Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
da babu karin ruwa a jiki da kallo, dan shine a saitinta, bakin hannunshi, yatsunshi take kallo, ance zakaga hannun yan shaye-shaye yayi baki, toshi nashi bakin ne, in ba dai karawa yayi ba, sai dai faratanshi farare ne kal, sai kace bashi da jini saboda haskensu, kamar rubutu take gani a jikin karamin yatsanshi, kafin kwakwalwarta ta hana zuciyarta harta kamo hannunshi, da nata duka biyun, taji hannun nashi yayi sanyi, ta duba yatsan nashi, rubutune kamar anyi shi da bakin fenti ko tawada zatace, ta karanta sunan jiki
"Aise"
Ta sake kallo tana tsintar kanta da shafa rubutun taji ko akwai alamar shi, ko kuma zai goge, yana nan, kuma babu alamar shi a jikin nata yatsan
"Aise..."
Wacece Aise?
Wanne irin suna ne Aise?
23
Kaman wanda yasha kasa haka yaji makoshin shi ya bushe, ga idanuwanshi sunyi masa nauyi sosai, da yake kokarin budesu ma sai yaji kanshi ya sara, ya dan sake runtsa idanuwan, ya kuma sake kokarin budewa, farin bango ya fara gani, ya dago hannunshi da nufin ya murza gefen fuskarshi da yaji yana kaikayi, amman sai yaji wani abu ya soke shi da ya sashi furta
"Ouch"
A hankali yana duba hannun, karin ruwane a jiki, dayan hannun kuma da yaja sai ya kalli gefenshi da saurin gaske, kwan dakin a kunne yake, tana zaune ta kife kanta a jikin gadon da alama bacci takeyi, hannunta yana rike da yatsanshi guda daya, karamin yatsanshi, yabi hannun nata da kallo kanshi yayi masa nauyi kamar an dora masa dutse, asibiti yake ya sani, ya kuma san itace ta kawoshi dole da taimakon wasu, shisa bai wahalar da kanshi wajen zurfafa tunanin suwa ba, balle kuma tayaya yazo asibitin. Saiya mayar da idanuwanshi ya lumshe, sai yake ganinshi a tsakiyar rusassun gine-ginen nan na Syria kamar an dauke shi an cilla can.
Ranar farko daya gane yana son yara, yana sonsu sosai, yana aji hudu ne a sakandiri, sunzo hutu, sai sukaje duba Barde da bashi da lafiya har an kwantar dashi a asibiti, lokacin da sukaje asibiti akwai yayarshi da tazo itama, da yaranta guda uku, dukansu mata ne, dayar ce jaririya da baisan ko 'yar wata nawa ba, su 'yan matan anyi musu wani kitso da aka jerawa beads, babbar daya fara hada ido da ita, sai tayi masa dariya, babu hakori guda daya a bakinta, baisan lokacin da murmushi ya kwace masa ba shima
"Zo mu gaisa"
Ya tsinci kanshi yana fada, sai kuma yarinyar bata bashi kunya ba, taje din tana rike hannunshi hadi da gaishe dashi cikin karamar muryarta, kanwarce dai taki zuwa ta sake makalewa a jikin Mamanta
"Wannan sarkin tsoron mutane ce"
Inji Maman, amman itama ta burgeshi sosai, kafin su tafi saida yarinyar nan da taje wajenshi ta bashi bead guda daya, yasan daya daga cikin na kanta ne data cire, haka suka bar asibiti da wannan bead din da yake ta wasa dashi a cikin hannunshi, a ranar, a karo na farko yaji cewa idan wata rana zai samu nashi yaran, to yana son mata ne, ko guda goma ne yana son duka su kasance mata ne. Kuma kamar wani hadin baki, daga wannan ranar zai wahala ya fita bai hadu da yara ba, har saida ya fara tunanin ko dai kula dasune bayayi da din shisa baya ganinsu haka, wata rana yana zaune a mota zai hangesu suna wucewa, wasu da uniform din makaranta da yan jakunkunansu, wasu ma ledace rike a hannunsu a maimakon jakar, uniform din nan yayi cuducudu da dauda kamar sun shekara basu ga ruwa ba, wasu kuma almajirai ne, 'yan kanana.
