Advertisements
Chapter 46 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   46 / 51

135K to 138K   out of 151K words

idan ya yarda zai koma Islamiyya ko zai samu Malamin da zai dinga zuwa gida kullum yana karantar dashi, ko shi ya dinga zuwa..."

Haris ya kalleta, sanda ya shigo dakin, duk da zuciyarshi ba karamin bugawa tayi ba, haka kawai yake da yakinin Maryama ba zata taba tona m"asa asiri ba, yasan wata rigimar ce zata janyo musu a gaban iyaye, amman wacce irin Islamiyya kuma? Shine zai koma Islamiyyar? Sai kace dai wani karamin yaro, yau kuma ta nan rigimar ta taso kenan, sun tabayin maganar kusan shekaru bakwai da suka wuce, shi in zai tuna ma banda dariyar daya kwashe da ita baice mata komai ba.

"Duk wanda zaifi masa sauki, zan koma ne in har ya yarda..."

Cewar Maryama muryarta na rawa

"Kuyi hakuri Baba...dan Allaah ku yafemun, amman idan ba zai zabi abu daya cikin biyun nan ba, ina so ku karbar mun takardata a wajenshi"

Ta karasa maganar tana kokawa da nauyin da kirjinta yayi, ita Haris yake kallo har lokacin, yana so ya fahimci abinda take nufi da maganganunta

"Allaah Yayi miki albarka Maryama..."

Cewar Alhaji Mustafa, dan ya rasa irin addu'ar da zaiyiwa Maryama, ko ta yanda zai fahimtar da ita yanda yake alfahari da kasancewarta surukarshi a tsayin shekarun nan, amman yau, a wannan zaman akwai tarin kunyar Maryaman a tare dashi bayan jin abinda Haris ya aikata mata. Ya tabajin wani wa'azi inda Malamin yake magana kan zamantakewar aure, ya dinga mamaki yana jinjina maganganun da Malamin yayi

"Iyayenka zasu bugi kirji suce sun haifeka, sun sanka, sunsan halinka, abokanka ma zasu iya wannan ikirarin, watakila harda 'yan uwanka, amman babu wanda ya sanka kamar matarka, saboda babu wanda ka raina kamar ita, duk wani halinka marar kyau da ba zaka bari wani ya gani ba, sai kaga ka nunawa matarka shi batare da wata fargaba ba, dan wani abu na fada maka ko da ta sani dole zata cigaba da zama da kai, inma bata zauna ba, ba zai hana ka nemi wani auren a baka ba..."

A lokacin da Alhaji Mustafa yaji, bai yarda da duka maganganun ba, yau kam ya aminta dasu dari bisa dari, dan babu wanda zai fadi halayen Haris sai Maryama, babu wanda ya sanshi kamar yanda ta sanshi, shi dai ya haifi Haris ne, yana sonshi saboda shi ya haifeshi, soyayya ce da bata zuwa da wani zabi, amman yana tir da halayenshi, kuma har kasan zuciyarshi yakejin inda Maryama ya haifa, sai inda karfinshi ya kare wajen ganin ya guntule wannan auren, yau dinma ba zaiyi son zuciya da yawa ba, in har Haris bai amince ba zai tsayawa Maryama. Sai dai abinda bai sani ba shine, Alhaji Sa'id dinma kawaicinshi ya kare, dan shi gani yakeyi bayan Islamiyya a duba wata makaranta da ake koya al'adu da kuma dabi'ar Malam Bahaushe a saka Haris din.

Farkon dawowarshi gidan, har ranshi haushi Haris yake bashi, kuma cike yake da dana sanin aura masa Maryama da yayi yake, amman kuma da duk ranar da zata wuce da yake ganin Haris a gidan da kuma yanayin yanda yake mu'amalantar kowa sai zuciyarshi ta dinga sanyaya, akwai wani hali na saukin kai da yake gani tare da Haris din, babu ruwanshi da matsayinka ko nashi, yana mu'amalantar kowane da fuska daya, ciki kuwa harda masu gadin gidan gonar Alhaji Mustafa da Alhaji Sa'id din yaja shi sukaje, zama yayi cikinsu sunata hira yana tambayarsu abubuwa.

Sun fita yafi a kirga kafin Alhaji Sa'id ya fahimci bawai Haris nayin sadaka kamar baisan zafin kudinshi bane dan ya burgeshi koya nuna masa yana shi din na kirkine, yana sadakar ne saboda ta zame masa jiki, musamman almajirai kanana, da kuma yara masu saida abubuwa a titina

"Inda ina da wani mukami dana hana wannan barar Abba, dana hana kawo yara kanana haka suna yawo a titi babu mai kula dasu...banajin dadin ganinsu, zuciyata namun zafi idan nagansu..."

