Advertisements
Chapter 42 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   42 / 51

123K to 126K   out of 151K words

da aka kwantar da Maryama, bacci takeyi har lokacin, sai Fa'iza da take zaune, ta rungume Awwab da shima yayi bacci

"Bata tashi ba?"

Ya tambayi Fa'iza

"A'a bacci takeyi, amman wata mai farin kaya tazo ta duba ta"

Ya jinjina kai yana ficewa, abubuwan da yake tunanin zasu bukata yaje ya sissiyo, tun daga kan ruwa da lemo, har da kayan marmari ya hado, ya kuma yo musu takeaway na abinci. Da yake Fa'iza ba yunwa takeji ba, saita ajiye abinda ya bata din, ta dai dauki ruwa roba daya ta fasa ta sha. Har dare suna asibitin, saida Alhaji Mustafa ya ga Maryama ta farka, tukunna yace ma Hajiya Rumana su tafi gida

"Ita da bata da lafiya, ku dai tafi, ku barni in kwana dashi"

Har ran Maryama taso ta kwana, taji dadin jikinta, daman rashin bacci ne yake dawainiya da ita, shima kuma Alhaji Mustafa sai yaga maganar Hajiya Rumanan akan gaskiya take, dan hakane ma ya saka su a gaba, bayan ya kwashe musu duk abinda ya siyo ya kai musu motar Maryaman

"Zaki iya tuki kuwa?"

Ta danyi murmushi

"Eh Baba, daman gajiya ce kawai, kuma ina samu nayi bacci na tashi shikenan"

Shima murmushin ya danyi mata

"Allaah Ya kara lafiya"

Ta amsa a hankali, harta bude murfin motar da su Fa'iza sun shiga baya ita da Awwab ya kira sunanta, ta juyo cike da ladabi a yanayinta

"Allaah Yayi miki albarka Maryama, sannu da kokari kinji, Nagode, bansan irin yanda zan furta godiyar dan ki gane girmanta kamar yanda nake nufi ba"

Tayi kasa da kanta kadan, kunya na lullubeta

"Allaah Ya kara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, Allaah Kuma ya shirya muku zuri'a. Allaah Ya kara miki hakuri da juriya"

Tanata amsawa a zuciyarta

"Ku tafi gida, dare yana karayi, a kula da hanya sosai kinji ko"

Kai ta jinjina

"In Shaa Allaah Baba. Allaah Ya kara lafiya"

Ya kara fadada murmushin shi

"Kiyi kwanciyarki tunda kinga shima da sauki, Doctor din yace withdrawal effects ne na abinda bai sha ba kwana biyu, ba wani abu bane ba, zai sake shi a hankali"

Zuciyar Maryama tayi wani tsallen murna, abinda bai sha ba, wiwi kenan, Haris bai sha ba na kwanakin nan shine abinda ya kwantar dashi, kamar hawayen farin ciki zasu zubo mata haka takeji

"In Shaa Allaah"

Ta fadi, tayi masa sallama ta shiga motar, bata gudu da mota, amman yau yanayin nishadin da takeji yasa ta dan taba, musamman da titin yake da saukin hada-hada saboda daren da yayi. Da suka karasa gida ta karbi Awwab taje ta kwantar dashi, Fa'iza ma sai da safe tayi mata, duk sunyi isha'i a asibiti, itama saita kwanta kawai, tanajin abinda ke cikinta nata motsi, ta dafa cikin tana murmushi

"Addu'a kake tayani? Allaah Ya shirya mahaifinku ko? Allaha Ya kara shirya shi Yasa ya daina duk abinda yakeyi"

Ya kuwa kara motsawa, sai tayi dariya mai sauti, kafin kuma ta furta

"Thank you"

Kamar Haris din yana gabanta, a karon farko ta dora da

"I love you"

Tanajin kalaman daban akan harshenta, kamar wasu baki, kamar wani abu da bata taba hasashen zata furta nan kusa ba, zata jira, har Haris ya dawo gida, zata rike shi a jikinta ta furta masa wadannan kalmomin, saboda zuwa yanzun itama tasan tana son Haris!