Akwai wani da yana tsaye wajen mai saida kayan marmari zai siyi Pear, dan yana son abin sosai, in dai zai gani saiya tsaya ya siya. Yaji an rike masa kafar wando
"Dan Allaah ka saimun abinci yunwa nakeji"
Yaron da Haris baya tunanin ya haura shekaru biyar ya fada, dayan hannunshi rike da wani katon kwanon silva, idanuwanshi da alamun sabon hawaye banda wanda suka bushe a idanuwanshi
"Ina mamanka?"
Shine tambayar da ta subuce masa, saboda a ganinshi wannan yarone da bai kamata ace yana waje a dai-dai wannan lokacin ba, kamata yayi ace yana gida, kusa da Mamanshi, anyi masa wanka, bashi da wata matsala banda ta wasanni
"Ance ta mutu ba zata dawo ba shine Baba ya kawoni nan na zama almajiri"
Wani abu ya takure a kirjin Haris har ya nawa fitar numfashin shi barazana, kudin da baiko kirga ba ya ciro ya bashi yana kasa cewa komai, wannan pear din daya siya a ranar a falon Hajiya Rumana ya barshi, akan kujera, saboda cikinshi ya cunkushe fal da kwashewa Baban yaron nan dama Malamin daya karbe shi a matsayin almajiri. Inda shi wani babbane a gwamnati a ranar nan da kwana zaiyi sintiri tsakanin makarantun alluna ana kama masa Malaman, ana kwashe wannan kananun yaran zuwa garuruwansu, saima an rufe masa iyayen a matsayin jan kunne. Ya jima abin na damunshi, in dai zaizo hutu ya fita ya dinga raba ido kenan akan tituna ko zaiga irin yaron nan ya basu kudi.
Shisa da tunani daya ya sauka kasar Syria, tunanin ya haskawa duniya wannan kananun yaran daya kamata ace sun hadu sun ba kariya, wannan kananun yaran da basu yiwa kowa laifi ba, yaran da basu ma san me duniyar take ciki ba, yaran da abinda wannan yakin yakeyi musu, album dinshi harya sama masa tittle tun tuni (Innocence in the face of war). Kuma a sati biyun nan babu abinda bai gani ba, jinsu yayi kamar shekara biyu saboda nauyinsu da kuma dadewar da kowacce rana takeyi masa, dare ma tsayi ya dingayi masa, saboda daga inda suka sauka baisan sau nawa yaji fashewar bomb ba, fashewar da take hadawa da wani sashi na zuciyarshi
"Yara nawa bomb din nan ya taba yau?"
Shine tambayarshi, idan ya kalli yaran nan da idanuwanshi sai ya gansu a matsayin yara, kyawawan yara, farare qal dasu, wasu cikin matan ma da mayafai an nada musu, sai yaga yanayi musu murmushi, saboda yanajin bashi da wani abu da yake dashi da zai ba wannan yaran banda murmushin shi, wasu su mayar masa, wasu har hannu suke daga masa, wasu kuma zasu kalle shine kawai. Idan ya daga camera dinshi, ya hangosu ta ciki sai yaga wani abu da baigani ba kafin ya daga camera din nan, sai ya ga wani firgici a cikin idanuwansu, wani tsoro da yake da yakinin har karshen rayuwarsu ba zai taba barinsu ba.
Lokacin ne yake kula da kurar da take jikinsu, wasu har a fuskarsu, wari da warin takalmin da yake kafar wasu, hujin da yake jikin na wasu, wasu ma 'yan kafafuwan nasu babu ko takalmin, busassun labbansu, yanda kashin kumatunsu ya fito alamar rashin wadatar abinci ko abubuwan gina jiki, busassun hawaye dama sababbi, ranar da sukayi kwana shida ne suka tsallaka wani waje da aka cilla bomb a safiyar ranar anata tono mutane da suka jikkata, wasu ma gawarwaki ne, ranar ne camera dinshi ta daukar masa kafa, 'yar karamar kafa da farin takalmin daya baci da jini, iya kafar, babu sauran jikin, kafar daya dauka yana ganinta dishi-dishi a tsakanin hawayen daya cika masa idanuwa taf.