Haris na da halaye masu kyau da sai ka zauna dashi zaka gane, sai dai babu digon al'ada da dabi'ar Malam Bahaushe a tare dashi, duk da ba bahaushen bane ba, tunda mahaifinshi bafullatani ne, mahaifiyarta Kanuri, amman duk da haka, , Alhaji Sa'id yaga dabi'un Haris din irin na turawa ne, duk kawaici da kunya irinta Hajja saida Haris yasa ta sauko. Babu ruwanshi da wata surukantaka, dan saida Alhaji Sa'id yayi da gaske ya iya riqe dariyarshi randa suke zaune a falo Haris din ya shigo, da karamin kwano a hannun Hajja ta zubo dabinon da taketa yiwa kowa rowarshi, Haris ya tsallaka yaje ya saka hannu a kwanon ya tsinta kuma yana mata magana kamar babu abinda ya faru, saima ya zauna akan kujerar da take yana kara fadin

"Wanne irin dabino ne wannan Hajja? Wani mai taurine Maryamm take siya kaman zai balla hakori, inaji dan karta sammun ne take siyo shi..."

Haka Alhaji Sa'id ya dinga tsokanarta

"Sai gaki kuna cin dabino a kwano daya da suruki"

Daya matsa matane ma tace

"Ai ba surukina bane, dana ne shisa"

Yanzun ma cike da wannan halin da a al'adar bahaushe za'a kira wauta Haris yace

"Islamiyya fa? Nine zan dinka uniform in koma Islamiyya kamar karamin yaro Maryamm?"

Dan yaga da gaske take, kuma kamar Alhaji Mustafa ya kama zancen dan yaji yana saka mata albarka, Hajiya Rumana ta tabe baki tana kauda kai gefe, in ita tayi magana babu abinda zataja mata sai tijarar Alhaji Mustafa, kilanma ya kunyatata a gabansu Alhaji Sa'id

"Waye yace maka zaka dinga uniform? Ai akwai islamiyyar manya, in kuma bakaso sai a samu Malamin da zaizo ya dinga karantar da kai a gida..."

Kai yake girgizawa tunda Alhaji Mustafa ya fara magana

"To shikenan, ai daman zabi ta baka, saika bata takardarta in ba zaka iya ba"

Cike da rashin fahimta yace

"Wacce takarda kuma Baba? Ni ai babu wata takardarta da take hannu na"

Hajiya Rumana da takejin kamar ta tashi ta rufeshi da duka tace

"Takardar saki, ka saketa kawai kowa ya huta"

Ya dan ware ido yana kallon Maryama da sai lokacin ta kalle shi

"Saki? Akan Islamiyya? Akan Islamiyya zaki rabu dani Maryamm?"

Haris ya karasa da wani irin rauni a muryarshi kamar ta zageshi, duk abubuwan da suka faru, duk tarin laifukan da yayi mata, akan Islamiyya ne zata tattara iyayensu tace ya saketa? Wanne irin abune wannan? To ko dai postpartum dinne bai gama sakinta ba? Ko da ta dawo hayyacinta ya bar mata wani ciwo ne? Daman ya shirya in sun koma gida zasu bar kasar dan a kara dubata sosai, bawai ya yarda da wannan likitocin bane in akazo maganar mental health.

"Abba kanajinta ko?"

Alhaji Sa'id ya numfasa zaiyi magana Maryama ta rigashi da fadin

"Dan Allaah Abba, muna bukatar komawarshi Islamiyyar ne...in dai bai yarda ba...dan Allaah kayi hakuri ka rabani da auren nan..."

Matsawa Haris yayi, ko yace rarrafawa har gaban Alhaji Sa'id

"Kara fada takeyi fa Abba, kayi mata magana..."