41

A LEAP

A kace lokaci na tafiya da komai, a wajen Maryama, zatace lokaci ya tafar mata da abubuwa masu tarin yawa, a cikin abubuwan nan akwai kuruciyarta, da yanzun inta kalli kanta sai tayita mamaki, itace fa, Mairaman Abba Sa'idu, ba kiba tayi ba, jikinta ya murje, irin murjewar nan da haihuwa inta hadu da hutu yake samarwa, kuma ko a yanzun idan zata kwana tana rantsewa wasu cewa shekarunta talatin da biyu, to haka wasu zasu rantse suna karyata cewar bata kai ba, musamman kuma ace an ganta tare da yaranta. Yaran da ake dauka biyu daga cikin hudun nan ne kawai nata, Awwab (Sa'id), Rauda (Rumana), Naadir (Mustafa), sai Aalim (Aminullah).

Haihuwar Rauda tazo mata da tarin alkhairi, tasan ra'ayin Haris ne ya barta a Najeriya, ya koma New York, kuma daya kammala karatunshi, lokacin business dinshi ya fara kafuwa, an fara gane motocin (HM Wheels), dan irin buses din nan ne masu kyau ake daukar fasinja tsakanin garuruwa, sannan yana da manyan motoci suma, a hankali yake tafiyar da HM Wheels, babu gaggawa a cikin lamarin, sannan duk wani aiki daya samu dangane da abinda ya karanta, kowacce kasa ce, yana tafiya

"Lokaci zai zo da in kika ganni a wata kasa, tare dakune gabaki daya da sunan hutu"

Tasan tazarar shekaru hudun data samu tsakanin Rauda da Naadir, Allaah Ne yaso ta da samun hutun, da kuma rashin zaman Haris din, yawanci lokacin da zaizo bama ta cikin abinda ake kira ovulation window dinta, bata kuma damu ba. Ta kula duk yanda take son yaranta, to Haris ya linkata sau babu adadi, a wadannan shekarun kallo daya zakayi masa kaga yanda sukazo masa da cigaba, bata fannin samu ba kawai, harda ma zama babban mutum. Kamar su duka suka hadu sukayi murjewar samun kwanciyar hankali, shi harda ma lafiya, kullum zata kalle shi sai taji kamar ta sake ce masa ta gode, ta gode daya watsar da wiwi, ta gode da yayi hakan kacokan saboda ita.

Dan wannan yana daya daga cikin abinda yayi mata da take yawan dubawa

"Kanshi fa ya taimakawa, ko da kece kikayi sanadi ya bari, kanshi ya taimakawa"

Haka Khairi tace mata, sai tayi murmushi kawai, to taya Khairi zata gane girman abin tunda babu soyayyar Haris cike fal da zuciyarta? Ita tasan ba kanshi kawai ya taimakawa ba a lokacin daya hakura da wiwi, harda ita, saboda bata shiryawa yin takaba ba, a cire batun doguwar jinyarshi a asibiti, bata shirya kallonshi cikin radadin ciwo ba, zuciyarta ba zata dauka ba. Sannan idan aka cireta, aka cire Haris a cikin lissafin nan, to ya taimakawa yaransu, ko babu komai yanzun bata da fargabar wata rana Awwab zai ga Haris da nadin wiwi a hannu, tunda ma yau da goben da ake cewa bata bar komai ba tana iya faruwa dasu.

Duk wanda zai shigo gidanta, ko bai furta ba, tana ganin yanda rayuwarta take burgeshi, wasu ma suna kasa hakuri, balle kuma idan sukayi katarin samun Haris a gidan, Haris da ko a wannan shekarun bayajin nauyin nuna mata kulawa, ko a gaban wanene, kuma ta tabbatar wannan kulawar na daya daga cikin dalilin da tarin shekarun nan ya kasa goge kiyayyar da Hajiya Rumana takeyi mata. Har zaunar dashi tayi tai masa magana sai ya kalleta kamar wanda tayiwa wani yare na daban

"Wacce irin kulawa?"

Dan da gaske ba zaice ya gane wacce irin kulawa take maganar ya rage nuna mata a gaban 'yan uwanshi ba

"Missing step kikayi, da kin fadi kin ji ciwo fa?"

