Advertisements
Chapter 23 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   23 / 51

66K to 69K   out of 151K words

saka dariya kwace masa ba, dariya tun daga zuciyarshi

"Taya kai zai gutsire ya fadi?"

Yayi tambayar yana dariya

"Ni ina na sani, ba abinda kaso kayi ba kenan? Ka kashe kanka?"

Ya dan girgiza kai kawai, har lokacin fuskarshi da alamar fara'a, bayani likita yayi mata sosai, dalla-dalla akan hadarin da Haris yake ciki, duk wani abu da bata gane ba haka ta dinga jera masa tambayoyi kala-kala yana amsata.

"Me yasa kake shan wiwi?"

Ta tambayeshi kai tsaye, idanuwanta fes akanshi, tambayar da yaji kamar ta sake mayar dashi ta kwantar saboda dukan da tayi masa, tunda a mafarki ma baiyi hasashenta ba

"Nasan ka jini"

Cewar Maryama ganin yayi wajen mintina uku, kamar bashi da shirin amsa mata, saiya juyo da kanshi yanda zai kalleta sosai

"Me zance miki?"

Ta dan daga kafadunta

"Gayamun zakayi me yasa kake sha bayan bakayi kama da wanda zai sha wani abu ba"

Yayi wani gajeran murmushi da bata ga alamun nishadi a cikinshi ba, asalima wani abune ya gilma ta cikin idanuwanshi

"Masu shan wani abu suna da wasu kamanni ne?"

Ta danyi shiru, ba zatace suna da kama ba, amman ai in an gansu ana ganesu, da yawa a iya tunaninta sun taso ne basu da tarbiya, sun taso a kangare babu wanda ya isa dasu shisa sukeyin shaye-shayen, shikuma bata ga alamar rashin ji a tare dashi ba

"Ban sani ba, kawai dai bakayi kama dasu ba, shisa nake so in san me yasa kake sha"

Yaja numfashi ya fitar a hankali

"Haka kawai"

Ya amsa da dukkan gaskiyarshi, rana daya ya kalli 2Pac yaji yana so ya busa hayaqin, yana so yaji abinda yakeji da baya gajiya da bankadawa cikinshi, shikenan kuma, daya fara sai ya kasa bari, ko dan ya taba gwada barin ma? Yana so ya bari kuwa? To me zai maye masa gurbin wannan buzz din da yakeji cikin kanshi?

"Sannunka...huhun naka ne baka so kenan?"

Ya nanata huhu yafi sau biyar a jere amman ya kasa gane menene shi

"Huhu? Menene huhu?"

Dariya ta kusan kwacewa Maryama da yanayin yanda yayi tambayar, saita fada masa da turanci

"Oh shine huhu daman?"

Ta jinjina masa kai

"Likita yace naka yayi bakikirin, saida ma na tambaye shi daman ba baki bane ba yace mun wai a'a..."

Idanuwanshi akanta yace

"Ke naki baki ne?"

Ta girgiza kai

"To akan me nawa zai zama baki"

Saita kalle shi kawai

"Wai wanne irin baki nake dashi a idonki Maryamm?"

Tayi dariya

"Ki amsani wanne irin bakina kike gani"

Ta makale kafada, ya kamo hannunta yana janyota ta kuwa rankwafa gabaki dayanta kamar zata fada masa, dan saida jikinta ya daga daga kujerar, ta soma kiciniyar kwacewa amman riko yayi mata bana wasa ba, baima san akwai wannan karfin a jikinshi a yanayin da yakeji ba, amman so yakeyi ya jata kan gadon, ya matseta saita bashi amsa

"Yi hakuri...tsaya in fada maka to, ka sakeni"

Saiya kara karfin rikon da yayi mata

"Allaah zan fadawa Hajjanka, ai tace zata dawo da safe"

Wani abu ya haska cikin idanuwan Haris din

"Hajja? Hajja tazo?"

Ta daga masa kai tana kiciniyar kwace hannunta, saiya sassauta mata rikon harta koma ta zauna, amman bai saki hannun nata gabaki daya ba

"Eh da Baban Tudun Wada, harda Abbana sukazo"

Yaji wani irin yanayi na shigarshi

"Ya akayi sukazo? Ke kika kirasu? Me yasa zaki kirasu?"

Ta girgiza masa kai, a hankali ta fada masa abinda ya faru tun daga farko

"Sunyi magana da Doctor dina? Yayi musu magana?"

