Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
da zasuyi mata, tasan mazan gidansu zasu dinga ware lokacin da zasuje har kabarinta suyi mata addu'a.
Tun a waya take fadawa Haris maganar bikin
"Aikuwa zan kirata, yanzun ma dan nasan dare yayi su acan, Allaah Ya kaimu lokacin, gaskiya bikin nan na musamman ne, kibari idan na dawo mu zauna mu fara tsara gudummuwar da zamu bayar ko?"
Anya tunda tazo kasar New York tayi farin ciki irin na ranar? Da Haris yazo kuwa da gudunta ta tarbeshi da runguma, dan ta riga Awwab din da yake ta kiran
"Appa..."
Ya kuwa ji dadi, dan saida ya dan cirata sama ya sumbaci fuskarta sannan ya sauketa ya dauki Awwab
"Nayi kewarku, sosai..."
Kwananshi biyar
"Muma haka, gidan yayi shiru"
Da Awwab din a hannunshi ya dan rage tsayi ya sumbaci cikinta yana dagowa ya shafa shi, ta danyi tumbi haihuwar Awwab, tunda Adda Zahra tace mata inta gasa sosai da ruwan zafi wajen wanka ta dinga daurewa, yanda taga anyiwa Adda Maimunatu lokacin data haihu, akwai zafi dai, haka ta daure
"In dai ba so kike kiyi dirkeken ciki ba, kuma ki kiyayi abubuwan sanyi aqalla har kiyi arba'in"
Sai batayi dirkeken cikin da take tsoro ba
"Har yanzun bai fara nunawa ba, wannan ba kamar na Awwab ba"
Dan shi ya nuna da wuri, ta danyi murmushi tana shafa dan tumbin nata ta cikin rigar da take sanye da ita, watakila yau farin cikin da takeji ne yasa taji kaunar abinda yake cikin yana ratsata a hankali
"Zan sha shayi"
Ya fadi, babu bata lokaci kuma ta hada masa shayin
"Muna da zuwa asibiti jibi"
Kai ya daga mata, yanata kokari, wannan karin, duk wani follow up da aka nemi suje baya kiyawa, bayajin dadin yanda in dai zai jijijjiga jikinshi tari yake kamashi. Haka kuma tun fitowarshi asibiti bai sake shan wiwi a cikin gidan ba, ba dainawa yayi ba, ko ragewa, kawai yana boyewa Maryama ne. Saida suka kwanta tukunna take ce masa
"Kaga tafiyar da zamuyi cikin May ne, bikin Adda Khairi kuma June akasa karshe, sai mu bari sai cikin June din"
Ya gyara mata kwanciya a jikinshi
"June, lokacin cikinki wata shida, ina zakije da tsohon ciki Maryamm? Ai daman nabari saikin haihu ne, dan nima zaifi mun dai-dai, akwai tafiyar da zanyi October, lokacin kin haihu, idan mukaje na ajiyeku sai in wuce, sanda zan gama komai ba sai in dawo mu tafi ba, watakila sati uku haka zanyi, kinga kowa, kowa ya ganku ko?"
Wani abune takejin yana tasowa tun daga bangarorin jikinta yana haduwa a cikin kirjinta inda yayi dunqule yake tokare mata numfashi
"Bangane ba, kana nufin ba zamuje ba?"
Ya girgiza mata kai
"Zamuje mana, amman saikin haihu"
Cewar Haris
"Bikin Adda Khairin fa? Kana nufin ba zanje ba? Kana nufin saina kara kusan wata bakwai a kasar nan banje gida ba...shekara hudu fa kenan, banga kowa nawa ba? Shekara hudu Ganja..."
Ta karasa tana zame jikinta ta tashi zaune
"Shisa nace ai zan kaiku sai in wuce, Japan zanje"
Cikin bacin rai tace
"Ina ruwana ko China zakaje, ni kawai gida nake so, ka mayar dani gida, duk inda zakaje sai kaje"
Batare daya tashi ba shi, dan kara gyara kwanciya ma yayi yace mata
"Zan kaiki, zamuje, da kin haihu"
Aikuwa ta birkice masa
"Nawa ne kudin jirgi? Ina da kudina, tafiya zanyi, kasan Allaah ba zan zauna ba, ya zan siyi ticket?"
