Advertisements
Chapter 20 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   20 / 51

57K to 60K   out of 151K words

mai kokari da son kyautatawa duk wanda yake tare da ita.

Haka tazo da poly bag dinta cike dasu busashen kifi, cryfish, da duk wani abu da take tunanin Maryaman zata iya rasawa harda busashen zogale mai yawa da dakakken quli, dawowa ta biyu ma saida ta siyo mata kayan ganye, danginsu lettuce, kabeji harda su karas ta taho mata dashi, itama Maryaman cikin kudin da aka bata ta kirgi dubu goman ta bawa Mummy, dakyar ta karba, tana godiya da addu'o'i, to fitar Khairin ne taji kadaici ya dameta, da yake da safen duk maimaicin episodes din jiya da suke kalla akeyi, saita shiga dakin Haris din ta gyara masa gadon, ta shimfida zanin gado, ta kara share dakin duk da babu wata kura da yayi, rashin abinyi ne da tunanin halin da yake ciki da yake ta nukurkusarta, har turaren wutar da sukayiwa gidan sai da takai dakinshi, ta saka har bayi, daga baya ta koma ta dauko kaskon ta rufo kofar.

Kuma wuni takeyi da mukullin dakin nashi a hannunta tana wasa dashi, rannan da ta fito daga bayi da mukullin a hannunta, Khairi ta gani ta jinjina kai

"Kin manta kina da tsautsayin mukulli ko? Bari ki batar masa ya dawo ya niqaki"

Ta dinga dariya, kuma bata ajiye ba, ko yanzun da taga ya nufi hanyar dakin nashi, da saurinta ta karasa cikin falo ta dauki mukullin da yake ajiye a kasa, kan kafet inda take zaune ta samu Haris din tana mika masa

"Ga mukullin dakin..."

Ya karba, tayi tsaye har saida taga ya bude, sai dai daya shiga, kofin hannunshi ya fara ajiyewa ya juyo ya zare mukullin batare daya kalleta ba, ya kuma rufe kofar, tana jinshi ya saka mukullin daga ciki. Ta danyi tsaye jim, sannan ta juya, saita wuce nata dakin inda ta samu Khairi a zaune gefen gado, tasa kaya, tana murza mai a jikinta.

"Ya dawo, yanzun ya dawo"

Ta fadi da farin cikin da zaka iya ganin kyallin shi cikin idanuwanta

"Wa?"

Khairi ta tambaya dan bata kawowa ranta Haris ba

"Haris din, yanzun ya dawo"

Kai Khairi ta jinjina

"Na fada miki ki daina gatsa sunanshi haka, ke baya miki nauyin fada a baki?"

Itafa a rayuwarta shine mutum na farko daya girmeta kuma taji tana kiran sunanshi duk nauyin da yakeyi mata

"Ko Yaya ne ba zaki kara masa dashi ba"

Tayi dariya mai sauti

"Haka kawai? Mijina ne fa, sai in kama ce masa Yaya ana zaune lafiya"

Ita abin baya burgeta, ko dan tana da Yayye da yawa ne? Khairi ta sauke numfashi kawai

"To kuma surutun me kika tsaya kinayi anan? Ba zakije ki same shi ko ruwa ki kai masa ba?"

Akan kunnenta ya murzawa dakinshi mukulli

"Yafa murza mukulli a dakin daya shiga, kuma ni banma taba kai masa ruwa ba"

Khairi saita rasa amfanin da karatu da kuma kallon Maryama yakeyi mata, tunda anayi ne dan a karu, ko babu komai zaka tsinci abu daya zuwa biyu dangane da zamantakewa, musamman ta aure. Marubuta na wannan kokarin cikin hikima

"Tam saiki samu waje ki zauna ko ki koma ki cigaba da kallonki, dan ni idan na karasa shafa mai na kayana zan harhada, in kira Abba in gaya masa dan ya aiko gobe idan Allaah Ya kaimu azo a daukeni"

So tayi taima Khairin magiya akan ta kara wasu 'yan kwanaki, amman tasan abinda yake gabanta, kuma saita zauna a gefen gadon har Khairi ta karasa shiryawarta

"Ke me yasa baki da hankaline baki san ayi miki gatse ba, ki tashi kije wajen mijinki kafin in kira Adda Zahra in fada mata shirmen da kikeyi bayan duk naji nasihar data dinga miki tunda aka daura auren"

Mikewa Maryama tayi tana ficewa daga dakin, kuma maimakon ta nufi kitchen sai tayi dakin Haris ta tsaya ta kwankwasa sau biyu, tafi mintina hudu, kamar ba zai bude ba, sai gashi ya taso, ya rage kayan jikinshi, dan yanzun din gajeran wando ne sai riga baka, sannan idanuwanshi sun sauya launi, bawai ja kawai sukayi ba, launin jan wani irine da bata taba gani ba, sannan tana jin wani irin kauri da ta rasa daga dakin nashi ne yake fitowa ko daga jikinshi

"Ruwa daman, nace zaka sha ruwa? Ko tea? Ko abinci?"