Ta daga masa kai a hankali, ya saki hannunta, ta rike shi da dayan tana murza inda ya riketa

"Damn"

Ya fadi kasan numfashinshi yana shafa sumarshi, karshen abinda zaiso a halin yanzun shine abinda zai taba alakarshi da Alhaji Mustafa, kuma tace harda Alhaji Sa'id akazo, kuma yana da tabbacin tare za'a hadu a fada musu komai, ya sake kallon Maryama, haka kawai yaji koda kowa ya sani, ko da kowa zai sani, yaso ace an tsame Alhaji Sa'id daga jerin wadannan mutanen, itama da ta sani babu abinda yaji, abinne yazo masa a bazata da kuma yanayin da tayi musu maganar

"Karka damu, naga fa duk ransu bai baci ba, kawai dai kowa hankalinshi ya tashi, kuma nasan saboda ance huhunka na gab da samun matsala ne"

Kallonta dai yakeyi, yanda take fadar duk wani abu da take so kanta tsaye

"Huhun naka ne yake da muhimmancin a wajen mutane da yawa, sai ka hakura da wiwin tunda babu wani dalili da yasa kake sha"

In ta cigaba da magana, zai jawota, zai matseta a jikinshi, saboda abinda yake so yayi kenan

"Kiyi mun shiru in koma bacci Maryamm"

Ta dan gyara zamanta, ita batajin baccin, tama manta tsakiyar dare ne

"Dan ina fada maka gaskiya? Hajja zata dawo ai, babu ruwana"

Tasan matar, amman jiya da ta matso kusa da ita, sai wannan micijin da akeyiwa lakabi da kububuwa ya dawo mata, duk da bawai ta taba ganin kububuwar bane, Hajiya Rumanan ce tayi mata kama dashi a cikin kanta, bata dai bata tsoro bane ko kadan, amman aishi mamanshi ce, dole zata bashi tsoro

"Ai kasan halinta"

Yanda ya juyo da jikinshi gabaki daya yasa tayi baya da kujerarta da sauri, ya kalleta, da idanuwan nan nashi, idanuwanshi da take ganin wannan ruwan a kwance cikinsu kullum, zuwa yanzun tasan ba hawaye bane, amman kuma akwai wani abu dangane da hayaqa Haris din da yakeyi mata dadi, yana mata yanayi da Khalifa, ita da yake tana da saurin shaqa, sai Alhaji Sa'id yace ta daina tsokanar kowa yanda itama babu wanda zai tsokaneta, sai ta kiyaye kuwa, Khalifan ne kawai take dan tabowa lokaci zuwa lokaci ta bakinshi yakan ce

"Jikinki ne yake miki kaikayi ko Maryama?"

Shisa tace

"Kuka zakayi? Dan Hajja zatazo? Karta zaneka?"

Cikin wata irin murya yace

"Zo nan"

Tayi dariya

"Ga idonka nan da hawaye"

"Zo Maryamm, zo kiji"

Ya sake fadi, ta karayin dariya tana jan kujerarta baya, idanuwan nashi take kallo, da wannan abin kwance a cikinsu, yanda idanuwan sukayi fari qal, kwayar ciki baka, sai take ganin maiqon cikinsu kamar ya karu ne

Wata rana,
Wata rana zata saka yatsantsa a ciki taga ko zata iya dangwalo maiqon nan,
Wata rana...

24

Kwana biyu ya kara a asibitin kafin su sallame shi, a kwana biyun nan kuma ya saka halayen Maryama cikin jerin abubuwan da ba zasu taba gajiyawa da bashi mamaki ba. A daren daya farka, daga shi har ita basu koma bacci ba sai bayan da sukayi sallar asuba, lokacin ne ta kira wani Nurse, namiji, yazo ya saka masa wani karin ruwan, kuma yanda ya fara jin idanuwanshi na rufewa da kansu, ya tabbata akwai allurar bacci cikin wanda yaga sun matsa a ruwan kafin su saka masa. Lokacin daya tashi ba zaice ko karfe nawa ba, amman yaga Maryama a zaune, ta canza kayan jikinta, ba zai tuna kalar kayan jiya ba, amman yasan basu bane a jikinta, yanzun wani material ne, mai dogon hannu da ya matse daga tsintsiyar hannunta, sai kuma hula data saka ja, saboda akwai ja a jikin filawar da akayiwa material din kwalliya dashi.

Plate ne a gabanta da take ta yayyanka wani abu a ciki da cokalin da take rike dashi, sai kuma kofi a ajiye, kallonta yakeyi, yanayinta, idanuwan shi sukayi tsaye akan wuyanta, siririn wuyanta da kamar ba zai dauki nauyin kanta ba, a wannan lokacin, sai yaji hannuwanshi nayi masa kaikayi, yana son ace akwai camera dinshi a hannunshi, yana so ya dauketa hoto, yana son ya ganta, a wannan zaman da tayi yasan dole akwai abubuwan da camera dinshi ce kawai zata daukar mishi, kuma kallon da yakeyi matane yasa ta daga kai, suka hada ido

"Ka tashi? In kirasu?"

