Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
da takeyi
"Ai wannan zumuncin na musamman ne, halan baka san yaran naka sun shirya kansu ba"
Shima murmushin yayi mai sautin da yake tattare da ma'anoni da dama
"Nifa har mamakin yanda Hausa ta zauna miki nakeyi, kinga yanzun magana kikayi mun, naji ki amman bangane abinda kike nufi ba"
Yayi mata maganar da yaren Kanuri, itama kuma saita juya harshe
"Aise da Haris nake nufi, dazun nan yake cemun zaka zo Maiduguri a karshen watan nan da muke ciki, nace ba zai wuce bikinsu Khalisa ba..."
Shiru yayi kamar mai jiran karin bayani, itama bata tsaya ba ta cigaba
"Shine yake cemun suma yanaso ayi maganarsu"
Da mamaki a muryarshi yace
"Ikon Allaah, magana kuma? Wacce irin magana? Kinsan har yanzun na kasa fahimtarki fa"
Ta kara tabbatar da baisan komai ba
"Ai sun jima da shirya kansu...maganar aurensu, dan shiririta irinta Haris wai manya yake so su shiga asan da zancen, ni kuwa nace zamu zuba musu ido ne, ai azo a tsayar da magana asa rana kawai"
Ko a yanda ta karashe maganar zaka tsinci tsantsar doki da farin ciki a muryarta, farin cikin da maganganun Alhaji Modu suka barbadar mata dashi
"Anya kuwa Rumana? Gaskiya ni bansan da zancen ba, duka Aise din nawa take da zata yanke irin wannan hukuncin? Kuma ma akwai yaron abokina da yake sonta tun bata kai haka ba, yana England yanzun haka, nine na dakatar dasu nace ya nutsu yayi karatunshi, itama ya barta ta nutsu, shiririta ce kawai irin ta Aise nasan shisa ni bata ma tunkareni da maganar ba"
Ta cire wayar daga kunnenta kamar mai neman tantance wata kira, ta mayar, ta gyara zamanta
"Dan abokinka Modu? Har dan abokinka zaifi Haris ne ko da ma rana aka saka masa da Aise balle magana ce kawai, ya za'ayi na gida yana so ace za'a dauka aba wani bare can"
Jin yanda ta harzuka lokaci daya yace
"Ke kam kin cika rigima, dan Allaah mu bar wannan maganar, kuruciya ce irin tasu daga shi har Aise din, amman ni ban shirya bada aurenta nan kurkusa ba, kuma ko da zan bayar din tunda akwai maganar wancen yaron babu yanda za'ayi in karbi ta Haris, ai sai in zubarwa da kaina mutunci, a daukeni karamin mutum"
Tabbas wannan aikin Binta ne, ita tayi nasarar rabata da dan uwanta harma ya samu damar gaya mata irin wannan maganar, ta numfasa kuma yayi saurin katseta da
"Zan kiraki, ana mun magana"
Ya kashe kiran daga nashi bangaren, idan ran Hajiya Rumana yayi dubu to kowannensu a bace yake
"Lallai Modu"
Ta furta a fili, haka ta wuni da wannan bacin ran har tanaji a ranta ai ko 'yar gwal ce shima Haris din ya hakura, sai dai sanda sukayi waya take nuna masa ya hakura da Aise tunda iyayenta basa so, ta wayar tana jin yanda ya birkice mata gabaki daya kamar zai biyo ta ciki ya dira a gabanta, dakyar ta shawo kanshi da alkawarin ba zata bari Aise ta kubce masa ba, ya bar komai a hannunta. Ta tsorata da kalamanshi matuka
"Na tambayeki abubuwa da yawa Mami, tun tasowata, kusan kullum ma cikin tambayarki nake, wannan karin roko nakeyi, dan Allaah ki taimaka mun, karki bari Aise ta subuce mun, wallahi idan na rasata zaki iya rasani"
Sai gata bayan sallar isha'i a ranar, tayi nafilar da rabonta da ita tun watan azumin daya wuce, wacce irin bakar magana Haris ya fada mata, zata rasa shifa? To ita kuwa ta zauna tayi me a filin duniyar da za'ace ta wayi gari babu shi a cikinta. In dai Aise ce zata lallaba Modu har sai taci galaba akanshi, watakila ya manta naci irin nata ne akan abinda take so, wannan nacin da Alhaji Mustafa zai shafe kwanaki yana bada labarinshi. Aikuwa babinshi ta budewa masa, kiran safe daban, na yamma daban da magana daya
"Wai ya za'ayi ka zabi wani a kaini Modu? Ko dan kaga iyayenmu basa nan ne? Shisa kake son fifita bare akan jininka? Ko dai Binta ce ta hana? Ashe mace zata shiga tsakanina da dan uwana"
Abinda ta mantane kawai bata gwada ba, kiran karshe da tayi masa ana gobe zai baro Italy ne, kuma ranar ne ya fito mata a mutum
"Dan Allaah kibari Rumana, banaso, Haris bai cika sharuddan da shari'a ma tace a bashi auren yarinya kimtsatsiya irin Aise ba..."
