Advertisements
Chapter 12 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   12 / 51

33K to 36K   out of 151K words

jin yanda jikinshi ya karayin sanyi da yanayin Haris din. Bai ga girman abinda ya aikata ba sai da aka kwana aka yini, fushin abinda Alhaji Modu yayi masa dana Rumana ya rissina, shisa ma ya yanke shawarar zuwa yayi magana da Haris din baki da baki, bawai ta waya ba dan yasan muhimmancin maganar, dan karya bashi kunya a idon mutumin da yake gani da daraja matuka. Da yace zaizo kuma sai zaman jiran nashi ya kara saukar masa da zullumi, ga shirun Hajiya Rumana a gefe, wani abu da bai saba ba, wani abu da ba halinta bane, ya tabbata akwai abinda take shiryawa, da kanshi yaje ya dauko Haris daga Airport bayan sun sauka, kuma baiga alamar tayi wata magana da Haris ba, itama ta kawo musu abinci anan bangarenshi bayan Haris din ya huta, tana ajiyewa tayi tafiyarta, inda lafiya zata zauna ne

"Haris"

Ya sake kira, kuma a duk maganganun da yaji saiya zabi ya mayar da amsa da tambaya

"Waye yace akwai macen da zata maye mun gurbin Aise Baba?"

Ya karasa maganar idanuwanshi fes a cikin na Alhaji Mustafa

"Ai addu'a nayi, nake fatan ta maye maka din, kasan ba zanyi maka zabin abinda zai cutar da kai ba"

Shifa so yake ya fahimci Alhaji Mustafa da maganganun shi yau, kamar yanda yake so shima ya fahimce shi, shekararshi hudu da dan wani abu a kasar Italy balle yace Hausa ta fara bace masa duk da yana dadewa baiyi ba in ba waya yakeyi da 'yan gida ba

"Ni kuma nawa zabin ya zanyi dashi?"

Ya sake tambaya yana kallon hannunshi wannan karin, yatsanshi karami, na haggun, daga ciki, ta gefe, tattoo ne da aka rubuta Aise, tare sukaje akayi musu, itama akwai nashi sunan a jiki, ita ta zabar musu inda zasuyi saboda tana tsoron fadan Binta, ta jima tana son yin tattoo ko da karami ne duk da a lokacin wasu taurari ne taso a zana mata a bayan wuyanta, amman Bintar tayi mata barazana da cewa in ma tayi, a ranar zata sakata a gaba har inda ake cire shi, kuma taji wanda akayiwa tattoo removal na fadin yafi ayi maka azaba, ninkin ba ninkin, saita hakura, har saida ta samu wannan dabarar, ranar haka ta dinga kama hannunshi tana gani kamar bata taba cin karo da wani abu da take so kamar yatsan nashi ba.

Shima in ya kalla yana mamakin kanshi, amman zai kara rubutawa a duk inda ta zaba in dai zai sake ganin wannan kyallin farin cikin a idanuwanta

"In Shaa Allaah ka samu mafi alkhairi...saboda..."

Kallon Alhaji Mustafa yakeyi, amman kalamanshi sunki karasawa cikin kunnuwanshi sam, kamar an dauke masa jinshi na wucin gadi saboda hutun rabin lokacin da kwakwalwarshi ta tabbar zuciyarshi na bukata shisa ta taimaka masa ta rufe kanta

Ya zaiyi da Aise
Ya zai tsaya a gaban Aise da auren wata

"Kasan me yasa nake karajin dadi da muka zo a musulmai?"

Ta taba tambayarshi, ya girgiza mata kai

"Saboda zan aureka, saboda aurenka zai bani abinda wasu mata ba zasu taba samu a tare da kai ba, saboda na fara addu'a tunda na fara sonka, kar Allaah Yasa ka kara auren wata bayan ni, ina maka son da zan iya hakuri har ka cire wasu mata daga rayuwarka, amman inajin zan mutu in ka ba wata mace kanka ta hanyar hada matsayinmu, ka soni, ka aureni, itama kaso ta ka aureta, mutuwa kawai zanyi"

Dariya yayi mata, shi ina zai iya aure sau biyu? Me zai kaishi? Abin bai taba burgeshi ba, har kallon Alhaji Mustafa yakeyi a wasu ranakun yana tunanin abinda yasa shi ya kara aure, duk da Hajiya Rumana ta taba ce musu 'yan uwanshi ne suka sakashi a gaba saboda bata haihuwa ba, amman ai ba yaro bane da za'ace anyi masa dole, a ganin Haris yaso ya kara aurenshi ne shisa kawai

"Zan iya tafiya Baba? Zan iya zuwa inyi tunani?"

