Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
mata mari, haka ta shanye da murmushin da bai kai zuciyarta ba. Data sake komawa kuma ko ruwa Hajiya Rumana batayi mata tayi ba, asalima haka tace mata zata kwanta saboda kanta yana ciwo tasha magani. Data tambayi lambar Anisa, kamar ba zata bata ba, sai kuma ta bata lambar sannan ta tafi, sai gashi kuma tasu tazo daya da Anisar matuka
"Kamar in miki karya, ince saboda muyi zumunci na karbi lambarki ba saboda Haris ba..."
Dariya Anisa tayi sosai
"You messed him up Aise, sosai...zanyi entertaining wannan maganar takine kawai saboda bana son wannan matar tashi"
A wajen Anisa ta samu lambar Haris, amman kamar layin nashi yana kan tsarin da in dai bashi da lambarka ba zaka iya kiranshi ka samu ba, saita dinga tura masa sakon text, ta dubashi baya kan kowanne social media, har Facebook saida ta duba, banda kamfaninshi da ta tabbatar bashi yake kula da accounts din ba, a Snapchat dai ta ganshi, tayi adding amman baiyi adding dinta back ba, sannan profile dinshi hoton Maryama ne, duk da ba fuskarta bace gabaki daya, rabin fuska ne, itace, a black and white, zuciyarta ta dinga bugawa da wani irin yanayi mai wahala. Ta dinga tunanin inda tayi hakuri a wancen lokacin, data bashi lokaci kamar yanda ya bukata, da ta basu chance, watakila da Maryama bata samu wannan matsayin ba, kilanma da inta shiga zata samu ta fitar da ita.
Kawai batasan Haris yaga duka sakonnin da take tura masa ba, tunda ya bude na farkon yaga itace sai yake gogewa batare daya karanta bama, daga karshe ma sai yayi blocking lambarta, ko data tura sakon ba zaije masa ba. Ba karamin mamaki tayi na yanda ya tarbeta wajen bikin Fa'iza ba, taji dadi, ta dinga murna, su Anisa na tayata, duk kuwa da zagin da suka sha a wajen Hajiya Rumana tana kara jaddada musu
"Aiko babu mata a duniyar nan Haris ba zai auri Aise ba, wallahi daya aureta gara inta ganinshi da Maryama zuciyata nayi mun baki, abinda Modu ya manta ne kawai bai fadamun ba sai kace 'yar gwal, ya dauketa ya bawa wani, sai yanzun data zama saura ne zata dawo? To me zaiyi da ita? Me ma zaiyi da wata macen tunda bai saki waccen yarinyar ba sanda naso, ai sai suje suyita zama"
Amman abinda su Anisa suka yanke shine, Hajiya Rumana ta rissina akan auren Haris da Maryama, ba zata taba fada bane ba, su kuma zukatansu sun kasa hakura, musamman yanda suke tunanin Maryaman nayi musu wani gani gani, shisa gara su hadu da Aise din su kunsa mata bakin ciki.
"Ina sonka Haris...ina so ka sake bamu dama"
Haka ta fada masa, sai kawai ya kwashe da dariya yana girgiza kanshi, saima ya mike ya fice yana barinta a office din, ganin ya shafe wajen mintina talatin tasan cewa ba dawowa zaiyi ba. Dan motarshi ya shiga ya kama hanyar gida, inda Aise tasan yanda ranshi yake baci duk ganin da zaiyi mata data daina nuna masa fuskarta. Duk wani bacin rai da bai samu ya amayar bane a tsayin shekarun yake taso masa inya ganta. Yara biyu ta haifawa wani, wani daban, shine zata dawo masa? Sai yanzun? To yayi mata me?
"Kinsan ya akayi na samu na raba kaina dake Aise? Saida na rasa kaina a wajen kokarin mantaki da tunanin kina tare da wani...ki taimaka mana ki daina zuwa wajena, ki daina damuna...ba zan iya ba, ko meye kike so dani ba zan iya ba"
Ya fada mata satika biyu da suka wuce, da yake a tsaye yake a cikin ofishinshi, saita mike itama, da murmushi a fuskarta
"Ka fadi abubuwa da yawa, amman babu inda kace ka daina sona, baka sona..."
Ya girgiza mata kai
"Aise..."