Sunje gaishe da Hajiya Rumanan ne, wajen tashi saita take doguwar rigarta data sauka sosai, ta lankwashe yatsanta na kafa shisa ma ta runtsa ido tana kiran sunan Allaah, zafin ya ratsata har kwanya, batasan ya akayi ta ga Haris a gabanta ba, ya kama hannunta yana zaunar da ita akan kujera, ya kuma tsugunna ya kama rigar ya daga sama yana dora kafarta akan cinyarshi tare da dubawa

"Saida nace miki ki canza riga saboda sau biyu kina take wannan din, amman kikaqi ji"

Watakila Haris baiji tsakin da Hajiya Rumana ta zabga ba, amman akan kunnen Maryama, kuma hankalinshi duka yana kanta shisa baiga tashin da tayi ta bar musu falon ba, saboda yanda yake bin kafarta yanata latsewa

"Ban fadin ba, amman kaga ko babu komai akwai kunya a gaban Mami ace ka kama kafata kana murzawa"

Sai abin ya bashi dariya sosai

"Kafarki na murza fa, kafa, bawai..."

Duka takai masa a kafada ya kauce yana cigaba da dariya, in dai zatayi masa magana akan irin wannan, to a haka zai shiriritar da abin, har saida ta gaji ta dauki ido ta saka masa, ta kuma hakurewa zuciyarta akan tsanar da Hajiya Rumana tayi mata, haka su Munira, ko haihuwa sukayi idan ta kira da nufin musu barka basa daga wayarta, sai ta daina kira, in Haris ya kira dai yakan saka a speaker suyi gaisuwar jeka nayi ka, haka kuma duk haihuwa zataje har gida tayiwa Hajiya Rumana barka ko da bata samun tarbar arziki

"Ko naman jikinki zaki yanka ki dinga mata farfesu wannan bakar matar ba zata soki ba Maryama, ki tattarata kawai ki watsar, ke dai kyautatawa iya wadda zaki iya, yanda ba zaki takura ba, kiyi, saboda har abada, duk lalacewarta, mahaifiyar mijinki ce, karki manta Hajja bata gajiya da jadda mana taya mazajenmu kula da iyayensu, amman cikin bakaken yayyenshi, duk wadda ta gaya miki marar dadi kikaji ba zaki iya dauka ba ki rama"

Haka takeyi da, maganar duk da zasu fada mata in sunyi haduwa goma tana da amsa, idan a gaban Haris ne kuwa kafin ta amsa ma ya rigata, tare mata fada yakeyi kamar itace 'yar uwarshi basu ba, tasan wannan ma ya kara rura wutar tsanarta a cikin zukatansu, har mamakin yanda suka tsaneta amman kamar su lashe su Awwab takeyi. Tana zumuncinta da yaran Umma Fadime, har hutu yaransu na zuwa mata, kuma tayi kokari matuka a shekarun nan wajen ganin ta kara gyara alakar Haris dasu, hakama dangin mahaifinshi, lokaci bayan lokaci take saka shi suyi siyayya niki-niki su zagaya su gaishe su daya bayan daya, wani abu da ranar farko da sukayi, har gida Alhaji Mustafa yazo ya dinga saka mata albarka dayi mata godiya sai da taji kamar zata nutse don kunya.

Tana da karamin cikin Naadir ne ta fara zuwa Maiduguri, za'ayi taron 'yan uwane, na bangaren Hajiya Rumana, taron da shine na farko da ake fatan ya dorar da zumunci da ma wasu abubuwan masu yawa, dan haka har wadanda basa kasar sun halarta, taso tayi gardama, amman Haris yabi duk wata kofa da zata kawo yana toshewa

"Inaso inje tare dake Maryamm, dama su Awwab, inaso in akace ina matata, in amsa tare da nunaki..."

Cikin rauni tace masa

"Kasan har yau, Mami bata karbeni ba Ganja..."

Ya daga yatsunshi, ta matsa baya da sauri tana yin murmushi, tasan bakinta zai dille

"Ba zaki daina ba ko? Kirana da sunan nan"

Tace masa Baban Rauda ko Baban Awwab ya zabi daya, a lokacin suna kan gadone, dan haka ya kaita can karshe yana matseta tare da fadin

"Ni? Maryamm nine zaki kira wannan sunayen?"

Yanda yayi maganar hankalinshi a tashe ya bata dariya ba kadan ba, yaran Papa suke ce masa, ita kuma suna kiranta da Ammi, Papan ma sai yaji shi kamar wani tsoho. Babu tunanin da batayi ba, kafin a wani film din 'yan kasar Turkiyya da take kallo taji

"Saheb"

Sai yayi mata dadi, data duba ma'anar ma saita zauna mata, amman lokacin ta kasa sabawa, Ganja ya kama bakinta, lokaci zuwa lokaci sai taji ya subuce

"Muyi maganar gaskiya, Mami bata karbeni ba, kana zaton danginta zasu karbeni ne alhalin tana qina?"

