Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
kan wayar da takeyi da aka ba Khairi, batason indomie dinta ta dafe, shisa ma ta gama da wuri, ta samu plate ta juye anan kitchen din, ta dauki lemo tana wayar tana cin abinta daga tsaye, yau babu mai ganinta balle ayi mata fadan cin abinci a tsaye.
Yunwa takeji, nan da nan ta gama cinye indomien tana kurbar lemonta a cikin roba, sosai zuciyarta takeyi mata sanyi, har yanzun murnar wayar taki sakinta, yanda kuma har Adda Asiya take ta mata hira sai take jinta wata daban, har Hajja mafa haka ta juyo tana cewa
"Maryama ce? Bani wayar mu gaisa"
Itace aketa nunawa kulawa haka, ana nan nan da ita kamar wadda suka shekara basu gani ba, dadi ya cika mata rai fal, ta shanye lemon tana wasa da murfin tukunyar da ta dafa indomie dinta saboda yanda wayar takeyi mata dadi tasan Haris fita yayi, ko kadan bata tsammaci dawowarshi ba, shikuma daya shiga kitchen din ba magana takeyi ba, ta dai juya masa baya saiya dan taba kafadarta yana fadin
"In ba zan takura miki ba ko..."
Bai karasa ba saboda yanda ta kwala kara jin an tabata, tana cilli da wayar, data juyo saita juyo da murfin tukunyar nan tana kwada shi da dukkan karfinta, duk da shima yayi kokarin yin baya amman yanajin yanda ta sameshi a kafada harda karar da kashin wajen yayi na haduwa da murfin tukunyar, wani irin radadi ya shigeshi, ita kuma Maryama da zuciyarta ke bugawa ta kula dashine,
"Dan Allaah ya za'ayi ka shigo waje ba zakayi sallama ba kuma ka taba mutun? Bakaji yanda zuciyata take bugawa ba"
Zuciyarta ce take bugawa yaji tace, shikuma kafadarshi fa?
"Meye kika bugamun?"
Ya tambaya yana murza wajen dan zafi yakeyi masa sosai, hannunta yake kallo, siririn hannunta, amman ko Barde ne ya kawo masa duka iya karfin da zai sauka dashi kenan
"Yi hakuri, dan murfin tukunya ne a hannuna, gaskiya ka dinga sallama, inda wukace kuma fa?"
Ya jinjina kai
Ko da Alhaji Mustafa ya fada masa ya karbar masa aure, daya hango Aise, ya hango zata iya juya masa baya, kafin ta aikata sai ya dinga hango rayuwarshi zata fara ne ta kare idan ta barshi.
Bayan ta barshi kuma sai yaga ashe ita din ba duka rayuwarshi bace, wani sashine mai haske, babu abinda ya same shi, ta dai tafi da wannan hasken ne.
Ashe rayuwarshi ba a hannun Aise zata kare ba
A hannun wannan mahaukaciyar ce da aka kakaba masa...
17
Duk wani dokin sabon waya a sati dayan nan Maryama tayi shi ta gama, data tashi da safe zata kira 'yan gidansu daya bayan daya tana gaishe dasu, Khalifa mane tunda ya watsa mata zagi sau daya ta kirashi wajen karfe bakwai da rabi bata kara ba. Sannan kuma kowa ya tashi yana saka mata kati, sunfi shan waya da Khairi, anan katin nata yake karewa tas, sai da Khairi tace mata ta bude Facebook sai su dinga hirar ta can, amman ta gaya mata tana bukatar eMail, ita duk abubuwan nan ba gane musu takeyi ba, nacin wayarta ya kare akan camera, tana son daukar hoto, sai game, sai kallo idan akwai film a wayar, to wannan babu film ko daya, ko radio data shiga sai taga takiyi wai saita saka earpiece tukunna.