Hajiya Rumana taja wani tsaki da sai da dakin ya kusan amsawa da kararshi, Hajja tayi murmushi kawai, dan zuwa yanzun matar ta daina bata haushi, dan bata mata kallon mai cikakken hankali

"Ni dai wannan shari'a taku na barwa Babanku"

Haris ya girgiza kai

"Kasani Abba, Baba zai goyi bayanta ne..dan Allaah karka barmu dashi"

Alhaji Mustafa yayi masa dakuwa

"Gidanku Haris, aini bayan gaskiya nake, kuma banga aibun komawarka Islamiyya ba, in kaga ba zaka koma ba, babu dole...Maryama"

Ta kuwa amsa

"Na'am Baba"

Da dan murmushi a fuskarshi yace

"Ki hado kayanki mu tafi gidana, sai ya biyoni da takardarki daga baya"

Haris ya kalli Maryama data mike, gidansu zata koma, sai dai yasan ko Hajiya Rumana bata isa ta bashi dakin zama a cikin gidan yanda Alhaji Sa'id yayi batare da izinin Alhaji Mustafan ba

"A samo mun Malamin...da zamu dinga karatu, a samo Malamin Baba"

Maryama ta lumshe idanuwanta hadi da sauke wani numfashi da takejin kamar ya fito ne da dan sauran karfin daya rage mata. Wannan zaman, shine sanadin komawarta gidan Haris, dan batason taja magana dashi a gaban iyayensu, daga dakin Alhaji Sa'id da suka sha addu'o'i daga bakin kowa banda na Hajiya Rumana da ta kara hade girar sama data kasa, Haris ya nemi su wuce gidansu. Hajja ta kara mata kwarin gwiwar cewa

"Kuje kinji Maryama, ki dauki Naadir, in kun kwana biyu yaran zasu taho da Fa'iza da sauran kayanki"

Tasa hannu ta goge hawayen daya zubo mata

"To Hajja"

Addu'a ta sakeyi mata, har mota ta rakasu, suka shiga suka tafi. Saima da sukayi parking cikin gidan nasu take tunanin ta inda zata fara, ta tabbatar gidan ya hada qura ba 'yar kadan ba, da ta sani ta taho da Fa'iza sai su hadu su gyara. Ba karamin mamaki tayi ba lokacin da ta shiga taji harda kamshin turaren wuta, ga ko ina fes, mamakin ne ya nuna har akan fuskarta, shisa Haris yace

"Ina dawowa in share, sai inyi mopping yanda naga kunayi kullum, in kunna miki turaren wuta..."

Ta kalle shi, kallo na sosai, yayi zuru-zuru, idanuwanshi sun shige ciki, bata lura ba saboda ba kare masa kallo takeyi ba

"Ina zama ne, idan na gama gyarawa, kamshin da ganin ko ina a haka, yana ragemun kewarki"

Batace komai ba, batasan me zatace ba, shisa ta zabi karasawa dakinsu, ta kwantar da Naadir da yaketa harba kafafuwa abinshi. Ta zauna daga gefen gadon bayan ta cire hijabin jikinta ta ajiye. Shima Haris zaman yayi, taji tsikar jikinta na tashi da tunanin zai riketa ne ya hadata da jikinshi, sai baiyi hakan ba, ta kuma san abinda yake so yayine, amman baiyi ba

"Maryamm..."

Ya kira sunanta, ta kalle shi

"Kiyi hakuri"

Kalmomi biyu, kalmomi masu nauyin gaske, kalmomi masu dauke da tarin ma'anoni, sai kawai taji hawaye ya balle mata, kafin wani irin kuka ya kwace mata, Haris bai motsa ba, kokari yakeyi da dukkan zuciyarshi, barinta yayi tai kukanta da yakejin kamar kwanaki ta dauka tanayin shi ba mintina ba, saida ta goge hawayenta sannan yace

"Zan iya hugging dinki?"

Tayi jim

"Dan Allaah..."

Shirun dai ta sakeyi

"Maryamm"

Harararshi tayi da idanuwanta da suka kode saboda kukan da tayi, sai kawai ya rungumota ta gefe, sai gata tana sauke ajiyar zuciya, duminshi da kamshin turarenshi sukayi mata maraba, sai takejinta kamar wadda taketa gararamba, ba don ta rasa wajen zama ba, sai dan ko ina baiyi mata kama da gida ba

"Nayi kewarki...da yawa"

Wasu hawayen suka sake zubo mata, tana ta addu'a, Allaah Yasa Haris ya daina neman mata, sai dai tanajin kamar kamata yayi ace ta roka masa Allaah Ya darsa masa tsoron saba masa, in har zaiji tsoro, zai guji fushin Ubangiji, zai bar neman mata, saboda ta gane abu daya, har yanzun Haris baya kallon abinda yakeyi a matsayin gagarumin zunubi, yana kallon neman matanshi ta fuska dayane, cewar ita yakeyiwa laifi, shisa yayiwa zinar kwaskwarima da kalmar 'cheating'. Gani yakeyi ita kadai yake yiwa laifi, ita kuma zuwa yanzun tasan zuciyarta zata cigaba da yafewa Haris ne, yanzun a cikin zuciyar tace

"Allaah Kasa masa tsoronKa, Allaah Ka nuna masa abinda zai tuna da girman ikonKa..."