Ya girgiza mata kai, yaga sun cire masa ruwan ma

"Zan shiga bayi, inaso inyi wanka, amman bani da kaya"

Ta kara gyara zamanta

"Na dauko maka jiya dana koma gida, harda brush dinka ma duk yana can..."

Ta karasa maganar tana nuna masa wata karamar jaka, baice komai ba ya sauko daga kan gadon zuwa inda jakar take, ya bude ya fito da duk wani abu da yake tunanin zai bukata, harda karamin towel data gani ta dauko masa. Sai dai towel din da kuma gajeran wando taga ya dauka sai su brush da kuma yar ziplock din data sako masa soso da sabulunshi a ciki. Kawai ta maida hankalinta kan alalenta da take jira ya huce, Mummy wajen karfe tara saura minti goma ta shigo da basket a hannunta

"Inata kiran wayarki bata shiga tun safe..."

Tace bayan sun gaisa

"Kar dai bai farka ba har yanzun"

Ta gaya mata ya tashi

"Inata sauri wallahi, da yake Kawunki ya dawo da daddare, sai yace ayi alale da kunun gyada da safen, aikin saiya hade mun, na dibo miki nasan kina son alale, shi dai bansan me zaici ba, ga shayi nan na dafo muku sai na soya masa dankali da kwai"

Cikin kudin da Alhaji Sa'id ya batane ma ta aika aka siyo mata dankalin, dakyar aka samu saboda safiya ce, dan aiken nata yace duk ba'a fito ba. Har kwan ma ciki ta siya, madara da milo suna dashi saita samu fararen ledoji ta diba ta qullo a ciki, tana fatan karsu Maryaman su raina

"Sannu da aiki Mummy, ni kam zanci alalen nan, kunun gyadar fa?"

Ta tambaya

"Na dibo miki, sikarin na nan a leda, dan kar in zuba a ciki ya tsinke...in dai bakwa bukatar wani abu inaso in koma dan in karasa aikace-aikace in dora abincin rana, me kike so? Shi me kike tunanin zaici"

Maryama tayi

"Ai wallahi Mummy karki wahalar da kanki, duk abinda kika dafa kawai ki zubomun iya cikina, ba abinci yake ci ba ko sanda yake da lafiya"

Itama dariyar tayi

"Sai mutum ya zauna haka kaman ganga"

Duk yanda zatayi ma Mummy bayani tasan ba zata gane ba, sai bayan ta rakata, ta dawo, tayi wanka ta sauya kaya, maine ma batayi tunanin ta dauko ba, gashi tanajin kamar jikinta ya bushe, tukunna ta zauna ta zuba alalenta da take ta faman tururi, irin kulolin nan ne nada masu rike zafi, saika rantse lokacin aka sauketa. Ta fara ci sanda taji Haris ya bude kofar bayin, ta daga kai, ta sauke shi da saurin gaske, daga shi sai gajeran wando, sai kuma wannan karamin towel din daya dora shi akan wuya. Taji kamar alalen zata shaketa, dakin ya matse mata sai kace suna cikin keji.

"Me kike ci?"

Haris ya tambayeta, cikinshi yakejin kamar an kwashe komai, harda hanjin, a zatonta ya saka kayane shisa yayi mata magana, amman da ta daga kai lokacin ma yake jan zip din dogon wandonshi hankali a kwance, bai saka riga ba

"Wai kai dan Allaah sai ka kama saka kaya a gabana, maimakon ka shiga dasu bandaki ka saka kafin ka fito?"

Tayi maganar muryarta na rawa, cikin rashin fahimta yake kallonta

"Me yasa zan shiga da kaya bayi? In ajiyesu ina?"

Idanuwanta kamar zasu fado saboda hararar data maka masa, sau nawa ake musu wa'azin kallon tsiraici da irin abubuwan da hakan suke janyowa

"Inda na ajiye nawa dana shiga mana, kawai saika fito sanqare-sanqare dakai a gabana, kuma daga shigarka har kayi wanka ka fito? Ka gurje kafarka ta fita sosai? Da kuma hamm...."

Sai ta cije lebenta, lokacin da ta fara wanka da kanta, fadan Hajja kenan intayi jiqa-jiqa

"Wannan kafar bata fita ba, ki koma ki dirjeta tas, ki kuma wanke hammata, ki daga hannun sama ki wanke, in ba haka ba zakiyi warin dauda..."