Sai kawai Alhaji Mustafa ya daga masa kai, daya mike ya fice daga bangaren Alhaji Mustafa, bai nufi nashi ba, wajen Hajiya Rumana ya tafi kai tsaye, ya sameta tsaye a falonta kamar wadda take jiranshi, sai ya karasa kawai ya rungumeta yanajin wani abu na karyewa a tare dashi, maganganun Alhaji Mustafa na dawo masa, ya kusan minti biyu kafin ya dago ya kalleta

"Me yasa Mami? Me yasa kikayi mun alkawarin da kikasan ba zaki cikamun ba?"

Kafin ta amsa ya kara cewa

"Me yasa zaki bari Baba yayi mun haka? Yaro ne ni Mami? Zuciyata da abinda nake so basu da wani muhimmanci haka? Kawai sai a daura mun aure da wata batare da an tambayeni ba kamar bani da wani 'yanci?"

Ya karasa maganar yanajin zuciyarshi kamar zata kama da wuta, ta sauke numfashi, ya fada masa kenan? Zata iya magana da danta yanzun, hawayen bakin cikin da suke neman zubo mata take ta mayarwa

"Ni bansan zaiyi haka ba Haris, ai kasan babu yanda za'ayi a hadu dani ayi maka abinda bakaso, ko da kanaso ma ba zan taba bari ka auri 'yar Sa'idu ba, shima kwadayin abin duniya ne yasa ya yarda da wannan auren ba wani abu ba"

Haris ya kalleta yana so ya fahimci abinda take fada

"Kwadayi?"

Ta jinjina masa kai

"Ni nasan wallahi kwadayine, yana tunanin abinda zai samu a wajen Babanka, dama abinda 'yarshi zata samu inta aureka, shisa ya amince"

Kai tsaye yace

"Bana sonta, koma meyasa aka auramun ita"

Amman kuma a kasan zuciyarshi yanajin wani abu na kullewa, yanajin kamar tun tashinshi alakarsu da Alhaji Mustafa hoto ce kawai, kamar baya ma ganinshi ne a cikin jerin yaranshi saita kama, sai yayi wani abu da zaiyi masa fada koya zage shi, duka ba'a shekara hudu ba daya fara jin yana da mahaifi kamar kowa ba, kuma wannan auren zai iya rusa musu komai, zai iya rusa masa wani abu da yake tattalawa, wani abu da bai taba tunanin zai samu ba, sai dai wannan bacin ran ina zai kaishi? Abinda yakeji wa zai saukewa?

"Zama zakayi mu tsara yanda zaka rabu da wannan alaqaqai din a tsanake, dan sakinta zakayi Haris, ba zaka zauna da Maryam ba, ba zaka zauna da jinin Sa'idu ba"

Maryam

Ya maimaita cikin kanshi

"Wanne tsautsayi ya sakaki fadowa rayuwata?"

Yayi maganar cikin zuciyarshi

"Kana jina?"

Ta tambaya, yana jinta, kamar yanda yaji Alhaji Mustafa, amman ai ita ta karya masa alkawarin da tayi masa, shikuma ya kakaba masa auren da baiyi shawara dashi ba, su duka sunyi abinda suke so batare dashi sun duba ko sunyi tunanin abinda yake so ba

Me yasa suke tunanin zaiyi abinda suke so yanzun?

"Sakinta zakayi"

Hajiya Rumana ta fadi, wata dariyar takaici mai sauti ta kwace masa

"Saboda me?"

Ya tambaya, cikin rashin fahimta ta kalle shi

"Ba ya daura auren ba Mami? Baba ya daura mun auren da baiyi shawara dani ba, kin karyamun alkawarin da kikayi mun, ke kika cemun kar in damu, ke kika cemun ba zaki bari Aise ta kwace mun ba Mami, to me yasa yanzun zanyi abinda kuke keso?"

