeyi, ya hadiye wani abu daya taso masa, sai kawai yasa kudin nan a cikin hannunta
"Bari in dawo"
Yace mata, kafin tayi wani yunkuri harya saki hannunta ya juya ya fice da sauri, yana barinta da nauyin kudin nan da kuma nauyin da dumin hannunshi ya bar mata, ta dafa kantar kitchen din tana jinta wata iri. Haris daya fita motar shi ya bude ya zauna, ya kwana biyu rabonshi da mace, yasan shine dalili, dalilin da yasa rike siririn hannun Maryama ya hautsina masa kai, in ba haka ba wannan 'yar yarinyar? To akan wanne dalili ma? Kuma daya ja motar tashi ya nufi kasuwar singa, har shagon su Lalaye, duk yanda Lalayen yayi na ya bada kudi a aiki daya daga cikin yaran shagon su siyo masa doya da dankalin kiyawa yayi, dole suka fita tare da Lalayen, ji yayi yana so ya siyo da kanshi.
In yaga ta soya tana ci kamar zaiji dadi, Lalaye ne ya hana shi kwasar komai da yawa yace masa tunda su kadaine zai lalace, inya kare sai a kara siya, flour dinma da yace a bashi buhu daya sai da Lalaye ya kwashe da dariya
"Wai kai Ganja me yasa baka da hankali ne? Ko kai zaka kwanta ta dinga barbadewa da filawar sai tayi kwari bata kare ba...".
Saiya dibar masa, baima karbi kudin ba
"Maza ka karya shagon"
Cewar Haris, Lalaye yayi dariya kawai
"Ya akeyi idan mutum zai yanka albasa idan ba'a so ya yanke hannu?"
Haris din ya tambaya, dan har yanzun yanajin shatin yankan da yake yatsan Maryaman cikin kanshi
"Bangane ba"
Ya numfasa
"Ta yanke hannu wajen yanka albasa, ba yanda akeyi kar a yanke?"
Lalaye ya girgiza kanshi cikin alamar tunani, gidansu akwai mata sosai, kuma yasha shiga kitchen ya gansu suna aikace-aikacensu, amman shi kam ba zaice yasan yanda za'ayi a yanka albasa batare da an yanke hannu ba in tsautsayin yankan yazo
"Ni kam ban sani bafa, in ba dai akwai wani abu da ake yanka albasa dashi ba"
Da sauri Haris yace
"Menene? Dame ake yankawa?"
Lalayen ya zageshi
"Wai ina zan sani ne Ganja? Ba saika karba ka dinga yanka mata ba, tunda daman ka auri wannan jinjirar ai raino ya ganka"
Cikin bacin rai Haris yace
"Wai dan uwarka Lalaye kare mata kallo kayi?"
Aikuwa me Lalaye zaiyi banda dariya, yayi dariya ba kadan ba
"Kwantar abokina, kai kasan ko mace kabi na hakura da ita, balle matarka, musulmin kallo ne wallahi"
Yanda Haris ya bishi da ido kamar zai kai masa naushi yasa shi sake kwashewa da dariya
"Bari in kira Raliya in tambayeta"
Raliya, kanwarshi ita ta fada musu a siyi chopping board, kuma da sukaje wani shago da ake siyar da kayan kitchen sukace a basu, mai shagon ya tambaya guda nawa kuma wanne iri, sai Haris yace
"Me kyau, wanda yafi kowanne kyau, guda shida"
A tunanin shi idan daya ya lalace sai ta dauko wani, kuma guda shidan ya siya, saita saka masa uku na katako, ukun kuma na roba. Haka ya koma gida da tarin siyayyar nan, da yake Lalaye yasa shi har kwai ya siya mata, shima ya fara shigarwa yana bata. Tana ta binshi da kallon mamaki da wani abu da bashi da fassara a wajenta, sai gashi da wannan chopping boards din ya kwaso ya zube a gabanta
"Abin yanka albasa, ki dinga yankawa akai karki sake yanke hannunki"
Harya wuce ya shige dakinshi ta kasa cewa komai, ta kalli yatsan nata, ba wani yanka bane mai girma, dan jinin ma kadan ya zuba, tunda tayi wanke-wanke a shekaranjiyan ta tsoma shi a omo ta nemi zafin ta rasa. Batasan me yasa ba, sai taji kamar kuka na neman kwace mata...