Ya riko hannunta

"Shisa nake so inje dake, in nuna ma kowa cewar in zasu tara mutanen Maiduguri da kewayenta ba zasu canzani daga karbar da nayi miki ba..."

Kafin tace wani abin kuma ya rigata

"Kina tare dani, tsoron me kikeji Maryamm? Ko kina tunanin akwai wanda ya isa yayi miki ko da kallon da bai kwanta mun bane balle kuma ya fada miki wata magana in barshi?"

Abinda take tsoro kenan, Haris yaje yana fada da 'yan uwanshi akanta. Tasan abune da mata da yawa zasu dauka soyayya ce da kuma samun gata a wajen miji, sai dai bakowanne fada bane idan miji ya tare maka yake zame maka maslaha, babu abinda wannan halin na Haris yake ja mata sai karin tsana, kuma ko zasu kwana tanayi masa bayani ba zai taba fahimtarta ba

"Tunda sai jibi zamu tafi, zanje gidan Khairi gobe idan Allaah Ya kaimu"

Yaja girar sama data kasa ya hade waje daya. AnO abinda baya kauna, fita idan bashine ya kirkirar musu ba, sai ankai ruwa rana yake barinta. Har yau din nan 'yan uwanta gani sukeyi itace batason makaranta shisa bata koma ba, itace taki yin dabarun mata tasa Haris ya barta ta cigaba da karatunta. Amman ita da take zaune dashi tasan cewa sai dai in anayi a Aljanna, ko Islamiyyar matan aure da taso shiga, sai yaje har makarantar ya samo Malama da zata dinga zuwa gida tana karantar da ita, da yake tasan muhimmancin karatun haka ta hakura, Malama Fatima take zuwa sau biyu a sati. Bata ma san ta yanda zatayiwa kowa bayanin tsananin Haris akan fita ba, sai dai ko idan matan da suke auren mazaje masu kulle irinshi ne zasu zauna su tattauna, su kadai tasan zasu fuskance ta.

Tunda Hajja ma ta kasa hakuri ta taba ce mata

"Saifa kin dage Maryama, sai kin nunawa mijinki muhimmancin 'yan uwanki, saikin nuna masa ba kowanne abu bane kudi zaiyi maka, ko baya gari ko da yaushe, ai ba zai rasa ganin yanda 'yan uwanki suke tsayawa akan duk wani abu naki da zai taso ba, sai kice ke ba zaki kamanta musu ba saboda ya hanaki zuwa? In hidimar nashi dangin ne na tabbata da rawar jiki yake barinki kije ai"

Haka tace

"In Shaa Allaah zan kara kokartawa Hajja, kiyi hakuri"

Dan ko ta tsaya bayani ma batasan kalaman da zatayi amfani dasu ba, me zatace? In ta gayawa Hajja a sha'anin nashi 'yan uwan ma haka yakeyi mata zata yarda? To yama zatayi da Haris tunda ya fita taurin kai, kuma ko da ta gwada masa nata taurin kan zata fitane bada izininshi ba? Hankalinta ya dan kwantane, dan tasan Hajja tayiwa Alhaji Sa'id maganar ne shisa ya kirata ya kwantar mata da hankali cikin tausasan kalamanshi

"Tsakaninmu dake yanzun kyautatawa ce, amman babu mai cikakken iko akanki sama da mijinki, kuma bin umarninshi in har bai sabawa shari'a ba, kiyi hakuri akai kinji ko? In ya barki kije sha'anin 'yan uwanki, idan bai barki ba kiyi hakuri"

Suka kara wayar yanata saka mata albarka. Koya zata shiga wani matsi na rayuwa in dai zatayi magana da Abbanta sai taji ta samu sauki da salama, kamar babu wani wanda yake da kalaman da suke nutsar da ita kamarshi, shisa bata gauraya soyayyar da takeyi masa da komai ba, kuma tana alfahari da biyayyar da tayi masa akan auren Haris.

*

Haka suka isa Maiduguri, daga Awwab har Rauda suna ganin Hajiya Rumana suka tafi wajenta, daga nan ita batama kara sakasu a ido ba, ta dinga jin wani iri ganin daki daya suka sauka da Haris a wani irin katafaren gida

"Wai nan zan kwana nima? Daki daya da kai?"