Tasan Haris dama duka yaranta basu saba tauna magana kafin su fada mata ba, duk abinda suke so shi suke fada tunda tabarsu, ita ta basu fuska, amman ta saba sakasu itama suyi mata abinda take so, sau babu adadi, kuma haka ta shiryawa zuciyarta zai faru akan wannan auren ma, murkushe shi zatayi kafin yaje ko ina, dan ta rantse ta kara rantsewa ba zata zauna da jinin Sa'idu ba, bama zata bari ta rabar mata yaro ba, amman tana ganin wannan gardamar da taurin kan na Haris na haskawa cikin idanuwanshi

"Ban fada masa ba, zan fara fada miki, na karbi auren nan Mami..."

Yayi maganar wani abu na rabewa a cikin kirjinshi daya tabbata ba zuciyarshi bace ba, tunda ai ita ance dukanta tsokace, abinda ya rabe kuwa yaji kararshi, yaji kamar ya kira masa sunan Aise, juyawa yayi yanaji tana kiranshi bai juyo ba, ya koma bangaren Alhaji Mustafa, yana nan zaune inda ya barshi

"Na karbi auren Baba..."

Ya furta, yana ganin wani numfashi mai nauyi da Alhaji Mustafa ya sauke, daya juya har ya taka kafarshi daya waje ya kirashi

"Haris..."

Sai ya juya kanshi

"Allaah Yayi maka albarka, Allaah Yasa auren nan yazo maka da alkhairai masu yawa"

Ya kamata ko bai amsa addu'a ta biyu ba ya amsa ta farkon, yana bukatar albarkar nan ko ba'a fada masa ba, amman ya zaice amin Mala'iku su dauka yana nufin duka biyun ne? Shisa ya juya kawai ya fice

Ba zai taba bari Aise ta subuce masa ba, kome zai faru, alkawari ne yayiwa kanshi, kamar yanda yayi alkawarin duk wani mai hannu a auren nan sai yayi dana sani

Amman alkawurra nawa kaddara take karyawa?

Akwai wani lilo mai circle lokacin suna yara, a hanyar Islamiyyarsu, duk zagaye uku kwandala lokacin, idan aka tashi haka zata kwasa da gudu ta bacewa sauran 'yan gidansu, lokacin da zasu cimmata har ta hau an zagaya da ita, akwai sanda Adda Zahra ta riketa kuwa, ta dauka zata kwada mata mari, sai tace mata

"Karki kara gudu kije kiji ciwo, ki dinga jiranmu saimu tsayaki ki hau lilon"

Watakila karancin shekaru ne ya hanata fahimtar muguntar da take kwance bayan murmushin Adda Zahran, dan a wannan ranar ne lilon ya fita daga ranta gabaki daya, ko wucewa sukayi ta ganshi sai taji kanta ya juya, dan Nairarta biyu ta Islamiyyar ta mika tunda ba sauri takeyi ba, sai dai tana hawa Adda Zahra ta karawa mai lilon Naira biyar, haka aka dinga wulwulawa da ita akai tun tana nishadi har taji jiri, ta fara ihu, lokacin da aka tsayar da lilon nan ko gani batayi, ta hada gumi da hawaye, ga kai da cikinta na juyawa kamar wadda zatayi amai, haka Khairi ta kamata suka nufi gida tana jerawa Addan Allaah Ya isa a cikin ranta.

Irin wannan yanayin take ji yau kwana biyu, kamar an koma baya da ita an dorata akan lilon nan ne anata juyawa, ta kuma kasayin ko da ihu ne balle wani ya fuskanci halin da take ciki ya kawo mata dauki, tunda a washegari data tashi ta shirya, ta saka uniform sai kawai Hajja tace banda ita za'aje makaranta, sai ta koma kan gado ta kwanta batare da cire kayan makarantar ba, kuma wata murya a cikin kanta ta hana mata samun natsuwa a cikin shirun dakin ta hanyar maimaita mata

"Ke matar aurece yanzun Maryam, ke matar Haris ce"

Haka ta dinga juyi batare da tasan yanda lokaci yake tafiya ba, kuma anan Adda Zahra ta sameta, ta mika mata kofin shayi tana fadin

"Tashi kisha Maryam"

Ta amsa da

"To"

A yinin ranar, duk wani shige da fice da Yayyenta mata dama mazan sukeyi akan idonta ne, abinda duk akace tayi saita amsa da

"To"

Idan ma nasiha sukayi mata da hakan take amsa musu, tana jin Adda Maimunatu taja wani tsaki tana fadin

"Allaah Ya kyauta, dan Allaah jiba yanda yarinyar nan tayi firgai-firgai a kwana daya kawai, ni na kasa daukar maganar ma gabaki daya, haka kawai nakejin inda wani ne can ba zai dameni kamar Haris din ba, ko ace shi din dan Umma Fadime ne, amman kinga wannan isashiyar matar hmmm"