*
Kuma tunda ya kawo doyar da dankalin, ta soya doyar da kwai, ta hada masa da shayi saiya girgiza mata kai
"Banyi jagwalgwalo ba wallahi, saida na wanke har hannu na tukunna, dan Allaah kaci kaji"
Maryama ta fadi tanajin babu dadi, har kayan kamshi ta saka a cikin kwan yanda taga Hajja nayi, duk yanda tattasai yakeyi mata zafi a hannu haka ta daure ta yayyanka ta watsa cikin kwan saboda yaga suyar tayi kyau yaci, yanda yayi mata kirki, itama tana so tayi masa kirki koya ne
"Bana son doya, tana mun nauyi a ciki, bana son abinci masu nauyi, basa narke mun da wuri, cikina zai kumbura"
Duk da Anisa ta taba ce masa
"Ai injinan da ake markada maka abinci dasune duk sun dakushe, sunyi tatsa, saboda yanda baka son cin abinci, shisa baya narkewa da wuri kake kumburin ciki, in baka maida hankali ba nan gaba kai da su shinkafa sai dai ayi blending ka kurba"
Ya dinga dariya kawai, in dai akan abinci ne duk wani da zai rabe shi haka zaiyi fama ya gaji ya kyaleshi
"Ba dan kinyi jagwalgwalo bane ba zanci ba"
Taji sanyi kuwa, data soya dankali ma ta hada masa harda kwai, haka ya fito mata da plate din ya cinye dankalin tas, amman kwan bata ga alamar ya taba shi bama. Da ta gane yana son dankalin, sai ta soya masa, meatpie din da tayi kuwa, hudu ta saka masa, amman rabi yaci, ita mamaki yake bata, yanda tasan mazan gidansu da kafirin ci, haka akeyin rawun ana kara abinci, randa akayi rana ba'a gama abinci da wuri ba kuwa duk wani dan cin-cin da biredi da yake gidan sai sunga bayanshi.
Idan lissafi bai bacewa Maryama ba, to kwanansu talatin harda biyar da aure, kuma a ranar ne Haris din ya sameta zaune kan kafet, ta jingina bayanta da gadon doguwar kujera, da remote a gefenta tana kallo, sai wani filet da ta zuba shinkafa da miya tana ci, sai kamshi abincin yakeyi, kuma daya tashi saiya zauna a gefenta shima yana sakata kusan shakewa da shinkafar da take bakinta, tunda ya zauna gab da itane har kafadarshi na gugar jikinta, a kwanaki talatin da biyar din nan ya shiga Kaduna sau hudu, sai dai bai kwana ba
"Ba zan daina zuwa in ganki ba Mami, amman ba zan saketa ba kamar yanda na fada miki, sannan in dai zanzo ki sake tayar mun da maganar nan kona zauna zan tafi abuna..."
Haka ya cewa Hajiya Rumana a zuwanshi na karshe ko zata hakura ta daina yi masa wannan maganar, ko zai samu ya kawo karshen wannan tashin hankalin nata akan aurenshi da Maryama, shi yanda ta daga hankalinta ma sai da ya dinga tunanin ko yarinyar na da wani nakasu ne, sai ya ganta lafiya kalau, banda shirme da yarinta baiga wani abu a tare da ita ba, kuma har kasan ranshi yanajin babu wani abu da zaisa ya saketa, tunda ya iya jure rashin Aise, yake kan jurewa saboda auren, me kuma ya rage masa da ba zai jure ba. Daman sallama zaiyi mata saboda tafiyar da zaiyi Syria, amman saita waya yayi mata sallamar tanata bambamin fada, baice komai ba ya kashe wayarshi, ya gama shirya komai, washegari da yamma zai wuce, shisa yake so ya fadawa Maryaman, sati biyu zasuyi
"Wai bakya gajiya da kallon Indian?"