Tun daga ranar har suka bar Syria da hawaye a idanuwanshi yake daukar duk wani hoto, batare da yasan nashi Ogan yayi masa hotuna da yawa a wannan yanayin ba, saida ya nuna masa, ya ganshi shima ranar kanshi da hannayenshi duk kura, haka bakaken kayanshi, saboda anyi tonon nan dashi, an kama gawarwakin da baisan adadinsu ba tare dashi, ya taya an daga gini an zaqulo uba, an zaqulo da, an zaqulo uwa, da hannunshi ya mikawa wani tsoho gawar saurayin danshi.
"Kamar ince maka zaka daina, wannan hawayen na idanuwanka zaka nemosu ka rasa, amman bana maka fatan nan, bana maka fatan ranar da zaka nemi hawayen nan naka ka rasa, ranar da zaka ganka a war zone amman babu inda zakaji wani abu yana zuba sai anan..."
Ya karasa yana dafa kirjinshi, Haris numfashi kawai ya iya saukewa, numfashin da har jiragensu suka daga, dan sun hau mabanbanta ne, kowa akwai inda zai nufa, shi Haris yayi Italy ne, saboda makarantar da yake shirin sake komawa dama wasu abubuwan da zaiyi, sannan zasu hadu da ogan nashi bayan sati biyu, akwai yiwuwar ya samu aiki a wajen yada labaran da ogan nashi yayi recommending dinshi. Gabaki daya bayajin dadin duniyar, kanshi yayi nauyi na gaske, tunda sukaje a sati biyun nan inya kwanta, jikinshi har rawa yakeyi yana neman abinda ya saba, yana neman wiwinshi ko zai samu natsuwar data kwace masa, shisa yana sauka Italy ya samu hotel ya ajiye kayanshi abinda ya fara nema kenan. Daman tun kwanansu biyu da zuwa abinci ya daina zauna masa a ciki, ko yaci sai yayi amanshi.
Kwana biyar din farko da yayi a Italy yana hidindimunshi abubuwa masu ruwane kawai suka dinga shiga cikinshi, suma dakyar yake iya hadiyesu tunda yasan jikinshi ba zai taba bashi hadin kai ba in har bai saka wani abu a cikin nashi ba. Ranar na shidan ne ya taka kafarshi zuwa makarantarsu Aise, inda yasan zai sameta, ya nemi waje yayi zamanshi da kofin ice tea a hannunshi da yake dan zuqa a hankali, har saida ya hangota, ita kadaice, da wani baggy din wandon jeans, crazy ne amman sai dai ba'a ganin jikinta a duk inda ya yayyanka din, sai riga da itama bata matseta ba, dankwaline ta daura akanta, dankwalin da Haris yake iya ganin santsinshi daga inda yake tsaye, dan itama ya zame mata, rabin gashinta a waje yake, gashin data rina, kala biyu brown da kuma baki, kamar kalbace kanana akan nata ko meye bai gane ba sosai, ta dai gyara edges din, da kwalliyarta ta sabo a fuskarta, ya tashi da sauri yana karasawa inda take
"Amore"
Ya furta muryarshi na fitowa a dishe, yanzun da take tsaye a gabanshi, zuciyarshi na kadawa da tarin soyayyar da yakeyi mata, da kuma kewarta, so yakeyi ya hade wannan yar tazarar ya riketa a jikinshi, idanuwanta ne suka dakatar dashi, abinda yake gani a ciki
"A'a!"
Ta fadi cikin daga murya, ta sake girgiza kanta
"Akan me zaka zabeta kuma kazo ka tsaya a gabana haka? Me yasa?"
Ya karasa da sauri yana riko hannunta ta fisge, tana tureshi da hannun nata, dan daya rike yake da takardun data daga masa
"Kaga takardun transfer dina?"
Ita yake kallo ba takardun ba, ta kuma juya masa hannunta na haggu, yana ganin zoben da yake yatsanta
"An samun rana, aure zanyi kamar yanda kayi aure, kace mun Babanka ne yayi maka aure, sai dai nima Babana yana nan, kuma nima auren zaiyi mun..."
Haris yaji dariya ta kwace masa, dariyar hasaso Aise da auren wani bashi ba, a wajenshi abin dariya ne saboda tunda yasan yana sonta yake hangota a gefenshi, yake hangota da igiyoyin aurenshi, ya za'ayi hankalinshi ya dauki cewar zata auri wani bashi ba?
"Baki da hankali ko? Ni zaki gayawa zaki auri wani?"