Aikuwa sai ta birkice masa, dan maganar tayi mata ciwon da batayi zato ba
"Yaran nawa kake neman jifa da muguwar kalma saboda yana son 'yarka? Abin naku har yakai da sharri?"
Tanajin numfashin daya sauke a gajiye ta cikin wayar
"Nifa ba sharri nayi masa ba, Allaah Ya shirya mana su, amman aiko ke ina ce dalilin da yasa kika nemi ya bar kasar nan saboda abinda yayi ne, abinda kika kira da karya akayi masa saboda ya shirya miki zance kin dauka, to gaskiya anan dinma bai daina ba, idan baki sani ba na fada miki, ni ba zan dauki 'yata in bashi alhalin nasan abinda yake aikatawa ba"
Ta share hawayen da suka zubo mata, zuciyarta nayi mata zafi, bawai dan ta yarda cewar Haris bai daina abinda yakeyi ba, a'a sai dan yanda Modu baiji kunyarta ba yake jifar mata yaro da abinda tayi kuskuren furtawa, Haris din da ko da ace a wancen lokacin da gaske ne yana shan wani abu, yanzun kallo daya zakayi masa ka tabbatar da natsuwa da kamalarshi, kullum Alhaji Mustafa cikin alfahari da hankalin da Haris yayi yake, fada sukayi sosai ita da Alhaji Modu, dan tun yana kwantar da murya harya biye mata, suka farfadawa juna maganganu marassa dadi, ya kashe wayarshi bayan yaja mata wani dogon tsaki. Haka ta dinga share hawaye cikin takaici, tasan shi kanshi makircin Binta ya hadu dashi bakomai ba, saboda tsabar yanda bata son Haris da Aise, shine ta nemi sharri ta kakaba masa.
Kuskurenta na farko kin sake yiwa Haris alkawarin sama masa Aise
Kuskure na biyu da tayi shine samun Alhaji Mustafa ta fada masa maganar
"Ikon Allaah, wai Haris din da kanshi? Yanzun fa muka gama waya amman yaron nan baiyi mun zancen ba"
Tayi dariya ganin yanda yaketa farin ciki, lallai addu'arshi taci, Allaah Ya amsa rokon daya jima yanayi akan Haris, wai yau Haris ne da kanshi yakeso aje a nema masa aure, shikuwa ina zai tsoma ranshi don farin ciki? Alhaji Jibril da kanshi ya tura masa da katin gayyatar auren yara shida da zasuyi a family din nasu, kuma ganin wannan aringizon aure yasa yake ta kokarin rage duk wani aikin gaggawa da zai iya taso masa, yayi niyyar halartar bikin daman, ko da kwana dayane, dan harya gayyaci amininshi Alhaji Sa'id, to amman yanzun dole ma tafiyar ta sake shiri, tunda bayan daurin auren ai zasuyi tambayar aure ne, kuma dai ba sun tafi su biyu ba.
"Kikace shi Modun zaizo wajen ko?"
Ta jinjina masa kai
"Duk da kasan Yayaa Jibril ne yake daurawa duk yaran aure, amman tunda shima yana wajen kaga abin zaifi tafiya dai-dai"
Ya sake jinjina kai, duk farin ciki ya lullubeshi
"Ki bani lambarshi to..."
Zuciyarta ta buga, tasan ko lokacin aurenta da Alhaji Mustafa, Modu yafi kowa murna, tare ya gansu a wancen lokacin, a wajenshi kuma ya fara neman izinin magana da ita, akwai wani girma na musamman da Alhaji Modu yake bawa Alhaji Mustafa, surukantaka yakeyi dashi ta gaske. Yace ba'a taba mutuntashi yanda yayi ba a wancen lokacin, kuma ya jima baiga mutum mai nagartarshi ba. Idan ita baya ganinta da gashi, ai zata ga yanda zai kalli idanuwan Alhaji Mustafa yace masa ba zai ba Haris auren Aise ba idan ya tambaya, musamman da ta tabbata ba su kadai bane a wajen, akwai mutane da yawa da idanuwansu zai hanashi wulakanta mata miji ta hanyar hanawa.