Taso ta bashi dariya
"Ke kadai zaki tafi amman dai ko? Dan babu inda zakije mun da yara"
Ta daga kai tana kokarin shanye hawayen da saida suka zubo mata
"Saiku zauna"
In dai Awwab ne, ai Allaah bai dora mata qulafacinshi ba, ko dan yanda ya mayar da dauke yaran ya fice dashi wata hanya ta kuntata mata, saita samawa kanta sauki, inta tafinma sai tayi zamanta, sanda ya gama karatun sai su tattaro su taho shi da Awwab din
"Hakanma yayi, ga Awwab, saiki zauna ki haifi na cikinki ki hada kibarmun su"
Da wani yanayi a muryarta tace
"Ganjaa"
Shima ya amsa da
"Na'am Maryamm"
Kawai saita fashe da kuka ganin yana murmushi, ta tashi ta fice daga dakin ta koma falo, ya kuwa bita falon, batare da yayi mata magana ba ya sungumeta, yakushi, kai duka babu wanda batayi ba, amman ya sake saka karfi ya riketa har dakin
"Ni zaki tashi ki barwa daki Maryamm? Ni zakiyiwa fushi, ina ruwan kwanciyarmu daki daya da fushinki?"
Tayi kuka ba dan kadan ba a daren nan, da safe ba zatace ga abinda taje dauka ba, a cikin drawer din da passport dinta yake, tun zuwanta yana wajen, amman da safiyar ranar baya nan, ta girgiza kai, hawayenta sunma kafe saboda yawan kukan da tayi jiya, Haris ne ya dauke, shi ya canza masa waje kamar mai tsoron da gaske zata hada kaya ya nemeta ya rasa, inda zata iya hakan, ai da ta jima da guduwa gida. Yanda duk yayi mata magana bata kula shi ba, daya gama abinda zaiyi ya fita, ta kira Khairi sai kawai ta rushe mata da kuka
"Wai ba zamu zo ba, ba zanzo bikinki ba Adda Khairi, ni duk wani biki da na rasa da wanda ma zan rasa wallahi in dai nazo naki ba zai dameni ba, wai saina haihu zamu zo, mun fasa...."
Kamar Khairi bataji komai ba sai maganar haihuwar tace
"Ciki gareki Maryama? Wani cikin?"
Jin dokin da yake muryar Khairi yasa Maryama kara rushewa da kuka
"Wai bakiji me nace ba? Bafa zanzo bikinki ba"
Amman sai Khairin tayi dariya
"Bikine fa kawai, kinsan banda kamu babu abinda za'ayi, zan saka a dinga turo miki hotuna da video sai kinji kamar kina nan, zan kuma ajiye miki ankonki, da kayan da zamu saka tare, ba zansa ba saikin zo, sai ayi mana sabon lalle da make up, muyi walimar haihuwar Awwab, muyi walimar bikina mu kuma yi walimar sabon baby..."
Duk yanda Khairi taso ta kwantar mata da hankali fur taki, saima ta kashe wayar kawai, ita ba bikin bane kadai, haihuwar da zata sakeyi ita kadai a kasar nan, yanda zata kara wasu watanni da take hangowa kamar shekaru batare da taga kowa nata ba shine damuwar. Wani abune ya taru a kirjinta ya danne, ta rasa yanda zatayi masa, kuma duk kokarin da Haris yayi wajen ganin ta sake ta kasa, duk maganar da zaiyi mata zata amsa da
"Eh..."
Ko kuma
"A'a"
Haka a shimfida duk abinda zaiyi mata ko motsin kirki batayi
"Dan Allaah meye haka Maryamm? Wai duk akan zuwa gidan ne? Na fada miki zamuje fa, Allaah zamuje, sai in barki ma kiyi wata daya..."
Amman batace masa komai ba, bata ko motsa ba, ita da zaiyi abinda zaiyi ya kyaleta ya fiye mata surutun da yakeyi mata, ba zai gane yanda takeji bane ba, ba zai gane yanda komai ma ya fice mata a rai ba, ciki harda zuwa gidan, su cigaba da zama kawai har randa zai gama su tattara su tafi gabaki daya, me wata daya zaiyi mata? Tun Haris na lallashinta har shima ya dauki fushi, sai zaman gidan nasu ya koma wani iri, Awwab ma a zuwan da yayi ya samu tana kwance akan kujera yayi bacci a kasa, kan kafet, ga sanyi anayi shikuma babu wani kayan sanyi a jikinshi baiyi mata magana ba, baice mata komai ba, ya dauke shi yayi daki dashi.