Saita lumshe idanuwanta, kamar zata iya ganin yanda addu'ata ta karbu, kamar kuma zata tsallaka cikin shafukan littafin kaddararsu da Haris, ta wuce kwanaki, watanni, ta kai shekarar da zata ga yanda addu'arta ta karbu...!

45

A yanda Haris ya dauki Fa'iza kamar 'yar daya haifa, Maryama tasan dole ne kowa zaiyi mamakin irin bajintar da zai nuna wajen bikinta. Abinda batayi zato ba, shine yanda Haris yake ta gayyatar mutane, da kanshi yake tura katin gayyata, harda 'yan uwanshi na Maiduguri, dangin Hajiya Rumana, abin ya dinga bata dariya, tasan dai dangin Alhaji Mustafa kowa zaizo, yanda suke sonta, sai wani yayi zaton itace 'yar dan uwan nasu ba Haris ba, dan kuwa zumunci sukeyi da ita bana wasa ba. Amman dai dangin Hajiya Rumana, inda ma ace bikin Rauda ne ya tashi, amman bikin Fa'iza, kanwarta, abin da kamar wuya.

"Kin duba store din nan kuwa Maryamm? Lemukan zasu isa?"

Tayi dariya, ta kama hannunshi, baiyi mata musu ba, ya zauna a gefenta, yau daya rage saura kwana uku bikin, shiga goma Haris zaiyi, saiya tambaya ko akwai abinda za'a karo, ko an mantawa Fa'iza wani abu, gidan Fa'iza two bedroom flat ne ya kama haya anan cikin Kaduna, unguwar dosa. Gidan yayi kyau, saima da aka tsarashi da tsadaddun kayan dakin da Haris ya siya, wasu cikin kayan kitchen dinta ma sai dawowa akayi dasu saboda kitchen din bashi da wani girma, Maryama tasan inda Hajiya Rumana zataje taga abinda danta ya kashe, saita hadasu ta tsine musu sunbi duniya

"Ka huta, dan Allaah..."

Sai yayi mata murmushi

"Ina naga hutu zan aurar da 'ya?"

Dariya Maryamm tayi mai sauti. Ba zatace komai na tafiyar mata babu wata tangarda ba, babu wani aure da za'ace yau babu matsala guda daya a cikinshi, babu wata mace da zatace bata da wani abu da take hakuri ko kauda kai akanshi game da mijinta koma auren gabaki daya. Ita ko kullen Haris aka barta dashi ya isheta jarabawa. Balle kuma ace an hada mata da kiyayyar mahaifiyarshi da 'yan uwanshi da har yanzun basa mata kallon arziki. Amman akwai abubuwan da tasan tana dashi a nata gidan auren da wasu matan suka rasa, kamar yanda tasan akwai abinda wasu matan suke dashi da ita ta rasa, mata da yawa in suka kalleta zasu fara duba sutturar jikinta, watakila da zobunan gwal din da suke hannunta.

Kilan ta burge da yawa a cikinsu in sukaji kasashen da ta zagaya da sunan hutu ko yawon shakatawa, Hajj nawa taje, Umrah kuwa duk sanda take so magana kawai zatayi Haris zai biya mata, zasu ga daular da take ciki, to ma sau nawa mutane nace mata

"Allaah Ya gama miki komai Maryama"

Wasu kuma suce

"Ke da kike da miji kamar Haris, baki da matsalar komai"

Murmushi take binsu dashi, to sirrikan gidan aure ai labule ne dasu, in ba ka daga ba, babu wanda zaisan dasu. A cikin masu yi mata irin wadannan maganganun, akwai wadda duk hidimar danginta idan ta tashi, mijin ne zai dauketa ya kaita da kanshi, akwai wadda mijinta yake da ilimin addinin da yake aiki dashi, mijin da zai tasheta sallar asuba, ya kuma tashi yaranshi ya sakasu a gaba su tafi masallaci, a cikinsu akwai wadda in zatayi alwala a gaban mijinta tayi kuskure daya zai gani ya gyara mata, akwai wadda zasu zauna da surukarta suyi hira suyi dariya, ta shiga cikin 'yan uwan mijinta su mu'amalanceta da girmamawa.