Kadaici ya fara damunta sosai, sai dai ta shiga wannan dakin ta fita, jiya har dakin Haris saida taje ta murda, taji dakin a kulle, ga tv amman ta kasa hadawa, haka abincin da take dafawa duk sun isheta, banda albasa da timatir din gwangwani da aka kawo ta dasu, babu wani kayan cefane, nama kuwa wasu kajine gasassu da aka zuba a fridge, guda hudune, dasu ta dinga amfani sun kare suma. Komai bayayi mata dadi, duk kuwa da
"Lafiya kalau, babu wata matsala Adda"
Da take amsawa Adda Zahra duk idan ta ta tambayeta, amman batajin alamar lafiyar a wannan zaman kadaicin da yake damunta, saima ta kwanta da daddare, jiya haka ta dinga share hawayen da in za'a tsireta bama zatace ga dalilinsu ba. Haris in ta fito da safe neman abinda zataci, bata ganinshi, tana gane ya fitane lokacin da zata ga babu motarshi inta leqa, sai dare sosai yake dawowa, inta duba agogonta zata ga karfe goma wani lokacin sha daya na dare, batama son jin karar motar shi inya shigo, sai kirjinta ya kulle waje daya, su biyu aka yiwa auren, amman ita take fama da kadaici, tunda shi zai fita duk inda yake so, haka kuma zaici abinda yake so, ita kuma zataci abinda ya samu.
Tana son indomie, amman bawai iri daya ba kullum, ta fita daga ranta, yau data tashi kujera kawai takebi, yunwa sai laliqarta takeyi, inda zata samu shayi da madara, ace da wani biredi mai laushi ga wainar kwai a tsakiya ba karamin farin ciki zatayi ba, amman ina zata same su? Hawaye suka cika mata ido, ta tsinci kanta da yiwa Abbanta addu'a, yanda yake tsaye akansu, duk yawansu basu taba neman wani abu suka rasa ba, dai-dai gwargwado rayuwa sukeyi cikin wadata, amman gata nan kwance yau tana neman abinda wata rana sai taga dama zataci, da yake gidan akwai maza, da yawansu kuma shayi da biredin baya rikesu, in shi za'a sha dole sai an hada da wani abin, su da zasuyi aikin, koma tace ita da baifi tayi abinda ba za'a rasa ba, bakinta kamar zai taba bango.
Idan ba Hajja ta gani a kitchen din ba haka zata dinga mitar anja musu aiki, ga kewa, ga yunwa, abin ya hade mata, sai share hawaye takeyi daga kwanciyar da tayi, a haka taji wayarta na ringing, kamar ba zata dauka ba, ganin Khairi yasa ta daga wayar ta amsa cikin karamar murya
"Lafiya? Me ya faru? Kuka kike ko?"
Cewar Khairi ta dayan bangaren, sai taji ta kasa daurewa, kukan ya kwace mata sosai
"Me yayi miki?"
Khairi ta sake tambayarta
"Ba komai"
Ta amsa tana kuka har lokacin
"Babu komai kike kukan nan Maryam? Ki fadamun menene? Ko in kira Hajja?"
Kamar tana ganinta tayi saurin girgiza kai
"Ba abinda yayi mun, yunwa nakeji, kuma nagaji, nagaji da zama ni kadai..."
A nutse tayiwa Khairi bayanin komai
"Shine zakiyi shiru, ai bawai zama zakiyi ba, magana zakiyi masa, ki fada masa yayi miki cefane, haka akace miki ana zaman aure? Ke baki ga komai ya kare a gida Abba ne yake siyowa ba"
Maryama tayi shiru
"Nafa ce miki ba ganinshi nakeyi ba yanzun, baya zama a gidan, sanda yake dawowa kuma karfe goma ta wuce..."
Khairi taja karamin tsaki
"Ko ki jirashi da safen, ko da asuba kije ki buga masa kofa, ko kuma da daddaren inya dawo kije kiyi masa magana, in kuma ulcer kike cigiya to Allaah Ya bada sa'a, ni banma san sanda kika koma haka ba da zaki kasa tunkarar wani da wata magana"
Ita tunanin ta sami Haris ne baizo mata ba, bawai dan tana tsoronshi ba, sun dan kara taba hira da Khairi, itace take gaya mata ta duba sosai a cikin kayan ta tabbata akwai sikari, a kwali yake dan cube ne, da suka gama wayar kuwa ta duba sai gashi ta gani, ta fasa ta dauko kwali daya. Da yake akwai kayan shayi, ta dafa, sai gashi yanata kamshi, indomie din da ta fita daga ranta ita ta dafa ta hada da shayin, ganyayyakine kala-kala aka harhada mata, yayi wani dandano da batasan lokacin data cinye indomie din nan tana korawa da shayin ba. Da ta gama saida ta karo rabin kofi tasha, sai taji dadin jikinta.