Ya tambayeta a maimakon amsar gaisuwar da tayi masa
"Yana da dadine, wannan tun ina gida ma muke kallonshi"
Ya jinjina kai
"Bai kare ba kuma?"
Ta danyi dabarar gyara zamanta dan ta matsa daga jikinshi, dan ji tayi kamar yana fitar da tiriri, dumin shi na ratsata har cikin ciki, kuma zuciyarta taki daina bugawa
"Ai yana da yawa sosai, ance ma ko rabi ba'ayi ba..."
Shikuwa ina zai iya wannan kokarin
"Tafiya zanyi daman, gobe"
Da saurinta ta kalle shi
"Tafiya? Ina zakaje?"
Ta karasa maganar tana ajiye cokalin da yake hannunta
"Syria"
Ta maimaita Syria cikin kanta babu adadi, kamar maison gano yankin da Syria din take
"Ba dadewa zanyi ba, sati biyu zanyi In Shaa Allaah, amman zan iya biyawa wani wajen, ban dai sani ba, kaman dai ba zan wuce sati hudu ba"
Abinda taji ya taso mata sai yayi mata tsaye cikin makoshi, sati hudu? Ita kadai zata dinga kwana kenan?
"Nikuma fa?"
Ta tambayeshi muryarta na fitowa a karye kamar mai shirin fashewa da kuka, shine tunanin da Haris baiyi ba, ita din, saboda tunanin nashi ya tsayane zata zauna anan, tunda ma inya yawata da tunanin nashi ai babu yanda za'ayi ya dauketa, shima da yaya aka sama masa clearance din tafiyar?
"Ni kadai zan zauna?"
Cewar Maryama idanuwanta cike taf da hawayen da Haris yaga kyallinsu tar ta cikin hasken dakin, raunin mace na daya daga cikin abu na farko a jerin abubuwan da yake so a tare da mata, in suna tare dashi yana son ganin rauninsu, yana son ganin wannan fragility din da suke tattare dashi, yanayi ne da yake tabashi har zuciya, shisa kukansu ma burgeshi yakeyi, kyau yake ganin sun kara yi masa, yana so yaga fuskar Aise in ta gama kuka, yaga gashin idanuwanta jiqe da hawaye, mascara din da baka raba fuskarta dashi ta sauko kasan idanuwanta da kuma gefe tanayi masa kama da panda, yana so yaji yanda jikinta ke amsawa da kukanta a lokacin da ya riketa a nashi jikin, yana so ya goge mata fuskarta yanajin sanyin hawayenta.
Amman yau, a karo na farko a rayuwarshi yaji bayason hawayen dake cike da idanuwan Maryama su zubo
Yau bayason ganin hawayen mace...
20
Haka tace masa
"Ka maidani Kaduna, ka kaini gidanmu inka dawo sai kaje ka daukeni mu taho nan"
Daya kalleta, yaga hawayen da take ta sharewa saiya girgiza kai, yarintarta ta kara fitowa, sai yaji babu wani abu da yake so irin yasan tana cikin gidan nan nashi, sai ya girgiza mata kai
"Ba zaki koma Kaduna ba"
Ta sake share hawayen daya zubo mata, hawayen da yakeji har cikin ranshi
"Ni kadai zan zauna? Dan Allaah karka barni ni kadai"
Ya sauke numfashi
"Akwai wanda zai iya zuwa ya zauna dake?"