Akwai wadda mijinta ya mayar da ita makaranta, akwai wadda duk fitar da mijinta zaiyi bata da wata fargaba, tasan ko da zai kula wasu matan, to ba zai ketare iyakokin Ubangiji ba, a wajen Maryama babu wani kudi ko daular duniya da zatafi hakan kwanciyar hankali, mijinka ya taka ko ina kana da yakinin zai kare mutuncin kanshi da naku baki daya. Abubuwa da yawa, manya da kanana, in kuma kowacce mace zata nutsu ta duba irin tarin ni'imar da Allaah Yayi mata a nata gidan, watakila sai ta dauki wasu kwanaki masu yawa tana neman gafarar Ubangiji akan hange-hangen da ta dingayi tare da godiya da irin ni'imar da take ciki. Shisa tunda aka shiga satin bikin nan, daga jiya da gidanta ya fara daukar baki, danginsu na bangaren Alhaji Sa'id, 'yan matan nan masu rawar kai, duk wadda tace

"Allaah Ya sakani a danshinki Anty Maryama, Allaah Ya bani miji irin naki"

Saita kwabesu da

"Kiyi addu'a Allaah Ya baki miji nagari, wanda zai zame miki alkhairi"

Tana kuma ganin wautarsu a gefe daya. Daga ganin mata da mijinta saiki fara rokon Allaah daya baki irinshi, dan kawai kinganshi a wanke fes, cikin suttura da rufin asirin da Ubangiji yakeyiwa kowanne bawa ta hanyar lullube aibunshi. Bakisan ainahin waye shi ba, me matarshi take shanyewa a zamantakewarsu, idan aka daga Labulen dake lullube da auren, watakila abinda zaki gani saiya kayar dake. Sai dai da gidan ya kara cika, kuma kamar ko da yaushe a shekarun, Haris baya kunyar nuna mata kulawa, ko a gaban waye, ai saiya kara rikita 'yan matan nan, ta dinga girgiza kanta ganin yanda wasu suke lankwasa harshe wajen gaishe dashi. Tabbas addu'a inka jure, ka tsarkake zuciyarka, ka kyautatawa Allaah Zato, sai dai ka jira lokaci kawai, amman a wannan hidimar bikin tasan Allaah Ya amsa addu'arta Ya saukaka mata azababben kishin da yake dawainiya da ita.

Sannan kuma a nutse take, ta tabbatar duk biye-biyen matan Haris, ba zai taba kusantar wata da yasan ta san wadda ta santa bama, balle kuma cikin 'yan uwanta. Tunanin dai ya sosa mata zuciya matuka, saboda bawai tana zaton ya daina bane ba, a'a yakini take dashi zaiyi duk wani abu da zai iya wajen boye mata. Ranar asabar za'a daura aure, ranar juma'a zasuyi sword crossing, wannan ma tun daga wajen da aka kama zuwa duk wani abu da za'ayi Haris ne ya dauki nauyi, wasu abubuwan sai da Maryama ta dinga taka masa burki

"Kabar yaron nan yayi nashi kokarin, karya ga kamar an raina masa ne, dan Allaah...kaji"

Amman duk da haka in dai zai gani sai yayi magana, tasan idan Allaah Ya tsawaita musu rayuwa za'a kwashi kallo akan Rauda. Ita kanta Fa'izar inka kalleta zaka ga yanda take alfahari da iyayen rikon nata, saima Haris ya shigo, cikin taron 'yan uwanta yace mata

"Stellina..."

Wato tauraruwa da yaren Italian, ko yace

"Amore mio..."

Duk yana kiransu hakan ita da Rauda, ta amsa da

"Si Papa"

Yau da gobe yasa tana jin kusan komai zasu fada da yaren, sai dai bakomai take iya mayarwa ba, haka za'a bita da ido, wasu najin kamar suyi musayar matsayi da Fa'izar. Yanda duk Maryama taso suki zuwa wannan sword crossing din, Haris yaki amincewa, ganin ranta zai iya baci inta ja musun yasa ta shirya itama. A maimakon ango da zasu jera su shiga hall din tare, Haris ne ya riko hannun Fa'iza, Tuxedo ma yaso sakawa, da magiya harda guntun hawayenta Maryama ta samu ya saka manyan kaya, shadda harda babbar riga. Abinda dai ya bawa Maryama mamaki shine ganin 'yan uwan Haris, motoci sukayo, harda su Munira, tare suka taho da Rauda, tun satin bikin ta koma gidan Hajiya Rumana, saboda bata son hayaniyar mutane, Awwab ne duk inda ka gilma zaka ganshi, anata hidima dashi, yana tayawa da abinda zai iya ko aka saka shi, don shi din na mutane ne.

Ko bai sansu ba kuwa, haka zai zauna yana musu labari da tambayar su din su waye,

46 / 51