Adda Zahra ta kada kai itama

"Ni kaina shine damuwata, dangin miji in ba tsananin dace kayi ba, basa ratsa matsalar da zasu dinga baka, balle kuma ace ita kanta uwar mijin ce baka dace da ita ba, Maryam tayi kankanta da ayi mata irin wannan, dama Asiya ya basu"

Ita dai bata ko motsa daga kwanciyar da tayi ba, basu bar gidan ba sai dare, washegari kuma suka sake dawowa, sai dai Adda Zahra tasa suka shirya ita da Khairi da bataje makaranta ba itama, dan ance za'a kawo lefe wai, suma din da suka fita a motar Addan, kasuwa ta wuce dasu, haka ta dinga yawo dasu tsakanin shaguna da wani list a hannunta da take ta faman siyayyar kayan kitchen, da zasu koma a gidan gaba suka zauna daga ita har Khairi saboda an cika motar da kaya, ba iya booth ba har baya.

Da yake lokacin da direban da Alhaji Jibril ya aiko ya kirawo Alhaji Mustafa sai ya fada masa inda zai tsaya ya jirashi, kai tsaye yayi masa jagora gidan kanwarshi Safina da take aure anan garin Kadunan, ya dinga mamakin irin kayan da aka aiko dasu, tun daga kan goro da biskit katan katan, harda lemuka da ruwan roba kamar za'a bude shago. Anan gidan direban yaci abinci, yace shi juyawa zaiyi, Alhaji Mustafa ya cikashi da abin arziki kuwa, da yake duk sunsan da zuwa neman auren da kuma yanda al'amari ya juye. Itace take tuna masa da batun lefe, yasan cewa Hajiya Rumana ba zata bashi hadin kai ba, yanda ta nuna tsanar auren karara.

A matakin da yake bayason wani abinda zai zubar masa da kima a wajen ahalin Alhaji Sa'id gabaki daya, bayaso ko dana yini daya yayi dana sanin bama Haris auren Maryam. Shisa ya cire kudi masu nauyin gaske ya tura mata dan ayi siyayyar lefen dasu, kuma daya fadawa Alhaji Sa'id za'azo kawo lefe sai yace masa

"Lefe kuma Mustafa? Wanne irin lefe?"

Dariya yayi

"Lefe dai da akeyi mana"

Kuma sanin zai iya fara musu dashi yasa shi dorawa da

"Ni dai ka fada ma Hajiya Asma'u, ranar litinin din nan zasu zo..."

Kuma daya fada mata sai tace masa

"Allaah Ya nuna mana lafiya"

Lokacin ne kuma ta kira 'yan uwanta da suke nan ta fada musu, shima tayi masa magana ya fadawa nashi 'yan uwan. Batayi mamakin ganin yanda sukayo gangami kamar ance za'ayi yinin biki ba, saboda haka gidan cike yake da mutane ko ina ka wulga idanuwanka, sanda su Maryam suka dawo ma sai taji daman ta cewa Adda Zahra ta sauke su gidanta suyi zamansu acan. Haka suka shige dakinsu, nan ma da wasu 'yan uwansu a ciki, sun baje zaka rantse da Allaah a gidan suke rayuwa, suka saka Maryam a gaba da tsokana har wata tana

"Kinga yanda kike ta kyalli, mu dai muna nan sai kin kira mana angon mun gaisa dashi"

Batace musu komai ba, Khairi ce ta dan dinga biye musu duk da itama bata cikin walwala. Tun daga nan dakin kuma suna jiyo gudar da wata ta rangada tana fadin

"Yarinya tayi goshi"

Dan kuwa lefe ne aka kawo irin wanda in aka bada labarinshi wani ma zai kwashe da dariya yace anyi masa karya, akwatina ne saiti uku, kowanne shakare yake da kaya, ga kuma sauran tarkace kama daga lemuka da biscuit. Ita kanta Hajja saida lefen ya bata tsoro, zuciyarta ta dinga bugawa, musamman bayan sun tafi, an kwaso komai an kawo dakinta, su Adda Zahra nata dagawa, tunda take bata taba ganin lefe irin wannan ba, kuma ko ba'a fada ba daga gani kayane masu tsadar gaske. Yanda take jinjina lamarin haka Khairi da taga lefen ta samu Maryam da take rakube can karshen gado tana ce mata

"Kinga lefen da suka kawo kuwa?"