"Ka tabbatar ita yarinyar tana sonka?"
Shine abinda ta tambayi Haris
"Ita tace mun in aika a tambayarmun aurenta Mami, ina sonta sosai, ina sonta fiye da yanda kalamai zasu misalta, amman da bata sona zan hakura, kinsan zan hakura, jininki ne fa yake yawo a jikina"
Ya karashe maganar cike da alfaharin da itama ya rufar mata, to tunda suna son juna ai angama magana.
"Kasan ya kamo hanya, to lambarshi ta can bata shiga, mun riga munyi magana, yasan da zancen"
Sai ya jinjina kai
"To bari zan kira Muttaka da kuma Alhaji Kabir sai mu hadu mu hudu da Sa'idu muje"
Muttaka din Kaninshi ne uwa daya uba daya, Alhaji Kabir kuma yana daga cikin abokanshi da yake ji dasu bayan Alhaji Sa'id
"Allaah Ya tabbatar mana da alkhairi"
Ta furta tana fatan addu'arta ta amsu, ita taso a sauya wata maganar ne, amman shi Alhaji Mustafa din babu abinda yakeyi sai maganar bikin da yanda zai kasance idan an tashi, wannan karin shine ya koma ita, saika rantse bai taba aurar da wani ba, akan Haris din zai fara
"Kayan daki fa? Kamar nawa kike ganin za'a kashe"
Itace maganar da yayi, da tasa ta dinga tuntsira masa dariya har tana mantawa da fargabar kar a samu matsala, shima kuma da ya gane baranbaramar da yayi sai kawai ya tayata dariyar. Haka suka kwanta cike da nishadin da suka jima ba suyi irin shi ba, da yake ranar ta kama juma'a ne, kuma a lokacin sauran kwanaki takwas bikin da za'ayi a Maidugurin. Haka ya wayi gari da wannan farin cikin daya dinga kiran danginshi yana rabawa dasu
"Danku fa ya jawo muku rikici, saiku fara shiri dan zamuje masa tambayar aure"
Kuma kowa ma tayashi farin cikin ya dingayi, musamman ma Alhaji Sa'id da yasan yanda aminin nashi ya damu da yaga rayuwar dan nashi ta dawo kamar yanda kowanne mahaifi yake fata. Tunda a wancen lokacin shiya fara kira, kuma bayan Hajiya Rumana da aka fada musu abinda Haris yayi, babu wanda ya gayawa sai Alhaji Sa'id
"To ni me nayi? Ina na kuskure?"
Shine ma ya kwabe shi
"Karkayi sabo Mustafa, ai ita jarabawa fuskokin da take dauke dasu masu yawa ne, akan yara kuma dukkanmu in zamu zauna muyi magana a tsorace muke, kuma tsoronmu bashi bane abinda zai hana yaran nan ture duk wani kokari da muke wajen ganin rayuwarsu ta inganta, abinda muke iya gani shine wanda muke tsawatarwa, sauran kuma idan babu idanuwanmu sune muke tsananta addu'a akai, muke rokon Allaah Ya dafa mana, Ya kare mana su...ai abin yazo da sauki tunda har aka sani, yanzun ba sai a dauki matakin daya dace ba? Kaddara ce shima ta fada masa, tunda har yayi kokarin boyewa kaga akwai kyakkyawan zaton yasan abinda yakeyi ba mai kyau bane, kuma yana tsoro da gudun bacin ranku..."