Abinda taso tace masa kenan, sai taga kamar bai kamata ba, kamar kalmar tayi nauyi ta gifta a tsakaninsu

"Bangane na gurje kafata ba..."

Cewar Haris da madaukakin mamaki, ya tabbatar Maryama ba zata wuce shekara goma sha shidda ba, hakan na nufin ya bata shekara goma sha, lokacin daya fara wanka da kanshi da wahala in ta gama hakora, amman wai ta kalle shi tana tambayar shi koya dirje kafa

"Kafa dame kuma?"

Ya kara tambaya ganin ta sauke kanta kasa, shiru tayi, ya kuwa taka har inda take, sai ganin kafafuwanshi tayi a gabanta

"Ki amsani inaji"

Ta kasa dago kanta, zuciyarta sai bugawa takeyi, saiya tsugunna, kuma taga bai saka riga ba har lokacin

"Kinsan Allaah saikin karasa maganar nan"

Cikin rawar murya tace

"To kasa riga dan Allaah..."

Ya maqale kafadarshi

"Saikin gayamun"

So take ya tashi, dan tayi yunkurin matsawa baya, amman jikinta yayi mata wani irin nauyi

"Hammata...kafa da hammata"

Tayi maganar, sai ya mike, ya kuma kamo hannunta ya mikar da ita, da tayi kokarin togewa saiya saka mata karfi yana dagota, bata da nauyi kamar yanda yayi zato

"Ai zuwa zamuyi ki dirjemun kafar da hammatar, kinga sai inga yanda ya kamata in dingayi"

Cikin wani irin yanayi tace

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."

Tashin hankali na rikito mata, idanuwanta kamar zasu fado waje

"Wasa nake maka fa, dan girman Allaah kayi hakuri"

Dariya ta kusan kwace masa ganin yanda ta firgice gabaki daya, sai firgicin ya haska masa wani abu a kanshi, yaji ilahirin jikinshi ya amsa, sai kawai yayi mata daukar da akeyiwa yara, irin ta gefen nan, salati Maryama takeyi tana karawa da karfinta, kar dai da gaske bayi zai jata, ita kuwa ta ina zata fara wankewa gardi kafa da hammata, gardin ma bakin gardi

"Na rantse da Allaah ka saukeni, kasan zan fadaka da Hajja"

Dariya yayi mai sauti

"Kice mata me? Kince ban iya wanka ba, nace muje kiyi mun ingani? Ai gode miki zatayi...kinsan irin son da Hajja takeyi mun?"

Ya sake gyara mata zama a kugunshi, dan jikinta gabaki daya ya mutu, ko kacaniyar kwacewa ta kasayi, idanuwanta ma cike suke da hawaye

"Dan Allaah kayi hakuri, dan Allaah fa nace maka Ganja"

Sunan ya kwace mata batare data shirya ba, dariyar da Haris yayi mai sauti ce

"Ai wankan ma zakiyi mun gabaki daya kawai..."

A dai-dai wannan lokacin ne aka kwankwasa kofar, kafin shi da yake tsaye yayi wani yunkuri Hajiya Rumana ta turo kofar, ta kuma shigo, ta kalle su, ta sake kallonsu, sai tayi tunanin kilan ta kifta idanuwanta shisa sukayi mata ganin abinda ko a mugun tunani bai kamata ace ta gani ba, saita kare ware idanuwanta, Haris ne dai, tsaye, babu riga a jikinshi, rike da yarinyar da a halin yanzun ta tsana fiye da komai, tana can tunanin ciwonshi ya hana mata wataccen bacci, ashe shi yana nan yana rungumeni in rungumeki da kaddararshi

"Sauketa dan ubanka"

Kalaman suka kwace mata batare da tama sani ba, to akan me zai dauketa ma? Akan wanne dalili? Anya wannan auren ba zai dasa mata ciwon ajali a irin tsanar da tayi masa ba, kuma batasan menene abinda ta fada na nishadi da yasa Haris din dariya ba, ya daiji ta, ya sauke Maryaman da ba tayi tunanin akwai ranar da zataji dadin ganin Hajiya Rumana ba, sai yau, tanajin ya direta kan kafafuwanta da suke rawa tayi saurin takawa ta koma kan kafet din da take zaune tana mayar da numfashi, takai hannu ta share kwallar data taru cikin idanuwanta

"Mami"

Cewar Haris da murmushi kwance akan fuskarshi, ta harareshi, saiya sakeyin dariya, ya taka zuwa inda take yana hugging dinta, ta ture shi hadi da kai masa rankwashin daya kaucewa da sauri

"Ina can ina tunanin ciwonka, ashe kai ka warke ma kana abinda bai kamata ba, saboda rashin hankali ko?"