Taje tayi wanka, ta kara share gidan da baiyi wani datti ba, ta koma kan kujera ta kwanta tana dan buga game a wayarta. Wajen karfe sha biyu taji motar Haris yau, da sauri ta mike zaune daga kwanciyar da take, idonta akan kofa ya murda ya shigo, wandone mai laushi a jikinshi da kuma riga, amman bakake ne, gani nawa tayi masa kenan? Duka ganin bakaken kayane a jikinshi, ko meye hadinshi da bakin kaya oho? Bambancin kalarshi da ta kayan bamai yawa bace, shi yana wani kyalli-kyalli ne kamar yasha mai, ya kalleta, sai ya dauke kanshi, har yanzun yanajin ciwo kadan a kafardarshi, wajen data kwantara masa murfin tukunya.
A ranar ne ma da daddare Lalaye ya addabeshi da kira, wai za'a bude wani restaurant washegari, dan Allaah ya fita suje tunda za'a dauki hotuna sai suyi hotunan, wajen na abokin baban Lalayen ne
"Waye yace maka irin wannan hotunan nakeyi Lalaye? Kawai sai in kwaso kayan aikina inzo daukar hoton bude restaurant?"
A wajen Haris wannan abune marar muhimmanci, bai fara daga camera dan ya dinga daukar abubuwan da yake ganin ba zasu amfani mutane ba, duk da akwai wasu 'yan ayyukan da yakanyi a Italy da yasan zasu kawo masa kudi, kamar hotunan biki da makamantansu, amman restaurant fa? Sai dai Lalaye mutum ne mai naci, daya fara jera masa kira sai gashi ya tafi wajen, ashe mutumin ma babban dan siyasa ne, bashi da wani mukami a wannan lokacin, amman ana damawa dashi a gwamnatin da take ciki, bayan kwana biyu yaga aikin da Haris din yayi, sai gashi yasa Lalaye ya nemo masa shi zasuyi wani taro, kudine masu dan dama. A satin ya samu ayyukan da ya kula suna rage masa damuwa, suna hana masa tunanin Aise da ya tabbata blocking dinshi tayi shisa baya samunta ta ko ina.
So yakeyi ya yaji ya take, ya danji muryarta ko kadan, a gefe daya kuma yanaso ya yakice ta, ya nuna mata bata isa ta bashi zabi ba tsakaninta da Maryama, tunda ai Maryaman zabin mahaifinshi ce, kamar tana cewa ya zabeta koya zabi Alhaji Mustafa ne, shikuma idan zai rayu sau goma, to tabbas a kowacce rayuwa zai zabi Alhaji Mustafa. Wanda ba zai rike hannunshi ya tayashi karbar wannan zabinba zai hakura dashine. To kuma idan ya gama aikin sai su tafi yawonsu ya kara ragewa kanshi damuwa da matan da suketa rububinshi, matan da Lalaye yake ta hadashi dasu.
"Kaji..."
Maryama tace masa, taga bayason Harisun, kuma yanzun ba neman magana takeyi ba
"Dan Allaah, abu zan fada maka"
Sai ya tako cikin falon sosai, tabi kafarshi da kallo, takalmin daya karaso dashi har yana taka mata kafet din da yake shimfide, ta daga ido ta kalle shi, shima kallonta yakeyi da nashi idanuwan da take ganin kamar hawaye ne kwance a ciki
"Me akayi maka?"
Tambayar ta subuce mata, cikin rashin fahimta yake kallonta
"Kullum kamar zakayi kuka, idonka da hawaye a ciki"
Ta karasa
"Kullum?"
Ya tambaya
"Tun rannan nagani, randa na fara ganinka, na dauka saboda an aura maka nine shisa kayi kuka, ko zakayi kuka"
Dariya mai sauti ta kwacewa Haris, irin dariyar daya kwana biyu baiyi irinta ba
"Kawai sai inyi kuka dan an auramun ke?"
Ta jinjina masa kai
"Eh mana, ai baka son auren, nima nayi kuka tunda banaso, dana ganka baki ma na karayin kuka"
Cike da mamaki Haris yace
"Bakin nawa ne ya saki kuka?"