Ya furta a hankali, ko giya yake sha ba zaice baya son Aise ba, ganinta da yake yawanyi na tasar masa da kwantattun abubuwa ne da yakeji a game da ita, son da yayiwa Aise, yakeyi mata irin soyayyar nan ce da zuciya take budar ido da ita, soyayyar da bata bukatar wani dalili, rana daya ta gifta ta gabanshi, wani kaso na zuciyarshi ya kwace ya bita, sai ace so so ne, amman kuma shi gashi son da yakeyi wa Aise, idan ya kalli Maryama ba irinshi yakeji ba. A ranar da yake kallon Aise yana iya hango sanda ya fara sonta da lokacin da ya sakawa soyayyar burki, yana iya tuna yanayin da zuciyarshi ta karye, halin daya shiga, duk babu abinda ya manta.
Maryama, soyayyar da yakeyi mata tana da dalilai da yawa, dalilan da in aka tsareshi ba zai iya lissafosu ba, yasan dai ba lokaci daya yaji yana sonta ba, soyayya ce da lokaci yake samarwa, irin soyayyar nan mai hade da shakuwa, soyayyar da yanayi yake kara mata yawa, soyayyar da yaji kamar tana hade ne da zaman lafiyarshi lokacin da ta barshi a Ingila, soyayyar da yake hango tsayawar rayuwarshi cak idan ya rasata. Soyayyar da tasa Maryama ta dinga gifta masa a ranar, ranar da Aise ta taka gab dashi har yanajin dumin numfashinta saman fuskarshi saboda dogayen takalma ne a kafarta
"Na rabani da kai, dan Allaah....dan Allaah karka rabani da kanka a karo na biyu...ban jure ba daga farko, ba zan iya ba yanzun ma"
Ta karasa maganar muryarta na rawa, tana kuma daga hannayenta ta dora akan kafadunshi. Idan akwai wani abu daya da Haris yake jinjinawa kanshi akai shine irin yanda yake iya mallakar kanshi akan mata, duk kuwa da soyayyar da yakeyi musu, komai nasu kyau yakeyi masa, yana kuma so yaji su a jikinshi, amman ba kowacce mace yakebi ba, yanzun da yake ta kokarin bari ma ya kara takaita yawan wadannan matan, sannan in bashi da kanshi yayo ra'ayin yabi mace ba, babu wani abu da zatayi ta ja hankalinshi, ko da zata cire kayanta ne tayi tsaye kuwa zai iya mallakar kanshi, amman Aise ba kowacce mace ba, Aise ko a baya ba karamin kokari yakeyi na ganin baiyi losing control dinshi akanta ba, a lokacin yana hango koma menene zai iya jira, shi da zai kare sauran rayuwarshi da ita, saurin me yakeyi.
Amman yanzun ko idanuwanshi ya rufe baya hango wajen zamanta a cikin rayuwarshi, yana sonta, amman ba zai iya ba
"Ganjaa..."
Maryama tace masa
"Idan aure kake so, ka kara aurenka, ba zan baka matsala ba In Shaa Allaah, zanyi kokari, zanyi kokari sosai, kawai kayi mun alfarma karka hadamu gida daya, da matar, ko matan, amman banda Aise, ka auro kowa zanyi kokarin jurewa banda ita"
Duk da hawayen da suka zubo mata lokacin da take rokonshi, sai da yace mata
"Me yasa?"
Ta sake goge wasu hawayen
"Saboda irin son da naga kayi mata"
Kallonta yayi sosai, na wasu dakika
"Ina sonki kema ai"
Murmushin da tayi bai karasa cikin idanuwanta ba, asalima wasu hawayen ne suka sake tarar mata
"Kagani, wani dalilin, kana sona nima kace Ganja...saboda itama kana sonta har yanzun...ka auro kowa banda ita, inda zan iyama sai ince inka aureta ni zan hakura da kai..."
Sai ya girgiza kai yana riketa a jikinshi kawai batare daya sake cewa komai ba. A ranar da Aise ta hade bakinta da nashi, ya kuma zagaya hannuwanshi a kugunta yana mayar mata da martanin abinda take so har saida tsayuwar ta nemi ta gagaresu, shi ya fara sakinta, ya kuma zameta daga jikinshi yana maida numfashi, tayi murmushi
"Karka hanamu abinda mu duka muke so"
Daya koma gida, sau hudu yanayin brush, yana kara kurkure bakinshi da mouthwash, haka kawai, a karo na farko, yakejin kamar yana hada bakinshi dana Maryama zata iyajin dandanon Aise a jiki, kirjinshi ya dinga dukan uku-uku da yaga ta kure shi da kallo, sai kawai ya dinga nanike mata, tunda a lokacin ma akwai tsohon cikin Aalim a jikinta, sai dai wannan third trimester din yazo mata da yawan kasala, duk bata da wani kazar-kazar, sannan abu dan kadan ne yake sata kuka, ba zai iya tashin hankali ba balle rigima da Maryama akan Aise a wannan phase din da take ciki.