Da mamaki ya kalleta

"Ina zaki kwana to in ba tare dani ba?"

Har ranta taji hankalinta ya tashi, so take yanda suka sauka lafiya su koma lafiya. Saida Haris din yayi mata bayanin cewa ai kowa in dai da matarshi yazo to daki daya ake basu tukunna hankalinta ya dan kwanta, a fuska dai babu wanda ya nuna mata wani abu, amman a darare take, tunda bayan gaisawar data dingayi da mutanen da bata koyi kokarin kiyasta yawansu ba, yara da manya, maganar da suke tayi da yarensu na Kanuri sukeyi, sai dai taga ana dariya, Haris ma da bai cika mayarwa ba, ranar idan sukayi masa mayar musu yakeyi, su Awwab ma zama da Hajiya Rumana yasa sunaji sosai, ga Awwab dai zaune kusa da ita, amman bai hanata jinta daban a cikinsu ba.

Ko da wasu ba 'yan uwa bane ba, sai taga kowa najin yaren, ko koya sukayi bayan auren bata sani ba, amman dai tabbas a ranar taji babu dadi. Karshe ta mayar da hankalinta kan wayarta kawai, da yake Haris da Awwab tsakiya suka sakata, sai da aka kawo abincine Awwab yabar wajenta, yanayin gyara zaman Haris taji, sai kuma hannunta daya kama ya rike, riko bana wasa ba. Ta daga ido dan taga abinda ya sauya masa yanayi lokaci daya, kirjinta ya buga, ya sake bugawa, kafin ya kwaso wasu ganguna da ba zatace ga kalar kidan daya farayi mata ba, aiko a mafarkinta akayi taron mata, fuskar Aise ba zata bace mata ba. Wannan bakar fuskar ta Aise da take sheki a wancen lokacin, yanzun dinma take shekin cikin kwalliyar da ta zauna mata das ba zata taba bace mata ba.

Aise da har yanzun in dai zata riko hannun Haris sai taji wani abu ya daki zuciyarta, saboda sunanta da yake rubuce jikin karamin dan yatsanshi, cikin jikinta daya nuna cikin shigar riga da wandon da tayi na wani material pink mai duhu bai hanata yin kyau ba, sai kuma daurin da tayi ta dan turashi baya har kana ganin gyaran gashinta, da wasu manyan dankunne masu circle na silver da suka kara haska kwalliyar da tayi. Wani abu ya daki zuciyar Maryama lokacin da Aise ta karaso inda suke zaune tana budewa Haris abinda Maryama take tunanin shi kadaine mai haske a tare da ita, wato hakoranta

"Kai baka zumunci da mutane ko?"

Ta fadi cikin yaren Kanuri, batasan ya gawa take ba, amman yanda hannun Haris yayi mata kamar katako a cikin nata sai taji kamar ta rike hannun gawa, ta dan kalle shi, sai taga yayi karamin murmushi

"Aise"

Ya kira, kalma daya, kalma daya tak, amman yanayin yanda ya furta kalmar sai ya tuno mata da wani scene a wani series film da ta kalla mai suna the originals, anan ne taji ance jini na tafasa, to duk wani jini da yake yawo a jikinta ne yake tafasa

"Maryamm...matata Maryamm"

Ya fadi yana nuna mata Maryaman, kafin ya dan kalli Maryama yana cewa

"Aise...my cousin"

Saida tayi kokari matuka sannan ta cewa Aise din

"Sannu"

Ta kasa mika hannu ta karbi na Aise din data miko mata, dan gani tayi kamar da gayya ta ware mata yatsanta taga sunan Haris da yake ciki, kuma zuciyarta nace mata meye wani aure Maryama? Meye auren balle kuma yara biyu da cikin na uku? Kinsan babu abinda wannan garun budus din zata diba a jikinki, kafin wani cikin 'yan uwanta yayi wani yunkuri kin kaita kasa kin tsige yatsan kin jefa a jaka. Watakila Haris yaji sautin duk wani tunani nata shisa ya gyara zamanshi yana kara dumtsa hannunta, lokacin ne kuma Awwab ya dawo wajen hannunshi rike da plates guda biyu

"Ammi karbi dan Allaah akwai zafi"

Yake fadi yana mika mata guda daya, dan baima kula da Aise ba sai bayan ya zauna, lokacin

42 / 51