Batare da wani bata lokaci ba ta daga masa kai
"Bana son bakin namiji"
Dariyar da yayi bata da alaka da nishadi, mamakinta yakeyi, ko dai da gaske bakin nashi yakai wani mataki ne ba'a taba samun wani ya gaya masa gaskiya ba? Ya kalleta, itama ba wata fara bace ba, tana dai da haske, ba zaka kirata baka kai tsaye ba, shi ba zaice ga kalar da yake so a tare da mace ba, abubuwan da yake so a jikin mace basu da alaka da kalarta, ko babu wadannan abubuwan ma in bukatarta ta taso masa zai iya hakura dasu, ita dai da take tsaye a gabanshi yanzun baiga wadannan abubuwan ba, siririya ce da zaka ga hakan a kallon farko, shisa yayi mamakin irin karfinta data kwada masa murfin nan, daga baya ya daina mamakin ya barshi a cewar tsoro ne ya kara mata karfi ba wani abu ba
"Daman kin tsayar dani ne dan ki fadamun bakya son bakin namiji?"
Da sauri ta girgiza masa kai
"Yi hakuri, zan fada maka bani da cefane ne ka siyomun, jiya ma fa taliya da mai da maggi naci, bansan ko an kawomun yaji ba, na duba bangani ba, dan Allaah kayi mun cefane dan in dinga girki, harda biredi ma da kayan shayi"
Cikin kanshi ya maimaita taliya da mai da maggi, yana kuma so ya hada hotonta, wani abu marar dadi ya dirar masa, shi abinci bai dame shi ba, in dai zai sha tea, ko da babu madara, to zai iya wuni bai saka wani abu ba, amman taliya da mai? Abin baiyi masa dadi ba sam
"Me kike bukata?"
Ta fara yi masa wani lissafi daya sashi fadin
"Ki shirya in fito muje tare kawai, sai ki duba abinda kike bukata"
Murmushi ya kwace mata
"Dan Allaah da gaske kake? In shirya? Zakaje dani?"
Akwai wani abu a tare da farin cikin nata da yaji yana so yasa murmushi ya kwace masa shima
"In na fito baki shirya ba tafiyata zanyi"
Da gudunta tabar falon, atamfa ce a jikinta dinkin doguwar riga, saita samu hula ta saka. Da taje dakin kuma saita rasa kayan da zata dauka, kawai saita dauki hijabi ta fesa turare a jiki ta dora a saman kayan ta samu takalmi ta saka ta fito tayi tsaye tana jiran Haris. Daman zaman kadaicin ya isheta, ko babu komai zata sha iska, iya harabar da suka fita sai da taji dadi. Balle kuma da suka shiga motar, haka ta dinga kallon hanya sai kace ta shekara bata fito ba. Wani babban shago suka shiga, ya dinga zagayawa da ita inta dauki abu guda daya saiya kara biyu, shisa siyayyar tasu tayi yawa, haka ta waro ido lokacin da aka lissafa taji kudin da zasu bayar, kuma Haris din ya bayar babu wani dar.
Cefanen nema taji yana waya da wani Lalaye yana tambayarshi inda zasu samu
"Sai dai ki rubuta list na abubuwan da kike so idan mun koma gida, sai in bayar a siyo"
Ya fada bayan ya sauke wayar, ta jinjina masa kai kawai farin ciki ya isheta
"Insa harda nama da kifi?"
Ya dan kalleta, kafin ya cigaba da tukinshi
"Kisa duk abinda kike bukata, komai da komai, karki zo ki dameni babu wani abu, ki saka komai"
Abinda yaji dazun, yanayine da bayason ya sake jin irinshi sam, gara ya ajiye mata komai saita karata ita da gidan. Da suka karasa gida, suka fito daga motar saita zagaya ganin ya bude bayan ya fara fito da siyayyar da sukayi, ta kinkimi wata katuwar leda
"Ki ajiye ki wuce, sai kin karya wannan siririn hannun naki"
Cewar Haris yana bata dariya
"Tafdin, ba zai karye ba, zan iya dauka, kasan abubuwan da nake dauka kuwa? Karfine dani, ko a makaranta ma ba'a kayar dani wajen dambe"
Ya juya yana harararta
"Ke dince kike dambe a makaranta?"