Kanshi kawai ya girgiza mata, ya mayar da kofar ya rufe, taji ta kasa juyawa ta tafi, akwai wani abu a tare da Haris din daya sauya, ba haka ya tafi ba, saida taji kafafuwanta sun fara mata barazana sannan taja su, sai dai falo ta koma ta zauna akan kujera batare da tasan takaimaiman abinda take tunani ba. Sunyi abincinsu ne tazarce, kudin da Haris ya bar mata data ga yawansu saida taji tsoro, bata ma taba yafi dubu biyar ba, duk abinda zasu siya cikin kudin hannunta ne sukeyi, Khairi taje musu kasuwa ta karo musu doya da kuma irish, harda dankalin hausa data gani, cikin kudin Haris dinne ta bayar aka siyo madara da kuma Milo, kar yazo ya duba yace bataji maganarshi tayi amfani da kudin ba.

"Ki tashi ki samu wani abin ki dafa masa"

Cikin sanyin jiki ta cewa Khairi

"Bafa zaici ba, abubuwan da naga yana ci basu da yawa..."

Lokacin da Khairin tayi mata magana ma takwas saura

"Allaah Ya kyauta muku to"

Shine abinda ta iya furtawa, saima ta shige daki da wayarta tayi kara, itama Maryaman taji tana son sake komawa ta tambayi Haris ko zata hada masa shayi, wannan karin bai bude kofar ba, cikin wata irin murya kamar wanda ya tashi daga bacci ya tambayeta menene, kuma ta hakan yace mata ba zai sha ba

"To dan Allaah ka fito ku gaisa da Adda Khairi, gobe idan Allaah Ya kaimu Abba zai aiko a dauketa...ko ba yanzun ba, zuwa safen kafin ta tafi, dan Allaah, kaji"

Saida ya amsa da

"Ok"

Sannan ta tafi, zuciyarta nayi mata babu dadi. Da tunani iri-iri ta kwanta. Ta dai ware dubu goma daga cikin abinda yayi mata saura ta sakawa Khairi cikin akwatinta tunda inta bata ba zata taba karba ba, da wani abinne ba kudi ba. Haris bai bata kunya ba da safen ya fito, suka gaisa da Khairi, sai dai fuskarshi babu digon fara'a ko kadan, ya dai ce mata

"Na dauka zaki kara yi mana wasu 'yan kwanaki kafin ki tafi"

Khairi ta girgiza masa kai, tana masa bayanin zatayi registration ne, envelope ya mika mata

"Banyi zaton da wuri zaki tafi ba haka"

Ta bude baki, kafin tace wani abu ya rigata da

"Ba zanji dadi ba in kikace wani abu, ki karba dan Allaah"

Saita karba din tanayi masa godiya, tunda direban sammako yayi, karfe takwas ma a Kanon tayi masa

"Allaah Ya tsare hanya, mungode sosai, akwai aikin da nakeyi, zan shiga in karasa"

Itama tayi masa fatan alkhairi, Maryama harda hawayenta lokacin data raka Khairin, ita kanta karfin haline

"A garin nan zanyi aure In Shaa Allaah, saboda ke, zamu zauna kusa da juna Maryama"

Kai ta daga ma Khairi tana share hawayenta, haka ta koma tana jin gidan yayi mata wani fadi na daban. Ta kwanta a falo, ko karyawa Khairi bata tsaya tayi ba, ita bata iya cin abinci tunda sassafe, ko ranakun makaranta zai wahala kaga ta saka wani abu a cikin kafin ta fita, sai dai ta tafi dashi. Bacci ne ma ya dauketa anan kan kujera, sanda ta tashi kamar anyi mata sata a cikinta, jikinta har rawa yakeyi, shayi ta hada, tana da sauran biredi, ko kwai bata tsaya soyawa ba, dan anan Kitchen din ma ta tsaya ta karya tanajin ta dawo hayyacinta, bata da jimirin yunwa sam, da azumi ba karamin galabaita takeyi ba. Ta wuce dakinta, tayi wanka ta canza kaya, duk ta rasa abinda zatayi yau din da zai rage mata lokaci da shirun da gidan yayi na rashin Khairi.