Amman kafin ma yayi wani yunkurin aiwatar da shawarwarin Alhaji Sa'idu, Hajiya Rumana ta dauke masa Haris din, shisa yanzun ya kasa hakura saida ya cewa Alhaji Sa'id
"Kaga danka ko? Allaah Ya amsa addu'ar mu"
Shima murmushin yake tayi, Alhaji Mustafa da iyayenshi sunyi masa halaccin da bayason yaga wani abu na rashin dai-daito ya rabi duk ahalinsu, komin kankantarshi, kuma tun kafin ma yasan wannan maganar ta an kama Haris na shaye-shaye a makaranta, Allaah ne shaidarshi, a duk sallar da zaiyi, yanda zai kira sunayen yaranshi da wanda suke karkashin kulawarshi daya bayan daya yanayi musu addu'a haka yake kiran sunayen yaran Alhaji Mustafan, da yasan matsalar Haris kuma tare suka raba ciwon da damuwar da amininshi, dan daya samu damar sadaka, addu'ar da zaiyi bayan yayi sadakar saiya hada da Haris
"Allaah ga dan aminina Haris, Allaah Ka shiryeshi, Allaah Ka shiga al'amarinshi, Allaah Karka jarabci iyayenshi ta sanadinshi"
Duka sau nawa ya taba saka Haris dinma a ido? Ba dan yanda Alhaji Mustafa yake da muhimmanci a wajenshi ba, ai zai iya cewa ma fuskar Haris ta bace masa
"Nama yankar mana tikitin zuwa dana dawowa, saika shirya"
Haka Alhaji Mustafan ya fada masa, shima kuma tun a ranar ya gayawa matarshi zancen tafiyar, take tayi musu fatan alkhairi, da alama ta ga farin cikin da yake ciki shisa take tayashi
"Kaga sai mamaki nakeyi, gaskiya tsufa ya kamamu, inata kauda kai daga kirga maka furfura..."
Yayi dariya
"Ai kanki ma yafi nawa in dai furfura ce, in kuma da ita za'a auna shekaru matso kusa a kirga aga ni dake waye tsufan zaifi dannewa"
Dariyar tayi itama
"Nifa ba haka nake nufi ba, meye na tone-tone? Kawai dai gani nake Haris din nawa yake? Kamar fa jiya ne mukaje sunanshi..."
Alhaji Sa'id ya numfasa kamar mai nazari
"Yaran ne muna ganinsu a gabansu, shekarun kuma nata ja, amman mun kasa ganin girmansu, kullum fata muke mu kara samun aron lokaci, su dan kara zama a matsayin yaran nan namu, amman Haris fa yanzun in dai lissafina zai tafi dai-dai ya kusan shekaru ashirin da bakwai"
Ta girgiza masa kai
"Anya kuwa? Da bakwai? Ni sai nake ganin kamar baifi da biyar ba, shisa ma ashe nake ta juya lamarin, kuruciyarshi nake gani, to duka Haris din nawa yake? In bama dai makaranta da ake sakasu da wuri ba, dama shi din daya bar kasar, tunda karatunsu na can da namu ba daya bane ba, babu ruwansu da wannan yajin aikin na fama..."
Alhaji Sa'id ya kalleta
"Shekara ashirin da biyar dinne auren wuri? Muna da nawa akayi mana mu?"
Ya kuwa bata dariya
"Ai zamanin ba daya ba"
Ta fadi
"Kice ke kike zugamun yaran nan, shisa suke kara mike kafa kowa ya tara kasumba, suna ganin har yanzun yara ne su ko? To kuwa zan tarasu inyi musu zancen aure tunda sun fara gane dadin samun na kansu...ai nima da auren na karasa karatuna"
Ta dingayi masa dariya kamar bashi bane ya gama maganar samun karin lokaci tare dasu. Yanda suke wannan lissafin, haka Alhaji Mustafa yayi, duk juyin da zaiyi, sai kawai ya girgiza kai, ko babu komai suna ganin tagomashin auren wurin, ga yaransu nan duk sun tasa, harma wani zai iya jinjinawa in sukace nasu ne. A ranar da zasu tafi Kano, daga nan Kaduna, dan ta can zasu bi jirgi zuwa Maidugurin, yana shirinshi Haris ya kirashi a waya
"Shiryawa nakeyi Haris"
Sai Haris din yayi dariyar da Alhaji Mustafa yaji kunya a ciki
"Abu fa zan gaya maka Baba"
Ya kuwa ce
"Ba wani nan, so kake kaji na shirya, ko mun kama hanya. Yanzun nan zan karasa sai mu biya mu dauki Kawunka dasu Alhaji Kabiru, yau zamu nema maka auren Aise Haris"
Babu abinda kunnuwan Haris suka tace suka adana masa sai
"...Yau zamu nema maka auren Aise"
Zasu isa Maiduguri lafiya,
Abinda Alhaji Mustafa bai taba hangowa ba shine alfaharin shi zai sashi nemawa Haris aure har sau biyu a rana daya,
Za'a hana shi daya,
Za'a bashi daya...