Washegari ya sama masa wani day care centre nan kusa da unguwar da suke, sai bayan ya dawo yake fada mata, da yamma ya sakata a gaba saida ta tashi sukaje suka dauko Awwab din
"Zaki dinga kaishi da safe, sai kije ki dauko shi da yamma, watakila zaki samu ko kanki ne ki kula dashi na wani lokaci"
Ya fadi wani abu na masa tsaye a wuya. Ya dauka zata iya zama dashi, ko da shekara goma zasuyi a kasar New York kuwa, amman kalli yanda ta birkice gabaki daya dan ya daga lokacin tafiyarsu, in ya zauna yana ganinta ranshi yakeji yana baci, kamar kawai yace mata sun fasa zuwa, in sun taka Nigeria to ya gama duk wani abu da zaiyi ne a New York sai yaga yanda zatayi, amman cikin jikinta, da yanda akace jininta ya danyi sama a zuwansu asibiti shine yake danne shi, kuma inda zai iya, inya tafiyarshi sai yayi satika bata ganshi ba, to kasawa yakeyi, duk wasu mata, duk girman nadin wiwin da zaiyi tana nan makale a kanshi, ya take, ta tashi taci abinci? Ya zaiyi ta dawo masa dai-dai, ko gida zai kira ya fada musu suyi mata magana, tunda ai suna waya da Alhaji Sa'id, yana kira ya gaishe dashi.
Gabaki daya ya rasa yanda zaiyi da Maryama, sai dai bashi bane ya fadawa Alhaji Sa'id, Khairi ce, kuma ranar duk wani kokari da Maryama takeyi in tana magana dasu sai ya barbade yabi iska lokacin da Alhaji Sa'id yace
"Haba Mairaman Abba, kin manta girman da nace ya hau kanki yanzun ne? Kin manta maganar da mukayi? Bayanin da nayi miki? In ba auren ba meye zai rabamu dake, balle har ya kaiki wata kasar?"
Kuka takeyi, irin kukan nan mai sauti, kukan da takejin yana warware wannan abin mai kama da ball da yake tokare a cikin kirjinta.
"Zanzo, In Shaa Allaah zanzo in ganki, kiyi hakuri kinji"
Ta daga kanta
"Ai nafiso ki bude bakinki inji da gaske kin hakura, maganar ta wuce"
Cikin kuka tace
"Na hakura Abba, na hakura"
Tanajin ya sauke ajiyar zuciya
"Allaah Yayi miki albarka"
Tana share hawayenta da hannu tace
"Yaushe zaka zo"
Ya amsa da
"Zanyi kokari inzo a kafin watan nan ya kare, In Shaa Allaah...."
Sai lokacin taji wani sanyi ya ratsata, lokacin da ta sauke wayar kuma, kuka ta sakeyi sosai, taji ta sakayau, nauyin nan ya warware, ta tashi taje ta wanke fuskarta, an kusan yin azahar, da ta dauro alwala saita dauki Qur'aninta, ta zauna akan dardumar, abinda ta kwana biyu batayi ba, ba karamin sanyi ta karaji ba. Bayan ta idar da sallah ne ta kira Khairi, sukayi hira kamar yanda suka saba, sai gata tana ta dariya
"Ko kefa, Allaah Ya kara miki hakuri kanwata ta kaina"
Maryama ta kwashe da dariya
"Ai yanzun nice babba ingaya miki, harda ni a masu yi miki nasiha in aka daura miki aure"
Ba karamar dariya Khairi tasha ba
"Ina mijinki? Yama kirani fa yake mun Allaah Yasa alkhairi, yake cewa kinata rigima saboda zakuyi missing din biki"
Taji zuciyarta ta dan doka, ita yau kira nawa ma Haris din ya jera mata bata dauka ba, kwana nawa yana kiranta bata dagawa
"Bama fa magana mukeyi ba sosai, Allaah naji haushin rashin zuwan..."
Cikin sanyin murya Khairi tace
"Shine kikayi masa halin, kika saka shi a gaba da rigima"
Kai ta girgiza, ta fadama Khairi iya abinda zata iya, abinda take ganin ya kamata
"Ai ba'a haka, fadan da kikasan zakiyi nasara shi zakiyi Maryama, dake wata ce ma da ba sai in baki shawara ba"
Tana 'yar dariya tace
"Shawarar me"
Maryama ta dinga tuntsira dariya tana karawa
"A wanne film kika ga anyi haka?"