Ya karasa maganar da dan karamin tsaki, shi dai ba zai kirga damben da yayi a makaranta ba, tun daga Primary harma secondary, wani lokacin idan ya zauna sai ya dinga mamakin kanshi, kamar yayi sanyi yanzun, ya rage zafin rai da saurin fushi, ko kuma masu harzuqashi dinne babu? Amman da fa kallon da bai gamsar dashi ba in ka dinga aika masa zai iya ja maka duka a wajenshi, shine yanzun wannan siririyar yarinyar zatace masa tana dambe, saboda cika baki
"Wallahi kuwa, babu wanda yake rainani, harma 'yan ss3"
Murmushi mai sauti yayi yana girgiza kai
"Ki ajiye ledar nan kafin in kwada miki gwangwanin madarar nan"
Kamar bata jishi ba, ta tallabi kasan ledar bayan ta dagata tana wucewa da saurinta
"Ke..."
Haris ya fara, saima ta kara sauri kamar zata ruga da gudu, ya sauke numfashi yana girgiza kanshi kawai, ba zai iya surutu ba, data kara dawowa baice mata komai ba ya kyaleta kawai, suka shigar da komai tare
"Nagode sosai, Allaah Ya karo kudi masu yawa da albarka, dan Allaah ka hadamun tv dina kuma, idan ka fita kaga zan dinga yin kallo tunda ana barin wuta sosai"
Ya daga mata kai
"Allaah Yayi maka albarka"
Wannan kalmomi ne da suka saba da fada a tsakaninsu, in dai wani zaiyiwa dan uwanshi abinda yaji dadi, kalmomi ne da suka sa Haris kallonta, saboda kalmomi ne da yake jinsu a bakin Alhaji Mustafa, kalmomin da sukayi karanci a tsakaninsu a shekarun baya, sai dai yaji ya furtawa Mukhtar, kalmomi ne da har yanzun da yake yawan furta masa su bai daina yunwarsu ba, haka kawai yaji yace mata
"Nagode"
Kafin ya fice daga kitchen din yanajin a yau din nan ma zai kirawo azo a hada mata tv din, tunda baisan me dame za'a bukata ba, shi dai ya taso yagani a dakinshi, da yake kallon bai dame shi ba, sai yayi kwanaki bai kalla ba, da suna makaranta kuma su Barde na janshi suje in ana wani wasan ball, to tunda canma ball din bata dame shi ba, yanzun kuma da babu wanda zai jashi suje kallo sai ya hutawa ranshi, da yaje kallon wata ball ma ai gara yayi bacci. Sai da ya kara yin wanka ya sake kaya tukunna ya fita daga gidan da list din da Maryama ta bashi bayan tazo ta kwankwasa masa daki ta tambayeshi ko yana da biro da takarda, ya dauka ya bata, yana tukin kuma yaji yana so ya warware takardar data linke gida biyu, ya duba, rubutunta yayi masa kyau a ido.
Ya sake linkewa ya cigaba da tukinshi, yana tunanin abinda zatayi da tattasan daya ga ta rubuta, dan a iya tunaninshi ya kasa hango gurbin tattasai a cikin abinci, ko dan babu wanda ya tabayin girkin a gabanshi? Idan ma zaici sai dai ya gani a girke...
18
Tunda tafiyar da zasuyi zuwa Syria ta tabbata yakejin shi cikin nishadi marar misaltuwa, sati biyu zasuyi, amman yasan sati biyu ne da zasu iya bude masa kofofin wasu satukan a kasashen da ake fama da hargitsi irin na Syria, sannan kuma mataki ne na farko da zai taka akan turbar da yake buri. Sai gashi su Barde kuma sun kara masa wannan nishadin ta hanyar dira a garin Kano shi da 2Pac
"Daman surprising dinka mukace zamuyi"
Cewar Barde, aikuwa sun bashi mamakin, dan ya kasa rufe bakinshi, da yake lokacin da suka shiga Kanon da yamma ne, sanda ya karasa wajensu ma ana kiran sallar Magriba, dan haka da sukayi sallah sai suka wuce gidan Lalaye suka baje kolinsu acan, wajen karfe takwas 2Pac yace wa Haris
"Tashi fa zakayi ka wuce gida, ka bar 'yar mutane ita kadai"
Su