Ta nufi dakin Haris ta kwankwasa

"In kawo maka shayi?"

Ta tambaya daga bakin kofar

"A'a"

Ya amsa mata, ta dawo falo kawai, tana jin babu wani girkin da zatayi, dankalinta zata soya ta kara shan shayin ko taci shi kadai.  Bawai zama sukeyi suna shan hira da Haris ba, amman ba haka yake ba kafin ya tafi, ko dan bata taba zuwa haka kawai ta same shi a daki bane ba? Ta dauka zai fito ya fita kamar yanda ya saba, shisa ta wuni a falon, har sallah anan tayi, da bayin falon ma tayi amfani, hijabinta kawai ta shiga daki ta dauko. Bata ga fitowarshi ba, bacci biyu tayi tana farkawa, tasan bata da nauyin bacci, kuma kofar dakin nasu tana yin kara idan za'a fita, yanda ta murza mukulli ma dole zataji idan akayi kokarin budewa.

Kwana hudu sukayi Haris bai fito daga dakinshi ba, jiya a falon ma bacci ya dauki Maryama saboda damuwar da ta tsinci kanta, dan yinin jiya tun safe da tayi masa magana ya amsata, muryarshi na fitowa kamar wanda aka shake zuciyarta ke ta bugawa, da rana ma sai taje ta dinga kwankwasawa, taji shiru

"Dan Allaah kasa wani abu a cikinka...ko kadan ne in kawo maka shayin, in baka so ka fito in ajiye maka a bakin kofa sai kazo ka dauka in na tafi...kaji?"

Baiyi magana ba, taje ta hado shayin ta kawo, amman haka ta koma ta dauke shi da daddare, maganar duniya bataji an amsaba, ta jijjiga kofar shiru, da yake ba wani bacci tayi mai natsuwa ba, sai gashi akan kunnenta akayi kiran sallar farko, ta tashi tayi alwala tazo tana gabatar da sallolin nafila kafin aka kira asuba ta gabatar da sallar, ko azkar ta kasa, ita kanta duk kaunar da takeyiwa abinci jiya kadan ta saka a cikinta, ko karfin kirki bataji, ta kwanta akan kafet din falon inda tayi sallah tana komawa wani wahalallen bacci data tashi karfe takwas da wani abu, taje dakinta tayi brush ta wanke fuska, ta fito ta nufi dakin Haris, bugawar duniya tayi amman shiru, ta kara kunnenta ko da zataji motsinshi. Saita tuna littafin data taba karantawa da kanin jarumin ya mutu a daki babu wanda ya sani saida aka wuni, anma dauka ya fice ne.

Zuciyarta tayi wani irin tsalle daya sa ta mike daga zaman da tayi a bakin kofar, idanuwanta cike taf da hawaye ta koma falo ta dauko wayarta tana dannawa Khairi kira har biyu, ana ukun ne ta daga

"Zan kiraki Maryam, ina zuwa"

Kafin ta amsa Khairi harta kashe wayar, tabarta da sauketa daga kunnenta tana tunanin wanda zata kira kuma, sai kawai ta tsinci kanta da danna lambar Abba, shi kam a bugun farko ma ya daga, kamar mai jiran kiranta

"Mairama"

Shine abinda ya fadi taji kuka ya kwace mata

"Subhanallahi...Mairama? Me yake faruwa? Ya akayi?"

Cikin sheshheka tace

"Abba...yana daki...bai bude ba...baya amsawa..."

Tayi maganar a rarrabe cikin kuka

"Ki natsu ki fadamun abinda yake faruwa kinji ko?"

Ta daga kai tana kokarin danne kukan da yake ta kara taso mata, dakyar ta fada masa yau kwana hudu Haris na dakinshi a kulle, kuma tun jiya baya amsawa ko ta kirashi

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...ina maigadinku?"

Ta maimaita maigadi cikin kanta

"Ki kirashi yazo yaga ko zai iya balla kofar a dubashi..."

Duk da tanata daga kai, sai tace

"To zaku zo Abba? Zaku taho dan Allaah?"