Hakan ne ma yasa da ta rokeshi yayi unblocking dinta saboda yayi adding dinta a Snapchat shima, saiya share kamar baigani ba, ba wani sosai yake amsa maganganunta ba, saita wuni tana ajiye masa sako, zai karanta, amman saiya zabi wanda zai amsa, wani abune yake fisgarshi game da Aise din, wani abu da ya kasa controlling, zuciyarshi ce kawai take gaya masa ya biye mata, su watse yanda yaga tana so, yanda yaga ta shirya tayi komai in dai zata sake samun waje a rayuwarshi. Zai iya cewa Maryama da maganganun Malamin da yanzun shine yake zuwa masallacin nan kusa dasu inda Malamin yake limanci yana daukar karatun, bama shi kadai bane ba, suna da yawa tunda makaranta ce ta manya da akeyi bayan isha'i zuwa karfe tara, maimakon farko da Malamin ne yake zuwa har gida.
"Sai kaita aikata zunubi kana ganin komai naka na tafiya dai-dai, dukiyarka na karuwa, baka wata rashin lafiya, amman in da zaka zauna ka nutsu tabbas da tsoro mai girma ya shigeka, saboda zakaga Allaah Ya kwace maka abubuwane da zasu zamarwa zaman lafiyarka a kabari, da kuma jefa wasi-wasi a samun aljannarka in harka mutu akan wannan turbar..."
Malamin ya cigaba da fada musu
"Zakaga sai a kira sallah kayita lakainiya ba zakayita akan lokacinta ba, idan kai namiji ne baka damuwa da yin sallah a cikin jam'i, sannan sai kayi watanni baka bude Qur'ani ba, balle ayi maganar wasu azkar da zasu taimakawa ruhinka..."
Haka kawai yana zaune ma wani lokaci sai maganganun Malam AbdulHadi su dinga dawo masa, ko idan yaje yabi wasu matan, shisa ma yake ta kokari wajen ganin ya bari, abinne ya zame masa jiki, kuma har yanzun yanajin kamar ba wani gagarumin zunubi bane, musamman da a wani karatun Malam da kanshi yace musu
"Allaah Mai Yawan Rahma ne...idan ka aikata laifi ka tuba, cikin tarin Rahmar Ubangiji saiya yafe maka"
Kuma yana gamawa yake tuba, sai dai su kansu sharridan tuban fa? Takesu yakeyi duk sanda zai sake komawa zunubin daya nemi yafiyar Allaah a kai, yana ganin amfanin dagewar da Maryama tayi akan Islamiyyar su Awwab, watakila da yasan abubuwan nan da karancin shekaru, ya maida hankali akansu, sun zauna a zuciyarshi, ba zasu dinga kokawa dasu ba a yanzun. Saiya kara hadawa da cewar ya jima rabonshi da mace, Maryama cikinta ya tsufa sosai, dan a halin yanzun ma Aise kadai yake magana da ita, itama ya kwana biyu basu hadu ba, ya yanka mata warning randa ta gwada shi akan zata kawo musu ziyara a gida, wajen sati ya dauka bai kulata ba, sai da taita bashi hakuri tana gaya masa wasa takeyi.
Baije HM Wheels ba a kwanakin, ya karbi wasu ayyukan daukar hoto ne da suke cinye masa lokaci, gashi bayason yayi nisa da Maryama kar nakuda ta kamata. Ita tace masa sunyi waya da Fa'iza tace mata zatazo ta wuni a gidan ranar Asabar, shisa ya amsa Aise da ta matsa tana so ta ganshi da
"Zamu hadu ranar asabar..."
Shi ya rubuta sakon, amman saiya dinga karantashi yana sakewa wani irin yanayi marar dadi na saukar masa, wani abu da baisan kaddarar da ta rantse tsakaninshi da Aise bace na danne shi...