Tayi masa wani kallo daya kasa gane fassararshi
"Kai daka fadamun ka auri wata meya faru?"
Yayi kokarin sake kama hannunta ta matsa baya da sauri
"Kabari, bana so, na fada maka, bana so! Aurena zanyi nima"
Sai ya girgiza kanshi kawai yana sake fadin
"Baki da hankali"
Ya juya yayi tafiyarshi, duk karshen sati Aise din na zuwa gida, kamar ka'idace a wajenta, shisa ya rabu da ita, daya tashi saiya bita gidan, ya samu har Alhaji Modu na gida kuwa, yanda bata kula shi ba data ganshi shima saiya shareta, to tambotsan Aise sai dai ya bada labari, wannan fushin nata ya sanshi, ya saba dashi. Bai bata dalili bama tanayi masa rikici balle kuma yanzun da take da dalilin. Ko a wajen cin abincin anata hira, shi dai shayine daman ya hada, yace musu baya jin yunwa
"Ya wajen matarka? Amman dai karatun nan da zaka dawo tare da ita zaka taho ko? Kaga itama sai ta cigaba da karatunta anan"
Idanuwanshi suka sauka kan Aise data kware, ta dauki kofin ruwa tana kwankwada, su duka suka hadu suna tayi mata sannu, hakan ya ba Haris damar zillewa tambayoyin Alhaji Modu din da bazai so ya amsa ko daya ba a halin yanzun, a gaban Aise
"Kanwar taka ta gaya maka an sa mata rana ko baku kai dayin maganar ba?"
Wani abu yayi tsaye a tare dashi gabaki daya da kalaman Binta, yasan ya ajiye kofin hannunshi, ya kuma daga kanshi ya kalli matar
"Ba kuyi maganar ba kenan, karshen watan nan za'a daura auren"
Sanyi yaji yanaji, kamar an watsa masa ruwan kankara
"Allaah Ya kaimu"
Ya furta muryarshi na komawa cikin kunnenshi kamar ba tashi ba, ya kalli Aise amman kanta na kasa. Sai kuma ya dauki kofin shayin nashi yana cigaba da kurba, saida ya shanye shi duka sannan yayi musu sallama, har suna cewa sun dauka kwana zaiyi ya girgiza musu kai, har ya taka kafarshi daya wajen gidan saiya koma, ya wuce su Alhaji Modu da suka rakoshi bakin kofar ya koma dining area din nan, inda Aise take zaune har lokacin
"Bracelet dina"
Ya fadi yana mika mata hannu, data dago hawayen da suke idanuwanta ne suka zubo
"Bani tafiya zanyi"
Ta kalli hannunta da bracelet din yake, na azurfa ne, customized ne yasa akayi mata daga gida Najeriya ya tafi dashi, shima gani yayi a hannun 2Pac yace masa a wajen wani Nakore ne ya biya akayi masa, daya duba akwai na mata kuwa, saiya bayar, da haruffan sunayensu yayi tunanin a saka, sai kuma ya tambayeta in zaiyi mata customized bracelet me take so a rubuta a jiki
"Haris"
Ta bashi amsa kai tsaye, bai tambayeta dalili ba yasa aka rubuta mata hakan, harda wani dan heart a gefe, daya kawo shine ya daura mata chain din da yake adjustable. Ya zauna a hannun nata yayi kyau
"Na tsaneki adadin lokuttan daya rike hannunki alhalin kina tawa"
Ya dora yanajin wani irin tiriri na taso masa
"Yanzun da kika zabe shi, kije Aise, na bar masa ke, amman ki bani abuna"
Tasa hannu ta share hawayenta, hannunta har rawa yakeyi lokacin data kwance bracelet din ta mika masa
"Zaki iya zuwa ki zama tashi, ina muku fatan alkhairi"
Ya fada yana juyawa, sai lokacin ma yaga su Alhaji Modu a tsaye, baibi ta kansu ba ya wuce ya fice daga gidan. Tunda baisan me suka tsaya kallo ba, abinda suke sone ya faru, sunyi nasara, sun karasa rabashi da Aise din, kuma ko itace mahadin numfashin shi ya bar musu 'yarsu. Har kasar ma duka zai bar musu, ya fasa komawa makarantar anan. Jirgin yamma yabi zuwa kasar New York City, ya samu Oganshi acan. Kuma ko daya gama abinda zaiyi din, sai ya tsaya yana duba makarantar Parsons School of Design, kafin ma ya zurfafa tunaninshi ya riga ya tsinci kanshi yana applying. Saida ya gama sannan ya tattara kayayyakinshi yayo gida.