Haka tace wai tabi Haris makarantarsu, ta dafa abubuwa kala-kala taje ta kai masa, tayi surprising dinshi
"Ke banza ce wallahi, ana koya miki 'yar soyayyar nan, ba kinsan inda yake zaune ba..."
Ta sani, bata taba zuwa ba amman har lambar gidan da Haris yake a kusa da makarantar ta sani, in ma ba zatayi karya ba zatace a cikin kanta ta hasaso yanda dakin nan nashi yake yafi a kirga, yace mata su hudu ne suke zaune a gidan, har sunan layin da komai ta sani, amman Haris da abinci bai dame shi ba, me zata dafa ta kai masa? Ita da suke fada ma, sai ta kwashi kafa taje? Ita da kafin ya tafi saida yayi mata kashedin banda kai Awwab day care da dauko shi karta je ko ina.
"Bafa abinci yake ci ba, na fada miki kaman aljani haka yake, baya shiri da abinci ko kadan, sannan ni da nace miki muna fada, yama kirani yau sau nawa ban dauka ba..."
Amman Khairi ta dinga tsarata, ta dinga fada mata dalilan da yasa zataje, tasan yanzun da zuciyarta tayi sanyi, yanzun da takejin kamar tayi masa abubuwan da basu kamata ba, yanzun ne in ya kula da ta huce zai tisa nashi, watakila zaiyi mata tashin hankalin da bata taba tunani ba, haka ta cewa Khairi zatayi shawara, a yanda Haris yace mata, tafiyar awa uku da rabi ce take kaishi makaranta, batasan dalilin da yasa ya kama musu gida a wannan unguwar ba inda nisa haka, bata tambaya ba tunda tasan babu amfanin da amsar zatayi mata, kuma ba zata canza masa ra'ayi ba tunda nan din yake so su zauna.
Da yamma da ta dauko Awwab, sai suka tsaya da Chloe, take ce mata ko zata dauko mata Awwab gobe daga day care, tana so tayi surprising din Haris ne, ta gandara mata karya kan cewa anniversary dinsu ne ranar, tunda tasan turawa da girmama irin abubuwan nan, aikuwa ta dinga washe baki tana musu fatan alkhairi, tace mata zata dauko shi, inma kwana zatayi babu damuwa zata kula da Awwab din. Haka ta koma gida ta kwanta da wani irin bugun zuciya, washegari da safe da Haris ya kira ta daga
"Kina neman rigima dani Maryamm, bakya ganin kokarin da nakeyi nakin biye miki ko?"
A hankali tace
"Kayi hakuri, inaso zan fita"
Ya danyi wani murmushi da ta tabbatar da sautin shi na takaici ne
"Shisa kika daga kirana, to ba zakije ba, karki fita ko'ina"
Jin kamar zai kashe kiran yasa ta fadin
"Dan Allaah, dan Allaah, karka kashe, dan Allaah yau daya dai, kayi mun alfarma"
Yayi shiru sosai
"Karki dade, kisaka facemask dinki...dan Allaah ki kula sosai"
Da sauri tace
"In Shaa Allaah..."
Sai kuma yace
"Wai ina ma zakije?"
Ita kuma ta amsa da wata tambayar
"Kuna da lectures da yawa yau? Ko kun fara exams din? Kamar kace zaku fara exams ko?"
Ya danyi shiru
"Yeah, bamu fara ba tukunna, ina gidama all day, zan dan rage aiki, sannan ina da assignments da yawa, duk zanyi su..."
Dan biye masa tayi sukayi hira, sai ta karajin kwarin gwiwar zuwa, tunda yana gida, haka ta shirya, tayi kwalliya mai sauki, humrar da take so tayi amfani da ita, saita jefa a jaka, ta kara extra kaya, in taje caj saita shafa kafin ta shiga gidan, tunda tana da karfi sosai, kuma tasan haramcin dake cikin ta tana baza kamshi. Zuciyarta sai bugawa takeyi, ta dauka doki ne, ko kuma taradaddin fita ita kadai
Bata san bugun na kashedi bane,
Nason kareta daga dayan Labulen da yake lullube da rayuwar Haris da zuwanta zai daga mata...