47
Ranar juma'a...
Ko kadan Haris baiyi niyyar fita ba, sai ga kiran Barde, yace masa yana Kaduna, da yake ya dawo daga kasar India, yayi karatunshi har zuwa matakin Masters, babu wani abu daya basu mamaki sai daya samu aikin lecturing
"Nifa na kasa hango Barde da dalibai a aji..."
Cewar Lalaye yana sheka dariya, sai dai bai hada shekaru biyar yana aikin ba sai ya koma aiki da wani NGO, aikinne ma yasa baya zama sosai, dan yawo sukeyi gari-gari, a halin yanzun yana da mata daya da yara uku. A cikinsu Lalaye ne yayi mata har biyu, kuma maganar kara ta uku ma yakeyi, yaranshi bakwai. 2Pac kuma shekararshi daya kenan da dawowa Nigeria, dan duk shekarun nan yana zaune a kasar Ingila ne da matarshi, yaranshi biyu duka mata, yanzun suna zaune a garin Abuja. Lokacin da Haris ya fita, zuwa inda Barden yace masa zasu hadu, sai bakinshi yaki rufuwa ganin tare suke da 2Pac
"Bakace mun tare da Pac kuke ba"
Barde yayi dariya
"Nace masa zan shigo Kaduna nefa, shine yace bari ya shigo shima..."
Da yake eatery ne, sai sukayi order din abinci, Haris dai ruwan kawai ya bude, sai dai anata kiran Barde a waya dan ana jiranshi, hakan yasa yayi musu sallama ya tafi, suna dan hira wayar Haris take ta vibrating ya dauketa yana duba mai kiran, yaja karamin tsaki ya kifeta saman teburin wajen. Yau da safe yayi unblocking din Aise, amman harta isheshi da kira, abinda bayaso kenan, abinda kuma yake gujewa, dole ya saka wayar a silent, sai da zai fito din nan nema ya cire ya mayar vibration dan kar Maryama ta kirashi bai sani ba, wajen kira na biyar ne daya daga ya sake kife wayar, 2Pac ya daga masa gira daya, sai yayi dariya mai sauti
"Har yanzun? Har yanzun Ganja?"
Cikin son kare kai Haris yayi saurin amsawa da
"Duka yaushe ka daina shaye-shaye?"
Wani abu ya gifta ta idanuwan 2Pac, wani abu mai ciwon gaske da yasa Haris yin dana sanin maganar daya fada
"Kayi hakuri"
Murmushi yayi mai ciwo
"Gaskiya ka fada ai, duka yaushe na daina, amman na daina, saboda nasan abune daya kamata, ina kuma kokarin ganin nayi ayyukan alkhairi da nake fatan Allaah Ya aramun rayuwa mai tsayi saboda in samu su danne shekarun dana shafe in aikata abinda bai kamata ba, amman ban taba rike hannun macen da ba muharramata ba Haris, ko a lokacin kuruciya balle yanzun da nake kallon yara mata a gabana, nake kallon matar da ba zan taba yin abinda mutuncina zai ragu a idanuwanta ba..."
Shiru Haris yayi
"Inaso ince maka kabari saboda Rauda, sai dai ina da yakini akan Rahmar Ubangiji, zai kare mana yaranmu, In Shaa Allaah kuskurenmu ba zai shafesu ba...ina maka addu'a, ban cire rai zaka bari ba tunda Lalaye da Barde suka daina..."
Muryar Haris can kasan makoshi yace
"Aise ce...ba wasu mata bane, Aise ce"
2Pac yasa hannuwanshi duka biyu ya dafe fuskarshi kafin ya bude yana kallon Haris
"You are going to destroy your family Man...Maryama ba zata yafe maka ba...saboda Aise ce"
A cikin abokanshi kaf 2Pac ne ya san dukkan sirrikanshi, duk wani fada da suka tabayi da Maryama, yasan komai akan Aise
"Nasani..."
Kai 2Pac din ya daga
"Kaima ba zaka yafewa kanka ba inka rasata...ka kyale Aise inda take Ganja...koma menene wannan kuke kokarin yi, ka tsayar dashi"
Sai dai ai anan matsalar take, shima Haris din baisan abinda suke kokarin yi din ba, balle yasan ta yanda zai tsayar dashi
"Ganjaa..."