Ta kalleta kamar bata gane abinda take fada ba

"Yanda kikasan za'a bude babban shago"

Bata dai ce komai ba

"Bari in zubo mana abinci, baki ci komai bafa tunda muka dawo"

Cewar Khairi tana mikewa, tana shiga kitchen din kuma, Saifullahi na turo kofar baya

"Yawwa, dan Allaah Khairi ki kawo mana abinci mana...ki hado da lemo"

Ta amsa shi, batasan ko su nawa bane ba, sai kawai ta samu wata babbar kula da Hajja kan zuba musu abinci wani zubin sai akai musu bangarensu, duk wani abu da aka dafa ta hada musu a ciki, meatpie dinne ma ta samu wata leda ta zuba, ta kinkima, sai taci karo da Saifullahin da yayi niyyar dawowa ya dubata, ya karba, ita kuma ta sake komawa ta dibi lemukan taje ta mika musu, tana dawowa ne taji an kirata, ta juya, sai da zuciyarta ta buga ganin Ishaq a tsaye

"Khairi"

Ya sake kira

"Yayaa"

Ta furta da mamaki

"Ki kiramun Maryam dan Allaah..."

Ta numfasa yayi saurin katseta

"Dan Allaah, dan Allaah ki kiramun ita"

Ya karasa da wani yanayi da ta kasa musa masa, ko da ta koma dakinma saida ta fara daukar hijabin da tayi sallar Magriba dashi, sannan ta kama hannun Maryam din tana janyota, akayi sa'a bata musa ba ta bita, ta kofar kitchen din sukabi, ta bata hijabin tana ce mata

"Yaya Ishaq ne"

Tasan ya kamata ace taji hawaye sun cika mata idanuwa, amman bataji ko alamarsu ba, ko takalma babu a kafarta suka taka har inda Ishaq din yake tsaye jikin bango, fitilun da suka haske harabar gidan tar a kanshi, tunda tasan shi

"Karki dade, kar wani ya ganku, zan jiraki a bakin kofa mu koma, dan Allaah karki dade"

Kai ta iya daga mata, a hankali take takawa saboda yanda takejin wani iri, tana taka kananun tsakuwa, kamar yaji takun tafiyarta kuwa ya dago daga jinginar da yayi, ba zata tuna lokacin da ta ganshi babu tulun sumar nan ba, watakila kuma rashin sumar ne yasa ta ga ya rame a idanuwanta, kamar ma yayi duhu, wani abu da bata taba danganta shi dashi ba, tunda Ishaq farine har wani yellow yakeyi saboda haske, kamar yasan gashin nashi ne abinda ta fara lura dashi sai yasa hannu ya shafi kanshi, lectures ya fito yau karfe sha daya na safe, sai ya wuce da niyyar siyan lemo, shine yaci karo da AbdulKarim, daman satin can da yaje Kaduna yaji yana cewa zai shiga makarantar, da yake ya kammala Masters dinshi, project yakeyi, wai zaiga supervisor dinshi

"Yau zaka juya ne?"

Tunda AbdulKarim ya kasance mutanen da basa kaunar zaman makaranta in ba dole ba, tunda ko lokacin ma da yake karatu yana hanya ne kusan kullum

"Kaman zan kwana, bana son komawa, gidan cike yake da mutane"

Da mamaki Ishaq yace

"Mutane kuma? Wani abu akeyi ne?"

Cikin halin ko in kula, yana surbar lemonshi amsa

"Kaman za'a kawo lefen Maryama naji Hajja tana fadi"

Ishaq yaji kamar wata guguwa ta gifta tana neman dagashi sama ta tiqa da kasa

"Lefe? Maryam?"

Ya daga masa kai

"Yep, an daura aurenta ran Asabar din nan, shine wai zasu kawo lefe, wani irin aure nema a hargitse"

Tunda shi da Alhaji Sa'id ya fada musu abin mamaki ya bashi, har yanzun dinma mamaki abin yake bashi, shi kadai idan ya tuna wai Maryam ce aka daurawa aure sai yaji kamar zai kwashe da dariya. Ya dauka itace mace ta karshe da zatayi aure a gidan nasu, lokacin da ta kammala makarantarta, watakila ta rage rigima, ta danyi hankali, sai su hadu har sadaka su bayar Allaah Yasa mijin

12 / 51