Baiyi magana ba, ya dai taka zuwa kan gadon dakin, ya dauki rigarshi da take ta kamshin wani turare da yaji duk dadinshi yayi masa karfi, ya saka a jikinshi

"Sannu da hanya"

Ya fadi bayan ya saka rigar, ta karasa shiga cikin dakin, sai kuma da ta ajiye katon kwandon hannunta tukunna ya kula dashi

"Ina kwana"

Maryama tayi maganar cikin karamar murya

"Lafiya"

Kawai Hajiya Rumana ta fada tana jan kujera ta zauna

"Kaci abinci?"

Ya girgiza mata kai yana cewa

"Yanzun Maryamm zata hadamun shayi"

Saita kalli Maryama da idonta yake kan alalen da yanzun ta fita daga ranta duk zumudin cin da takeyi, tana ta kissima yanda zata rama abinda Haris yayi mata ne kawai

"Tunda bakaci ba, ga abinci nan na taho maka dashi"

Ya zauna gefen gadon, yasan Hajiya Rumana da nama, yanzun haka duk tarin kulolin nan data jibgo idan aka budesu nama ne da aka sarrafa shi kala-kala, da wahala idan akwai wani abinci, shisa ya girgiza mata kai

"Ba zanci nama bafa Mami, bari ta hadamun shayin"

Wani abu yazo wuyan Hajiya Rumana yayi tsaye, Maryama na jinsu, kuma data dago sai yanayin dake fuskar Hajiya Rumanan yayi mata dadi, shine ma abinda yasa ta fito da kofi da kayan shayin data gani a ledoji

"Meye wannan a ledoji?"

Hajiya Rumana ta tambaya

"Madara ce da Milo"

Madara da Milo a leda? Saboda tsiya kome?

"Baku da kayan shayine za'a qullo madara a leda? Wacce irin tsiya ce wannan? Haka kukeyi a gidanku daman?"

Maganar tayi ma Maryama zafi, amman sai tayi murmushi tace

"A'a Mami, muna da kayan shayi fa, kinsan suna gida tunda an taho asibitin a hargitse, wannan ma taimakawa akayi aka sammana shisa kika gansu a leda"

Ran Hajiya Rumana ya kara baci

"Sammuku akayi? Rokowa kikayi kenan kome?"

Murmushin ta sake fadadawa, kafin ta amsa Haris ya rigata

"Mami mana"

Ta juya ta harareshi

"Kai yanzun abinda aka roko din zaka sha? Sai kace wani almajiri? Idan ita tasha ba wani abu bane ba tunda ubanta yayi yawon bara, amman kai akan wanne dalili"

Haka kawai daya janye idanuwanshi daga kan Hajiya Rumana saiya kalli Maryama, maganganun ne sukayi masa wani iri, shisa yake so yaga ita da aka fadawa me sukayi mata

"Mami please"

Ya sake fadi, sai taja wani irin tsaki, ita duk fadan da tayi tashen yi da mutane a makaranta, koya zaka zageta bata taba ramawa, gara ta kamaka ta jibga, saboda ance wanda ya zagi wani kamar ya zagi kanshi ne, to idan kuma iyaye ne, ta ina bakinta zai fara budewa ta zagi su Abba? In wani ya zagesu ma ba zai wanye lafiya a wajenta ba, amman gashi yau, haka kawai, babu wani dalili Hajiya Rumana ta zauna tana zagar matashi, tana kiranshi da almajiri, ai ya fada musu tabbas, an kawoshi almajiranta, amman yanda tayi maganar da izgili, a kunnuwan Maryama dai-dai yake da zagi, kuma tarbiyar Hajja ce ba zata taba watsarwa ba duk runtsi da ta gaya mata abinda zai hanata bacci, sannan ga Haris da takejin idanuwanshi na yawo a kanta, shisa ma ta cigaba da hada shayin, saida ta kurba taji yayi yanda ta saba hada masa tukunna, sai ta bude yar karamar kular nan, ta samu plate ta juye masa dankalin da wainar kwan da tasha yankakkun kayan miya sai kamshi ke tashi, ta saka cokali a ciki tace masa

"Ga shayin"

Dan bata yarda da kanta ba, karta mike kai masa ta watsawa Hajiya Rumana shi

"Nan zaizo ya karba saboda baki

23 / 51