Kai ya daga da wani yanayi akan fuskarshi, sai 2Pac yayi murmushin takaici yana girgiza nashi kan
"Ka jini, amman baka dauka ba ko?"
Shirun ya sakeyi, sai kawai 2Pac ya canza maganar suka dauko wata hirar bayan Haris ya turawa Aise gajeran sakon cewar yana wani abune, itama saita dawo masa da sakon da bai bude ba sai bayan sun rabu da 2Pac tukunna, yaji zuciyarshi ta buga ganin adireshin hotel ne da kuma lambar daki, yasan ma hotel din, ya sha zuwa, amman wannan karin wani irin yanayi ne marar dadi ya rufar masa. Ya goge sakon nata da kuma wanda ya tura mata shima, sannan ya koma gida inda ya samu Maryama a kitchen tana gyara zogale zata dafa
"Kin cika rigima Maryamm...ba saiki bari su Awwab su dawo makaranta ba ya dafa miki"
Tunda yayi mata magana ko za'a kawo mata mai aiki tace masa a'a
"Su Awwab zasu wuce gidan Mami, ka manta yau juma'a..."
Dan Naadir ma tunda safe Hajiya Rumanan ta aiko aka daukar mata shi, lokacin Haris ko tashi daga bacci baiyi ba. Hannu ya saka yana tayata tsige zogalen
"Kafata ta gaji fa, kizo mu koma falo"
Tayi dariya
"Babu mai gyaramun zogale a falo...kabarmun abuna yanzun zan karasa gyarawa aina kusan gamawa"
Bai tafin ba, tsayawa yayi suka karasa gyarawa sai dai yanata mata mitar da bata kulashi ba, itafa wannan cikin ko dogon surutu gajiya yake kara mata. Batasan yara nawa Haris yake so ba, basu taba maganar ba, amman ita dai har kasan ranta tanajin wannan hudun sun isheta, tana fatan Allaah Ya raya mata su, zata tsayar ta numfasa, da take maganar da Khairi saita dingayi mata dariya
"Haba mana, aina dauka sai kinyi kamar takwas haka..."
Duk da Khairin bata ganinta saida ta watsa mata harara ta wayar
"A'a sha biyu ne ba takwas ba"
Khairi ta sakeyin dariya
"To ai naga kuna da kudin, saiki samu masu tayaki kula dasu...kikasan ko shi Haris din da yawa yake so?"
Da wani daci a kasan makoshinta tace
"Inya auro Aise ai saita karasa masa sauran"
Idanuwanta na cikowa da hawayen da basu zubo ba, a gabanta Anisa ta cewa Haris
"Nifa na fara shiri Haris, tunda Aise ta fito nasan rabon zama da kaine ya fito da ita, gara kazo kayi abinda ya kamata kaima dai auren soyayyar nan kayi shi"
Duk da cike da kashedi Haris din ya kira sunanta bai hanata yin dariya tana kallon Maryama da cewa
"Ai kinsani ko Maryama? Kanina mijin mace hudu ne, kuma bai tara kudin nan dan ya zauna dake ke kadai ba..."
Itama murmushi ta dora a fuskarta duk da kirjinta bugawa yakeyi da wani irin abu mai ciwon gaske
"Wai meye haka Anee?"
Haris ya fadi ranshi a bace, Maryama ta sake fadada murmushinta
"Gaskiya ta fada fa, ga gidan nan ma ya ishemu"
Anisa dake wata dariya tace
"Zata takura, kinsan yanayin gidan da ta taso ba daya bane da naku..."
Haris zaiyi magana Maryama ta rigashi
"Eh mu gidanmu ma ban taso naga kishiya ba, amman na dauka ba zai zama matsala ba, tunda duk abu dayane dasu Mami, kuma banga sun takura juna ita da Umma Fadime ba da Baba ya hadasu"
Kuma sai Anisan taji haushi
"Zagina zakiyi Maryama?"
Haris yace
"Idanma dukanki tayi ai cikin gidanta kikazo kike nema ki daga mata hankali..."
Sai fadan ya koma kanshi, Maryama ta bar musu falon ma, batasan sanda Anisa ta shigo ba, shima daya zo ya fara jaddada mata ba auren Aise zaiyi ba, bata kulashi ba. Tunda suka fara maganar ai tasan sai abinda ta gani, ba tun yanzun suke neman hanyar da zasu quntata mata ba, sai su zuba ruwa a kasa susha, dan kuwa sun samu