10
Karfe goma na safe akayi daura duka auren, kuma daga can kai tsaye gidan Alhaji Jibril aka kwaso su, dan anan za'ayi 'yar karamar Walima, duk girman falon nashi, inda duk ka kalla mutane ne anata hada-hada, da hira irin tasu ta manya, kowa ya cire babbar riga an ajiye saboda abinci da ake taci, duk hirar nan da ake ana dariya banda Alhaji Sa'id da yake zaune cikin kujerarshi, abincin ma kadan yaci, saboda akwai tuwon shinkafa da miyar ganye da yasha naman kaji, kuma yana daga cikin abincin da yake so, haka kawai bayajin yunwa, shi tafiyar ma tun jiya jikinshi yake a sanyaye da ita, haka suka iso suka sauka hotel din da suka kwana.
To yau daya tashi ma komai nashi a sanyaye yake, da Alhaji Mustafa yayi masa magana sai yace
"Kilan zaman jirgine, kasan abinka da wanda bai saba ba"
Sosai yaba Alhaji Mustafan dariya
"Ka kyauta Sa'idu, ni zaka gayawa bakar magana"
Shima sai yayi dariya, dan ya bar maganar ne daman ya sako raha a ciki, shima baisan abinda yake damunshi ba. Jin hayaniyar da ake tayi ta ragu yasa shi maida hankali kan abinda yake faruwa a cikin falon, sai yaji neman aure ne, akwai yarinyar da Alhaji Jibril yake rikewa, yar 'dan uwansu ce daya rasu, to shine wakilan yaron da yake sonta da yake suma sanannu ne anan garin Maidugurin suke neman auren
"Ma Shaa Allaah, ai da kunzo da wuri ma da an hada gabaki daya..."
Cewar wani cikin Kawunan yarinyar
"A shirye muke, a yanka mana sadaki kawai a daura, in yaso sai a hada sauran walimar ta mata da zasuyi ayi tare, da sauran al'adu In Shaa Allaah..."
Cewar daya cikin wakilan yaron, nan da nan aka yanka musu sadakin da suka fito dashi aka kirga aka bayar, sai ga wani auren an daura, anata addu'a da fatan alkhairi, Alhaji Mustafa ne zaune a kusa da Alhaji Modu, da yake cikin farin ciki yake, sai abin ya kayatar dashi, ya kuwa juya ya cewa Alhaji Modu
"To ai muma a shiryen mukazo, wajenka za'a nemi auren Aise ko gurin Alhaji Babban Yayaa zamu mika kokon barar mu"
Kallo kuwa ya koma kansu, Alhaji Modu da sanyin dakin bai hanashi hada zufa lokaci daya ba, ya gyara zamanshi, wani irin bacin rai yana dirar masa lokaci daya, babu wanda yayi masa wannan abin sai Hajiya Rumana, ko rantsuwa yayi ba zaiyi kaffara ba, itace ta hada abin nan, saboda tasan akwai kunya a tsakaninsu da Alhaji Mustafa, ga mutane nata kallonshi
"Auren Aise?"
Alhaji Jibril ya katse shirun, sai kuwa Alhaji Mustafa ya daga masa kai
"Yaronka muke nemawa Auren, Haris"
Ganin yanda Alhaji Jibril ya fadada murmushin da yakeyi yasa Alhaji Modu saurin fadin
"Na dauka ma ai kunyi magana da Rumana..."
Dan ya shirya bata mamaki, kamar batasan girman son da yake yiwa yaranshi, idan duk idanuwan duniya ne zasu tarar masa, ba zai taba mikata inda zata cutu yana cikin hayyacinshi ba, kunya da nauyin Alhaji Mustafa bakomai bane, wasu abubuwa ne da a yau ya turesu gefe daya kamar basu taba wanzuwa ba
"Na fada mata akwai yaron da yake neman Aise din, kaga ba'a nema cikin nema"
Lokacin dasu Alhaji Mustafa suke yara, idan akaji shiru irin wannan sai manya suce
"Mutuwa ta gifta"
To kwatankwacin wannan shirun ne ya ziyarci falon, a tare dashi wata irin iska mai sanyin gaske data lullube Alhaji Mustafa, lokaci daya kwakwalwarshi take son fahimtar abinda yake faruwa, kamar in yaji dai-dai auren Aise dinne Alhaji Modu ba zai basu ba
"Subhanallah...to ya akayi haka?"
Maganar Alhaji Jibril ta kutsa cikin rudanin da Alhaji Mustafa yake ciki
"Wallahi ban sani ba, dan ni ba muyi magana dashi ba, ita dai Rumana tayi mun zancen na gaya mata akwai yaron da yake nemanta, karatun shi yake karasawa itama tana karasa nata, ba zai yiwu ayi karanta ace za'a shigo da zancen Haris ba"
Kenan Hajiya Rumana ce ta wulakanta shi haka?