35
Lokacin data kwankwasa kofar nan, bugunta ya koma kunnuwanta ne tare dana zuciyarta, tayi sau daya, sau biyu, saita dagata jin alamun taku, wani matashin saurayine da kai tsaye ba zata auna yawan shekarunshi ba ya bude mata kofar, fari tas dashi harda wani caki-caki a fuskarshi, ya dan runtsa idanuwanshi, alamar hasken yayi masa yawa, Maryama taga yanda ya dafe kanshi yana furta
"Damn..."
Sannan ya dan bude idanuwanshi kadan yana kallonta
"Haris, I'm looking for Haris please"
Ta fadi, da kunyar yin turanci takeyi inta fita, sai taga kamar yanda suke lankwasa harshe inta bude baki tayi nata na 'yan Nigeria za'a sheke da dariya, sai a hankali taga babu wanda ma ya damu da yanda take turancinta, itace ma kafin ta saba, ta dinga tattara duka hankalinta ne wajen ganin ta fahimci abinda suke fada, da hannunshi ya nuna mata alamar ciki, sannan ya matsa mata, ta shiga da sallama a hankali, taga inda suke cire takalma, sai kawai ta cire nata anan, falone matsakaici, ya danfi na gidansu girma, ganin ta dan daburce yasa ya nuna mata kofar dakin Haris din, ya koma kan doguwar kujerar da take da fadi sosai, ya kwanta ruf da ciki da alamar bacci zai koma.
Takun da ya sadata da kofar dakin daga inda take bai wuce guda takwas zuwa tara ba, bugun zuciyarta ya dan tsagaita mata jin wani irin sauti da kamar daga dakin yake fitowa, ta daga hannu zata kwankwasa ne, taji ta kasa, ta kara matsawa kamar mai shirin shigewa cikin kofar, data dora hannunta jikin handle din ta murda, sai taji kofar ta bude, alamar babu mukulli daga ciki, ita har fentin dakin nan tasa hasashen bakine, tunda dakin Haris ne, inda suke ma kamar wallpaper ne ba fenti ba, in fentinne to an danyi masa wani ratsin kwalliyane ma golden mai kamar walqiya, yayi mata kyau shisa ma batayi masa mitar bakin ba.
Baki na da abinda bature yake kira da shade, akwai baki mai haske, akwai baki mai ratsi-ratsi, ko a bakaken mutane sun rabune kashi-kashi, sannan ko a cikin duhun dare, bakin yakan bambanta ne da yanayin lokaci, amman tunda Maryama take a duniya bata taba sanin akwai abinda inta kira da baki kamar batayiwa kalmar adalci ba sai da ta tura kofar nan, ta taka kafarta tana shiga da sallama, ta kalli Haris, kwance akan gadonshi, kwance cikin yanayin da in tace zata lissafa sau nawa ta ganshi a ciki ba zata iya ba, jikinshin nan, bakar fatarshi da inta hadu da wani kalar zanin gadon da take shimfidawa sai ta jima tana kallonta, farin zanin gado saiya kara masa baki, sai kuma ta dinga mamaki idan yanayin yayi mata kyau, ruwan toka kuma saiya hadu da kalar jikin nashi ya bada wani launi da Maryama take maraba dashi duk safiya.
Haris dai, amman yau kalar tashi ce ta hade mata da ta farar baturiyar da take samanshi dare-dare, samanshi, babu komai a jikinta, hannuwanta duka biyun dafe da kirjinshi, nashi kuma akanta kamar mai bata tallafi, yanayine da yake so, yanayi ne da tasan ta gaza masa a darare da yawa saboda yanda yake gajiyar da ita. Batasan me sukaji ba, karar budewar kofar? Takunta? Ko karar wani abu da ya rushe a cikin kirjinta takejin duminshi yana bin kafafuwanta, idanuwanshi Haris ya fara sakawa cikin nata, idanuwanshi da suka sake launi, kuma yanda yayi motsine yasa ta kalli abinda yakeyi, yarinyar dake kanshi ya ture
"Maryamm"
Sai sautin ya shiga kunnenta kamar mashi, ya kuma yi nasarar toshe mata karasawar wani sautin bayan wannan kiran da yayi mata, ta daiso ace yanda jin nata ya dauke ganinta ma yayi mata wannan taimakon, bata ga sanda ya maida kayanshi ba, sanda yayi wa budurwar nan magana, taga tayi mata wani kallo, sannan ta dauki rigar da Haris ya jefa mata ta saka a jikinta, ta kuma saka wani dan karamin wando, Maryama ta kalli rigar, ruwan tokace mai duhu, rigar Haris ce, rigarshi ce da ta zaba da hannunta,