Cikin sanyin murya yace mata

"In Shaa Allaah...yanzun kije ki kira maigadin"

Sauke wayar tayi, sai Alhaji Sa'id dinne ya bude daga nashi bangaren, ta fita da saurinta tana kiran maigadin, dan dattijon ya wullar da radio dinshi da yake ta murza yana biyo bayanta cikin barin jiki, sai dai koface da tunda ya ganta yasan ko a zamanin kuruciyarshi bai isa ya karyata ba

"Bari in kirawo taimako Hajiya, wannan kofar ba zan iya karyata ba"

Sai gashi sai da mutum kusan biyar suka hadu sannan aka iya karya kofar nan, lokacin wayar Maryama nata ruri, ta daga ganin Alhaji Sa'id ne

"An bude Abba..."

Ta fadi tana karasawa cikin dakin, zuciyarta ta rikito, ta koma mazauninta ta sake rikitowa kamar zasu fadi a tare ganin Haris shimfide akan gadonshi, dakin kauri yakeyi har lokacin daya cakudu da turaren wutar data kunna duk da an kwana biyu, saiya bada wani irin kamshi marar dadi, idanuwanshi ba rufe suke gabaki daya ba, amman bakar fuskar nan tashi tayi fayau kamar takarda, labbanshi a bushe kamar yana wani motsi dasu zasu iya tsagewa, ga guntayen takardu nan har akan gadon, ba karshen sigari bane ba, dan Maryama tasan ya yake, suna gani ai a hanya.

"Ya rasu ne?"

Muryar wani cikin mutanen da suka karya kofar ya tambaya

"Ya rasu..."

Ta maimaita a hankali, a kunnen Alhaji Sa'id

"Mairama? Waye ya rasu?"

Sai kawai kuka ya kwace mata, yau ta fara shaida menene tashin hankali

"Mairama!"

Kuka takeyi da yake fitowa tun daga kasan zuciyarta, wayar ta subuce daga hannunta ganin yanda aka dago Haris din ya subuce ya koma luu kan gadon, suka sake dagoshi

Bata taba ganin gawa ba tunda take
Amman yanayin Haris yayi mata kama da gawa

"Wannan fa sai dai a samo dan sahu a kaishi asibiti...Hajiya ko kin iya mota?"

Ta girgiza kai

"Ina mukullin?"

Wani ya sake fadi, jikinta nata rawa ta karasa ta bude inda taga mukullin ta dauka ta mika masa

"Kizo mu tafi asibitin Hajiya, ki kira gida ki sanar, inda kudi kuma saiki dauko kinsan ba lallai su dubashi ba"

Kudin dake wardrobe din iya wanda hannunta zai iya damkar mata ta dauka tana bin bayansu, ta koma da sauri ta dauki wayarta, saida aka saka shi a motar, itama bayan ta shiga, maigadinsu daya rufe gate din gidan kuma ya shiga gaba, asibitin Aminu Kano suka wuce kai tsaye, ganin halin da suke ciki ne yasa aka kawo gadon marassa lafiya aka dora Haris din aka shiga dashi ciki, Maryama ta bisu, tanajin yanda take taka tsakuwoyi, haka sanyin tiles din daya ratsa kafafuwanta yana sanar mata da babu takalmi a kafarta balle kuma wata hijabi, wata Nurse ce ma ganin yanda take a firgice, ga wayarta sai qara takeyi yasa ta kamata ta zaunar da ita akan wata kujera, ta karbi kudin da take rungume dasu ta gyara mata hargitsinsu ta sake damka mata

"Ki daga wayarki anata kira..."

Ta daga wayar, fuskarta duk busashen hawaye sai ajiyar zuciya take saukewa

"Muna asibiti Abba...muna asibitin..."

Ta kalli Nurse din da ta danyi mata murmushi

"Aminu Kano..."

Ta dayan bangaren Alhaji Sa'id yace

"Gamu nan zamu kamo hanya In Shaa Allaah...ke da waye a asibitin?"

Ta hango maigadinsu

"Ni da maigadi"

Ta amsa cikin karamar murya

"Bari in kira Murtaka, ki rike wayarki a kusa kinji, yanzun za'a zo a sameki kafin mu karaso"

Kai ta daga tanajin sababbin hawaye na zubo mata, kafin ta sauke wayar daga kunnenta, haka tayi zaune tana kallon reception din emergency din, kafin wannan Nurse din mai kirki tazo ta tabata

"Ki taso ana nemanki"

Ta mike, tana jin kamar jiri na dibarta, bata san cewa yau din za'a yaye mata wani Labule guda daya daga cikin Labulayen da suke lullube da sirrikan Haris,
Kamar yanda batasan cewa idan an daga mata Labulen nan zata kamashi ta sauke suyi tsaye ita da Haris a bayanshi ba...