Khairi ta fara fado mata a rai, sai dai tasan da wahalar gaske Abbansu ya yarda da wannan lamarin, ba zata manta lokacin da Adda Zahra ta samu cikinta na farko ba, ta dinga fama da wani irin laulayi mai tsanani, ita da mijin sukazo suka roki Abban akan ya bari wani a cikinsu ya koma a dinga tayata zama da aikace-aikace, sai yace musu a nema mata 'yar aiki, ko cikin danginshi wani yaje ya zauna tare da ita, babu yanda ba'ayi ba amman yaki amincewa, da Hajja tayi masa magana sai yace
"Bani da natsuwar irin wannan gwamutsin zaman, inda matar su Khalifa ce, sai su tafi hankalina a kwance, ai akwai mata a gidansu, ya daukar mata guda daya"
Sai mai aikin aka samar mata kuwa
"Adda Khairi ce, kuma Abba ba zai bari ba"
Haris ya jinjina mata kai
"In dai Abba ne zan hadashi da Baba, zai barta tazo idan yayi masa magana...ki daina kukan nan, bana so"
Ta daga masa kai tana jan hanci, ita dai ko mai aikin ce a samo mata, dan ba zata zauna gidan nan ita kadai ba, idan Abban bai bar Khairi tazo ba, in ya tafi akayi ruwan sama fa? Ya zatayi? Dan tama manta ba lokacin damuna bane ba. Data mike sai yace mata
"Ina zakije?"
Ta sake jan hanci
"Fuskata zan wanke in kwanta"
Kai kawai Haris ya jinjina, yana kallo ta shiga dakinta, sai lokacin ya kula ko rabin abincinta bataci ba, ya dauke plate din, ya kashe kayan kallon, ya kai kitchen, da yake su can in anyi sauran abinci ba almajiri suke dashi ba, a shara kawai ake zubawa, haka ya juye a shara, ya wanke plate din ya kife shi inda yaga wasu irin shi, sannan ya wuce dakin nashi yana kiran Alhaji Mustafa, da yake sunyi waya ma da yamma, bugu biyu ya daga, suka kara gaisawa
"Baba daman tafiyar da zanyi ne, bana so in barta ita kadai, nace ko zakayiwa Abba magana, tace akwai 'yar uwarta Khairi sai tazo su zauna kafin in dawo"
Daga yanayin yanda Alhaji Mustafa ya amsa yasan yaji dadine, kafin ya kashe wayar kuwa saida yace
"Allaah Yayi maka albarka Haris"
Haka ya kwanta kalmomin na zagayawa cikin kanshi suna sanyaya masa zuciya har bacci ya dauke shi. Da safen kuwa Alhaji Mustafa ya sake kiranshi ya gaya masa Khairin zata zo, za'a kawota, daya samu Maryama a kitchen ya gaya mata sai tayi masa murmushi tana dorawa da
"Nagode. Karfe nawa zaka tafi?"
Ya duba wayarshi, lokacin takwas da rabi ne
"Karfe tara da dan wani abu"
Lalaye ya kira dan ya kaishi filin jirgi, tunda anan gida zai bar motarshi
"Zan bar miki mukullin motata, idan Adda Khairin tazo sai ki bata ko da kina son wani abin saita fita ta siyo miki, ke dai karkije ko ina kina jina? In ba rashin lafiya ba, karki fita ko ina"
Ta daga masa kai dariya na kwace mata da jin wai zai bar mata mukullin mota dan Khairi tayi amfani da ita
"Ai bata iya ba... motar, bata iya tuki ba"
Ya dan nuna alamar mamaki a fuskarshi, shi ba zai tuna ma tun yana da shekara nawa ya fara koyon tuki, ya kuma fara daukar mota yana fita ba, haka ma sauran 'yan gidansu duka, har matan, ko yaran Umma Fadime ma yana ganin suna fita da mota, to idan yaran Alhaji Mustafa ma basu iya