Daya shiga daki, ko kwan dakin bai kunna ba, yanda yayi wani duhu-duhu sai yaji abinda yake bukata kenan, kamar bayason ganin haske, kamar duk wani karfi da ya bar Syria dashi ya gama karewa ne daga lokacin daya shigo cikin gidan, banda nauyi babu abinda kanshi yayi, babu komai a ciki, bayajin komai sai wani irin kadaici daya lullube har ruhinshi. Kadaicin daya saukar masa da gajiya yaji bayason ganin kowa, bayason yin komai banda kwanciya, sai kuma wiwin da take tayashi hira, wayarshi ma kashewa yayi tunda bayajin yin magana. Saida ya kwana ya yini, tukunna ya sauka daga kan gadonshi dakyar, ya hada sallolin da ake binshi yayi, bashi da karfin bude kofa shisa ya amsa Maryama daga nan inda yake. Da ta kira masa shayi ma ji yayi amai na taso masa, bayason yasa komai a cikinshi.
So kawai yakeyi ya kwanta, ya cigaba da kwanciya, in zai iyama ya bace cikin duhun da yakeji ya zame masa aboki a cikin dakin. Tun yana gane gari ya waye, yana bacci ya farka ya tashi ya shiga bayi, ko wanka baiyi ba a kwanakin nan, bayajin karfin yin wanka, dakyar yake sallah, shima harhada wasu da wasu yakeyi, har yaji komai yayi shiru, shirun da yake bukata, shirun da yasan a cikinshine suka dauko shi zuwa asibitin nan. So yake ya tashi yanzun, yasha ruwa, yana bukatar ruwa, amman ko daya zare yatsanshi daga hannun Maryama sai yaji jiri na dibarshi da yayi yunkurin tashi, dole ya koma ya kwanta, a hankali ya dan bubbuga gefen gadon da hannunshi, ta kuwa tashi da saurinta
"Ka tashi? Sannu...bari in kirasu in fada musu ka tashi"
Shigowar likita uku, taje ta kira Nurses yafi sau bakwai har saida baccin nan ya dauketa, tana cewa suzo su duba sugani, me yasa bai tashi ba har yanzun tunda likitan karshe yace mata zai iya farkawa kowanne lokaci, tana ganin yanda suka gaji da kiran da takeyi musu, bai dameta ba, ai aikin da aka biyasu suyi kenan, taji ya riko hannunta ya dan murza
"Ki bani ruwa in sha..."
Ta daga masa kai, taje ta dauko ruwan ta bude robar ta mika masa, sannan ta fita, ko ta kira Nurse din tazo ba wani abu tayi masa ba, ruwan da saura kiris ya kare ta cire da nufin canza wani Haris yace mata
"Nagaji, kibarni in huta"
Ita kuma tana wani lankwasa murya kamar ba ita bace ta ware makoshinta kamar bututu ta amsa Maryaman da taje kiranta ta amsa Haris din
"Da kayi hakuri an saka maka tunda saura guda biyu, sai kaga kafin gari ya waye angama"
Maryama Haris ya kalla, da take tsaye tana kallonshi itama, tana jiran taji abinda zaice
"Ki fada mata, ko ta sakamun zan cire ne"
Sai kuwa ta kalleta
"Kibarshi tunda bayaso"
Akan dole ta fita bayan ta gimtse fuska, kamar gani Maryama tayi ta harareta kafin ta fitan. Ta tabe baki ta koma kan kujerar data tashi ta zauna
"Kaina yayi mun nauyi"
Yayi maganar a hankali, da bata kusa dashi ma ba lallai taji ba, ta kalleshi, ta tuna yanda ta dinga kwankwasa masa kofar nan shiru, wani abu ya taso ya tokare mata wuya
"Kan ba tsoranka yakeyi ba da zaka kulle daki kwana hudu bakaci komai ba kace ba zaiyi maka nauyi ba, ai so kayi ma kan ya gutsire ya fadi"
Baisan yanayin yanda tayi maganar bane ko hararar data maka masa cikin takaicin da yake gani a fuskarta koma maganarce ta