22

Tambayoyi ne likitan yayi mata, shekarun Haris, kalar jininshi, duka kai kawai take girgizawa, dan tana jin idan ta bude bakinta to zata iya fashewa da kuka

"Ina iyayenku? Ko wani babba?"

Tana sauke ajiyar zuciya tace

"Basu karaso ba, mu kadai ne sai maigadinmu daya taimaka mun muka kawoshi asibiti"

Likitan ya kalleta, kallon da yasa taji rashin hijabin da bata saka ba, balle kuma ayi tunanin takalmi

"Yayanki ne?"

Ta girgiza masa kai, cikin karamar murya tace

"Mijina ne"

Kallonta dai ya sakeyi, sai takejin ko da bai bude bakinshi yace wani abu ba, ta karanci kalaman shi, kallon yarinta ne yayi mata yanzun

"He's extremely dehydrated, jininshi ya hau sosai..."

Ta gyada kai tunda ta fahimci abinda yace

"Kinsan yana shan wani abu ne?"

Taji anyi maganar daga bayanta, saita juya, wani mutum ne, gajere ne sosai, duk da a zaune yake kan daya daga cikin gadajen marassa lafiya na ward din da babu kowa akai, yanda kafafuwanshi suke lilo ne yasa ta gaje gajartarshi, Psychiatrists ne, dan yana aikine a wani private rehabilitation centre, ya shigo wajen abokinshi ne, likitan da yake duba Haris, tunda aka shimfide shi kan gadon nan, kallo daya yayi masa ya gane cewa yana shaye-shaye

"Ko kwaya haka ko taba"

Mutumin nan ya kara fadi, Maryama taji kamar an dauraye mata kanta da ruwan omo, bata jin komai sai wannan kalmomin daya furta, kwaya da kuma taba, a iya sani da fahimtarta 'yan kwaya kullum a buge suke, wasu ma ance bambancin da yake tsakaninsu da mahaukata kalilan ne, ita dai Haris bai tabayi mata kama da wanda yayi nisa da hankalinshi ba, tabar dai yanzun taga wani abu ya haska cikin kanta, wannan guntattakin abubuwan da ta gani birjik a dakin Haris dazun, ko itace tabar? Ita ba sigari bace ba?

"Tun yaushe yake haka?"

Likitan ne yayi mata wannan tambayar yanzun yana sa ta mayar da hankalinta kanshi

"Ban sani ba...kaman tun jiya"

Ta karasa fada da rashin tabbas a muryarta, tana kallon likitan ya dago da Haris din yana cire masa bakar rigar da take jikinshi mai dogon hannu, tana da dan kauri, lokacin da yayi kokarin ajiyeta ne wani abu ya fado daga ciki, a cikin irin ledar nan da ake dura magani a asibiti, sai dai abin yayi mata kama da ganyen shayi, kamar wani hayaqi da aka taba ba Adda Zahra a islamic chemist, lokacin tana fama da wani irin ciwon kai, akayi zaton ko shafar aljanu ne. Likitan nan ya tsugunna ya dauka, saiya dagawa gajeran mutumin nan

"Weed"

Cewar mutumin yana girgiza kanshi

"Amman kasan wannan babban case ne ko?"

Da harshen turanci likitan yayi maganar, kuma dashi mutumin ya amsa masa

"Ka bashi taimakon daya ke bukata kawai, kayi kamar baka gani ba, a kasar nan dai babu wani amfani, in iyayensu suka zo sai kayi magana dasu a nemar masa taimako ta hanyar daya kamata"

Likitan ya kalli Maryama da take tsaye tana jinsu, watakila yanayinta da tayi firgai-firgai ne yasa su duka biyun sukayi zaton ba zataji turanci ba

"Ki kira mun wata Nurse, zan rubuta abubuwan da ake bukata, aje a siyo yanzun, kice su nuna miki pharmacy..."

Sai ta juya din, tayi hanyar data shigo da ita dakin. Lokacin da ya gama rubutun, suka nufi hanyar pharmacy da Nurse din nan ne kiran Mummy ya shigo wayarta, dan Maryama ta kwance dankwalin kanta ta ninka tayi mayafi dashi ko zai kare mata wani abin, ta daga kiran, sai Nurse din data kula da yanda take tafiya ta karbi kudin hannunta tace mata ta koma bakin emergency din

20 / 51